Sashe 6
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannunsa ta kama ta riƙe gam wanda sai da ya ji ɗumin jikinta, har cikin bargon jikinsa, ya rintse idanunsa yana jin yadda yake jin ɗumin na ratsa ko ina na jikin shi yana saukar masa da natsuwa, wanda ya sanya shi zare hannun da sauri yana istigifari da ta'awizi kan Allah ya kawo masa ɗauki tunkafin sheɗanin da ke ƙoƙarin galaba a jikinsa ya yi.
Ba tare da ta fahimci halin da ya shiga ba ta ƙara kama hannun a karo na biyu ta riƙe sosai.
"Ya kafahimce ni wallahi bani da masaniya kan lamarin nan."
"Ok." Ya ce cikin basarwa ya cigaba da aikin shi yana tunanin mai zai ce mata.
Ganin shirun da ya yi ya sa ta fara magana da cewa,
"Ko ma waye wannna tabbas ya cika mahaukacin masoyi, domin ina ya taɓa ganin an yi soyayya a ɓoye? Wataƙila kuma mahaukaciyar zuciyarsa ta gaya masa zai iya siyen soyayyata da kuɗi ne, ba tare da ya san bani cikin makwaɗaitan matan da suke sayar da rayuwarsu saboda kuɗi ba. Namiji mai ilmin addini da boko nake nema, wanda zai amfani da ilminsa duka a cikin rayuwar aurenmu. Kuma ai ina da wanda zai aura don haka ya kama kansa."
Wani kallo ya juyo ya watsa mata, take zuciyarsa ta fara zafi na kishinta, sai kuma ya juya zai ci gaba da aikin wanda ya sanya ta kama hannunsa.
"Yaya, ka yi shiru ba ka ce komai ba."
"Me kike so na ce domin na ga lokacin da Hammad ya ce yana sonki ba ki gaya mini ba." Ya jefo mata maganar cikin bazata.
"Bani da zaɓi ne, bisa umurnin Ummu da ta ce kar na sake na gaya maka, ganin yadda kake tada hankalinka kake nuna kai xaka saɓa mini miji da kanka. Cewarta shi na gida ne, kuma ya cika criteria da kake son mijin da zan aura ya cika." Ta ba shi masa.
Shiru ya yi dama ya san tursasawar Ummi ne har ta fara kula wani ba ta gaya masa ba.
Karɓar wayar ya yi daga hannunta ya ɗan tsaya yana karanta tsaƙon tare da dogon nazari game da abin da zai ce mata.
Bayan ya gama nazarin sai ya ije wayar saman cinyarsa yana ƙare mata kallo ganin yadda ta wani firgice.
Tattara dukkan hankalinsa ya yi gareta ya ce,"Wa ki ka gaya ma wa?"
"Babu kowa sai Afrin ƙawata, bayan ita babu wanda ya sani."
"Good! To kiyi shiru karki gaya wa kowa har muka mai zai yi nan gaba. Ki bar wannna kuÉ—in a account É—inki."
"No Yaya, sai dai na yi maka transfer ba zan iya ije maƙudan kuɗi haka ba." Ta ba shi amsa cikin sauri.
"Ki barshi dai gurin ki kafin na gama tunani sai na san yadda za mu yi da kuÉ—i."
"Tom, amma kana tunanin ɓoyewar ba zai kawo matsala tsakaninmu da iyayena ba? Musamman Ummu don Abu ba zan samu sausauci ba."
"Duk da hakan mu jira muga abin da zai yi kafin mu sanar musu ba. Sannan ki kwantar da hankalinki kar ya taɓa karatunki kin ji sis? Kin san kina da musabaƙa. Kwana uku ne ko?" Ya ce mata cikin tsigar rarrashi.
"A,a biyar ne sun tura mana tsaƙo sun ƙara kwana biyu."
"Masha Allah! Kin ga kin samu ƙarin kwana biyu za ki yi karatu sosai."
"Na ma gama kawai dai ƙarin kwanar zai bani lokacin na ƙara bita."
"Yauwa ma za tashi ki tafi makaranta ko na kai ki?"
"Karka damu zan koma da kaina." Ta ce tare da miƙewa.
Murmushi ta yi tana kallonsa wanda shima ya miƙe yana miƙa mata wayarta.
"Mahaukacin masoyi!" Ta ce tare da jan tsaki da ƙarfi.
"Mutumin nan ya raina mini wayo sosai Ya Huwais. Ga shi gabakiɗaya ya ɓata mini mood ɗina zai sanya na raba tunani gida biyu."
"No kar mu yi haka dake, ki kauda lamarin kin san dole sai kin ciyo mana tropy É—in nan." Ya faÉ—a yayin da yake jin babu daÉ—in kalaman da ta furta amma sai ya daure bai nuna koma ba ya ce.
Ajiya zuciya ta saki mai ƙarfi tana ƙoƙarin comforting ɗin kanta domin gabakiɗaya ta ruɗe.
"In sha Allahu, bari na tafi na yi wanka na koma school."
"To shikenan, 'yar ƙanwata."
Fita ta yi wanda tana yin nisa ya durƙushe a gurin yana jin yadda zuciyarsa ke masa zafi. Ji ya yi idanunsa sun cika da ƙwallah shi kan ya san yana cikin jarrawa, domin ya sanya a ransa ita ce jarrabawarsa.
"Tabbas na cika mahaukacin masoyi! Domin soyayyarki gab yake da fallasuwa cikin raina, wanda zai sanya mutane sun tabbatar da na haukace game da sonki, amma kuma a shirye nake da na amshi duk wani ƙalubalen da zan fuskanta, domin ba zan yi sakaci ba ina ji ina gani wani ya aure ki. Kece farincikina kuma zuciyata."
Kamar yadda ya gaya mata kar ta sanar da kowa. Ba ta gaya wa kowa ba, amma wunin ranar ta yi shi suku-suku, domin ta kasa samun natsuwa. Burinta kawai ta san wanda ya tura mata tsakon, amma iya hatsashenta ta yi ta yi hakarta ba ta cima ruwa ba. Don haka ta ga ji ta haƙura da tunanin sakamakon wani irin ciwo da kanta yake yi.
Wuni ta yi tana duba tsaƙon da ta ji muryar Ummu ko 'yan uwanta sai ta yi maza ta kife wayar.
Da ta zo bacci kasa bacci ta yi ta rinƙa juye-juye a kan makeken gadon da ke barazanar cinye ɗakin, wanda da ƙyar da siɗin goshi baccin ya yi nasarar ɗaukarta wanda sai da ta riƙe carbi tana ta Sayyidil istigafari.
Ya rage gasar su saura kwana biyu, ta yi ƙoƙarin watsar da komai ganin tunanin na son zubar da haddar da ta yi. Ga shi ta burin amso wa Ƙasarta tropy da zai zamo abin alfahari ga al'ummar Musulmai.
A ranar da ta kasance ranar tafiyarsu suka shirya da misalin ƙarfe goma suka ɗauki hanya.
Hilah tana tsaye a gurin da za su fara musabaƙar.
Idanunta ta runtse tana yin addu'a samun nasara.
Da ta tuna irin yadda iyayenta da yan'uwanta suka ƙarfafa mata guiwa, sai ta ji wani irin ƙwarin gwuiwa ya zo mata.
Wayarta ce ta yi ƙara wanda ta duba da sauri.
Ganin numbar anonymous ya sanya ta ƙi dubawa, domin ganin tsaƙon na neman rikita tunaninta da matsuwarta. Sai dai, duk iya ƙoƙarinta na kar ta duba sai ta tsinci kanta da son duba tsaƙon, wanda har ta kasa jurewa ta buɗe cikin ƙarfin hali.
"Ina miki fatan alkhairi ma'abociyar ilmi da baiwa. I know that you gonna rock it. Eh tabbas za ki ci. Ina kallon ki domin ina daga cikin mutanen da suka zo, domin sauraron daddaÉ—ar muryarki da fatan ki cinye wannan gasar. Jikina yana bani za ki ci, domin ba bu faÉ—uwa a rayuwarki. gani a cikin dubban mutane ina murmushi zuciyata cike da miki fatan nasara."
Da sauri ta shiga duba mutanen dake gurin jin gaya mata yana wurin
"Wane ne wannan! Wane ne wannan yake son wasa da hankalina?" Ta furta tana waige-waige.
Iya hangenta ba ta kowa ba sai Ya Huwais da yake sakin mata murmushi tare da ƙarfafa mata gwiwa da idanunsa.
Da ta kalli sauran 'yan'uwanta sai ta ga kusan irin murmushi da yake kan fuskarsa iri ɗaya ne, musamman Abu da ta ga ya duƙufa yana ta kwaroro addu'a.
Ta shiga ruÉ—ani sosai tana ta tunanin sa. Zuciyarsa ta kwaÉ—aitu da ta gan shi. Haka kawai ta ji tana son ganin ko wane ne, amma iya tunaninta da son ganinsa ba ta gan shi. Da ta tuna dubban mutanen da suke gurin sai ta daina wahalar da kanta, domin ta san ya faÉ—a mata ne don kawai ya wahalar da ita, ko ya sa ta faÉ—i. Sai ta saka wa kanta anya mahaukacin masoyi sonta yake? Ko an yi amfani da shi ne don ta faÉ—i gasar. Ganin yadda ta rikice lokaci guda!
A lokacin da ka aka kira ta sai ta ji ta rasa natsuwarta da karatun da ta yi bakiÉ—aya.
Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta har ya sa ta dafe ƙirjinta tana jin gadda yake bugawa cikin rashin ƙa'ida.
Da ta tsaya a gurin ta buɗe baki da nufin ta fara karatun sai ta ji ta kasa. Idanunta suka cika fal da hawaye. Tana jin yadda komai yake neman fin ƙarfinta.
Huwais da yake kallonta cikin tsananin ƙauna da bege. A lokacin da ya tura mata tsaƙon, ta buɗe tana karantawa sai ya ji tamkar ya isa gareta ya kamata ya rungume ya ƙarfafa mata gwuiwa.
Ganin ta tsaya tana duba tsaƙon ya sashi ɗan sakin murmushi yana kallonta. Burinsa bai wuce ace ta zamo ta ɗaya ba. Tabbas hakan zai ƙara masa sonta da begenta, kuma hakan abin alfahari ne ga zuriyarsu baki ɗaya.
Ya fara shiga cikin tashin hankali lokacin da ya ga tana ta wilƙita idanunta wanda ya tabbatar da gaya mata cewar yana gurin ne ya sa take duba shi.
Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya ga layi na gab da zuwa kanta amma har lokacin nemansa take yi.
Wani irin juya ya ji yana kama shi a zaunen har ya ji kanshi ya sara. Miyau bakinsa na neman ƙafewa.
"Mai ya sa ta damu da ta ganshi, kuma mai ya sa na tura mata da tsaƙon?" Ya tambayi kansa cikin tsananin mamakin yadda ta rikice har yana jin in har ba ta ci gara ba ba zai yafe wa kansa ba.
A lokacin da ta tsaya za ta yi karatun sai ya ga ta kasa idanunta cike da ƙwallah. Miƙewa ya yi cikin dana-sani zai fita daga gurin, domin yana ji ba zai iya ganin ta kasa cin gasar ba. Rintse idanunsa ya yi ya tsaya jin ta fara karatun cikin rawar murya.
Tsaya wa ya yi tare da kafe ta da idanu wanda cikin ikon Allah sai ta kalle shi.
Da hannu ya yi mata maganar kurame na ƙarfafa gwiya.
Ga mamakinsa sai ya ji muryata ta dake ta fara karatun wanda tun da ta fara ba ta tsaya ba sai da ta dire.