← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 40

Sashe 40

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mace ɗaya kawai yake so kuma yake burin ya yi rayuwar aure da ita. Ita ce wacce yake ganin duk ji da kansa da yake yi, zai xama bawa matuƙar xai mallaki zuciyarta, amma kuma ba zai iya bijirewa umurnin Ummu ba.

Miƙewa ya yi, ya kulle masallacin sannan ya shigo cikin gidan. Zuciyarsa na yi masa nasihar ya bi umurnin mahaifiyarsa.

Jin alamun buɗe ƙofa, ya sa ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurin ƙofar don ta buɗe masa, dama ta kulle ƙofar saboda ta san lokacin da xai shigo.

Buɗe ƙofar ta yi da murmushi a fuskarta."Barka da dawowa farincikin rayuwata." Ta faɗa cikin wani irin murya yayin da ta matsa kusa dashi kamar xa ta rungume shi.

Karo na farko ya yi mata kallon tsanaki, domin tun lokacin da ta fara nuna maitarta a fili ya ji babu wacce ya tsana fiye da ita, kuma tun daga lokacin bai ƙara yi mata kallon da xai gane yadda take ba.

Ganin ya kalleta ya sanya ta ƙara matsowa kamar xa ta shiga jikinsa.

Ya buÉ—e baki da nufin ya magana, amma sai ya ji ya gaza furta kalami.

Wucewa ciki ya yi, ba tare da ya ce mata komai ba, wanda ganin haka ya sa ta bishi zuwa É—akinsa.

"Ya Huwais, na kawo maka abincin ka ɗaki?" Ta yi masa tambayar tana ƙarasowa inda yake xaune.

Ƙara ɓata fuska ya yi tare da kauda kai.

Kusa da shi ta isa ta rage tsawo."Don Allah Ya Huwais ka ji abincin nan, horas da kanka da yunwa babu abin da zai jawo maka sai cuta."

"Bana buƙata." Ya furta a gajarce yana kauda kansa.

Shiru ta yi take ranta ya ɓace, ganin duk wahalar da ta sha ya tashi a banxa. Idanunta suka ciko amma sai ta jure ta fita daga cikin ɗalkin

"Haƙiƙa duk macen da take son wanda ba ya ƙaunarta, tana cikin jarrabawa." Ta furta hakan tare da warware ɗaurin ɗankwalinta cikin takaici.

Har ta ɗauki waya xa ta kira Ummu, sai ta fasa ta wanke fuskarta, da ruwan hawaye ya gama jiƙata ta gyara kwalliyarta.

Numbar Wahida ta lalubo tare da danna gurin kira,"Hello," Sai kuma ta fashe da kuka."

Cikin takaici Saboda ta zabga tsaki daga cikin wayar ta ce,"Na gaya miki zuba mishi maganin yaci shi kawo zai karkato da hankalinsa gareki. Ki cire tsoro da tunanin komai. Mijinki ne kuma in ba ta haka kika yi masa ba, wannan mutumin ba zai lalle ki ba."

"Ba ya sona ya tsane ni. Ban san ya zan yi ba." Ta ƙarshe maganar cikin kuka tana wurgi da filo.

"Na gaya miki abin da za ki yi kenan, wanda zai jawo hankalin sa gareki, amma kika tsaya kallon ruwa har kwaɗo zai yi miki ƙafa. Maganin yana da ƙarfi, don sai ya raina kan sa."

"Ok, na gode." Ta furta tare da ije wayarta kan dressig mirror.Kayan bacci ta sanya ta koma É—akinsa.

Bayan fitarta ya bi ta da kallo yana son ganin inda ta gaza, amma ya san Wajnah tana da duk abin da É—a namiji yake so a jikin mace. Shi kawai babu soyayyarta a cikin zuciyarsa.

Yana wannan tunanin ta murÉ—a É—akin sai ta ji a kulle. Fara bugawa ta yi tana kiran sunansa.

Har ya yi banxa da ita sai ya tuna umurnin Ummu. Da sauri ya miƙe tare da buɗe ɗakin ya tsaya a bakin ƙofar ta yadda ba za ta iya shigowa ba.

"Lafiya?" Ya yi mata tambayar fuska a É—aure.

"Ummu, ce ta ce na shigo na kwanta in kaƙi buɗe ƙofar na kira ta."

"Ke zan yi mugun ɓata miki rai, matuƙar za ki rinƙa haɗa ni da iyayena." Ya faɗa cikin ɗaga murya.

"Ni fa bani na kirata ba ita ta kira ni yanxu, kuma ta ce za ta ƙara kira."

Matsawa ya yi ta wuce yana faÉ—in,"Ga É—akin nan sai ki cinye."

TO MASU KARATU.. AN CE LAIFIN DAƊI ƘAREWA.LITTAFIN RANAR WANKA... BOOK ONE YA ƘARE SAI MU HAƊU A BOOK TWO.

Mai ke faruwa ko na ce mai ya ke shirin faruwa?🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄🙄

Wajnah na yin nasarar sace zuciyarsa har ya maida ita cikakkiyar mace? Ya kuma manta da HIlah a rayuwarsa?

Mai ya sa Huwais ya ke jin kamar Hilah za ta iya zama matarsa?

Wai ku tsaya masu karatu. Hilah dai ƴar Ummu ce ta uku, saboda me Huwais zai rinƙa tunanin ba yar uwarsa bace?

In har ta gane shi ne mahaukacin masoyi ya za ta yi, kuma wane mataki za ta É—auka?

Shin in Wajnah ta gane Hilah ce wacce ya ke so kuma yake wulaƙanta ta saboda ita. Wane mataki za ta ɗauka?

Soyayyar da suke yi wa junansu zai ɗaure bayan ya bayyano sirrin da zai canza rayuwarta? Duk da cewa ranar wanka, ba a ɓoyen cibi.

To ita É—in wace ce kuma su waye iyayenta? Sannan mai ya faru ta shigo cikin rayuwarsu?

Shin zai yi nasarar mallakarta a matsayin mata, kuma ya rayuwar aurebsu xai kasance? Hilah za ta zauna da shi a matsayin miji, ko kuma a matsayin Æ´aÆ´anta za ta É—auke shi?

Huwais zai É—auke idanunsa a kanta ya zauna da ita ba tare da ya amshi sadakinsa ba? Ko.kuma girma ne zai fadi ya yi rayuwar aure da ita?

Ina Wajnah mai kishin mijinta da sha maganin mata? Za ta iya barin mata Huwais ko kuma za ta zauna a fafata zaman kishinda ita? Sannan burinta zai cika na fatan ya mallaka mata kansa su zamo abu É—aya?

Ya rayuwarta xai kasance in har ta cigaba da shan maganin mata?

Shin za ta daina sanar da ƙawayenta rayuwar aurensu ko kuma za ta ci gaba?

To ku sha kuruminku domin duk amsar tambayarku. Yana cikin littafin book two wanda yake paid kan Naira 500 kacal, in kuma aka gama ya zama complete 600 wanda Jamsy ƴar baiwar mai son faranta muku ba ta bar amsar tambayoyinku ko ɗaya ba, domin ta wasa ƙwaƙwalwarta ta bayyana muku har abi n da ba kubsani ba.

labarin cike yake da rikita-rikitar soyayya da tausayi haɗe da jimami da shakwakiya. Ma za ku garzayo ku biya don ku karanta. Kar ku bari a baku labari, domin ya tsari kuma akwai soyayya mai tsuma zuciya. Ƙayataccen littafin naira 500 ne kacal, amma in aka gama rubuta shi 600 ma za ku garzayo ku biya don ya ɗebe muku kewa.

Duk wacce ta shirya biya sai ta tura kuÉ—in ta a wannan asusun

8144072423

Jamila lawal opay

Sannan a tura shedar biya ta waÉ—annan numbar nan. 08144072423

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 08144072423

Ga masu buƙatar turo katin waya sai ku tura ta wannan numbar 08144072423
Ko kuma wannan 07072971093 a Turi da sheda ta É—aya daga cikin wannan numbar ta Whatsapp.

Shin kin karanta littafin "SAKACINA KO HALIN MAZA" ko kuma "KURA DA FATAR AKUYA"? In har ba ki karanta ba ma za garzayo ki siya kan naira 600 kacal dob ki more karantunki. Labarine masu daÉ—i da darasi a cikin su, wanda shararriyar marubuciyar na . Jamila Lawal Zango
Jamsy
Chapter 40 · 0% Book details