← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 40

Sashe 26

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Minti goma sha biyar bai iso ba, sai ta É—aga waya don ta kira shi. Gabanta ya faÉ—i jin wayar a kashe, saboda ko da safe sun yi waya.

Datar wayarta ta kunna, tare da shiga Whatsapp don ta yi masa magana. A nan ta tsinci tsakonsa da sai da ta yi taga-taga za ta faɗi Afnan ta riƙe ta.

Hawaye shar! Suka wanke mata ƙuncinta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta tare da dafe kanta da take jin juya na ibanta.

"Lafiya Hilah?"

"Don Allah ki riƙe ni kar in faɗi."

Da sauri ta kamata, ta buɗe murfin motar ta shigar da ita, ganin yadda take haƙi kamar wace ta yi gudun famfalaƙe.

"Wayyo Allahna!" Ta furta tare da rushewa da kuka.

"Lafiya, don Allah ki yi mini bayani."

"Mayaudari ne mahaukacin masoyi! Ya turo mini da tsaƙon, na manta da shi a rayuwata zai bar ƙasar."

Jikin Afrin ya yi sanyi, har ta kasa cewa komai, musamman yadda ta ga ta ruɗe matuƙa ta fita hayyacinta.

"Don Allah ki natsu, ni dama tuntuni zuciyata ba ta aminta da shi ba, saboda bai kamata ki mallaka masa zuciyarki ba tare da haÉ—uwa ta zahiri ba.!"

"Ya cuce ni ya sanya mini soyayyarshi ya guje ni ya zan yi?" Ta yi mata tambayar tare da kama hannunta.

Wayarta ta zaro ta danna numbar Huwais, da yake cikin taro, zuciyarsa a cinkushe tunanin halin da za ta shiga yake yi.

Ganin kiranta gabansa ya faɗi matuƙa. Ya kasa ɗaukar kiran har sai da ta yi masa yafi goma. Ganin ba za ta daina ba, ya kai hannu zai kashe sai ya ga rashin adalcin yin hakan.

"Ya Huwais, mahaukacin masoyi mayaudari ne, ya tura mini da tsaƙo na manta da shi ya bar ƙasar." Ta furta cikin tsananin kuka.

Rintse idanunsa ya yi, cikin wani yanayi yana jin babu daɗin yaudararta da ya yi, saboda shi da zaɓin da ya wuce haka.

"Ni ma na zama mahaukaciya kamarsa, tun da na aminta da soyayyarsa." Ta ƙarasa faɗin hakan cikin kuka ganin ya ƙi cewa komai.

"Ki natsu Hilah, ki bawa Afrin motar ta tuƙa ki ku da... Ko kuma ki faɗa mini inda kuka na zo."

Wayar ta miƙa wa Afrin." Ki yi masa kwatance ba zan iya ba."

Afrin ta yi masa kwatance tare da kashe wayar, tana rarrashinta da take kuka kamar ranta zai fita. Wani irin ƙaunarsa take bijiro mata ganin ta rasa shi.

Duƙawa a gurin ta yi, ta saki kuka duk irin rarrashinta da take yi ta tashi taƙi.

Huwais kuwa cikin tashin hankali ya miƙe xai fice.

"Ina za ka ga baki kana da su?"

"Ka kula da su, ina zuwa Najib." Ya furta hakan ba tare da ya amsa kiran ya juya ba.

Yana isa guri ya buɗe motar ya fito. Tana ganinsa, ta fashe da kuka tare da miƙe wa ta isa gareshi ta faɗa jikinsa.

"Ba zan yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata ya yaudare ni."

Kama hannunta ya yi suka shiga motar bayan ya bawa Afrin umurnin ta tuƙa motar ta dawo gida.

Ganin irin kukan da take yi, ya yi matuƙar daga hankalinsa matuƙa. Yana tuƙi amma shi kansa ba shi da natsuwar da zai mayar da hankalinsa ga titi.

Kukan na ƙara mishi ƙunci a zuciyarshi sosai, musamman in ya tuna shi ne sanadin zubar hawayenta.

Gangarawa ya yi ƙasan titi ya sauka, tare da paking ɗin motar ya kifa kansa a sitiyarin

"Ya Huwais, ba zan taɓa yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata. In har ya san ba ya ƙaunata mai xai sanya ya shigo cikin rayuwata?" Kukanta ya ƙara tsananta bayan ta furta hakan.

Jiyowa ya yi yana kallonta, yadda ta ci uban kuka, abin ka da farin mutum fuskarta har ta canza ta ƙara haske.

"Hilah," Ya kira sunanta can ƙasar murya, wanda ya sa ta ɗago kanta da sauri tana kallonsa.

Girman idanunta da suka canza kala, ya sanya ya kasa rarrashinta da ya yi ninyar yi, wanda ganin hakan ya sanya ta ci gaba da kukan har da ƙara sauti.

"Please, don Allah ki daina kuka domin zuciyata na zafi." Ya furta cikin sanyin murya.

Jin ta rage sautin kukan, ya sanya shi buÉ—e motar ya fito. Ta inda take zaune ya zagaya ya buÉ—e motar.

A gabanta ya tsuguna yayin da ya yi narai-narai da fuskarsa.

"Kina son damuwa ya sanya na mutu kuma ki ga hawayena ko?" Ya yi mata tambayar cikin wata irin murya tare da saukowar tagwayen hawaye a fuskarsa.

Hankalinta ya tashi sosai! Da sauri ta share hawayenta tana kallonsa.

"Don Allaah kar ka yi kuka na daina."

Ajiyar zuciya ya yi lokacin da ya ji muryarta na faÉ—in haka.

"Ina jin rayuwata wani iri Hilah. Yau ake mini auren dole, kuma ƙanwata wacce na fi ƙauna tana cikin wani yanayi. Ban san da wani irin kalamai zan rarrashe ki ba, amma na yi miki alƙawarin nemo mahaukacin masoyi duk inda ya ke, tun da na fahimci ya riga ya sace zuciyarki."

A yadda ya yi maganar, ta kasa gane ko bai ji daÉ—in irin yadda ta nuna tashin hankalinta ba ne, ko kuma tsananin tausayin halin da take ciki, ya sanya shi shiga cikin yanayin.

"Ka yi haƙuri ka gafarce ni, na sanya mahaukacin masoyi a raina, amma halayensa da iya kalamansa suka sanya na mallaka masa zuciyata ba tare da dogon nazari ba, kuma Yayana, duk wanda zai shiga rayuwata, ba zan taɓa ba shi matsayinka ba."

"Na fahimta yadda kike ji, da kuma yadda soyayya take tasiri a zuƙatan masoya, ba tare da tsimi ko dubara ta masoya ba. Sam ban yi miki mummunan fahimta ba, saboda ni ma ina jin kwatankwacin ɗacin da kike ji."

Miƙewa ya yi, tare da sanya hannu sa ya riƙe murfin motar, sai kuma ya saki ya kama gefen hijabinta.

"Share hawayenki ƴar ƙanwata kin manta na gaya miki matuƙar ina raye ba za ki taba yin kuka ba?"

ÆŠaga masa kanta ta yi tana murmushi tare da saukowar hawaye a fuskarta.

Gefen hijabinta da ya ɗauke hawayen da suke zuba, ya ƙara sanyawa ya ɗauke mata wasu da suka ƙara zubowa.

Rufe motar ya yi, bayan ya sakar mata murmushi, ya zagaya ya koma ta bangaren mai tuƙi ya shiga.

Bayan ya tada motar sai ya tsaya yana kallonta yadda ta ƙurawa titi idanu.

"Yayana, ina sonka." Ta furta daidai lokacin da ta juyo ta kalle shi.

Rintse idanunsa ya yi tare da jin wani irin tsau a ransa.

"Ba irin wannan soyayyar na ke so ba Hilah;wace za ki zamo murfin asirina kuma farincikin rayuwata uwar Æ´aÆ´ana."

Murmushin ya mayar mata sannan ya fara jan motar.

"Ni ma ina sonki ƙanwata."

A hanya suna tafe Hilah ranta a ɓace. A ranta tana jin in har ya ƙara kiranta, sai ta yi masa rashin mutunci, duk da cewar ba halinta ba ne.

"Mai ya sa zai guje ni bayan ya yi mini alƙawarin kasancewa a tare da shi? Shi kenan ya guje ni na rasa shi har."

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 16

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Mai ya sa zai guje ni bayan ya yi mini alƙawarin kasancewa a tare da shi? Shi kenan ya guje ni na rasa shi har abada?" Ya zan yi da soyayyarsa da ta shige mini zuciyata. Wayyo Allah ka dawo mini da shi a cikin rayuwata, domin shi ne irin mijin da nake masifar so." Haka ta rinƙa addu'a har ta fara jin sauki a cikin zuciyarta.

A maimakon ya kai ta gida, sai ta ga ya ɗauke hanya. Gurin shaƙatawa ya kai ta mai kyau, ya kashe motar ya fito tare da zagayowa inda take.

Hannu ya miƙa mata bayan ya buɗe motar.

"Ya Huwais, mai za mu yi nan, kar ka manta yau ne fa auren ka? Mutane na can na jiranka."

"Karki damu, farincikin ƙanwata kawai na ke so." Ya ce mata tare da kama hannunta da ta miƙa masa.

Cikin gurin suka isa, wanda wurin ya yi kyau matuƙar haduwa iya gaya! Hilah ta sha zuwa gurin, domin yana ɗaya daga cikin guraren shaƙatawa da take so, kuma ya ke yawan kawo su.

Siyayya ya fara yi mata har sai da ta riƙe masa hannu.

"Don Allah ka bar kashe kuɗinka Yayana, hidima ce a kanka. Ko ka manta yanzu kai mai iyali? Ba zan so Anty Wajnah ta sha wahala a gidan ɗan'uwana ba." Ta faɗa cikin sanyin murya tare da riƙe hannunsa.

Harararta ya yi, sai kuma ya ƙwace hannun ya ɗauki ƙaton biskit, wanda yasha cakulate ya saka a kwandon.

"Kar ki damu farincikin ƙanwata kawai na ke so. Sam ban damu da kuɗina su ƙare ba, matuƙar hakan zai sanya ki farinciki."

Murmushi ta yi tare da jan hannunsa suka fara tafiya.

"Haƙiƙa ka zamo ɗan'uwa mai kau da damuwar ƙanwansa. Fatana na samu miji mai irin kyawawan halinka da nagarta, wanda hakan yana da nasa ba da fara soyayyata da mahaukacin masoyi, saboda yana da kyawawaan ɗabi'u irin naka."

Ba tare da ya ce mata komai ba, ya fara tafiya, saboda in har bai bar gurin ba, zuciyarsa za ta iya fallasa abin da ke cikin zuciyarsa, saboda yabansa da ta yi.
Chapter 26 · 0% Book details