← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 40

Sashe 20

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaɗa kansa yake kamar ƙadangaren kutu!"Ya kamata gaskiya ki gayyace shi, amma kar ki ce za ki rabu da shi, don ya ƙi zuwa bikina in har kina sonshi, domin jikina yana bani mahaukacin masoyi shi ya fi dacewa ya aure ki. Wani ne can wanda ba ki taɓa tunanin yana sonki ba, ya ke fama da dakon soyayyarki tsawon lokaci. Da ya ke ƙanwata mai zafi ne kuma kyakykyawa dalilin da ya sanya ya kasa bayyana kansa gareki."

"Ni ma haka nake ji musamman a duk lokacin da na yi istikhara."

"Da kyau malamar ƙanwata. Daɗina dake komai sai kin nemi zaɓin Allah. Ki ba shi lokaci matuƙar bai bayyyana kansa ba, ni da kaina zan gaya miki ki haƙura da shi."

"Amma kai ma Yaya kana da kyau, domin ban taɓa ganin namijin da yake da kyau kuma ya iya tsara rayuwarsa da kula da addini kamar kai ba.

Jin abin da ta faÉ—a kansa ya fasu har ya ji kamar zai cika duniya.

"Duk kyawuna, bai kai ƙanwata sarauniyar kyawu da kula da addini ba."

"Wannan dalilin ya sa na ke jin matuƙar haushin mahaukacin masoyi da kike sonsa."

Ta buɗe baki xa ta yi magana, ya rigata daidai lokacin da suka isa ƙofar gidan, ya tsaya a get ɗin ba tare da ya yi hon ba.

Kashe motar ya yi ya kalle."Please, na gaji da maganarsa as usual. Ke kullum damuwarsa kike kawo mini, da kuma na yi ƙorafi kice ba haka ba."

Dariya ta yi tare da ce wa,"Kai Yaya,"

"Ki bani shawarar yadda zan zauna da Wajnah a matsayin mata."

Kallonsa ta yi kamar ba ta gane mai yake cewa.

"Yes, ina nufin wane irin zama za mu yi, domin kin san ba ta a cikin zuciyata. Tsoro na karna cutar da ita Allah ya kamani."

"Ta ci albarkacin Mommy mahafiyarta. Ka yi adalci a zamanku."

Kwantar da kansa ya yi kawai a saman kujerar motar domin ba haka ya so ta ce mishi ba.

Gani suka yi an wangame get É—in gidan. Najib ne da matarsa tsaye cikin mamaki suna kallonsu.

"Kai! Wallahi kana da abin mamaki Huwais, na ɗauka amarya ka kawo mini kuka tsaya kana soyewa tun ɗazu a waje ashe ƙanwarmu ce." Ta faɗa daidai lokacin da ya shigo da motar cikin yana ƙoƙarin buɗewa.

Hilah da ke dariya ya watsawa kallo ba tare da ya ce komai ba. Ya ɗauko pos ɗinta da ta barshi a motar ya miƙa mata.

Najib da ya san dawar garin bai yi ƙorafi ba. Ya yi musu jagora suka shiga ciki.

Hilah ta zauna a gefen kujerar da ya zauna bayan ta gaida matar Najib mai suna Samahatu.

Cikin sakin fuska ta amsa mata, daidai lokacin da ta ije musu gorar ruwa da drinks a gabansu.

Huwais ya sanya hannunsa ya ɗauki ruwan ya buɗe, tare da ɗaukar kofi ya zuba mata. Miƙa mata ya yi yana murmushi. Ita ma murmushin ta mayar masa tare da karɓa ta ce masa,"Thanks, Ya Huwais."

Da idanu ya amsa mata tare da ije gorar yana mata wani irin kallo.

Samahatu ne ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallonsa. Ta juya ta kalli Hilah da take kurɓan ruwan cikin yanga kamar ba ta son sha, yayin da hankalinta yake kan wayarta.

Idanunta ta mayar kan Huwais da har yanzu ita yake kallo, duk da maganar da Najib ya ke mishi, amma hankalinsa ba shi a kansa.

Ƙara kallonsu ta yi tana son ƙara ganin kamar su. Ta san cewa Najib ya taɓa nuna mata hotonta har ya sanar da ita ciki ɗaya suka fito. To amma wane irin kallo yake mata kamar na soyayya? Ƙwaƙwalwarta ta rikice sai kuma ta fara tunanin ko dai ba ita ba ce.

Gyaran muryar da ta yi ya sanya dukanninsu hankalinsu ya dawo kanta.

"Baby, bari na haÉ—o abinci." Ta ce tana sakar masa murmushi.

"Ok, honey, please ki kawo wa Huwais juice É—in goribar da na haÉ—a ya ji na iya abinci."

Dariya ya yi jin abin da ya ce ba tare da ya ce komai ba.

Zubbur Hilah ta miƙe tare da kallonsa."Yayana, let me help her." Ta furta cikin taushin murya.

"Haba, ƙanwarmu karki wahalar da kanki ai na kusa gamawa."

"No, kar ki damu in ba ki gama ba, ki ba ta ta yi girkin domin she is the best cooker in the world" Ya furta hakan cikin tabbatar wa.

Murmushi ta yi." No, kar ki damu yanzu xan gama." Ta ce za ta juya.

Hannunta Hilah ta kama tare da cewa,"Mu je Anty Samah, kar ki damu. Amarya ce ke bai kamata ki yi aiki ba."

"Good girl, na gaya miki ƙanaata akwai hankali da son taimako, domin zan iya cewa tafi ko wace mace hankali da natsuwa da iya komi."

Sororo ta yi sai kuma ta yi yaƙe kawai ta kalleta da take murmushin jin kunya ganin yadda yake kurantata.

Harararsa ta yi cikin wasa shi kuma ya aika mata da kallo suka shiga kicin.

"Huwais, kana cika zaƙewa fa! Ba ka tunanin abin da kake yi kowa zai iya gane sonta kake yi? Kuma yabon ta da kake yi ba ƙaramin matsala zai jawo maka da iyalinka ba, domin babu macen da za ta zauna ta ji kana yabon ko da ƴarka ce haka, ba tare da ta ji kishi ba."

"Let her be. Ai dama ta shiga gonar da mallakinta ba ta shiga."

No, absolutely you need to change. Wallahi za ka iya jawo ma kanka rashin zaman lafiya da iyalinka, kuma irin kallon da kake mata duk yana wuce gona da iri."

"Hmmmmmh," Kawai ya ce tare da mai da hankalinsa kan tibi.

"Don't be delusional Huwais."

Ƙin tanka masa ya yi, wanda ya sa shi mai da hankalinsa kan tibin suka ci gaba da kallo.

A kicin suna aiki Samahatu na satan kallonta, musamman da ta cire gyalen da ta yi rolling É—in kanta da shi.

Da ta ga gashinta sai da ta yi wa Allah tasbihi. Satan kallonta take yi ba tare da ta kula ba, da ta maida hankalinta gurin haÉ—a salat.

"Ance mutum tara yake bai cika goma ba, haƙiƙa wannan halittar ta cika." Ta furta a zuciyarta ganin yadda take da tsatsan kyau.

Babu abin da ya ƙara ɗaukan hankalinta irin yadda gashi ko ina ya kwanta a jikinta, kamar wata balarabiya.

Ƙara kallonta ta yi daidai lokacin da take goga karot. Murmushi ta sakar mata tare da cewa,"Sannu da aiki."

"Yauwa Anty Samahatu, kin ga Yaya Huwais, yana mugun son salat. In har na yi masa santi yake yi, don yau sai kin yi haƙuri domin sai na yi masa waigi."

Dariya ta ba ta musamman yadda take maganar cikin tsigar tsokana.

"Yauwa ba ni lemun tsamin na saka, domin ya ce ina É—iga kaÉ—an kunninsa har zut!Zut! Suke masa, kar kuma na cika ban san ko kuna so ba?"

Dariya sosai ta yi, jin abin da ta ce,"Ki sa shi ma ya sanar dani tun kafin mu yi aure yana ci, kuma Yayanki ya koya masa."

"Eh, ai ban taɓa ganin aminan da suke ƙaunar junansu kamar su ba, don ban taɓa ganin sun samu saɓani ba."

"Saboda sun haÉ—a ilmi da hankali ne."

"Haka ne Anty Samah." Ta ba ta amsa tana juya salat É—in.

"Gaskiya kina ji da Yayan na ki, ko na ce kuna ji da juna, amma sai dai na shiga kokwanto ko ƙanwarsa ce wacce suke ciki ɗaya, ko matar da zai aura?"

Dariya ta yi, ta tsaya da abin da take yi,"Saboda me kika tambaya?"

"Kulawar ta yi yawa."

"Eh, yana ji da ni sosai. A cewar shi ni ce mace ta farko, da ya fara samu bayan ƙanninsa maza uku. Yayana yana ji dani sosai, wanda hakan ya samu asali ne da shi ya yi ɗawainiya da ni tun ina ƙarama, kuma ya kamata ki ga kama, musamman diple ɗin mu, duk da shi ba shi da hasken fata sosai kamata."

"Na shiga kokwanto ne irin kulawar da kuka ba wa junanku, kamar na ma'aurata, amma kuma jin yadda kuka taso, gaskiya kin cancanci fiye da haka."

"Sosai kamar yadda ni ma nake ji da shi."

KaÉ—a mata kanta ta yi tare da É—aukar tiren abincin suka fito falo, yayin da Hilah ta É—auki tiren juice É—in.

Tashi ya yi ya karɓi tiren yana faɗin,"Ina fatan ba ki wahalar mini da ƙanwata ba?"

"Ni na isa a kore ni a garin Abuja?" Ta ce cikin dariya.

Zama suka yi a dinning suka fara cin abincin.

Yana kai abincin bakinsa ya tauna ya lumshe idanunsa yana kallonta.

"Ƙanwata, ke kika haɗa salat ɗin nan ko?"

"Please, Anty Samah, ki bani waigi na yi masa kar ya faÉ—i."

Dariya suka kwashe da shi, ban da shi da yake harararta cikin wasa.

Suna cin abincin kiran Hajiya ya shigo wanda ya tabbata Hamad ne ya gaji da jira.

Dama tun da suka shigo ya fakaici idanunta ya É—auki wayarta ya kashe.

Kiran Hajiya bai daÉ—e da tsinkewa ba, na Ummu ya shigo.

Zuciyarsa ne ya buga ya kalleta da sai wasa fa cokali take yi, domin ba ta jin yunwa.

"Ki yi sauri ki gama za mu tafi."Ya ce zuciyarsa na bugawa, don tun da ta kira hankalinsa ya tashi abincin ya fita a ransa.

Kasa ɗauka ya yi, don ba shi da abin da zai ce mata, kuma in ya kashe wayar hukuncin da za ta yi musu, sai ya fi muni sosai, musamman Hilah laifin duk a kanta zai ƙare wanda ba zai so hakan ba, don gara ta hukunta shi.

Bayan sun kammala suka miƙe za su tafi. Samahatu ta shiga cikin ɗaki ta ibo mata kayan kwalliya da yawa ta miƙa mata a leda.

Hannu ya sanya ya amsa yana faɗin," Kawo kar ki wahalar mini da ƙanwata."Miƙa masa ta yi tana dariya ba ba ta ce komai ba.

"Ina fatan za ki dawo sis É—inmu za ki dawo kin burge ni."

"Zan dawo Anty Samah."Ta ce tana É—aga mata hannu har suka fita.

"Baby, na shiga cikin ruɗu! Wannan soyayyar da abokinka yake nuna ma ƙanwarsa na aure ne ko jinintaka?" Ta yi masa tambayar daidai lokacin da majgadi ya rufe get ɗin gidan.
Chapter 20 · 0% Book details