Sashe 4
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To mene ne amfanin tunanin abin da ba za ka samu ba? Saboda abu physical wanda kake da tabbacin samunsa shine za ka yi tunani akai, amma abin da muka san yafi ƙarfinmu ko mallakin wani ne, tunaninsa babu abin da zai sa mana sai damuwa da ƙunci. Ka cire yarinyar a ranka hasashena yana bani ƙila ita ɗin matar aure ce ko kuma budurwar abokinka. Kaga waɗanɗan Allah ya hana neman aure cikin aure."
"Haka ne kina da gaskiyarki na ga wauta na da na kamu da soyayyarta duk da cewa mutum ba shi yake sawa kansa so ba Ubangiji ne, amma soyayya
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 3
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Haka ne Hilah, kina da gaskiyarki na ga wauta na da na kamu da soyayyarta, duk da cewa mutum ba shi yake sawa kansa so ba Ubangiji ne, amma soyayya wata aba ce da take shiga zuƙata ba tare da umurni ba ko neman izini. Soyayya wata abace da take girmama a zuciyar mutum. Ta canza maka muƙaminka ko da ace Sarkin da yake kan karagar mulkinsa ne, sai ta sanya ga zama bawa ga abocin begenta."
"Na fahimta amma..."
"Wai Hilah abincin duniya kike girka ma wa da kika daɗe a kicin ɗin?" Muryar Ummu ta katse mata maganar da take yi, wanda ya sa ta yi saurin fara ƙoƙarin karɓar tukunyar da yake wankewa suka fara kokawar sai ya gama har ta shigo ta same su.
Tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta domin ba ta yi tunanin yana kicin É—in ba.
Ƙarasowa ta yi cikin tsanannin fushi ta kwashe ta da mari da idanunta da suka firfito tun kafin ta ƙarasa.
Kallonta ya yi zuciyarsa a harzuƙe tare da dafe ƙuncinsa domin ya gwammace ace shi ta mara ƙila marin zai fi masa sauƙi.
'Haba Ummu! Kan me za ki mare ta bayan ni nake da laifin na zo har inda take?"
Ko za ka rama mata ne eh? Saboda na ga yadda kake cika kamar za ka iya rama mata?" Ta ce masa cikin tsananin fushi.
"Allah karya nuna mini wannan ranar." Ya ce muryarsa a sanyaye.
Sai ta ɗora da cewa ganin bai ƙara cewa komai ba, sai ƙasa da idanunsa da ya yi zuciyarsa na suya.
"Na ga 'yata ce ni na haife ta kuma nake da iko da ita."
"A gaskiya abi da kike yi Ummu bai dace ba kin nuna bambanci a tsakaninmu kuma bayan duk É—aya muke a gurinki. Bayan kina da sani Hadisi ne ingantacce kan bambanta 'ya'ya."
"Ok, ka je waje ka koyo rashin kunya za ka fara yi mini a gaban ƙanninka ko?" Ta tambaye shi tana kallon ƙanninsa da suka yi cirko-cirko Azerh, Umnaah, da Amnaah hawayen tausayin 'yar'uwarsu suke yi.
"Ki yi haƙuri Ummu. Ya Huwais, don Allah ka daina ƙalubantarta ita uwace agare ni." Ta ce cikin muryar kuka tare da durƙusawa sai ta fashe da gigitaccen kuka.
"A'a ki barshi ya yi mini rashin kunya, kin ga sai na san wuyansa ya isa yanka ya kai munzalin da zan kafa doka ya ƙi bi. Tarbiyarku nake dubawa domin boko ba zai sanya na bari ku aikata abin da ba daidai ba. Idan da ƙuruciya a yanzu kun girma ko su Amnaah da Fu'ad ba na barin su cika shaƙuwa sosai ballantana ku da kuka girma kuka mallaki hankalin kanku. Ku ɗin haƙƙi ne a kaina na kula daku, don haka kar ku ga kamar ina takurawa rayuwarku ne" Ta ce musu haka don su daina mata kallon da sam ba ta jin daɗinsa, yayin da fuskarsu take ɗauke da tarin tambayoyin da ba ta da masarsu.
"Ummu, ina da hankali kuma kin bamu tarbiya kar ki bari temptations ya sanya ki zargin 'ya'yanki. Ko da kika ga na fi shaƙuwa da ita ina yi ne saboda ita ce mace ta farko da aka fara haihuwa a gidan, amma bayan wannan babu wani abu saɓanin hakan."
"Munafuki duk mai hankali daga kallonka zai fahimci ƙaunarta kake. Ballantana ni mahaifiyarka da na raine ka na san abin da kake so da wanda ba ka so." Ta ce a ranta a fili kuwa cewa ta yi.
"Na dai gaya maka sai ka kiyaye." Ta ce tare da ficewa.
Ransa ne ya ɓace idanusa suka yi ja sai ya juya ya fice ba tare da ya kalli kowa ba.
Yana fita Ummu da ke ƙoƙarin haye sama ta saki ajiyar zuciya tana jin wani irin tashin hankalin da yana saukar mata da ciwon kai ta nufi ɗakin Abu.
Duƙawa ta yi ta saki kuka sosai wanda 'yan'uwanta suka yo kanta suna rarrashinta
Kuka ta saka masa tare da faɗawa jikinsa wanda hankalinsa ya yi matuƙar ta shi ya fara rarrashinta.
"Yaron nan daga dawowarsa yana son ya cigaba da sani cikin damuwa. Na yi tunanin shekarun da ya É—auka zai sa ya daina haka, amma abin ci gaba ya yi.
"Lafiya mai kuma ya yi?" Ya tambayeta cikin mamaki wanda ya sa ta share hawayenta ta ce,
"Shaƙuwar da bana son yan nuna mata dai yake nunawa. Wallahi bani da kaffara mahaukacin yaron nan sonta yake. Ko a ina ya taɓa ganin an so wacce babu aure a tsakani? I don sonta da ƙyawunta yake ruɗarshi har yake jin ƙyashin wani ya aureta, ai akwai mata waɗanda suka fita kyawu sai ya je ya nema, amma ba wai ya tsaya yana nuna wa 'yar'uwarsa wacce suka fito ciki ɗaya soyayya ba."
"Haba Laila, har yanzu hasashe kike baki tabbatar ba, kuma bai taɓa gaya miki ba. Yana da hankali ba zai aikata hakan ba. Duk kyawun da take da shi ai dole wani ya aureta tun da babu aure a tsakaninku. Ku dai mata kuna da sauran camfar abu don babu komai a tsakaninsu sai shaƙuwa. Tun suna yara ya kamata ki raba shaƙuwar ba wai sai da suka girma ba don hakan zai yi miki wuya."
"Shiyasa na ce ayi musu aure kawai! Tun da ya dawo a haɗa aurensu tare ga Wajnaah har ta gama karatu aiki take yi. Ta yi haƙurin jiransa."
"Eh, zan yi mishi magana amma ita Hilah gaskiya ba yanzu ba sai ta gama makaranta." Ya ce tare da ɗaukar agogonsa zai ɗaura wanda ta taso ta ƙarɓa tana ɗaura masa.
"Ina kashedi da jawo hankalinka da ka da yaron nan ya kasa controlling emotion É—insa ya aikata ba.."
"Haba ke fa uwace don Allah ki daina faɗin haka domin in sha Allahu hakan ba zai taɓa faruwa ba." Ya katseta cikin tsawa wanda ya sa ta yi shiru amma a ranta ita tasan abin da take tunani.
Sai kuma ta ce"Haka ne Allah ya shige mana gaba." Tare da É—aukar wayarta da ba ta san me za ta yi daita ba sai juya ta take yi.
Huwais, zaune a kan kujera cikin ofis É—in abokinsa kuma amininsa Doctor Khair.
Kallonsa yake yana jin bayanin da yake masa wanda ya É—ora da cewa,
"Sam bana shawartarka da ka cigabada shan irin waÉ—annan maganin it been for a while kana sha wanda a shawarce bai kamata ba ace kana sha ba. Duba ga illolinsa da abin da zai haifar nan gaba, saboda za ka kai mizanin da za su zamo maka illa..
Shiru ya yi cikin tunani ganin bai ce komai ba ya É—ora da cewa.
"Please, ka daina shan maganin ɗauke sha'awa ka yi aure. Wata ƙila perception ne kawai na ka kan babu macen da za ka ji feelings a kan ta sai ita. Ta iya yiwuwa negatives ne ba gaskiya bane. Kai namiji ne cikkake mai ba dutse bane, bana tunanin za ka iya kaɗaicewa da mace ba tare da ka ji wani ba. Ka ga ƙila albarkacin auren ya ɗauke maka sha'awarta da ƙaunarta, don ƙila sheɗan ne yake saƙa maka hakan don ya yi nasara a kanka ka aikata ba daidai ba, saboda tun da nake ban taɓa jin wanda ya kamu da son yar'uwarsa biologically.
"Ya zan yi, ya kake son na yi Khair? Ba ka san abin da nake ji game da ita ba shi ya sa kake cewa haka. A irin yadda na ke jin sonta sai zuciyata take kitsa mini akwai lauje cikin naɗi, amma na kan kore hakan ina tuna da rayuwarmu bakiɗaya. A gabama aka haife ta na raine ta ta girma. Ni na san soyyayarta ita ce ƙaddarata wace za ta kai ni kushewata lokacin abai yi ba." Ya ƙarashe maganar cikin murya mai rauni tare da saukar hawaye masu zafi kan ƙuncinsa.
"Yanzu me kake son yi?" Ya tambayesa cikin tsananin tausayinsa na jararabawar da Allah ya yi masa.
""Ban sani ba! Ni ma ban sani ba." Ya faÉ—a yana watsa hannunsa cikin damuwa sai ya É—ora da cewa,
"Amma sai dai ina jin zuciyata tana bani shawarar da zai iya zama mini ƙadangaren bakin tulu a rayuwata, domin zabbi shawarar da take bani, wataƙila bayan lalacewar lamarin sai na samu mafita a cikinsa. Zanbi makauniyar zuciyata domin samun mafita, duk da ance son zuciya, ɓacinta."
"Karka je ka aikata abin da za ka yi dana sani. Ka amince da aure kawai shine mafita."
Kallonsa ya yi ba tare da maganarsa ta shigesa ba.