Sashe 2
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke ni sa'arki ne?" Ta nufe ta tare da ɗaga hannu za ta kai mata duka, wanda ganin hakan ya sa ta ruga ta ɓoye a bayansa.
"Ke da ma baki da kunya sam! Shi ya sa na fi shiri da Umnaah ai."
"Duk ku bar maganar bari na je na yi wankan, Abincin ma kisa Abidin ya kawo mini" Ya faÉ—i tare da kama hanya zuwa É—akinsa.
"No Yaya, gaskiya ya kamata ayi lunch a tare. Ka daɗe outside country, ya kamata ace ko ɗan ƙwarya-ƙwaryar liyafa mun haɗa." Ta ce mishi cikin damuwa.
"Ke!" Ta ji muryar Ummu ta daka mata tsawa da take saman bene wanda sai da ta ji cikinta ya murÉ—a.
"Kin san na tsani shegen kaÉ—ifirin ki da iya surutu marasa kan gado. Ya dawo ba za ki barshi ya huta ba? Ke ce za ki gaya masa abin da zai yi?" Ta ce cikin tsananin zafi tana huci
Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta sai ta fara ruwan hawaye tana jin babu daÉ—i a ranta.
Huwais sai ya ji babu daÉ—i duk da hakan ba sabon abu bane, amma yayi tunanin Ummu ta daina ashe ba ta sake zani ba.
"Wuce ka tafi ka yi wanka, zan sanya a kawo abincin sai ka ci ka yi baccin gajiya." Ta ba shi umurnin haka wanda ba shi da zaɓin da ya wuce ya bi.
Kallon Ummi ya yi ba tare da ya amsa ba sai kuma ya juya ya kalleta har yanzu hawaye ta ke yi ya fice yana jin babu daÉ—i a ransa.
Yana fita ta sakko ƙasan tare da ƙarasowa gurinda take tsaye kamar icce.
"Ki kiyaye ni Hilah na gaya miki bana son wannan kusancin tsakaninku, duk da cewar nina haife ku, amma cases nawa ka samu na aikata ba daidai ba tsakanin 'yan'uwa. Ina kiyaye haƙƙin tarbiyarku da Ubangijina ya bani ne, don haka na gaya miki ki daina shishshige masa."
Ɗaga mata kai ta yi alamun ta ji, a ranta take tunanin Ummu ta kasa fahimtar 'ya'yanta, ba su daga cikin irin waɗannan 'ya'yan. Ta yadda ta amince sun shaƙu da shi fiye da ƙanninta da suke mata, amma karta manta shi ɗin ta fara sani a lokacin da ta girma domin ya ci kashinta da fitsari. Shi ya fara ba ta abinci da shi ta yi wayo har ta girma."
"Ma za ki wuce ki bani guri." Ta daka mata tsawar da ta fi wancan.
Shiga ɗakinsa ya yi wanda yasha gyara yana ƙamshi turare mai daɗi. Ɗakin ya bi da kallo ya san cewa ita ta gyara ba masu aiki ba, domin gyaranta daban yake da na kowa. Ta san tsarin da yake so a ɗakinsa da yadda yake son a ije masa takalminsa da kayansa. Kai hatta hulunansa da dressing mirrow Hilah duk ta haddace yadda yake son su kasance.
Ɗakin ya ƙara bi da kallo takaddun ne da bulunbulun masu kyau ta yi kwalliya da su, haɗe da sunansa tana masa murnar dawowarsa.
Ɗaya daga cikin bulun-bulun ya ɗauko tare da rungume shi a ƙirjinsa yana jin tamkar ita ya rungume.
Ya daɗe yana ƙarewa ɗakin kallo sannan ya miƙe zuwa bayi tare da shiga bayi.
Wanka ya yi ya fito dga shi sai tawul ɗaure a ƙirjinsa.
Tsayawa ya yi yana shafa mai daidai lokacin da Abidin ya yi sallama da tiren abinci ya ije tare da fita.
Bayan ya gama gyara jikinsa ya feshe jikinsa da turare mai ƙamshi.
Yana cikin riga da wando jeans da tishet ruwan bula domin shi ma'abocin ƙananan kaya ne, kuma suna mishi matuƙar ƙyau sosai tare da karɓar fatar jikinsa, da take ruwan tarwaɗa. Gashin da yake kwance a jikinsa ya ƙara ƙawata jikinsa, domin hatta yatsunsa ga shi ne kwance a jikinsu.
Haƙiƙa yana da kyau mai ɗaukar hankali da rikita zuciyar 'yan mata. Yana da idanu amma ba manya sosai ba. Sai dai, duk macen da ya kalla sai ta ji tamkar ta yi tsuntsuwa ta ɓace daga gurin, domin wani irin ƙwarjini da haiba da ke cikinsu. uwa uba maganaɗinsu da suke da shi tamkar an zuba zaiba.
Bashi da hasken fata, amma kuma yana mafani da mayuka masu kyau da tsada, waɗanda suke ƙara fito da ainihin kalar fatarsa da kyansa.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 2
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Ba shi da hasken fata, amma kuma yana mafani da mayuka masu kyau da tsada, waɗanda suke ƙara fito da ainihin kalar fatarsa da kyansa.
Sajensa da ya zagaye duniyar fuskarsa, da ɗan gemunsa mai kyawu. Shi yake ƙara rikitar da duk macen da ta yi tozali da shi, har ta ji ba ta wata addu'a face samun miji ko saurayi kamarsa.
Dogo ne sosai yana da ɗan jiki kaɗan, wanda ya ƙara kyautata kyawun surarsa da halittunsa. Ƙirjinsa mai faɗi irin wanda mata suke kira da gadon bacci.
Abin da zai fi ɗaukar hankali a halittunsa; idanunsa. Tabbas yana da wata irin idanu irin wanda turawa suke laƙabi da golden eyes, domin in yana kallon, sai ka rasa natsuwarka. Hakika kyawun idanunsa baiwan ne da Allah ke bawa wanda ya ga dama. Kasancewarsa mai rahma mai yin kyauta na baiwa ga wanda ya so, ba tare da ya duba cancantar hakan ba.
Mutun ne mai yanga. Eh tabbas yana da yanga sam bai cika shiga rayuwar wasu ba, amma kuma yana da sauƙin mu'amala domin ba shi da zafi sosai, ko 'yan'uwansa shedane, saboda tun suna ƙanana har suka girma bai taɓa ɗaga hannu ya doki wani ba, sai dai faɗa wanda shi ma ba kasafai ba.
Ballantana Hilah da take rayuwarsa gabakiɗaya, domin tun a ranar da aka haifeta Allah ya sanya masa sonta na mutuwa, wanda ada yana tunanin saboda ƙanninsa uku duk maza ne, sai ita ta zo a na mace shi yasa yake mutuwar sonta. Amma da tafiya ta yi tafiya girma ya kamasa sai ya fahimci soyayar aure yake mata, wanda yake kallonsa mahaukaci wanda bashi da cikakken hankali.
Zama ya yi yana buɗe kular abincin. Wani irin ƙamshi ya ziyarce sa, wanda ya sa ya lumshe idanunsa da ake kira sexy eyes.
"Anya yana ganin kwai macen da tafi Hilah ɗinsa iya abinci? Kai da wuya domin in har akwai to bayanta take, domin Hilah ɗinsa gwanace gurin iya girki sam ba ta da ƙiwa, a gurin haɗa abincin da mutum zai ci ya samu natsuwa. Tabbas duk namijin da ya same ta ya more rayuwarsa domin an gama ba shi rabonsa na duniya sai na lahira.
Take ya ji wani irin tsananin kishi mai zafi, ya taso masa tun daga kan ƙafafunsa har i zuwa kansa, ya mamaye shi har baya iya ganin abincin sai dai dishi-dishi. Sai ya miƙe yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa, tamkar ruwan xafin da aka ɗora na mai jegen da ta yi haihuwan fari ake shirin sauke mata don ta yi wanka. Idanunsa suka kaɗa har ya ji abincin da yake sha'awarsa da muradinsa sun gimsheshi ba tare da ya ɗanɗana ba.
Zuciyarsa na tururi tamkar ya haÉ—iye kansa ya mutu.
"Ni dai na shiga uku! Allah ka jarabce ni da abu mafi girma soyayya kuma ƙanwata wacce muka fita ciki ɗaya. Tabbas wannan girman jarrabawar ta zarce tunanina."
Wani irin sha'awarta da ƙaunarta suka taso masa, har suna ƙoƙarin kawar da hankalinsa. Musamman yadda ya ga ta canza ta girma ta zama babbar mace. Duk wata halitta da zai sa a kira mace da cikakkiyar budurwa ta kai, domin in har memerinsa will served him well, ranar Juma'a 20/02/25. Za ta shiga shekara sha tara a duniya. Wato birthday ɗinta wanda ya shirya wa ranar domin ya tana ji kyauta ta musamman a ranar.
"Allahumma gafirli, warahamni, waj burni, wahdini warazuqni." Ya fara faÉ—i a zuciyarsa yana maimaita domin tabbas Allah ya jarabce shi.
Miƙewa ya yi, domin a halin yanzu babu abin da idanuwansa suke kwaɗaita masa son gani face ita, don samun natsuwar zuciyarsa.
Ba tare da ya ci abincin duk da yunwar dake ƙwaƙularsa ya mai da abincin ya rufe.
Ko da ya shiga falon sauran yaran ne a falo, amma ban da ita wanda ya san tana kicin domin É—ora girkin dare.
Yana mamakin yadda Ummu ta hana rayuwarta saƙat ta mai da ita kukun gidan, duk da tarin masu aikin da suke cikin gidan. A cewarta abincin ta yafi daɗi kuma gata take mata, amma abin da yake ɗaure masa kai sam ba ta barin Azerh, Umnaah da Amnaah su shiga ko kaɗan.
Don ance mutum tara yake bai cika goma, ba da sai ya ce takai. Ta fannin addini malama ce wacce ta samu tropy da yawa na gasar karatun alqur'ni har waje ta je. Sannan a makarantar boko ita ce best student a fannin computer Jami'ar Abuja birnin tarayya.
"Laa Ya Huwais ka dawo mu yi hira?" Umnaah ta miƙe da sauri ta isa gare shi tare da kama hannun shi tana murna.
"Taɓ! Ta ya ya zai iya cin abinci Ummu ta taɓa 'yar gidansa? "
Azerh ta yi maganar tana kallonsa da ya ƙarashe shigowa falon.
"Ya Huwais, tana kicin tana dinner." Cewar Umnah da ta kama hannunsa, ganin yana ta waige-waige.