Sashe 9
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 6
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Ummu, ba za ta barni na hau motar haya ba, ko na ce mata motata ta lalace za ta ce na É—auki nata ko na Ya Naufal. The worse part É—in ma za ta iya saka direba ya kai ni. Zan fita da motata sai na jira ka gaba da gidanmu."
"Yauwa haka ma yafi kai waye, kin ga sai na dawo a ta haya, kuma zamu fi samun natsuwa domin akwai shawarar da nake son na baki. In a gida ne ba zamu samu damar zantawa sosai ba. Ni kam na rasa mai ya sa Ummu ke son sanya shamaki a tsakaninmu!" Ya yi maganar cikin tsananin fushi da damuwa.
"Wataƙila tana da haujjar hakan, kuma ita uwace dole ta kula da amanar da Allah ya bata." Ta gaya masa hakan.
"Wataƙila ta gano soyayyar da nake miki tana tsoron abin da zai je ya dawo ne." Ya faɗa a ransa wanda har ya fara tunanin ko a fili ya faɗi hankalinsa ya tashi, amma sai ya ji ta yi ajiyar zuciya ta ce,
"Tom Allah ya kaimu bari na tashi na yi karatu ga shi har past three." Ta miƙe da nufin shiga bayi ta ɗaura alawala.
"Ok, bye." Ya ce tare da kashe wayar.
Bayan ta yi karatun ta yi sallar asuba ta zauna ta ci gaba da karatu. Tana ƙoƙarin miƙewa sai Ummu ta tura ƙofar ta shigo hannu ta riƙe da carbi.
"Ina kwana Ummu." Ta ce tana mamakin zuwanta duk da ta sa baya wuce ta yi mata ƙorafin kalacin safe, amma ai ta shi da wuri.
"Lafiya kau." Ta amsa a daƙile sai ta ɗora da cewa,
"Na zo kiji tsoron Allah ki gaya mini wane ne mahaukacin masoyi? Domin zuciyata ba yarda da ku biyun ba, kamar a kwai abin da kuke ɓoyewa."
Zare ido ta yi tana mamakin kalamanta da abin da za su iya ɓoyewa don ba ta fahimci komai ba.
"Ummu wallahi babu komai da muke ɓoye wa kuma kamar yadda ma gaya muku initially, bayan kyautar da tsaƙon da ya turo mini na farko babu komai tsakaninmu." Ta ƙarashe maganar za tai kuka.
"Idan hawayenki ya zuba saina tsintsinka miki mari! Shashashar banza, da an yi miki magana sai ki ce za ki yi kuka kamar ke kika fi kowa hawaye. Allah Ubangiji ya sa na ji wata maganar bayan wallahi dake da shi sai ranku ya ɓace. Kuma ba ki da miji sai Hammad. Ni uwa ce ina da ikon zaɓa miki wanda za ki zauna da shi. Allah ya sa mahaukacin masoyi duniya zai baki ko ya bayyana na haramta miki aurensa matuƙar ina raye."
"To Ummu, ai dama ina son Hammad É—in ba zan iya rabuwa da shi ba." Ta ce da sauri don ta kwantar mata da hankali ganin yadda ta fusata da lamarin
"GargaÉ—i nake miki ai." Ummu ta faÉ—a a ranta ta ji daÉ—in abin da ta faÉ—a.
Bayan ta kammala ta shirya ta sanar masa da ta gama shiryawa.
Ummu dake falo ta fito ta same ta tana karwa ..
"Ummu zan wuce school sai na dawo."
"Ki dawo lafiya." Ta ce fuska a É—aure.
Tana ƙoƙarin fita Huwais ya yi sallama ya shigo, gaishe shi ta wanda ya amsa ko kallonta bai yi ba ya shiga cikin falon ita kuma ta wuce.
Ummu ta amsa gaisuwarsa, tana kallon yadda ya yi kyau sosai ya ƙara zama wani handsome da shi. Kallonsa take cikin tsananin ƙaunar ɗan nata ganin yadda girma da kamala ya kama shi.
"Ummu zan fita ni da abokina doctor Khair, ba zan daÉ—e ba."
"Ok, ba komai sai kun dawo amma ga su Umnaah sun shirya ka wuce dasu school."
Da sauri ya kalle ta jin abin da ta ce ganin tana son ɓata masa shiri.
"Ba da mota zan fita ba don Allah Abidin ya yi mafani da motata ya kai su fita ce ta gaggawa, in tashi babu mai."
Kallonsa ta yi cikin rashin yarda da maganarsa.
"Anya kai ɗinne za ka fita ba da mota ba? Ko dai da inda za ka kake ɓoye mini?Domin ma san in dai ba lalura ba ba ka ko iya fita in ba a abin hawa ba."
"Ummu a ƙofar gida zan jira shi yanzu haka ya ce miniti biyar zai ƙaraso."
"Ai sai ku wuce da su Khair baƙo ne ƙanninsa ne." Ta ce mishi.
"Don Allah Ummu ki sa Naufal ko Abidin ya kai su bari na je kinga har ya ƙaraso yana kirana." Ya ce tare da saurin ficewa ba ya ji abin da za ta ce ba.
Yana fita sai ta ji ba ta yi na'am da maganarsa ba.
Hamsiya ta ƙwala wa kira wanda ta fito ta durƙushe a ƙasa tana jiran umurni.
"Ma za ki bi Huwais ya fita ki ga wa zai ɗauke shi a mota. In kika bari ya ganki sai na ɓata miki rai."
"To." Ta ce tare da fita da sauri.
Sai da ya yi nisa sosai ya hangeta a lokacin tana ƙoƙarin kiransa ganin ya buɗe motar ya shigo ya sa ta yi murmushinta ja motar.
Hamsiya da take bin bayansa tana raɓewa a jikin gini, sai da ta ga ya hau motar da ta tabbatar na Hilah ce ta koma gida tana mamakin dalilin da ya sanya ta ce ta bishi, kamar wani ƙaramin yaro da dalilin da ya sa bai shiga motar ba, sai da suka fito waje. Taga ita ɗin 'yar'uwarsa ce ta jini. Tunanin kuma irin ɗan takurawa mata da take yi ya ɗan faɗo mata, amma kuma da ta tuna ƙaton enlergment na hotonsu da suke tun yarinta wanda ita Hilah, a lokacin har da na jarintaka, sai ta cire komai kamar yadda dama ba ta wani zargi komai ba.
"Motar Hilah ya shiga wacce take ta jiransa tun da ta fita." Ta bata amsa wacce jin hakan sai da ta yi suman wucin gadi.
"Amma yarannan sun yi masifar raina mini wayo.Huwais, za ka ja wannan karon ka yi tafiyar da harbabada ba za ka dawo ba, domin inta yi ƙamari zan yi maka aure na turaka Ƙasar waje tare da yi maka baki matuƙar ka dawo Ƙasar. Domin abin da kake shirin yi tamkar so kake ka ruguza farincikin iyalina. Ban taɓa ji ko a mafarki an taɓa soyyaya da ƙanwa ba." Ta faɗa tana wani irin zafafan hawaye yana bin ƙuncinta a ranta ita kaɗai ta san abin za ta yi musu in suka dawo.
Hilah ta juyo tana lallonsa da yake kallon waje ganin ya ƙi magana kuma har ta kusa kai get ɗin da za ta shiga makarantar su.
"Ya Huwais, ka yi shiru na zaƙu na ji shawarar da ka yanke." Ta ce mishi tare da shan kwana.
"Jiya na yi mafarkin mahaukacin masoyi kuma har an nuna mini shi a mafarki." Ta ce tana kallonsa ta gefen ido.
"Kim gane shi?" Ya jeho mata tambayar cikin mamaki.
"A'a na gane wasa da hankalina kawai yake son ya yi, saboda na yi ta mafarkin shi ina ɓata lokacina.
"Yauwa kin jina?".
ÆŠaga masa kai ta yi ba tare da ta kalle shi ba.
"Na ce mu yi wani abu mana shi mahaukacin masoyi ki nuna masa kin amince da soyayyar shi, domin ta haka ne kawai zamu iya gano wane ne."
Da sauri ta kalle shi jin abin da ya ce sai ta ci gaba da tuƙi ba ta ce komai ba.
"Akan me zan fara soyayya da wanda ban sani ba ko aljani ne, musaki ne duka ba ni da matsaniyar hakan?"
"Ni ma ai ba wai son gaskiya nake nufin ki yi masa ba. So nake ya yarda kina sonsa har ya bayyana kansa." Ya ce mata yana kallonta.
"A'a, wannan ba mafita bace." Ta ce tare da kallonsa sai ta mai da hankalinta kan tuƙi ta ci gaba da cewa,
"Hakan ba mafita bane ina tsoron kar na ƙara amincewa, abu ya kwaɓe ka zo ka barni a ciki irin wancan. Kuma Ummu yau ta yi mini kashedi mai ƙarfi kan ko waye kar na kuskura na amince masa. Don haka mu bar maganar in ya gaji da haukarsa zai daina. Da zarar na kammala karatuna na yi aure ai dole ya haƙura ya zo ya karɓi kayansa ko?" Ta ƙarashe maganar tana tambayarsa.
"Over my dead body! Ke tawa ce kuma an halicce ki saboda ni." Ya faÉ—a a ransa ganin kallon da ta tsaresa ya ba ta amsa da cewa,
"Mu gwada hakan wataƙila ma dace. Kuma na yi miki alƙawarin a duk lokacin da lamarin ya kwaɓe zan karɓi hukuncin duka."
"Promised?" Ta tabbaye shi.
ÆŠaga mata kansa ya yi wanda ya sa ta ce,
"To shikenan zan gwada. I will do as you said." Ta ce daidai lokacin da ta ƙaraso ta yi paking tare da kashe motar tana kallon shi.
"Yauwa ƙanwata. Ma za ki shiga aji bari na koma gida."
"A motar haya? Na san fa ba ka son hawa. Kawai ka je da motata sai ka sanya direba ya kawo mini amma a waje za ka ije karka shiga ciki da ita saboda Ummu."
"Mai zai kai ni bayan na san ƙaryar da na shara mata." Ya ce yana dariya.
Tsayawa ta yi har ya tada motar ya fara tafiya, sai ta ɗaga masa hannu tana kallonsa cikin tsananin ƙauna. Tana son yayan nata don ya damu da lamarinta. Rungume laptop ɗinta ta yi ta shige departmen ɗinsu.