Sashe 36
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sashinsa suka shiga, inda suka same Hilah da su Azerh suna ta kallon hotunan biki. Shi kuma hankalinsa na kan wayarsa, yana duba chatts É—in da suka yi a matsayin mahaukacin masoyi, yana murmushi sai kuma ya É—ago ya kalleta ya girgiza kansa.
"To ni zan wuce, don Allah ku rinƙa haƙuri kar ku ɓata zumunci." Ta ce tana kallonsu duka.
"In sha Allahu Anty Sauwama, Allah ya kiyaye hanya." Ta ce mata cikin sakin fuska kamar babu abin da ya faru.
"Hilah ku tashi muje."
"Ki barsu mana na kai ki, zuwa anjima sai su koma."
"Ƙafata kafarsu tun da ka ga Ummu ba ta so zuwan ba."
"Ni ma zan biku." Cewar Wajnah tana kallonsa da tun da ta shigo bai kalle ta ba.
"To ka ji Huwais ta raka ka sai ku dawo tare?"
"Ina da inda za ni." Ya faÉ—a fuska a É—aure tare da hanyar waje.
"Ki yi haƙuri da kanshi zai kaiki kin ga duka jiya aka kawo ki, kuma mutane ma ba su gama watsewa ba, sannan ki xama mai biyyaya kin ji?"
"To,"Ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa ta bisu zuwa waje.
Abu da ya koma ɗakinsa wayarsa ya ɗauka ya yi kiran Ummu. Shi kansa lamarin ya rikirkita shi tare da tabbatar da zargin Ummu, wanda yake ƙoƙarin ƙawar da zargin da yake yi.
Ummu ce ta shigo fuskarta a É—aure ta zauna a gefensa.
"Ni kaina na fara tunanin abin da kike zargi."
"Tun tuntuni na ke gaya maka a ɗauki mataki tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada."
"Amma yaron nan ba shinda hankali. Wane hauka zai sa ya rinƙa kallon ƴar'uwarsa da kallon soyayya. Tuntuni na ke ganiin haka daga gare shi, amma sai na watsar da batun."
"Wataƙila dalilinsa na ban shayar da Hilah ba..."
"Kan me zai É—auki wannan a matsayin hujja har ya fara sonta? Yana gani ko Umnah ciwon mama bai bari an shayar da ita ba. A gaban idanunsa aka yi cikinta kuma aka haife ta. Yaron nan ba shi da hankali. Tun kafin ya ja mana abin kunya, ayi mata aure kawai xan sanar da Hamad ya turo ayi auren in ya so ya kama mata haya in ta gama karatun su koma Kaduna."
"Hakan shi ya fi. Tuntini na ke gaya maka ka É—auki mataki. In aka yi musu aure hankalinmu zai kwanta."
"In sha Allahu, zan kira mahaifinsa na yi masa magana, amma kafin nan ya kamata mu kira shi Huwais É—in, sai mu sanar mishi da za a sanya mata rana, in ya so sai muga yadda zai yi."
"Wane hujja kake son ka tabbatar? Karka manta haukar da ya yi lokacin da Hamad ya nuna yana sonta kuma aka bashi damar ya rinƙa kiranta sau ɗaya suna gaisawa."
"Duk da haka mu ƙara kwatanta sa mu gani."
Bayan ya dawo da su gidan Najib ya wuce. Yana ganinsa ya kwashe da dariya suka tafa.
"Ango kasha ƙamshi."
Tsaki ya yi jin abin da ya ce sai ya zauna yana kallonsa.
"Ina madam? Ta kawo mini abinci yunwa na ke ji."
"Ikon Allah! Ango kamarka yana É—auke da yunwa."
"Hmmmh! Ba za ka gane bane. Yau korar kare Ummu ta yi mini ni da gidammu."
"Dama ta haÉ—a maka da duka, saboda na tabbata ba yunwa ya kai ka ba."
"Kamar ka sani, amma ai a banxa nama na jan kare. Saboda ita wacce na je gani tare muka koma gidana."
"Hmmmmh! Iska na wahalar da mao kayan kara." Ya ce yana ƙoƙarin kunna tibi.
Banza ya yi da shi daidai lokacin da Samahatu ta fito daga kicin.
"Baby, kamar ango na ke gani."
"Shi ne ba gizo idanunki suke miki ba. Ki taimaka masa da abinci karya mutu."
"Haba! Mai amarya guda yake neman abinci. Ko da amarya na hutun girki, ai ya kamata a restourant za su yi oder.
"Ki taimaka masa, ƙila kuma amaryar ce ya yi mata laifi ta yi masa horar yunwa." Harararsa ya yi, ba tare da ya ce komai shi kuma yana dariya.
Abincin ta kawo masa sannan ta shiga cikin É—akinta.
"Ina fatan jiya ka bai da kai bori ya hau? Saboda yadda na ga amaryarka jiya, na san cewa ba za ta yi wasa da wannan ranar ba."
Ƙaramin tsaki ya ƙara ja."Ni kuma da yake shashasha ne sai na biye mata ko? Kana ganin irin iskancin da ta fara yi mini. Kulle ƙofata na yi, domin mace mai arha ba ta birgeni."
Takaicin abin da ya faÉ—a ya kama shi."Arha fa ka ce Huwais? In kai ba ka kai kanka ba sai ta kawo matarka ce fa."
"Please, don Allah ni ban zo gidanka ba don ka dame ni da surutu. In kuma abincin ne ba ka son na ci sai ka gaya mini."
"Gaskiya ce dai ba ka so, amma kuma dole a matsayina na abokinka, na tuna mala da haƙƙin da ke kanka."
Ture abincin ya yi yana harararsa."Ga abincin ka nan sai ka cinye, ai na lura dama ba ka so a kawo mini ba." Ya faɗa tare da miƙewa zai fice.
Dariya ya yi tare da kama hannunsa bayan ya miƙe."Ka dai ƙoshi amma ai na san ba za ka yi fushi ba, saboda ba ka wasa da abinci."
Tare suka fito yana ta bashi baki kan ya yi haƙuri su zauna lafiya.
Bayan ya fita daga gidan sai ya ji baya son komawa gida. Sam ba ya ƙaunar ya ganta a cikin gidan. Gidan abokinsa Isma'il ya wuce. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya kwanta. Da yake ba shi da mata. Bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi.
Wajnah bayan fiyarsa, tun tana sanya ran xai dawo da wuri har ta cire. Tana kwance a falo da wayarta a hannunta cikin ɓacin rai.
Baƙin da ta ke yi suka ɗan rage mata damuwar da take ciki.
Sallamar su Wahida ya sa ta miƙe da sauri ta tare su.
"Amarya ba kya laifi." Suka haÉ—a baki gurin faÉ—in haka.
Taɓe bakinta ta yi, sannan ta shiga kicin ta kawo musu snaks da drinks
Hira da ta yi daÉ—i daga falo suka koma cikin É—aki suka yi É—are-É—are kan gado.
"Wai ina angon ne? Tun da muka shigo bamu gansa ba, irin maganin da kika sha, ai kamata ya yi yanzu yana maƙale dake." Ta faɗa tana kallonta
Ƙaramin tsaki ta ja sannan ta yi ƙuta ta ce,"Ya fita tun ɗazu nake jiransa amma shiru. Ni fa ina cikin damuwa, saboda gabakiɗaya hankalinsa ba shi a gareni."
"To tsayawa xa ki yi kina gani ya wulaƙanta ki? Zagewa xa ki yi ki nuna masa ke wayyayace ƴar boko. Sai ka ce ba mace ba, wallahi in ni ne duk yadda zan yi ya faɗa tarkona sai na yi, saboda yadda kika shirya kanki da zarar ya ɗanɗani zumarki shi ke nan."
"Ba za ku gane ba! Ya ƙi yadda ya kusanta kansa da ni. Jiya fa kulle ɗakinsa ya yi." Ta faɗa tana kallon Maryam da ta gama magana.
"Yau da daddare ki É—auki safaya na makullin É—akinsa, kar ki shiga ki bari sai dare can bacci ya fara É—aukarsa. Ki cire kunya mijinki ne kar ki ji shakkar yi masa komai. In kuma hakan ba ki ci nasara ba, zan siyo miki maganin tada sha'awa ki sanya nasa a cikin abinci, wanda dole shi zai kawo kansa gareki.
"Ba na tunanin zai iya cin abincin da zan girka ba ku san shi bane."
"Shi ke nan zana za ki yi kina kallonsa yana miki ƙwalele?"
"Hmmmmmh!" Kawai ta ce musu.
Ƙara zugata suka yi tare da gaya mata yadda xa ta jawo hankalinsa.
Sun daÉ—e a gidan suna jiran ya dawo, har suka gaji suka shirya gab da magariba suka tafi.
Wajnah ganin bai dawo ba ta rinƙa kirabsa amma ya ƙi ɗauka.
Miƙewa ta yi bayan tafiyarsu ta shiga kicin ta ɗora abinci.
Girki ta yi mai daÉ—i ta jera a dining sannan ta shjga wanka. Bayan ta yi wankan, ta shirya cikin wata doguwar rigar da ta matseta kuma ta yi mata kyau.
Falo ta dawo ta zauna ta kunna kallo, amma hankalinta ba shi a kallon. Ganin ya ƙi ɗaukar wayarta ya santa yi masa text message.
Huwais bai tashi dawowa gida ba sai gab da magariba. A wajen gidansa ya yi parking É—in motarsa ya yi alwala ya shiga massalaci. Ko da aka idar sai ya yi zamansa yana karanta qur'ani har aka yi isha.
Bayan an idar da sallar ya tuƙa motarsa zuwa ciki. Tana jin dirin motarsa ta saki ajiyar zuciya tare da leƙa shi ta windo. Tana kallonsa ya kashe motar ya fito daga motar ya nufo cikin gida.
Sakin labulen ta yi, tana gyara zaman rigarta sai kuma ta ruga da sauri ta É—auko turarenta ta fesa.
Ta fito daga ɗakin daidai da ya buɗe ƙofar.
"Sannu da dawowa baby." Ta furta cikin salon jan hankali tana kallonsa.
Ba tare da ya amsa ba ya ƙarasa shigowa ciki.
"Ya Huwai.." Ta daina kiran sunan ganin ya shige É—akinsa.
Fara diddira ƙafafunta ta y,i cikin takaici tana zaginsa a zuciya. Haƙuri ta bawa kanta ta jera abincin a faranti ta ɗauka ta nufi ɗakinsa.
Da sallama ta shiga cikin falon tana riƙe da farantin abincin. Ganin ba shi a falo ya sanya ta ije abincin ta nufi ɗakinsa.
Murɗa ƙofar ta yi da sallama."Ya Huwais, ga abinci na kawo maka." Ta faɗi tana kallon ƙirjinsa da ya cire rigarsa zai shiga wanka....
"Ke! Ba na hana ki shigo mini É—aki ba? Ma za fita."
"Don Allah ka tausaya mini ni fa matarka ce." Ta furta cikin muryar kuka sai kuma hawaye suka wanke mata fuska.
Ƙaramin tsaki ya ja ya wuce bayi ba tare da ya ce mata komai ba.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸