← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 40

Sashe 30

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta miƙe, tare da zura dogon hijabinta ƙasa kasancewar kayan bacci ne a jikinta.

Ba ta yi fargabar fita ba, saboda Ummu tana can da Æ´an bikin da ba su gama watsewa ba.

Hannu ta sanya ta murɗa ƙofar get ɗin gidan, daidai lokacin da ya gaji da jira ya ƙara kira. Ganin ta fito ya sanya ya kashe wayar yana kallonta dusu-dusu da hasken watan da bai gama girma ba ya haska gurin

Da sauri Najib ya fita daga motar ya koma can baya, wanda hakan ya yi masa daÉ—i sosai, ta yadda zai samu damar magana da ita sosai.

Kallon juna suka yi na Æ´an sakanni. Ita ce ta fara cire idanunta ta buÉ—e motar ta zauna a kujerar gefensa.

"Na kasa tafiya har sai na ganki. Ina jin wani iri yau zan bar Æ´an gidanmu da gidanmu na koma rayuwa da wata can."

"Anty Wajnah Æ´ar'uwa ce ba bare ba, ka daina kiranta da wata can." Ta furta tana kallonsa.

"Haka ne, amma ba kamar jinina waÉ—anda muka fito ciki É—aya ba."

"Za ka saba da ita kuma ina gaya maka za ka ji daÉ—in zama da ita."

"Hmmmmh!" Ya ce wanda ya sanya ita ma ta yi shiru ta kasa cewa komai.

"Zan tafi gidana, amma ki sani duk da Ummu ta yi hakan ne don ta nesanta ni da ku, ba za ta yi galaba ba."

"Ummu, fa gata ta yi maka kar ka yi mata mummunar fahimta."

"Zan wuce ki yi mini fata na gari. Ina sonki ƙanwata."

Hannunta ta zare da ya riƙe cikin nasa."Allah ya xaunar da ku lafiya ya baku ingantacciyar zuriya."

Addu'ar da ta yi masa sam ba daɗaɗa masa ba, har ya ji da ya san abin da za ta roƙa masa kenan, da bai roƙi addu'ar ba."

"Shikenan, ki kula da kanki, kuma ki cire tunanin mahaukacin masoyinki za mu yi maganar."

"To Yaya, Allah ya tsare ka gaida Anty Wajnah sai mun zo."

Ba tare da ya amsa ba, ta fito motar wanda ganin haka Najib ya shigo motar suka kama hanya.

Sai da suka biya suya spot, sannan suka siya tare da siyan drinks masu yawa suka kama hanya.

Bayan sun shiga cikin gidan sauran abokannasu da suke jiransa a ɓangarensa suka fito.

Yana ƙoƙarin shiga cikin falon, ya ji darararrakun ƙawayenta wanda ya sanya shi dawowa da sauri ya kalli Najib

"Ba na son shiriritar nan ka gaya ma ƙawayenta su tattara su bar mini gida so na ke na kwanta."

"Kar ka yi mini haka don Allah. Yau rana É—aya ka daure mu sayi baki, sanin kanka al'adace ta Bahaushe don haka kar ka wulakanta matarka."

Jan numfashi ya yi tare da jan ƙaramin tsaki.Tafiya yake yi tamkar ba shi ba har ya shiga cikin falon.

Sallamar su ya sanya suka natsu, yayin da masu gyara zaman gyale su na yi masu ajusting zaman su na yi.

Wajnah kuwa jin siririyar sallamar da ya yi, ya sanya ta É—ago idanunta da saurinta zuba masa.

Wani iri ta ji a cikin ranta yayin da kwalliyar da ta yi ya tafi da imaninta.

Abokannasa suka xauna a sauran kujerar, sai wanda Wajnah take ita kaɗai, wanda hakan ya sanya ba tare da zaɓi ba, ya zauna a kujera.

Zamansa ga sanya ta ji ta rasa natsuwarta gabakiɗaya. Ƙamshin turarensa da saukar numfashinsa suka sanya ta shiga cikin wani irin yanayi.

Lumshe idanunta ta yi, tana jin kamar ta kwanta a jikinsa.

Cikin dubara ta matso kusa dashi ta yadda jikinsu yana gogon juna, wanda yanayin da ta tsinci kanta ta rasa kasa bayyana shi.

Huwais yana jinta, amma bai kula ba sai dabara ya yi ya matsa. Ƙara matsowa ta yi sosai. Ganin ya ƙure kujerar ya sanya shi haƙura a zuciyarsa yana alla-allah a kammala siyan bakin ya kwanta.

Yayin da yake wannan tunanin Wajnah tunaninta ya tafi ga yadda first night ɗinsu zai kasance. Tunanin yadda za ta rama wulaƙancin da ya yi mata za ta yi, domin sai ta bari ya shiga hannu za ta nuna masa ita ma mace ce da ranarta.

Gabakiɗaya ta rasa natsuwarta. Buƙatar mijinta da magungunar da ta rinƙa sha ba tare da ka'ida ba suke ɗawainiya da ita.

Najib ne ya yi gyaran murya tare da buÉ—e taronnda addu'a. Bayan nan sai kuma aka fara tsokanar juna. Duk maganganun da suke yi bai tanka musu ba, duk da cewar a kanshi da Wajnah suke yi.

Wajnar ce kawai ta buɗe baki tana kare shi, da ita wanda hakan ya ƙara ɓata mood ɗinsa, domin ya tabbata da Hilah ce a matsayin amaryarsa, kunya da natsuwarta ba zai sanya ta rinƙa magana haka ba.

Tunaninsa ya yi nisan kiwo gurin tunaninta ya ji muryar Najib na faÉ—in,"To ango, zamu wuce da Æ´an matan, sai na ce asuba ta gari. Ubangiji ya ba ku zaman lafiya da zuriya É—ayyiba. "

Ba tare da ya amsa addu'ar ba, ya miƙe sai ita ta masa da sauri tana faɗin,"Amin,"

ÆŠago manyan idanunsa ya yi, ya kalle ta jin rashin kunyar da ta yi na amsawa, amma bai ce komai ba ya fara tafiya don ya raka su.

Ganin haka ta bi bayansa suna magana da ƙawayenta.

Maryam ta kama hannunta tana faɗin,"Don Allah karki manta asubar fari ki kiramu ki gaya mana yadda daren zai kasance, domin bana jin zan iya bacci, saboda ƙosawa na ji yadda ya kasance. Wallahi kin yi sa'ar miji da za ki more rayuwarki, kuma ki ci duniyar aurenku da tsinke."

"Karku damu da zarar komai ya wakana zan sanar muku conference calls zamu haÉ—a duka na gaya muku, ai sam ba zan yi wasa da wannan ranar ba. Wannan gayen sai na nuna masa iyakansa, domin sai ya zamo tamkar bawa a gareni."

Dariya suka kwashe dashi tare da tafawa.

Najib ya kama hannunsa tare da raÉ—a masa.

"Please, kar ka ɓata muku first night ɗinku. Kana ganin amarya ta shirya duba ga irin yadda take yi kamar ta haɗiye ka. Ka ba ta haɗin kai ku samar mana takwarar Hilah."

Ƙara ɓata ransa ya yi jin abin da ya ce."Zuciyata da gangar jikina na Hilah ce."

Da sauri ya shige motar jin yadda ya yi maganar da ƙarfi domin a tunaninsa wasu sun ji abin da yake faɗi.

Bayan sun fita maigadi ya rufe get, Huwais ya ɗan tsaya a farfajiyar gidan yana ƙarewa gidan kallo.

Tun lokacin da Abu ya fara ginin gidan ya sanar masa da mallakinsa ne. Ya yi buri da addu'ar shi da Hilah xa su yi rayuwa cikinfarinciki a cikin gidan, amma sai dai ya san da wuya gurguwa da auren nesa. Yau ga shi da macen da ya tsana a rayuwarsa fiye da komai a matsayin wacce za su yi rayuaar aure a cikin gidan. Ko ya ya rayuwarsu xai kasance, domin ya san gangar jikinsa ta aura, amma zuciya da ruhi na gurin ƙanwarsa abin begensa Hilah

Rintse idanunsa ya yi ji yake ina ma ace yau ita ce daga shi sai ita a cikin wannan gidan. Da hannunsu na maƙale da juna za su taho. Bayan sun tafi shi zai ɗauke ta har zuwa cikin gidansu. A wannan ranar sam ba xai barta ta rintsa ba, domin zai kasheta da zazzafar soyayyarsa wanda ba zai sa ta manta da wannan rana ba..

Yana cikin wannan tunanin, Wajnah da ta gaji da jiransa ta fara kiran sunansa, amma ta ji ya yi shiru babu amsa. Hannunsa ta kamo tare da kwantawa a kafaÉ—ansa.

"Babyna, ina ta..."

Maganar ta maƙale sakamakon tureta da fara tafiya da ya yi.

Sororo ta tsaya cikin tsananin mamaki. Abin da yake mata yana mugun ci mata tuwo a ƙwarya, musamnan inta duba ta ga babu inda Allah ya rage ta. Duk da cewar ta san namiji ne ingarma a cikin mazaje. Ita ma babu wata makusa a jikinta da xai sanya ya rinƙa wulaƙanta ta, domin duk da cewar ita ba fara sosai bace, amma ta haɗa da na kanti wanda ya ƙara mata haske mai kyau sosai, don ba ta siyan kashama marasa kyau, kuma dama siyen na gari mai da kuɗi gida. Tana da zubin aje bota kalar jikinta kamar fanta. Don da ka ganta kaga jiki duk madara😄😄😄

Idan kuma magana ake ta ƙira, ta kuma ya haɗa duk wani sura da xai jawo hankalin ɗa namiji gareta. Mace ce wacce ta yi amanna da supplements na gyaran jiki masu kyau da in ka sha magani take take siye. Musamman da bikinta ba ƙaramin siye magungunan ta yi ba.

Ƙuta ta yi ganin yadda ya kusa shigewa ya barta. Da sauri ta fara binsa a ranta tana faɗin,"Za ka sani in ka shigo hannu, da xarar ka ɗanɗani zumar jikina za ka manta da ƴar'iskar da take ɗauke mata hankali, domin hatta shegiyar ƴar'uwark da kake so da Ummu sai ta gane ɗanta ya canza."

Da sauri ta buɗe ƙofar falon da ya buga da ƙarfi.

Huwais kuwa cikin ɓacin rai ya buga ƙofar falon ya shige. Yana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinsa ta ya ƙaraso inda yake.

"Haba mijina, ina ta yi maka magana ka yi banxa da ni. Karka manta yau rana ce ta musamman a garemu." Ta faɗa cikin wani irin murya da zai ɗauki hankalin duk wani ɗa namiji tana ƙoƙarin haɗa jikinsa da nata.

"Ke!" Ya daka mata tsawa tare da kaucewa ya É—auki wayarsa.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI
Chapter 30 · 0% Book details