← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 40

Sashe 38

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Babu wani bakinta da za mu ji ai ta san da maganar aurensu." Ummu ta faÉ—a.

Miƙewa ya yi, yana jin kamar ƙasa ba zata iya ɗaukarsa ba. Siraren hawayen da suƙe ƙoƙarin saukommasa yake son mayarwa. Gfen hannunsa ya sanya ya share hawayen

Ba tare da ya ce musu komai ba ya miƙe xai fita, saboda in har ya yi magana za su fahimci halin da yake ciki.

Binsa da kallo suka yi ganin yadda yake tangaÉ—i kamar zai daÉ—i.

"Na gaya maka wallahi wannan mahaukacin yaron sonta yake yi. Gara mu yi mata auren shi ne kawai sanun kwanciyar hankalinmu.".

"Ummh! Biri ya yi kama da mutum." Abu ya ce cikin tsananin mamakin halin da ya shiga.

Huwais na fitowa ya shiga cikin motarsa. Kifa kansa ya yi kan sitiyarin motar. Wasu irin zafafen hawaye suka sauka a ƙuncinsa.

Ba tare da ya share ba ya kunna motar ganin maigadi ya buɗe masa ƙofa.

Sai da ya yi nisa da gidan sannan ya faka motar ya tsaya. Hawaye ke bin ƙuncinsa yana jin tashin hankalin na ƙara ninkuwa..

"Ba zan taɓa barin ki auri wani ba matuƙar ina raye. " Ya furta tare da duka sitiyarin motar.

"In har ba zan aure ki ba mai ya sa ba ke son ki?" Ya yi wa kansa tambayar cikin tashin hankali.

"No, Hilah tawa ce an halicce ta don ni. Matuƙar ban aure ta ba sai na kashe duk wanda ya aureta." Ya furta hakan tare da figan motarsa aguje.

Ikon Allah ne kawai ya kaisa gida. Hon yake yi babu ƙauƙautawa. Da sauri maigadi ya buɗe masa get yan kallonsa. Gaisuwar da ya yi masa bai amsa ba ya buɗe motar ya shiga cikin gidan.

Ko motar bai kulle ba ya shiga gidan. Wajnah da ke zaune tana kallo da saurinta miƙe.

"Ya Huwais, lafiya?" Ta yi masa tambayar ba tare da ya kula ba ya wuce ciki. kai tsaye bayi ya shiga ya kunna shower.

Ga mamakinsa sai ya ji wasu irin zafafen hawaye suna sauka daga ƙuncinsa. Ya daɗe yana sakarwa kansa ruwa, har sai da ya ji ɗan dama-dama a zuciyarsa sannan ya fito ya sanya kaya.

Key É—in motarsa ya É—auka ya fito falo.

Wajnah da ke tsaye hankalinta a tashi tana jiran ya fito ta sha gabansa.

"Matsa ki ba ni guri!" Ya furta cikin kakkausar murya.

Da sauri ta kalle shi jin muryar da ya yi amfani da ita. Tsoro ya bayyana a fuskarta, amma sai ta dake.

"Don Allah ka sanar da ni abin da ke faruwa. Ni fa matarka ce dole na damu da lamarinka."

Jin abin da ya ce ya sanya yaja tsaki tare da tureta xai wuce.

Gefen rigarsa ta ja cikin ɗaga murya ta ce,"Dole sai ka gaya mini abin da ke damunka, ai ni matarka ce ina da haƙƙi .."

Maganar ta maƙale mata, sakamakon marin da ta ji ya wanke ta da shi, wanda ya sanya ta sake shi da sauri tare da dafe ƙuncinta.

"Marina fa ka yi?" Ta furta cikin muryar kuka.

"Abin da yafi mari xan yi miki matuƙar kika ƙara yunƙurin dakatar da ni." Ya furta cikin ɓacin rai xai fice.

Wani irin ƙara ta saki saki ta ruga da gudu cikin ɗakinta.

Tsaki ya ja yana kallonta."Wawiya kawai!" Ya furta sannan ya murɗa ƙofa ya fice.

A hanya tafe yake yana tsaƙa da warwara. Gani yake sam iyayensa ba su yi masa adalci ba, amma kuma in ya tuna lamarin da yake shirin ibo ma kasa sai ya ji damuwa sosai.

Shi kansa ya sani ihu yake bayan hari. Ko da ace ba a yi wa Hilah aure ba, ba shi da damar da xai bayyana yana sonta.

Wayarsa ya É—auka da ya sanya a caji. Numbar Hilah ya nemo sannan ya danna kira.

Hilah da ta fito daga lectured kenan suna tafiya da Affrin za su je Cafateria.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

'*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 24

Jin wayarta na ringing, ya sanya ta buÉ—e jakarta ta É—auko.

Ganin Huwais ne, sai ta tsaya tare da danna gurin kiran, ta kanga ta a kunni.

"Hello Yayana." Ta furta da muryarta da ya bayyana, tsantsar gajiyar da take ciki.

Jin muryarta ya sanya shi rintse idanunsa, yana jin wani abu yana yawo a kwanyarsa.

"Hilaaah, kina ina?" Ya yi mata tambayar tare da jan sunanta.

"Ina school mun gama lectured zan nemi abinci."

"Ok, ki yi ma za ki ci abincin zan jira ki a bakin get ina kan hanyar makarantarku."

DaÉ—i ta ji a ranta sosai, dama tuntuni take son ya sanar mata da ranar da za su huÉ—u.

"Ok, sai ka zo amma Yaya lafiya kake?"

"Lafiya lau." Ya ce mata tare da kashe wayar yana sauke numfashi.

Bin wayar ta yi da idanu, tamkar za ta ga abin da ke damunsa a wayar.

"Ya Huwais, ne ya kira ni yana kan hanyar zuwa makarantarmu. Mu yi sauri na mu ci abincin kafin yazo."

"Yayanki yana matuƙar ji dake. Ina ma ace ni ce na samu wannan gatar. Na ɗauka zai canza in ya yi aure, amma abin gaba ya ci."

Dariya ta yi jin abin da ta ce."Wannan dalilin ya sa na ke son shi sosai."

Suna gama cin abincin kenan, ya kira wayarta tare da sanar mata da ya iso.

"Tashi mu je kar na barshi jira."

"Ki dai je in har kuna tare mantawa muke da kowa."

"To shikenan, tun da ba za ki je ba." Ta ce tana dariya.

A hankali take takunta cikin natsuwa kanta a ƙasa. Yana tsaye ya hangonta. Gyara tsayuwarsa ya yi, tare da zuba mata idanu, tamkar zai cinyeta har ta ƙaraso tana masa murmushi.

"Yayana," Ta ce tana kallonsa.

Yanayin fuskarta ya canza hannunsa ta kamo.

"Lafiya Ya Huwais?" Ta yi masa tambayar cikin damuwa.

"Mu samu guri za mu yi magana." Ya ce mata tare sakin hannunta.

Babu musu ta shiga gaban motar ya ja suka fara tafiya. Sun yi nisa sosai, babu wanda ya yi magana, sai ita da take satan kallonshi cikin damuwa.

Ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi wanda ya sanya ta kalle shi.

"Yayana, mai ke faruwa? Na damu da halin da kake ciki."

Bai ce mata komai ba, sai da ya yi parking sannan ya fito. Ganin haka ya sanya ta buɗe ƙofar ta fito.

Gurin wasu fararen kujeru suka samu suka zauna.

Kimanin Æ´an sakanni sun zauna babu mai cewa komai.

"Hilah Abu ya gaya mini xai sanar da iyayen Hamad su kawo kuÉ—in aurenki."

Ras! Ta ji gabanta ya yi matuƙar faɗi. Miƙewa ta yi, yayin da hawaye ya wanke mata fuska.

Ganin razanar da ta yi ya sanya shi jin sanyi. Hannunta ya kamo ya xaunar da ita.

"Kina son Hamad?" Ya yi mata tambayar yana kallon ƙwayar idanunta.

Kallon da yake mata ya sa ta ji wani irin nauyi. Domin kalar idanun da ya canza ba ta taɓa hango hakan a ƙwayar idanunsa ba.

"Bana sonsa, amma kuma matuƙar xan samu saɓani da Ummu kan auren ba ni da xaɓi." Ta faɗi haka cikin rawar murya.

Ransa ya ɓace jin abin da ta ce."Kenan za ki sadaukar da kanki saboda farincikin Ummu? Karki manta rayuwar aure ana samun natsuwa ne, in har mutum ya auri xaɓin rayuwarsa. Ki duba halin da nake ciki tun da aka ɗaura mini aure ban samu kwanciyar hankali ba."

"Ya zan yi Ya Huwais? Ka san halin Ummu, ko soyayyarsa ita ta sanya na amince har na yarda da zan aure shi."

"Shikenan kin haƙura da mahaukacin masoyinki?"

ÆŠago idanunta ta yi da sauri jin sunan da ya kira.

"Zan iya haƙura da shi tun da bai damu da ni ba. Zan yi wa Ummu biyayya na san cewa ba zan taɓa taɓewa. Mahaukacin masoyi ya cuce ni ya yaudare ni. Auren da zan yi shine kawai zan baƙanta masa rai. Ya san cewa ban rasa masoya ba. Hamad yana da nagarta kum...."

"Ya ishe ni! Ban zo nan don ki gaya mini nagartar sa ba." Ya katseta cikin fushi yana huci.

Shiru ta yi tana kallonsa tare da share hawaye.

Miƙewa ya yi, ya fara taku sai kuma ya tsaya ya juya mata baya.

"Na san wane ne mahaukacin masoy..."

"What!" Ta furta cikin tsananin razana tana kallonsa.

Yadda ta ruÉ—e ya firgita shi. Kama hannunta ya yi ganin ta fara kuka.

"Please, ki zauna mu yi magana na fahimta."

Zama ta yi hawayen na bin ƙuncinta."Haba Yaya, da kai xa a haɗa baki a ruguza farincikina. Dama ka san mahaukacin masoyi ya rinƙa wasa da rayuwata? Haba Yaya! Sam ban yi taɓa tunanin zaka yi mini haka ba why?" Ta ƙarashe maganar tana gurzar kuka.

Huwais ya yi shiru cikin tashin hankali yana kallonta. Irin tashin hankalin da ta nuna ya sanya shi ƙara shiga cikin damuwa sosai.

A koda yaushe gani yake tana ƙara son mahaukacin masoyi. Shin idan ta ji shine za ta so shi kamar haka?" Tambayar ya sanya cikin shi murɗawa.

"Mai ya sa aka haɗa baki aka cutar da ni?" Ta ƙara cewa ganin ya yi shiru.

"Waye shi? Waye wannan mugun azzalimi wanda ya yaudare ni? Na zaƙu da na san ko waye na ɗauki hukunci mai zafi a kansa.".
Chapter 38 · 0% Book details