Sashe 14
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ta gama shaanye ruwan mamakin ba kawai ta ga kiransa, wanda saboda tsananin farinciki da mamakin kiran ya sanya ta kasa É—auka.
Miƙewa a zabure ta yi, har tana bugewa da gefen gado, amma ba ta kula ba, ta dawo falo don kar ta tashe su.
"Mahaukacin masoyi ya kira ni? Ko dai mafarki na ke, ko kuma mantuwa ya yi?" Ta tambayi kanta cikin tsananin mamaki, tare da ci gaba da kallon wayar har sai da kiran ya tsinke.
Ganin ya yanke bai sake kiran b,a takaici da jin haushi da kuma wautan rashin ɗaga kiran ya kamata, wanda ba tare da sani ba ta ji hawaye na sintiri a ƙuncinta.
Da sauri ta lalabu layinta da har ta fara bacci.Kiran ya farkar da ita ta miƙe tama mutstsuka idanunta. Ɗaukar wayar ta yi tana mamakin dalilin kiran da addu'ar Allah ya sa lafiya.
"Hello." Ta furta cikin muryar bacci tare da sakin hamma.
"Sahiba! Mahaukacin masoyi ya kira ni."
Jin abin da ta faɗa da kuma muryar da ta yi amfani da ita, ya sanya ta watstsaƙe cikin tsananin mamaki.
"Haba! Da yaushe kuma mene ya ce?" Ta yi mata tambayar a jere.
"Yanzu, amma abin takaici na kasa É—auka har ta katse." Ta furta tamkar za ta yi kuka.
Wani irin baƙincikin da takaici ya mamaye ta jin abin da ta ce, musamman da ba su yi magana.
"To yanzu mene ne amfanin gaya mini, kuma ke da kike jiran wannan ranar, ban ga dalilin da zai sanya ki kasa É—auka ba."
"Tsoro ne da fargaba."
"Bai kamata ki ji ko ɗaya daga ciki ba, tun da kin ji kin gani xa ki iya. Ni wallahi na ɗauka ma kin ganshi a zahiri ne. Ƙila ya ga ɓoye-ɓoyensa ya ga babu amfani zai bayyana kansa. Allah ya sanya ba tsoho bane wanda ya takwarƙwashe."
Takacin abin da ta ce ya sanya ta saki tsaki za ta kashe wayar, daidai lokacin da kiransa ya ƙara shigowa cikin wayar.
"Kashe yana kirana don Allah." Ta furta wanda ya sanya ta daƙile wayar tana mata dariya.
Wani irin kyarma hannunta yake yi wanda ta rasa dalili. Garin ta danna inda ake masa kiran ta kashe, saboda takaici kawai sai ta sanya kuka, tare da jifa da wayar.
Ba a É—auki lokaci ba kawai ya sake kira.Cikin rawar hannu ta yi nasarar danna gurin amsawa.
"Ni mutum ne mai tsananin kishi! Sam ba zan lamunta wacce Allah ya halicce ta don ni kaɗai tana waya da wasu ƙarti suna ji mini muryarta ba." Ta ji muryar ta yi magana cikin wani jrin zaƙi da daɗin saurara a zuciya, wanda ya sanya ta nemi natsuwarta ta rasa.
"Eh a'a ba.... Ka yi haƙuri ba za ka sake kiran wayata ka ji ina waya ba." Ta furta cikin wani salo da muryar da bai taɓa tunanin tana da shi ba, don ko ita ba ta tunanin ta taɓa magana da muryar.
"Ya kamata ki kiyaye domin a kanki zan iya kashe duk mazan duniyar nan, matuƙar za su raɓe ki."
Nauyauyar ajiyar zuciya ta saki tana son inda ta taɓa jin muryar nan, ko za ta gane wane ne mahaukacin masoyinta, amma iya tunaninta ba ta taɓa jin muryar ba.
"Am sorry gimbiyata! Kamata ya yi na yi miki sallama kamar yadda addinimu ya sharanÉ—a, amma sonki da ya yi mimi dabaibayi ya hana ni sukuni da kishinki ya sanya na manta hakan."
"Ok, na fahimta kuma.."
"Ki kwanta ki yi bacci zan kira ki gobe." Ɗif ya kashe wayar yana riƙe da ita tare da sakin tsadadden murmushi.
Sororo ta yi na Æ´an sakanni ganin ya kashe wayar. Halinsa É—aya da ta tsana kenan, nuna isa da yanke shawara ba tare da ya ji ra'ayinta ba, domin ta so ace sun kwana suna waya.
Cikin sanyin jiki ta kwanta a kan gadon ruf fa ciki tana kallon wayar tamkar zai fito a cikin.
"Oh, Allah ka jarrabace ni da soyayyar wanda ban san asalinsa ba." Ta furta cikin hawaye.
Ta yi iya ƙoƙarinta don ta yi bacci, amma ta kasa domin muryarsa, ke yi mata amsa kuwwa a kunenta. Tunani take yi kamar ta taɓa jin muryar, amma duk iya tunaninta ta gagara tuno inda ta ji ta.
Wajnah zaune a ƙaton falonsu da ya sha kayan alatu. Wayarta a hannunta tana dannawa, wanda gabakiɗaya rabin hankalinta na kan wayar, tana duba wasu kaya da ƙawarta ta saro daga Dubai za ta siya.
Kayan dogayen riga abayas da gyaluluwa sai kuma takalma. Bayan ta gama zaɓen kayan ta ije wayarta kan stool ɗin da ke gefenta, tana kallon mahaifiyarta da take zaune da aminiyarta Hajiya Fatiha suna hira.
"Mom, na kammala abincin kuma is ready. Na kawo miki nan ke da Momy Fatiha ko a dinning?"
"No, ki kawo nan sai ko kira Binta ta haÉ—a mini salat ta kuma kawo mini yajin da na siyo jiya."
"Mom, ai na shirya duka har salat É—in."
"Masha Allah! Yarinyar kirki ma za ki kawo mana nan." Mom ta furta tana kallonta cikin so da ƙauna.
"Wai ni Hajiya Fati, ya maganar haÉ—in auren da za a yi da É—an Æ´ar'uwarki? Na ji shiru tun lokacin da za a yi Engagement aka ce biki sai ya dawo daga Turai?"
"Eh, wallahi haka ne. Ai ta nan ɓangaren duk mun shirya, amma shi yaron ne yake wasa da hankalin iyayensa."
"Anya haka ne, ko dai ba sa son haÉ—in ne?" Ta yi mata tambayar tana kallonta.
"Kai bana tunanin Lailah, za ta ƙi auren, saboda duk wani ƙoƙari ita take yi."
"To ai abin ne da mamaki domin ya kamata ace an yi tuntuni."
"Haka ne wallahi kin san komai lokaci ne."
"Eh, amma da zafi-zafi a kan bugi ƙarfe! Saboda samun irin namiji kamarsa sai an tona."
"Haka ne, in sha Allahu za a yi auren."
"Allah ya tabbatar da alkhairi."
Wajnah bayan ta kammala jera musu abincin ta haye sama.
Kan gado ta hau tare da sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Tana matuƙar sonsa amma sam hankalinsa ba ya gareta.
Wayarta ta jawo ta danna nambobinsa da tuni ta riga ta haddace. Sai dai har ta gama ringing ba'a É—auka ba.
"Da ma na san ba zai É—auka ba, Ubangiji ka karkato mini da hankalin bawanka." Ta furta cikin hawaye tare da shiga Whatsapp ta shirya mishi kalaman soyayya ta tura mishi.
A lokacin da tsaƙon ya shigo yana zaune a cikin bedroom ɗinsa yana aiki a cikin laptop ɗinsa.
Tsaki ya yi ganin saboda rashin zuciyarta bayan ƙin ɗaga kiran sai da ta tura masa da tsako.
Ba tare da ya karanta ba ya goge tsaƙon tare da riƙe wayar ya faɗa kogin tunani.
Abu ne zaune a gaban mota suna tafiya. Huwais ne ya ke jan motar cikin natsuwa.
Abu da ya ke karanta magazine na daily trust ya ije jaridar, tare da juyowa ya kalle shi, da hankalinsa yake kan tuƙi.
"Huwais," Ya kira sunan shi tare da gyaran murya.
"Na am Abu,"Ya waiwawo yana faÉ—in hakan.
"Maganar yarinyar nan Æ´ar gidan Alhaji Tukur. Shiru muna ta jiran bayan dawowarka za ka yi maganar bikin ku, amma shiru?"
Jin abin da ya faÉ—a ya É—aga hankalinsa ainun. Da sauri ya waiwaya ya kalle sa cikin tashin hankali.
Ya buÉ—e baki xai yi magana sai ya rasa abin da xai faÉ—a, domin a wannan karon bai san uzurin da zai bayar ba.
"Umh! Eh..."
"Dakata." Abu ya ce masa yayin da lokaci guda fuskarsa ta canza.
"Ka san cewa a wannan karon ba zan lamunci duk wani uzuri da za ka bayar ba ko? Domin in har da na É—auki maganar mahaifiyarka, ba za ka yi tafiyar nan ba sai da matarka?"
"Eh, Abu. Don Allah a wannan karon ina son a ƙara bani uzuri, domin sam Wajnah ba na jin ƙaunarta a cikin zuciyata."
"Kana da zaɓinka kenan?" Ya yi masa tambayar kai tsaye.
"Eh, amma akwai abin da na ke son na tabbatar. Don Allah Abu ka ƙara mini lokaci." Ya faɗa tamkar zai yi kuka.
"Ba ka da wani mafita wanda ya wuce ka amince, domin ba za ka mayar dani ƙaramin yaro ba. Haba, Huwais, ka yi wa yarinyar adalci mana. Tsawon shekaru na wa ta ɗauka tana jiranka."
Ransa ne ya ɓace ya rasa mai zai furta domin shi kasa ya san ba shi da hanyar da zai ce mafita ce a gare shi. Kawai zuciyarsa ce take ƙarfafa masa da kuma tabbatar masa da Hilah ta shi ce kuma watarana zai aurenta.
Ganin ya yi shiru ba tare da ya furta kalami ba ya sanya shi gyaran murya a karo na biyu ya ce,
"Mun gama magana da mahaifiyarku in sha Allah gobe zan tura su Kawunka Sulaiman su je su ji magana.
Wani irin tsau ya ji a kansa wansa ya sanya shi juyowa cikin sauri yana kallonsa.
"Don Allah Abu, kar a yi gaggawan yin lamarin nan, saboda na gaya muku bani da ra'ayin zama da ita."
"Mun riga mun gama yanke shawara sai ka jira lokaci ya yi. Ka sani a wannan karo.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 9