← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 40

Sashe 31

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 19

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Haba mijina, ina ta yi maka magana ka yi banxa da ni. Karka manta yau rana ce ta musamman a garemu." Ta faɗa cikin wani irin murya da zai ɗauki ha kalin duk wani ɗa namiji tana ƙoƙarin haɗa jikinsa da nata.

"Ke!" Ya daka mata tsawa tare da kaucewa ya É—auki wayarsa.

Ƙarar da ya yi mata, ya santa matsa tana xare idanu. Wayarsa ya ɗauka tare da fara tafiya xai shiga cikin bedroom ɗinsa.

Ganin zai shige ya santa ta ƙara sauri ta tsaya a gurin ƙofar.

"Wallahi ba xan yarda first night É—ina ya tafi a banxa ba, domin ban san yadda xan yi da maganin da na É—irka wa kaina ba." Ta furta a cikin zuciyarta tare da kashe masa ido.

"Haba Ya Huwais, karka manta ni ƴar'uwarka ne. Ko babu aure bai kamata ka wulaƙanta ni ba. Matarka ce ina da haƙƙi a kanka. Karka ruguza ranar farkon mu domin na yi wa wannan rana tanaji na musamman da ba zamu manta da shi ita."

"Ni sa'an ki ne? Kauce ki bani guri." Ya ce tare da sanya hannunsa ya tureta ya shige cikin É—akinsa.

Takaicin abin da ya yi mata ya sanya ta fara hawaye. Ganin kamar haƙarta ba xa ta cimma ruwa ba, bayan cika baki da kuranta wa ƙawayenta yadda daren zai kasance fa ta yi.

Tana tsaye sororo tamkar gunki, ya murɗa ƙofarsa ya shiga tare da bugata da ƙarfi.

Da sauri ta juya don ta shirya kanta ta shiga cikin É—akin, domin ta rantse ba za ta bar wannan rana ta wuce a tutan ma"aho ba.

Ɗaki ta shiga ta faɗa kan gado tare da sakin kuka. Sai kuma ta miƙe ta tuɓe kayanta ta shige bayi. Wanka ta sheƙa wanda ta ɓata lokacinta tana dirzar jikinta da mayuka masu ƙamshi da kyau.

Bayan ta gama wankan, ta zauna zaman shafa. Inda ta ɓata lokacinta gurin ƙyalƙyale jikinta da mayuka da turare masu ƙamshi da daɗin shaƙa.

Wata doguwar rigar bacci ta sa mai kyau fari. Rigar har ƙasa take, amma kuma ta na bayyana surar mutum.

Ƙara ɗauko turaren da Hajiya Zamzam ta ba ta yi tare da ƙara shafe ko ina na jikinta. Sannan ta sanya a rigar baccin.

Wayarta ta ɗauka ta duba kanta a madubi sannan ta rufe ƙofar.

A lokacin da ta murɗa ɗakin yana kwance a kan gadonsa, hannunsa riƙe da wayarsa. Bayan ya yi wanka ya canza kayan jikinsa zuwa kayan bacci. Riga ya sanya da ƙaramin gajeren wando.

Kyawawan dogayen cinyoyinsa masu ɗauke da zararan gashi ya kwantar a saman filo, sannan ya kwantar da kansa a ɗayan filon. Kallon hotonta yake yi, yayin da hawaye suke zuba a ƙuncinsa.

Hannunsa ya kai ya shafa fuskarta, tare da sanya yatsarsa a saman idanunta, yana shafa idanunta da suke ɗaukar hankalinsa ƙwarai.

Ya faɗa cikin kogin tunaninta, ba tare da ya san Wajnah na tsaye tana ƙarewa halitarsa kallo ba.

Wajnah kuwa ji ta yi kamar xa ta sume. Haƙiƙa Allah ya yi mata tagomashi da samun miji mai kyawu kuma ɗan gayu, musamman da ta kalli yatsun ƙafarsa sai ta ji kamar ta duƙa ta lashe.

"Huwais," Ta ce tare da ƙara matsowa kusa da shi.

Da sauri ya miƙe tare da kifa wayarsa domin ya ɗauka ta ga abin da yake kallo.

"Ke! Uban me ya kawo ki cikin ɗakina?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai yana zare mata idanu.

Wal ta yi da idanunta tare da yi mata fari."Ni da É—akin mijina sai na tambayi izinin shigowa? Karka manta da kai da duk gidan nan mallakina nane."

Tsaki ya yi, tare da da É—aukar wayarsa ya fita a cikin galary sannan ya ije wayar.

Ganin tana matsowa tana son haɗa jikinsa da nata, ya sanya shi matsawa tare da ƙara daka mata tsawa. Yana ganin zallar rashin kunyarta na shigo masa a haka.

Ransa ya ƙara ɓaci sosai, ganin rashin kunyarta da tarbiya, domin ya tabbata da Hilah ce mai kunya ba za ta taɓa bayyana surarta ba.

"Ya Huwais, don Allah ka bari mu more rayuwar aurenmu. Wallahi na yi maka alƙawarin yin maka biyayya da zama tamkar baiwa a gareka. Ina sonka duk abin da kake son xan yi maka Yayana."

"Ba za ki taɓa samun zuciyata ba, domin na gaya miki tun farko baki cikin jadawalin matan da nake so. Sam ba ki yi mini ba, amm kika na ce sai kin aure ni. Ga gidan nan sai ki zauna a ƙarƙashin aurena, amma ni da jikina ba xa ki taɓa mallakarsu ba."

Duƙawa ta yi jin abin da ya ce. Jawaye ta fara tare da kai hannu za ta kama ƙafarsa wanda ya janye da sauri ya yana harararta.

"Don Allah mijina, ka soni mu zauna lafiya. Ka dubi tsarina da surata babu wacce mace da za ta tsere ni."

"Akwai ta ita ce wacce take zaɓin raina kuma na ke sonta. Ko da ace ba ta kaiki sura ba, amma ta fi ki komai a gurina." Ya faɗa tare da toshe hancinsa saboda ƙamshin turarenta dake hawa masa kai.

Ganin ya toshe hancin ya ƙara baƙanta ranta matuƙa. Ita da take tunanim ƙamshin zai karkato da hankalinsa, sai ga shi yana nuna baya son ƙamshin.

"Wallahi baka isa ba, matuƙar ina cikin gidan nan babu wata ƴar iskar da xa ta shigo gidan nan, in ba so kake mu yi mutuwar kasko dukanninmu ba."

"Karki ƙara zaginta domin a kanta xan yi mummunar saɓa miki."

"Ka kashe ni in ka so, ai xanfi jin daÉ—i ranar aurenmu ka yi mini shegen duka, kan babu abin da ya shiga tsakaninmu."

Hannu ya É—aga, sai kuma ya fasa don ya san za ta iya gaya wa a gida.

"Dama na san ba ki da kunya, amma wallahi ba xan É—auki rashin kunya ba."

"Matuƙar za ka rinƙa kiran wata banza a gidan nan, ni kuma abin da ya fi banxa zan kirata da shi."

"So kike na canza miki halitta." Ya ce tare da komawa ya kwanta.

"Ya Huwais, don Allah ka tausaya mini ka karɓe ni a matsayin mata." Ta ce cikin rawar murya jin mararta ya ƙara murɗawa.

Tsaki ya yi mata tare da komawa ya kwanta.

Ganin haka ya ta bin bayansa ta kwanata tare da rungumeshi ta bayansa.

Wani irin wawan ajiyar zuciya ta saki jin yadda gabakiÉ—aya tsigar jikinta ya tashi.

Da sauri ya miƙe yana mata mugun kallo da mamakin zallar rashin kunyarta.

"Tashi ki fita ko na saɓa miki."

Abin da ya faɗa, ya sanya ta ɗago idanunta, da ƙyar da suka rine suka canza kala.

"Don Allah ka taimaka mini ina cikin wani hali."

Hannunta ya kama, ya janyota har ƙofar ɗakin ya watsar da ita, tare da mai da ƙofarsa ya rufe.

Kallonta kawai ya yi, ya fahimci halin da take ciki. Sai dai inhar jikinsa zai mallaka mata ba zai taɓa ba, domin komai na sa mallakin Hilah ce.

Komawa ya yi ya kwanta, yana mamakin yadda ta nuna zalamarta da shan kayan matan da ta yi wanda ya san su suke É—awainiya da ita.

Takaici da baƙinciki suka cika mata rai. Duba ga maza masu kyau da suka nuna suna son aurenta, amma ta nace sai shi. Ga shi ta aure shi yana wulaƙanta ta.

Ƙara ta saki jin mararta ya murɗa sai kuma ta fara ciwo.

Da kyar ta miƙe tana faɗin,"Na shiga uku! Ya Huwais, don Allah ka taimaka mini xan mutu cikina, marata."

"Ya Huwais," Ta kira sunan a gigice jin yadda mararta ta ƙara murɗawa.

Huwais kuwa yadda ya ji muryarta ya rikice sam bai damu ba. Kwanciyarsa ya yi tare da kunna karatun qur'ani, ta yadda xai daina jin buga ƙofa da sunansa da take kira.

Wayarsa ya jawo ya kunna data ya hau online.

Zuciyarsa ke kwaɗaita masa, ya tura mata da tsaƙo, amma wani bangare na zuciyarsa na yi masa gargaɗi.

Sauka ya yi dafa kan gado tare da buÉ—e labulen windon É—akin. Tsakar gidan yake kallo, wanda hasken wutan lantarki ya haskaka farfajiyar gidan tankar rana.

"Anya zan iya daina waya da ke? Kai ina ba zan iya ba, domin ta hakanne kawai na ke samun natsuwa a cikin raina." Ya tambayi kansa tare da furta hakan cikin ransa.

"Hilah, ina sonki." Ya ce yana kallon fuskarta a wayarsa, sai kuma ya sanya bakinsa kan nata, ya yi mata kis yana murmushi.

Har ya fara yi mata typing, sai kuma ya kashe wayar duka ya ja bargo ya kwanta.

"Ya kamata na ba ki lokaci."

Wayar kuma ya kunna tare da tura mata tsaƙo.

A lokacin da tsaƙon ya shigo, tana zaune a kan sallaya bayan ta idar da sallah tana kuka.

Sosai take jin zafin yaudarar da ya yi mata, domin ta É—auka yadda yake kalamansa da natsuwarsa, da kuma kyautar ban girma da yake mata mutum ne mai nagarta. Ashe mayaudari ne.

"Wayyo Allahna! Haƙiƙa ka cutar da zuciyata." Ta furta cikin muryar kuka tana jin zuciyarta kamar za ta yi bindiga ta fito.

Wayarta ta É—auka tana duba duk chatts É—in da suka yi. Wasu ta yi dariya wasu kuma ta yi murmushi mai haÉ—e da kuka.

"Ina sonka, why za ka yaudare no?" Ta rubuta mishi hakan sai kuma ta ƙara da

"Don Allah ka bayyana mini kanka, wallahi na yi maka alƙawarin zan aureka matuƙar kana sona."

Ji fa ta yi da wayar, ganin duk tsaƙonnin da take tura masa babu amsa, domin tun jiya lokacin da suka yi alƙawarin xa su haɗu, ya kashe waya bai ƙara hawa ba.

Tana ije wayar tsaƙo ya shigo, wanda da sauri ta ɗauka a ranta tana addu'ar Allah ya sa shi ne.

Ƙaramin tsaki ta ja, tare da canzawar fuskarta ganin tsaƙon Yayanta ne.

"Ya Huwais, ya ke yi? Shi da ya kamata ya kasance da matarsa." Ta yi ma kanta tambayar hakan.

Tsaƙon ta duba inda ta ga ya rubuta jamar kamar haka;
Chapter 31 · 0% Book details