Sashe 37
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 23
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Murɗa ƙofar ta yi da sallama."Ya Huwais, ga abinci na kawo maka." Ta faɗi tana kallon ƙirjinsa da ya cire rigarsa zai shiga wanka....
"Ke! Ba na hana ki shigo mini É—aki ba? Ma za fita."
"Don Allah ka tausaya mini ni fa matarka ce." Ta furta cikin muryar kuka sai kuma hawaye suka wanke mata fuska.
Ƙaramin tsaki ya ja ya wuce bayi ba tare da ya ce mata komai ba, wanda gabin haka ya sanya ta zauna a gefen gadonsa.
Bayan ya fito kai tsaye ya wuce wandrop É—insa, ya É—auki kaya ya wuce bayi ya sanya sannan ya fito zuwa falo
Ranta ya ƙara ɓaci, amma sai ta danne ta ɗauki abincin zuwa falon. Yana zaune da remote a hannunsa ta ije abincin ta xauna gefen shi.
"Ya Huwais,"
Ransa ya ɓace ya juyo yana kallonta."Sau nawa xan gaya miki bana buƙatarki cikin rayuwata?"
Duƙawa ta yi a ƙasa tare da ɗaga hannunta cikin muryar kuka ta ce"Don Allah ka tausaya mini ka soni, wallahi ina matuƙar sonka, kuma zan yinduk abin da zai faranta ranka."
Shiru ya yi ba tare da ya tanka mata ba. Ganin haka ya sanya ta miƙe tare da ɗaukar filet ta zuba masa abinci. Duƙawa ƙasa ta yi ta miƙa masa.
"Mijina ga abinci."
Juyowa ya yi yana kallonta. A rayuwarsa baya ƙaunar wulaƙanta mutum, musamman mace da suke da daraja, wannan dalilin ya gargaɗeta da kar ta yarda ta shigo rayuwarsa.
Miƙewa ya yi zuwa ɗakinsa saboda zuciyarsa ta fara karyewa. Ɗaki ya koma ya sanya ɗan makulli ya kwanta cikin damuwa.
"Ya zan yi na manta da ke Hilah na karɓi Wajnah a matsayin matata?" Ya yi wa kansa tambayar yana sosa fuskarsa.
Damuwa ta ƙara kama shi, yana jin yadda take buga ƙofar cikin muryar kuka, tana kiran sunansa.
Ganin ba zai buɗe ba, ya sanya ta shiga ɗakinta ta ɗauko ɗan makullin za ta sanya, amma sai ta ji ya ƙi shiga saboda akwai ɗan makulli a ciki.
Tana ta buga ƙofar da kiran sunasa amma ya ƙi buɗewa. Da ta gaji a gurin ta xauna har zuwa ɗayan dare, sannan ta tashi ta koma ɗakinta.
Kuka ta fashe da shi a zuciyarta tana jin ba za ta iya jure wulaƙanci ba.Kwanciya ta yi cikin damuwa, ta kasa bacci har zuwa ƙarfe huɗu.
Huwais kuwa yana jin tana buga ƙofa amma ya yi biris da ita. Jin ta daina bugawa ya miƙe ya shiga cikin bayi ya ɗauro alwala.
Sallah ya fara yi yana roƙon Allah ya kawo masa ɗauki a rayuwarsa.
A karo na biyu ya sake janyo wayarsa tare da yanke shawarar tura mata da texts na ban haƙuri.
"Ina son ki Hilah ba zan iya haƙuri da ke ba." Ya ce tare da rubuta mata tsaƙo kamar haka.
"Haƙuri da rarrashi ba za su ta ɓa wanke laifin da na aikata ba. A shirye na ke da na karɓi duk wani hukuncin da za ki yi mini tauraruwar zuciyata. Ki gafarce ni rashin haɗuwarmu, maihaifiyata ce ba ta da lafiya aka kira ni wanda ya sanya dole na je. Amma in sha Allahu zan bayyana kaina gareki.
Tura tsaƙon ya yi zuciyarsa na zillo. Ya san cewa abin da yake yi bai kyauta ba, amma ya xai yi kece kaɗai wacce ya ke son ya yi rayuwa da ita. Ya furta hakan cikin damuwa.
Hilah na kwance da waya a hannunta ta na yin assigment tsaƙon ya shigo. Da sauri ta miƙe tana zare ido.
Jikinta na kyarma ta fara karantawa. Ta karanta ya fi sau uku sannan ta ije wayar cikin damuwa. Tura tsaƙon na sa sai ta rasa gane farinciki za ta yi ko baƙinciki. Wataƙila in ta ƙara aminta da shi ya yi mata abin da ya fi haka.
"Wannan mutumin ya raina mini wayo." Ta furta cikin ɓacin rai tana ƙara karanta tsaƙon sau ba adadi.
Tsaki ta yi, sai ta yi wurgi da wayar, amma kuma hankalinta na kan wayar. Tura tsaƙon da ya yi, sai ta kasa samun natsuwa a zuciyarta.
Sonsa ne da take ƙoƙarin ɓoyewa ya fara bijiro mata. Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska.
Tana cikin wannan halin kiransa ya shigo. Jikinta ya É—auki rawa tana kallon wayar har ta tsinke, amma ta kasa É—auka.
Wayar na tsinkewa ta É—auki wayar. layin Huwais ta kira. Ganin kiran wayar ya sanya shi sakin murmushi domin dama ya xargi za ta kira.
Ƙin ɗaukar wayar ya yi har sai da ta kira sau biyu. Tana gabda tsinkewa ya ɗauka.
Cikin muryar bacci ta fara magana."Hello Hilah,"
Jin yanayin muryarsa ya sanya ta yi dana sanin kiransa. Ta manta shaf yanzu yana da mata.
"Ya Huwais, mahaukacin masoyi ya kira ni."
"Kin manta ina da mata shi ne xa ki kira ni da tsakar dare?"
"Yi haƙuri halin da na ke ciki ya sanya na manta." Ta faɗa tare da kashe wayar ba tare da ta jira ya ce komai ba.
Dariya ya yi ganin ta datse kiran. Layinta ya kira, amma har ta katse bata ɗauka ba. Ƙara kira ya yi. Tana gabda katsewa ta ɗauka.
"Am sorry Yaya, ka kwanta za mu yi maganar gobe."
"Ok, ki É—auki wayar ki ji mai zaice."
"Ba zan ɗauka ba zuciyata cike take da ɓacin rai na wulaƙancin da ya yi mini. Sai da safe." Ta ce tare da kashe wayar.
Murmushi ya saki yana kallon wayar.
Zan shigo makarantarku mu yi magana.
Ya tura mata da tsaƙon ya kashe wayarsa ya kwanta. Tunani fal a zuciyarsa. Bacci ne mai ƙarfi ya kwashe shi.
Hilah kuwa kasa bacci ta yi. Gani take kamar mahaukacin masoyi ya mai da zuciyarta abin wasa.
"Anya da gaske yake xai aure ni?" Ta yi wa kanta tambayar haka.
Kiran sallar farko ya miƙe ya shiga bayi. Wanka ya yi sannan ya canza kayansa ya wuce masallaci. Bayan ya yi sallah, ya zauna a masallacin yana karatun qur'ani har gari ya yi sha, sannan ya miƙe ya shigo ciki.
Falo ya sanya karatun qur'ani ya wuce ɗakinsa. Kan gadon ya hau ya ja bargo. Bai farka ba sai ƙarfe tara, ya yi wanka ya shirya.
Falo ya fito daidai lokacin da Wajnah ta ƙara shigowa.
"Ina kwana Ya Huwais?" Ba tare da ya amsa ba ya nufi hanyar fita yana gyara hularsa.
"Don Allah ka tsaya ka ci abinc..." Maganar ta tsaya ganin ya fice.Maigadi ya wangale masa get ya fice.
"Ka gama guje-gujenka dole ka shiga hannu tun da aka É—aura ai an yi mai wuyar. Ba ka da matar da ta wuce ni. In sha Allahu ni ce uwar Æ´aÆ´anka." Ta furta tare da sakin labule ta shiga kicin.
Karyawa ta yi sannan ta É—an gyara gidan ta yi kwanciyarta. Wayarta ta É—auka ta hau online suka fara hira a group É—insu. Nan kowacce ta fara kawo rayuwar gidanta da abin da mijinta ya yi mata suna dariya suna shewa da tsinewa rijalu.
Maigadi yana buÉ—e masa get ya shiga cikin gidan. Ganin Abu da jaka a hannunsa da alama gurin aiki xa shi ya sanya shi fitowa da sauri.
"Ina kwana Abu." Ya ce yana kallon Ummu da ta fito daga ciki hannunta riƙe da ƙaramar wayar Abu da alama ya manta da wayar ne ta ɗauko masa.
"Ina kwana Ummu?"
"Lafiya lau, ya kwanan Wajnah?" Ta yi masa tambayar cikin sakin fuska.
"Tana lafiya." Ya ce yana kallonta.
"Abu, fita aiki za ka yi?"
"Eh, amma da ma ina son magana da kai. Tun da ka zo mu koma ciki mu yi maganar."
Gabansa ne ya faɗi a tunaninsa ƙararsa Ummu ta kai na zaman gidansa.
"Ok," Ya ce tare da bin bayansu ganin sun juya za su shiga ciki.
Abu ya yi gyaran murya ya ce,"Game da Æ´ar'uwarka Hilah."
Gabansa ne ya ƙara faɗi tun bai san mai ya faru da ita ba.
"Tun da ka yi aure, sai muke ganin ita ma ya kamata mu ɗaura mata aure da Hamad, in ya so sai ya kama mata gida a Kaduna har ta ƙarasa karatu..!
Zubbur ya miƙe yana xare idanu cikin tashin hankali.
"Aure Hilah?" Ya furta cikin É—aga murya wanda ya tabbatar nusu da zarginsu.
Ummu ne ta kalli Abu, sannan ta kalle shi da yake share zufa da ke keto masa. Jijiyoyinsa suka miƙe yana jin wani tashin hankali na ziyartarsa.
"Abu, kan me xa a yi mata aure bayan ba ta kammala karatun ba?"
"Saboda gaka ya kamata. Kuma ya kamata mu tausayawa yaron nan, tuntuni yake jiran ta kammala ba tare da ƙorafi ba. Yanzu semester biyu ya rage, ai karatu ya zo ƙarshe."
"Gaskiya bai kamata ayi mata aure ba, saboda za dakusar da karatunta. Kuma Hilah ɗin ba ta da ra'ayin haɗa aure da karatu. Don Allah ku yi haƙuri har ta kammala karatunta." Ya furta kamar xai yi kuka.
"Ita ta gaya maka haka? Ka san irin son da Hilah ke yi wa Hamad. Ko bakinta za ka ara ka ci mata albasa?"
"Hilah ba ta son Hamad, ni na sani sam ba ta ƙaunarsa."
"Ko ba ta sonsa, dole ta aure shi mun sanar maka ne a matsayinka na É—an'uwanta."
Tashin hankali ya ninku a fuskarsa idanunsa suka firfito ji yake kamar zai yi hauka.
"Kai ina!Hilah tawa ce ba za ya taɓa auren wani ba ni ba." Ya ce aransa yana firfita da hannunsa.
Abu ne ya miƙe ganin yadda ya riƙice ya kasa cewa komai.
"Ni zan wuce ofis kar na yi latti. In sha Allahu yau zan yi wa mahaifin yaron magana."
"Abu, ka bari ka ji bakinta.."