← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 40

Sashe 39

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miyau ya haɗiye da ƙyar, yana jin yadda maƙoshinsa ya bushe, babu ɗigon miyau.

"Yaya Huwais ka gaya mini wane ne?" Ta ce tana girgiza shi.

"Zan gaya miki, amma ki natsu mu yi magana ta fahimta." Ya ce bayan ya mayar da ita inda ta xauna.

Zama ta yi tana share hawayen da yake xubo mata.

"Tabbas Hilah na san shi. Abokina ne kuma yana matuƙar sonki. Saboda kyawunki da matsalar da yake hango ya kasa bayyana miki soyayyarsa. Saboda yana da hankali kuma ya dace dake shi ya sa na ƙyale shi, ya fito miki a matsayin mahuakacin masoyi don ya samu soyayyarki ya sanya ki bijire auren Hamad."

"Amma mai ya sa ya kasa bayyana kansa a gareni? Mai ya sa ya yi mini alƙawarin xamu haɗu ya ƙi zuwa?"

"Kamar yadda ya gaya miki, mahaifiyarsa babu lafiya za a yi mata aiki a ranar kuma zai sanya hannu."

"Saboda me ya kasa bayyana mini domin zan fahimce shi. Wannan ba hujja bace mai ƙarfi. In har zan iya yafe masa saboda kai ne, da kai ne don na san ba za ka taɓa yadda a haɗa baki a cuce ni ba."

Rintse idanunsa ya yi yana jin babu daÉ—i jin abin da ta ce.

"Ki yafe mini Hilah ba ni da zaɓin da ya wuce na samu soyayyarki ta haka."

"Na san duk abokananka don Allah ka gaya mini wanne ne daga ciki."

"Ba ki san shi ba Hilah, kamar sau ɗaya ya ganki a taron da kuka yi na musabaƙa tun daga ranar ya nuna yana sonki. Na ba shi shawarar ya fito miki ta wannan tsigar, saboda na san yana bayyana kansa za a dakatar da shi."

"Don Allah ka nuna mini hoton shi." Ta ce cikin zaƙuwa.

"Ba zai yiwu ba saboda ya roƙe ni kar na nuna miki."

Ɓata ranta ta yi jin abin da ya ce." To ya kamanninsa yake?"

"Shin idan kika samu miji mai irin surata da halina ya za ki ji?"

"Zan yi farinciki saboda samun miji kamarka, sai macen da Allah ya yi mata tagomashi. Shi yasa kullum na ke ganin Anty Wajnah a mace mafi sa'a da ta same ka."

Jin abin da ta faɗa kansa ya fasu. Ji ya yi kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukarsa ba.

"To ki ayyana surarsa da haliinsa kamar ni, amma kuma ni na fi shi sonki." Ya ce cikin murmushi.

Dariya ta yi cikin farinciki."Aiko na samu mijin aure in har kamanka yake."

"Ba ki da kunya Hilah a gabana kike wannan murnar ko?"

Rufe fuskarta ta yi tana dariya."Amma abokin nan na ka ya cutar da xuciyata."

'Ki yi haƙuri xai bayyana kansa ba da jimawa ba. Yanzu wane shawara kika yanke game da auren Hamad."

"Zan fito fili na gaya wa su Ummu akwai wanda na ke so."

Gabansa ne ya faÉ—i tuna in har aka ce ta kawo shi ya xai yi.

"Yauwa ƙanwata, karki bari Ummu su yi miki auren dole kamar yadda aka yi mini."

Yadda ya yi maganar ya ba ta dariya."Ya Huwais, ka amshi Anty Wajnah a matsayin mata ku zauna lafiya. In Allah ya sa wacce kake so matarka ne sai ka aureta."

"Ba za ki gane yadda zuciya take ƙuntata ba, yayin da mutum ke zama da abin da ba ka so."

"Na fahimta, amma ka yi mata adalci ko don zumuncin da ke tsakaninku."

Shiru kawai ya yi, bai ce mata komai ba sai ya nisa ya ce,"Ki rinƙa ɗaukar kiransa, kuma ku koma kamar da in sha Allah zai bayyana kansa a lokacin da ya kamata."

"To Yaya." Ta faɗa tare da miƙewa ta maƙala jakarta, ganin shi ma ya ɗauki wayarsa ya miƙe.

Tafiya suka fara yi har suka isa mota suna hira. Daga nan makaranta ya ije ta hankalinsa ya ɗan kwanta, ganin yadda take matuƙar ƙaunarsa, ya san ba za ta yadda ayi mata auren dole ba.

Wajnah kuwa bayan ta shiga cikin ɗaki tana kuka, wayarta ta ɗauka tare da danna kiran numbar Mommy, ta zayyane mata ƙarya har da gaskiya.

Ranta ne ya ɓaci sosai ta shiga rarrashinta.

"Ki kwantar da hankalinki yanzu zan kira mahaifiyarshi, don ba xan lamunta ya rinƙa dukanki ba, daga yin aure ai ba jaka na auro masa ba."

Bayan ta kashe wayar cikin fushi ta danna layin Ummu ta zayyane mata.

Matuƙar mamakin marin da ya yi mta ya kamata.

"Ki yi haƙuri kin barni da shi xai gane ba shi da wayo."

Tana gama waya da mommy ta kashe wayar tare da neman layinsa.

A lokacin da ta kira, yana kan hanyar dawowa da ga makarantar su Hila. Ganin kiran gabansa ya faÉ—i amma ya daure ya É—auka.

"Huwais, ashe ba ka da hankali? Amaryar da ko sati ba ta rufa a gidanka ba za ka dake ta."

Ransa ya ɓaci jin abin da ta ce."Umm.."

"Ma za ka zo gida ina nemanka." Ta furta cikin ɓacin rai tare da daƙile wayar.

Wayar ya bi da kallo cikin ɓacin rai, yana tunanin abin da zai yi mata don ba zai lamunta, ta rinƙa haɗa shi da Ummu ba.

Juya motar ya yi zuwa gida. A falo ya same ta, zaune ta haɗe girar sama da ƙasa tun da ta ji shigowar motarsa.

Ganin yadda ta sha kunu, ta amsa sallamar ba tare da ta kalle shi ba, ya sanya gabansa ya faÉ—i.

Zama ya yi cikin sanyi jiki tare da gyaran murya ya ce,"Ummu ga..."

"Ashe ba ka da hankali? Kan me za ka daki Wajnah?" Ta katse shi cikin ɓacin rai tana faɗin haka.

"Ummu, k..."

"Ba ka da hujjar da za ka kare kanka da shi. Kuma ka ji na rantse maka wannan ya xama na farko na ƙarshe da za ka kai hannunka jikinta. Sannan a matsayina na mahaifiyarka, ina umurtarka da ka karɓe ta a matsayin mata ka sauke duk haƙƙinda ke kanka, matuƙar ka ƙi yin hakan za ka fuskanci fushi mai tsanani. Kan auren nan matuƙar ba ka cire banzar tunanin da kake yi ba, kun zauna lafiya zan iya maka mummunar lafazi, domin ba zan bari a cikin dangina ana yamaɗiɗi da ni, cewar ban isa da ɗan cikina da na haifa ba"

Kansa ya É—ago da sauri cikin tashin hankali jin hukuncin da ta yanke.

"Amma Ummu sam ba a yi mini adalci ba na gaya miki bana..."

"Ai bakin alƙalami ya bushe, tun da aka ɗaura aurenku, ba ka da wani xaɓi da ya wuce ka zauna da ita."

Miƙewa ya yi, cikin damuwa xai fice sai ya ji ta kira sunanshi.

"Huwais, wannan ya xama magana ta ƙarshe kan aurenka. Kar na ji kuma kar ta ƙara kawo mini ƙararka."

Ƙarashe ficewa ya yi cikin ɓacin rai zuciyarsa na tafasa.

A hanya tafe yake, yana tunanin abin da Hilah ta gaya masa. Tabbas Allah ya ba shi damar da xai iya auren mata har huɗu, amma ba ya jin zai iya karɓar Wajnah a matsayin mata. Kalaman da Ummu ta gaya masa, suka ƙara rikita ƙwaƙwalwarsa har ya gaza tunanin mafita.

A lokacin da ya isa gida. Ƙarasa shiga cikin dakin yana huci tamkar mesa."Da ma kin aure ni ne don ki haɗa ni da iyayena?" Ya yi mata tambayar cikin fushi yana tsaye a kanta.

Raurau ta yi da idanunta tana kallonsa."Don Allah kar ka yi mini mummunar fahimta, wallahi ina sonka Ya Huwais."

"Ki ji daÉ—i kin haÉ—a ni da mahaifiyata. Ki sani ko zan zauna da ke bisa umurnin mahaifiyata ce, amma bana sonki kuma babu soyayyarki a zuciyata."

Miƙewa ta yi, cikin sanyin jiki tana jin ɗacin kalmar bana sonki, da yake gaya mata.

"In har na ci albarkacin Ummu, zan yi farinciki na sam watarana za ka so ni."

"Kin yaudari kanki domin ba zan taɓa ƙaunarki ba." Ya ce tare da wucewa fuu zuwa ɗakinsa.

Jaɓar ta xauna kan kujera, tana jin babu daɗi yadda yake gaya mata ya tsaneta. Hawayen da ke zuba a ƙuncinta, ta share tare da miƙewa zuwa ɗakinta.

Wayarta ta fara ƙara alamun ana kira. Ganin kirar Ummu ce ya sanya ta ɗauka da sauri ta shige cikin ɗakinta.

Bayan ta É—auki wayar ta yi sallama ta gaishe ta.

"Ki na jina Wajnah? Dole sai kin yi haƙuri tun da kin san dole aka yi masa. Ki daina rashin kunyar da kike masa sannan ki zama mai biyayya, cikin sauƙi za ki mallake shi a hannunki. Ita wacce yake son hauka yake yi, saboda ko mutuwa zau yi don sonta ba zai aureta ba."

Mamaki ya kamata, domin ba ta taɓa sanin Ummu ta san wacce yake so ba.

Ajiyar zuciya ta yi jin abin da ta ce take hankalinta ya kwanta.

"Ba ya cin abincina kulle ɗakinsa yake yi da na shiga yake koro ni." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.

"Kar ki damu ki yi masa girkin, kuma ki shirya kinje ɗakinsa, na yi masa mummunar lafazi matuƙar ya ƙi kula ki."

Zuciyarta fes ta rinƙa murna tana gode wa Ummu.

"Duk abin da xai yi miki karki kula shi ki yi masa biyayya kin ji?"

"To Ummu," Ta ce tare da kashe wayar tana tsallen murna.

Miƙewa ta yi cikin farinciki, ta shiga kicin ɗin, tana kallon ƙaton kicin da aka cika shinda kaya.

Tunanin abin da za ta girka masa ta yi. BuÉ—e frij ta yi ta É—auko naman kaza ta kunna famfo don ta saki.

Cikin farinciki take yi masa tuwon shinkafa da miyar taushe. Bayan ta kammala ta koma ta dafa masa farfesun kan rago.

ÆŠaki ta koma ta yi wanka ta sanya kaya masu kyau.

A lokacin da ta fito falo shi kuma ya fito don ya je sallar isha'i. Kallonsa ta yi cikin shauƙin ƙauna tana wani tafiya tana yauƙi.

Ko inda take bai kalla ba ya wuce zuwa massalaci. Ganin haka ita ta miƙe cikin gaggawa ta yi nata sallar sannan ta fito tana jiran dawowarsa.

Bayan an idar da sallar zama ya yi, yana tunanin umurnin da Ummu ta yi masa, domin bai san ta yadda xai É—auke ta a matsayin matarsa ba.
Chapter 39 · 0% Book details