Sashe 27
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin haka ta fara tafiya da sauri har ta kamo shi.
Daga gurin da ake sayar da kayan maƙulashe gurin shaƙatawa ya kai ta.
Tana son ta yi masa maganar su koma gida, amma in ta buÉ—e bakinta sai ya tsareta da idanunsa, masu kama da an zuba zaiba sai ta kasa cewa komai.
Ganin an ɗauki lokaci suna gurin, kuma ga Najib sai kiran sa a waya yake yi, wanda daga ƙarshe ya kashe wayar ya yi gabakiɗaya.
Wayar Hilah ce ta yi ƙara alamun ana kira. Da sauri ta duba mai kiran. Kamar yadda ta ayyana Ummu ce. Ilai kuwa ita ce.
Da sauri ta kanga wayar a kunnenta."Kina ina tun rana ban ganki ba, kacaniyar biki ya É—auke mini hankali, ban lura ba ki cikin gidan ba, sai yanzu da na zo É—akinki?"
"Na raka ƙawayena ne Ummu." Ta shirga mata ƙaryar hakan, tana kallonsa da hankalinsa ya ɗauku gurin tuƙi kuma yana sauraren mai za ta ce.
"Ok, to ki yi sauri ki zo ina nemanki."
"To Ummu." Ta faÉ—a tare da ije wayar.
Waiwawo ta ya yi yana kallonta, daidai lokacin da take share sauran hawayen da yake maƙale a fuskarta.
"Ya kamata ki wanke fuskarki in da hali ki yi make up kar Ummu ta gane halin da ki ke ciki."
Babu musu ta buÉ—e jakarta, ta É—auko kayan kwalliyar wanda ganin haka ya yi parkin tare da kashe motar.
Fita ta yi zuwa waje ta wanke fuskarta ta fito
A ƙofar gida ya ije motarsa ta shiga ciki shi kuma ya yi bangarensa.
Najib da yake zaune cikin tsananin ɓacin rai, da waya a hannunsa. Layinsa yake ta gwadawa amma a kashe.
"Ba ka da hankali ko Huwais? Shin ka san abin da ka aikata yau kuwa? Wannan wulaƙancin da ka yi mana, ko ni kaɗai ka yi wa da na san halin da kake ciki ba zan ji daɗi ba." Najib ke magana cikin tsananin ɓacin rai yana kallonsa da ya buɗe ƙofa ya shigo.
Shiru ya yi masa, ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa kan kujera ya zauna jaɓar tare da sakin ajiyar zuciya ya dafe kansa.
"Ina magana ka yi shiru? Wallahi ji na ke kamar na rufe ka da duka, saboda takaicin abin da ka aikata. Just see the time, this isn't good."
Jajayen idanunsa ya watsa masa, tare da miƙewa bai ce masa komai ba zai wuce.
"Sam bana jin daɗin abin da kake mini da halin da ka sanya kanka. Ya kamata ka farka da ga mafarkin da kake yi. Toxarcin da kake yi wa yarinyar nan ya isa haka. Ta bani tausayi da ta kira ni tana kuka. Don Allah ka tausaya mata ka amshe ta a matsayin mata, domin aurenku an riga an ɗaura yanzu tana da haƙƙi mai girma a kanka."
'"Please, I need my space." Ya ce tare da yin hanyar É—akinsa yana tangaÉ—i kamar wanda ya sha giya.
Najib takaici da ya ibe shi gabansa ya sha.
"I will inform Ummu, Huwais. Bana son ka kai ni iya wuya, domin zan sanar mata da duk abin da ke faruwa. Haka kawai ka sanya wa kanka damuwa da Hilah, don Allah kaÉ—ai ya san halin da take ciki.".
"Then go ahead." Ya ba shi amsa tare da kaucewa, zai shige É—akin duk da cewa ya ji tsoron abin da ya faÉ—i.
Tsaki ya yi, tare da kaucewa ya ba shi hanya ya shige ɗakin ya rufo ƙofar garam
Sharaf! Ya faÉ—a gado yana mai da numfashi, yayin da cikin zuciyarsa Allah kawai ya san halin da yake ciki.
"Ya kamata ka miƙe ka shirya ka san dinner ɗin nan ya kamata a fara da wuri."
Tsaki ya yi tare da janyo wayarsa yana kiran numbar Hilah ba tare da ya tanka masa ba.
"Hello, ƙanwata." Ya furta cikin sanyin murya.
"Na'am Yayana," Ta bashi amsa tare da saukar da zafafen hawaye a ƙuncinta.
"Har yanzu kuka kike yi ko?" Ya yi mata tambayar kamar yana ganin hawayen.
"A'a, kawai ina jin zuciyata kamar za ta fashe in har na tuna da cutar da zuciyata da ya yi."
"Ba na yi miki alƙawarin nemo miki shi ba, ko kina tunanin ba zan iya share miki hawayenki ba?"
"Ina jin babu daÉ—i ne, amma na san kai Yaya ne da ya cike ko wane gurbi."
"To shikenan, ki daina kuka ki ci abinci ki kwanta."
"To, amma sai dai bana jin zan iya cin komai. Yaya Huwais, yau rana ce mafi daraja. Ranar da kake yin aure ya kamata ace na fi kowa farinciki, amma sai na tsinci kaina akasin haka. Ina maka murnan samun abokiyar rayuwa, Allah ya ba ku...."
"Ina fatan Ummu, ba ta yi miki faÉ—a ba?" Ya katse ta yana faÉ—in haka don ba ya son maganar.
"Eh, saboda yau tana cikin farinciki matuƙa, saboda kallonta ka yi kawai za ka tabbatar da hakan."
"To ki ci abinci kisha magani ki kwanta, ko na zo na baki? Na san ba kya son magani."
Dariya ta yi." Kai haba! Gidan a cike yake Yaya, zan sha da kaina."
"Ok, to ki kular mini da kanki. Ni ma wanka zan yi na samu na kwanta."
"Yaya, dinner É—in fa..."
Katse wayar ya yi jin tambayar da za ta yi masa.
"Wallahi inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan." Cewar Najib cikin tsananin ɓacin rai.
"Tun da aka fara shirye-shiryen bikin ka ban huta ba Huwais! Wannan ko ni zan ƙara aure iyakan wahalar da zan yi kenan. In ba ka tausaya mini ba, ka tausaya wa matata da ke fama da laulayi. Ƴan matan amaryar kamar za su yaga ni, suna tambayata inda na ɓoye ango. Yanzu kuma sai ka ce ba za ka je dinner ba?"
Jin ya yi shiru yana kallon wayarsa wanda ya tabbatar hoton Hilah yake kallo, ya sanya shi fara duba contacts a wayarsa yana ƙoƙarin nemo numbar Ummu.
"Ba zan ɗora wa kaina wahala ba. Kai da aure ni da shiga damuwa. Ummu zan kira na sanar mata da wulaƙancin da kake yi a wataƙila ta sanya ka kaje."
"Bana son wulaƙanci Ummun za ka kaiwa ƙarata?"
"To ya kake son na yi Huwais? Kai ma ka san iya rufa maka asiri ai na yi."
"Bana jin zan iya halatar dinner É—in. Xuciyata xafi take yi na yaudararta da na yi. Halin da ta shiga yau na ji babu daÉ—i da tsanar kaina."
"I warned you! Na gargaɗe ka several times, amma ka ƙi saurare. Don haka yanzu kai za ka ji da lamarin ai dama duk tsuntsun da ya ja ruwa, shi ruwa kan duka. "
"Bari na yi wanka na shirya na je, amma duk abin da ya faru ka yi kuka da kanka." Ya ƙarashe maganar tare da shigewa bayi.
Najib ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi, domin ya ƙosa a kammala bikin ya huta da kiran Wajnah.
Bayan ya fito ya shirya cikin shadda mai kyau. Kayan sun amshi jikinsa sai ƙyalli yake yi..
Wayarsa da ke kan dressing mirrow ya É—auka. Numbarta ya kira tare da kanka wayar a kunnensa.
"Yayana, kuma angon Anty Wajnah." Ta furta da dariyarta ƙasa-ƙasa wanda ya san ta yi ne don ya ɗauka babu abin da le damunta.
"Kina ina?" Ya yi mata tambayar yana sanya handsfree a wayar ya ije ta kan gado yana É—aura agogo.
"Ina harabar gida ni da su Umnah da Yaya Naufal za mu tafi."
"Ki jira ni yanzu zan fito mu tafi a motata."
Jin abin da ya ce ya sanya ta zare ido da sauri.
"Ka rufa mini asiri! Ango kake yau. Kamata ya yi ka je ka É—auki Anty Wajnah ba ni ba."
"Na damu da halin da kike ciki ne kina buƙatar na..."
"Am ok Yaya, karka damu ka je ka É—auko ta, kuma in har Ummu ta ji a motarka na tafi za ta yi..."
"Kin..."
"Please Ya Huwais, I insist!" Ta furta cikin muryar shagwaɓa.
"Kashe wayar ya yi da jan tsuka mai ƙarfi.
"Ƙanwarka ta fi ka hankali da sanin abin da ya kamata, ko da yake kai kasan kana cikin haukar soyayya shi ya sa." Najib ya ce tare da ɗaukar wayarsa ya yi masa tsaye aka don ya miƙe su tafi.
Bisa dole ya miƙe suka tafi. A motar Najib ne suka tafi.
Tsananin ɓacin rai ya ninku kan kyakykywar fuskarsa.
"Na gaya maka ba zan je a É—auko ta da ni ba, amma shi ne za ka kawo ni gidansu?"
"Don Allah karka kunyata yarinyar nan a gaban ƙawayenta." Najib ya ce ba tare da ya amsa tambayarsa ba.
Ƙara tsuke fuskarsa ya yi yana danne-danne a wayarsa, ganin ta fito ita da ƙawayenta.
"Amarya ba kya laifi." Cewar Najib bayan ya fito ya buÉ—e mata bayan mota.
Murmushin yaƙe ta yi, yayin da burinta ta yi tozali da angonta wanda tun da aka fara hidimar bikin ba ta ga ƙewarshi ba.
Wani wawan ajiyar zuciya ta saki, lokacin da ta hango shi a hakimce yana danna wayarsa tamkar basarake.
"Ni ban san wane irin mutum bane angon nan, sai rowarshi ake magana. Bari dai na ganshi sai na gane ko kina ɓoye shi ne don kar ayi miki ƙwace."
Ƙawarta Hindatu ta furta tare da duƙawa cikin motar.
Da sauri ta ɗago kanta, don ya firgitata musamman yadda ya haɗe girar sama da ƙasa babu fara'a.
"Wai wannan miji na ki ai dole ki yi rowarshi.Kyawu kamar shi ya yi kansa." Ta ce tana mamakin inda ta samo shi duk da ita ma Wajnah ba baya ba, domin har ta fishi hasken fata. Sai dai na shi zallar kalar fatar ce, ita kuma tana haÉ—awa da shafe-shafe.
A hankali ta shiga cikin motar, tamkar ba ta son ta shiga. Kallonsa ta ƙara yi tana jin kamar ta ji ta a ƙirjin shi yadda ya yi kyau.
Wani irin wawan ajiyar zuciya ta furta ganinsa domin Allah ya jarabce ta da ƙaunarsa.
Najib ya rufe motar yana faÉ—in,"Ku shiga ga motoci nan birjik sai mun haÉ—u a gurin dinner."
"No, bamu buƙatar mota saboda ina da tawa." Cewar Hindatu tana wani yauƙi.
Shiga cikin motar ya yi jin abin da ta ce.