← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 40

Sashe 15

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Mun riga mun gama yanke shawara sai ka jira lokaci ya yi. Ka sani a wannan karon sam ba zan lamunta ka watsa mini ƙasa a idanuna, don haka ba za a sanya lokacin bikin da tsawo ba, saboda in har muka biye maka, ban san lokacin da za ka yi aure ba, kuma kullum ƙara girma kake."

Ajiyar zuciya kawai ya saki ba tare da ya furta komai ba, sai kaɗa kansa da yake kamar ƙadangaren kutu.

"Maganar aikin da za ka fara a companyna ya kamata ka fara shirye-shiyen duk da kai za ka zama c.e.o na wurin.

Cikin rashin ƙarfin jiki ya amsa masa wanda ganin yadda ya yi, sai ya ba shi tausayi, amma yi masa auren shi ne kawai mafita a gare shi da su duka, musamman Ummu da kullum take ta da hankalinta.

Shiru suka yi babu wanda yake magana har suka shawo kwanan gidan.

Huwais hankalinsa a tashe yana ta tsaƙawa da kwancewa. Idanunsa suka kaɗa sosao ji yake kamar ya ɗora hannu a sama ya rinƙa ƙwala ihu.

Tunaninsa yadda zai yi rayuwa da wata ƴa mace a matsayin matarsa ba Hilah ba, domin ba ya jin zai iya mallakawa wata gangar jikinsa da zuciyarsa, don an halicce su saboda ita ne, domin matuƙar ta aminta da aurensa aka yi. To tamkar ta siyar da farincikin rayuwarta ne, don gangar jikinsa kawai ta aura, amma zuciya da ruhi suna gurin ƙanwarsa abin begensa, wacce da ita kawai yake jin zai iya rayuwa har ya shayar da ita madarar ƙauna.

Abu kuwa bayan ya sanar masa bai ɓata lokaci ba, ya kira Kawu Sule kamar yadda ya gaya masa aka tura don a tsayar da rana.

Wannan lamari ya yi wa Wajnah daɗi, domin da fari ta ƙi aminta sai take gani kamar mafarki ne. Lokaci guda kuma murnarta ta koma ciki tuna, wancan lokacin da har an sanya rana ya bar ƙasar, saboda haka sai ta rage murna ta bari sai ranar da ta wayi gari ta ganta a cikin gidansa. Tabbas ranar babu macen da ta kai ta sa'a a duniyar nan.

Sai ya rinƙa jin kasa kamar zai rabu gida biyu. Yana isa cikin ɗaki ya faɗa kansa. Wani irin ƙunci yake mamaye zuciyarsa, ganin duk guje-gujen da ya yi wa auren bai hana yi ba.

Kwanciya ya yi yana jin ransa babu daɗi don ƙirjinsa har wani fat!Fat! ya ke yi tamkar za ta fito waje.

Kawu Sule a ranar ya shirya aka je suka ji magana wanda nan take aka tsaida biki wata É—aya. GabakiÉ—aya kowa murna yake yi in ka É—auke uban gayyar.

Zaune suke a dining ana cin abinci inka É—auke Huwais da yanzu ya yi sallama ya shigo.

Sallamarsa ya sanya Hilah da take bawa Umnah abinci a baki ta ije spoon É—in tana kallonta da ya shigo fuskarsa tamkar ta shanu.

Ummu kuwa murmushin jin daɗi ta ji, tuna cewar yanzu hankalinta zai kwanta domin da ya bar gidan shi kenan ba ta da wata matsala da shaƙuwarsu. In kuma sha'awa ke damunsa har yake ɗora ƙwaɗayinsa kan ƙanwarsa auren zai kawo ƙarshen matsala. Don haka hankalinta kwance take cin abincinta don har wani murmushi fuskarta ke ɗauke da shi.

A hankali ya jawo kujerar da ke kusa da Abu ya zauna yana faÉ—in,"Barka da hutawa Abu, Ummu sannu da hutawa." Ya ce tare da ije wayarsa kan dining.

A tare suka amsa sannan ƙanninsa suka haɗa baki gurin gaishe shi. Ba tare da ya amsa ba, ya ɗauki wayarsa jin alamun tsaƙo ya shigo.

Tun da ya zauna gabakiÉ—aya hankalinta ya tashi, musamman da ko kallon inda take bai yi ba.

Miƙewa ta yi za ta sanya mishi abinci, amma sai ya dakatar da ita ta hanyar karɓar serving spoon ɗin ya ce," Thanks." Ya yi maganar ne ba tare da ya yi dubi gareta ba.

Komawa ta yi ta zauna tana kallon yadda yake cin magani, bayan ya saka cokali É—aya na dafadukar shinkafa da ta ji bushashshen kifi.

Wani irin tauna yake mata tamkar yana cin magani, tare da juya abincin filet É—in yana jin kamar guba yake ci, duk da irin daÉ—in da ta yi.

Abu da Ummu duk abin da yake yi suna kallonsa, amma sam ba ta ji wani iri ba, ji take kamar da ma yanzu aka yi auren don ya tattara ya bar mata gidanta.

"Kyakykywar albishir! Duk wanda ya canka zan canza masa waya." Ummu ta ce cikin tsananin murna tana dariya.

"Ummu, ni zan faÉ—a." Cewar Azerhl tare É—aga hannnunta.

"No Ummu, ni zan faÉ—a." ya saukar da hannunta yana faÉ—in haka.

Umnah ce ta miƙe ta isa ga Ummu tana dariya ta ce,"Ni ce Ummu, ni zan cinka." Sai ta kwashe da dariya ganin yadda suka cika falon da ihu.

"Ke Hilah, ba za ki cinka ba?" Abu ya ce yana dariya.

"Abu, ai na ga duk suna son su cinka ne, shi ya sa na bar musu." Kowa ya faÉ—a duk wanda ya canka mota zan ba shi kyau, in kuma Abidin, Naufal da Hilah ne canzawa zan yi.

Jin abin da ya faɗa ya sanya su ƙara saka ihu kowa yana faɗin shi ne har da Hilah.

"To shikenan, bari a fara kan ƙanana sai kowa ya faɗa."

"Ok, bari a fara ta kan ƙanana, Umnah ki fara."

"Abu, zai koma Ummara."

"Ba ki ci ba." Ummi ta ce tana dariya.

"Amnah, ina jin ki."

"Ya Huwais, zai koma abroad."

"Ke ma kin faÉ—i." Ta furta cikin dariya.

"Abu ya canza mana gida." Dariya Abu ya yi.

"Kai ma ka faɗi, saura Abidin." Ya faɗa yana kallon Huwais da ya wani ƙara cin magani, saboda ya san me za su faɗa.

"Za mu yi relocating zuwa abroad." Ya faÉ—a da fatan ya ci.

"No, kai ma ka faÉ—i. Saura Hilah."

Kallon Huwais ta yi ganin yadda baya ko kallonsu, hakan ya sanya mata zargin ko maganar aurensa ne ya tashi, aanda ta san abin da zai sanya shi a cikin mood É—in kenan.

Ta yi shiru kamar ba za ta yi magana ba, tana tsoron kar ta faÉ—i, amma sai ta daure ta ce,"An sanya ranar bikin Ya Ayaan."

"Yes, ta ci." Ummu ta furta tana tafa hannunta wanda jin haka ya sa gabakiɗaya suka miƙe suna ihun murna tare da nufar gurinsa za su rungume shi, har da Hilah da ta manta gargaɗin Ummu saboda tsabar murna da ya cikata.

Da sauri ya miƙe tare da daka musu tsawa."Wannan wane irin sakarci ne? Sai ka ce gidan biki. Ku yi mana shiru."Tsit suka yi suna zare idanu.

Ummu bakinta ta taɓe ba ta ce komai ba ta ci gaba da cin abincinta.

"Ƙyale su Huwais, murna ce su yi, saboda mahimmancin wannan ranar anjima ku shirya zamu fita."

"Yeeeee! Suka haÉ—a baki suna faÉ—i cikin murna.

"Our Ya Huwais, is gonna be married. We can wait to see!" Umnah ta furta tana ihun murna.

"We need to celebrate Anty Wajnah will be part of us! Ya Huwais happy for the engagement." Hilah ta furta tare da miƙa mata hannu.

Saboda tsabar takaici na rashin kishinsa da ba ta yi, bai san lokacin da ya É—aga hannu ya wanka mata mari ba.

Gabakiɗaya falon suka miƙe cikin razana.

"Are you mad! Kanka ɗaya kuwa? Saboda me za ka mare ta?" Abu ya furta cikin tsananin ɓacin rai yana kallonsa da ya haɗa girar sama da ƙasa.

Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba sai kuma ya juya ya fice ba tare da ya damu da kiran da Abu ya ke masa ba.

"Ƙyale shi aure babu fashi." Ummu ta ce tana hararar inda ya wuce.

Abu ya kama hannunta ya zaunar kusa da ita yana rarrashinsa.

A hankali ta miƙe tare da share hawayenta ta kama hannun ƙanninta da suke jin kamar su yi kuka ganin marin da ya yi mata.

Abu ya bi bayanta da kallo tare da farin zargin abin da Ummu ke faÉ—a masa gaskiya ne.

Yana shiga É—aki ya shige bayi tare da sakar ma kansa ruwa. Haushn marin da ya yi masa da ihun murnar da suke yi ya dame sa.

Wani irin haushi ta ya ƙara mamaye shi ganin yadda take murna, sai kuma ya fara jin haushin kansa, saboda tunawa da ba ta san yana sonta ba, kuma dole ta yi murna saboda a matsayin ɗan'uwa ta ɗauke shi.

Ya É—auki tsawon lokaci yana watsa ma kansa ruwa har sai da yaji sanyin ruwan ya fara damunsa.

Tawul ya janyo ya ɗaura iya ƙugunsa sannan ya ɗauki ƙarami yana tsane kansa.

Bayan ya gama tsane kansa, ya shirya kansa cikin doguwar farar jallabiya da gajeren wando, ya zauna a falo yana tunanin yadda zamansu zai yuwu da Wajnah a matsayi matarsa. Yarinyar da sam tsarin rayuwarsa ba ta yi mishi ba, domin ko a cikin Æ´an'uwansa ba ya shiri da ita, saboda yadda take nuna tsantsar wayewarta.

Hannu ya sa ya tallabe goshinsa yana jin yadda tempareco na shi ke hawa.

Hilah kuwa bayan ta shiga É—aki gefen gado ta samu tana zubar hawaye.

Mamakin marin da ya yi mata take yi, don kawai ta taya shi murnar samun iyali da zai yi.

Maganar da ya gaya mata ya faÉ—o mata da ya ce mata yana son wata.

Zubbur ta miƙe tare da ɗaukar hijabinta. Kai tsaye ɗakinsa ta nufa. Yana zaune ta tura ƙofar ta shigo.

Da idanu ya raka ta har ta ƙaraso gefensa ta zauna.

"Yayana!"Haƙiƙa ban kyauta maka ba, kuma na cancanki fiye da mari." Ta yi shiru ko zai ce wani abu sai kuma ta ga ya ƙara cin magani, bai ce mata komai ba, sai juya kansa da ya yi zuwa wani gefen.

Tashi ta yi ta koma gefen da ya juya kansa.

"Yayana." Ta furta cikin sanyin murtasai kuma ta ɗora da cewa," Don Allah ka yi haƙuri."

Ƙaramin tsuka ya ja saboda muryarta ta rikita shi tare da gusar da fushinsa.

Wani irin kallo ya yi mata yana faÉ—in,"Dole ba za ki damu da auren dole da za a yi mini ba, tun da kina tare da mahaukacin masoyinki."
Chapter 15 · 0% Book details