Sashe 25
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Gaya mini Hilah in har mahaukacin masoyi ya bayyana yana da mata zaki aure shi?"
"Mai yasa ka tambaya Yaya?"
"Saboda ni ma na gane, in har wacce nake so ta ji ina da mata za ta iya aurena." Ya ba ta amsa jin tambayar da ta yi masa a maimakon amsar wace ya yi mata.
"Eh, zan iya aurensa saboda ina matuƙar sonsa, zan auresa matuƙar ya cika duk sharuɗan, da ya kamata na aure shi a addini ban damu ba."
Da fari murmushin jin daÉ—i ya yi, amma da ya ji ta ce sharuÉ—a, sai ya tuna da matsayinsa a gurinta, wanda ya faÉ—ar masa da gaba.
Ba tare da ya ce komai ba, ya kwanta a kan kujera bayan ya ɗora filo a samar ƙirjinsa.
Bayan ta gama gyaran ɗakin ta ja masa ƙofa ta fice ganin bacci yake yi.
Ya rage saura kwana biyu biki, Hilah ta cika da matuƙar murna. Shirye-shiryen haɗuwa fa mahaukacin masoyi take ta yi.
Ta je ta gyara kanta, ta yi ƙunshi mai matuƙar kyau. Sannan har dilka ta sanya aka yi mata. Duk lokacin da ta shigo masa tana murnar zasu haɗu da mahaukacin masoyi sai hankalinsa ya ƙara tashi.
"Yaya, zan É—auko maka hotonsa, na san zai kasance kyakykyawa kamar kai." Ta furta mishi lokacin da take bashi indomie da ta dafa masa.
Murmushin yaƙe kawai ya yi masa, amma yama jin babu daɗi sosai.
"Ya ce zai gaya mini sunan shi, kuma na san cewa sunan yana da daɗi. Ni fa ina jin kamar na sanshi, domin na tana zuwa gasar musabaƙa ƙawata ta ce wani matashi ya tambaye ta sunana da inda nake. Jikina yana ba ni shi ne."
"Huhm!" Ya ce cikin damuwa yana mata kallon tausayi.
Miƙewa ta yi ta ce,"Yaya, bari na je na yi wanka. Za muje walima gidan su Anty Wajnah."
ÆŠaga mata kai ya yi ta fice tana É—aga masa hannu.
Siraran hawaye masu tsananin zafi suka wanke masa fuska." Haƙiƙa na zama mayaudari, kuma na biyewa zuciyata na sanya ƙanwata cikin wani yanayi. Ban san ya ya za ta ji ba, in har na ƙi zuwa." Ya furta maganar cikin nadama da damuwa.
"Ka yi kuskure Huwais, tun farko sai da na gargaɗe ka da hakan, babu abin da zai haifar sai ɗa mara ido." Amin ya furta cikin wayar ransa a ɓace.
"Ban san ya zan yi ba Najib, ko na yi ninyar daina kiranta, sai na ji ba zan iya rayuwa ba in ban ji muryarta ba." Ya furta jin abin da ya ce.
"Ka daure ka karya layin, sannan ka daina kiranta ka rungumi matarka da za a aura maka. Wajnah na da kyau za ka sota. SheÉ—an ne ke yi wa rayuwarka ingiza mai kantu don ya kai ka duniyar nadama."
"Kana da gaskiya Najib! Kuma in sha Allah zan bi shawarar ka." Ya ce tare da rintse idanunsa da suka yi masa nauyi.
Rana ba ta ƙara, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. A yau ranar Juma'a ya kasance family ɗin gidan Alhaji Nadabo suke cikin matsanancin farinciki. Ganin dubban mutanen da suka fara zuwa don halarta bikin Huwais da Wajnah.Kowa fuskarsa ɗauke da farinciki. Gurin ya cika maƙil da manyan mutane. A masallacin Juma'a za a ɗaura auren, daga nan sai a wuce gurin cin abinci.
Abu zuciyarsa fara ƙal tamkar gonar auduga. Sai haba-haba yake da mutane yana tarbarsu cikin karamci.
Ummu kuwa tafi kowa murna, domin ji take babu wanda ya kaita farinciki. Tun safiyar sai dai kawai ta ji hawaye sun zubo mata na farinciki. In ta tuna dargar da ya sanya ta da tashin hankalin da ta fuskata kafin bikin, da ƙalubalen da ya rinƙa faruwa sai kawai ta zube ta yi sujjada shukuriya. Shikenan daga yau ta huta Huwais ba xai ƙara sata damuwa ba, don ta gama yadda sha'awace take damunsa wanda kuma ya ɗora kan ƴar'uwarsa.
A ranta duk ta ƙosa a ɗaura auren ya tattara ya bar mata gidanta.
Najib ne zaune a cikin ɗakin Huwais, da sauran abokanansa suna ta fama da shi ya shirya, za su inda suka kama don masaukin baƙinsu bayan ɗaurin auren amma ya ƙi.
Cikin ɓacin rai Taufiƙ ya kalle shi,"Wannan abin da kake yi sam ba ka kyautawa Huwais, ni wallahi zan iya yarda da aljana da aureka, saboda babu yadda za a yi ka kai har wannan lokacin baka yi aure ba." Ya tsagaita ko zai ce wani abu, amma sai ya ga ko kallon arziki bai samu ba.
"Please, ka tashi."
"Ka barni domin babu inda zan je."
Caa suka yi masa ganin ya ƙi tashi ya yi wankan ballanatana su sanya ran za shi.
Banza ya yi dasu, yana ta tunanin halin da Hilah za ta shiga, in har ta kira wayarsa ta ji a kashe, domin saura minti talatin lokacin da suka sanya za su haÉ—u ya cika.
Ganin sun kaɗa sun raya, amma ya ƙi tashi sai Najib ya kalle su ya ce,"Ku ƙyale shi na san wanda za ta sashi ya yi wankan."
Wayarsa ya É—auko tare da fara neman numbar ta. Huwais ya É—auka Ummu ce har zuciyarsa ta fara bugu.
"Yauwa, ƴar halak ƙin ƙi ambato." Ya furta lokacin da ya ji muryar Hilah na yin sallama.
Jin an bata damar shigowa ya sa ta shigo cikin natsuwa.
Gabakiɗaya idanunsu suka hau kanta. Wani irin tsau ta ji tare da kunya ta lulluɓe ta.
Kanta ta duƙar ƙasa cikin sanyaruar murya ta gaishe su.
"Wow! Huwais ƙiri-ƙiri ka hana ni auren ƙanwar nan na ka." Ya furta yana mata kallo tamkar zai cinyeta.
Zumbur ya miƙe cikin ɓacin rai ya ce,"Ba na hanaki shigowa ba in na yi baƙi?"
"Ka yi haƙuri Yaya, zan tafi ne kuma ina ta kiran wayarka ba ka ɗaga ba."
Muryarta ba shi kaÉ—ai ba, duka mutanen É—akin sai da ta É—auki hankalinsu.
Sai a lokacin ya tuna wayarsa, na cikin bedroom É—insa, tun safe da Wajnah ta kira ya yi wurgi da wayar.
Hannunta ya ja cikin tsananin jin haushin yadda suke kallonta. Bedroom suka shiga.
"Kai anya na taɓa ganin mace mai kyau irin ƙanaar Huwais?" Adnan ya faɗa shakku.
"Dole ya rinƙa kishinta sosai. Wannan fulawar tun da babu aure a tsakaninsu, dole ya kula da wanda zai ba shi ya amanarta." Sudais ya ce.
"Yayana, zan tafi saura minti ishirin mu haÉ—u da mahaukacin masoyi."
Idanu ya zura mata na tsawon lokaci ya kasa cewa komai. Kwalliyar da ta yi da kyaunta, suka tafi da imaninsa. Ji yake kamar ya rungumeta ta rarrashe shi.
"Har kin yadda da shi, da ya ce zai zo? Gani nake kamar yaudararki yake yi. Kuma in har da gaske yake yi gida ya kamata ya zo. Ki haƙura da shi ki manta shi a cikin rayuwarki."
Raurau ta yi za ta yi kuka, sam ba ta son ya hana ta tafiyar."Don Allah ka barni na je, ni da Afrin zamu. Kasan Ummu ta hana ni kula sa, matuƙar ta ji ina tare da shi ranta zai ɓace."Ta ƙarashe maganar tare da kama hannunsa.
"Ok, ni ban ce kiyi mini kuka ba." Ya ce yana xare hannunsa.
"Yauwa Yayana, sai na dawo. A É—aura aure lafiya."
Tsaya ya yi, tare da zura hannunsa a cikin aljihun wandon, kayan baccin da yake sanye da su ba tare da ya ce mata komai ba.
Har ta buɗe ƙofar za ta fita, sai kuma ta tsaya tare da ƙare masa kallo.
"Yayana, ango sukutum guda bai yi wanka ba?"
Æata fuska ya yi, jin abin da ta ce tare da gyara tsayuwarsa.
"Yauwa, gara ki san ya shi ya yi wankan, domin tun ɗazu muke fama da shi, ga kayan shi can wanda Affan ya kawo ya ƙi sakawa." Cewar Najib da ya shigo.
Æata fuska ta yi tare da kama hannunsa."Don Allah ka yi wanka..."
"Je ki kar ki ɓata masa lokaci kinga lokaci ya kusa."
"Pleas.."
"Hilah, ki je na yi miki alƙawarin zan yi."
"Promise?"
"Sure," Ya ce mata to sai ka shiga bari na haÉ—a maka ruwan wankan.
Da sauri ta nufi bayinsa, wanda ko minti uku ba ta yi ba ta fito.
"Yayana, na haÉ—a maka. Ka yi mini addu'a zuciyata na bugu."
"Fatan alkhairi sis." Ya furta cikin wani irin yanayi.
Ba tare da ta kula ba ta fice da gudu.
Kallon ƙofar da ta fice suka yi." Ka cutar da yarinyar nan Huwais! Shin me kake tunanin za ta ji in har ba ta gan shi ba?"
"Za ta ji babu daɗi na yi kuskure, amma yanzu zan tura mata da tsaƙon haƙuri, kuma ba zan ƙara kiranta ba."
"Hakan shi yafi,"
Da ya shiga cikin bayin sai ya tura mata da tsaƙo kamar haka;
Ina ba ki haƙuri bisa laifin da na yi miki. Haƙiƙa na cutar dake, amma soyayyarmu ba za ta yiwu ba.In a roƙon ki yafiya don a yau zan bar Ƙasar nan ki yafe mini na ɓata miki lokacin da na yi. Sai dai ina son ki sani ina matuƙar ƙaunarki daga Muhammad na ki.
Sai ya tura hoto wanda daga baya ya goge.
Wayar ya ije cikin ƙunci sai kawai yaji hawaye na zubar masa a ƙunci.
"Da gaske ba zan auri Hilah ba za ta zamo mallakin wani? Innnalillahi wa inna ilaihir raju'un!" Ya furta a cikinn zuciyarsa.
Wankan ya yi, sannan ya shirya cikin tsadaddiyar shadda. Haƙiƙa ya yi kyau duk da ramar da ya yi bai hana shi kyawu ba.
Yana shiga cikin gidan, abokan wasa suka yo kanshi wanda ko murmushi ya kasa yi musu.
A mota Hilah da take tuƙi cikin rashin natsuwa ta waiwayo ta kalli Afrin ta ce,"Har yanzu gabana faɗuwa yake yi, ji na ke kamar a mafarki zamu haɗu, da mahaukacin masoyina. Ko ya ya haɗuwarmu zai kasance? Ina fatan wannan haɗuwar ya zama sanadin da zai jagoranci zamanmu a inuwa ɗaya."
"Amin," Afrin ta ce cikin zaƙuwa, domin ta ƙosa ta ganshi wanda ya sanya ta fara samun saɓani da ƙawarta.
Parking suka yi ta tsaya tare da fitowa. Ganin babu motarsa a inda suka yi za su haɗu ya sa ta jingina da motar ta ɗan bashi lokaci ƙila yana hanya.