← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 40

Sashe 23

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki barta ta ci gaba bakinta ne ai. Gajiya da maganar ne ba ta yi ba, kuma kema in ban da abinki har akwai abin da za ta faɗa ya dame ki. Ita da take yi wa mijinta biyayya ai kin ga sakamakon da yake mata. Ƙiri-ƙiri ya muzanta ki a gabanmu, amma kike wannan maganar. Habiba ki zauna ustazanci ya kashe ki, kar ki nuna wayewa kina abu kamar ba graduate mai digiri da masters ba."

"Sai ilmina ya sa na kar na yi wa mijina biyayya? Faɗa ya yi mini kan na yi dare ban dawo ba, kuma in har da bai yi mini faɗa ba, sai na yi tunanin baya sona, saboda duk namiji mai hankali da kishin matarsa ba zai ƙi yi mata faɗa ba a lokacin da muka dawo."

"Eh, ai kin san ni mijina baya kishina, baya ƙaunata shi ya sa bai ce mini komai ba. Ki yi ta zama yana kashe rayuwarki kina fakewa da sunan biyayya."

"Ki ƙyaleta Fahima ta yi ta yi dama ta saba. Cewar Wajnah da take harararta.

"Ni har mamakin yadda muka kasa daina ƙawance dake na ke yi, domin Hausawa sun ce sai hali ɗaya ya zo ake ƙawance, amma sam ke ba ki wayewa kina abu kamar ba cikakkiyar wayyaya ba."

"Ni dai ba zan fasa daina gaya muku haskiya ba. Don haka shawara ya rage ma mai shiga rijiya. In kun ga dama ku daina shaye-shayen kayan mata. In kuma ƙun ƙi ina jiye muku ranar da za ku yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa ɗankada don za ku tsinci Talatarku a Laraba."

"Ke ce dai za ki tsinci Talatarki a Laraba, saboda yadda kike nuna kina tsoron Abban Iklas, watarana sai ya sanya ki kuka, don sai dai ki ji a shanun tashi ya yi auresa."

"Wannan tsakaninsa da Allah ne. Ƙin gaya mini shi ne kawai laifin, amma ni ba zan iya hana shi abin da Ubangiji ya ba shi dama ba."

"Allahu Akbar! Sannu mai sani. Allah ya sa da gaske kike kar kizo mana kina kuka. Ni da kika ganni mijina da kishiya sai dai na ƙiyama da ba ni da ikon hanawa, amma bai isa ya ce zai yi aure ba."

"Lailai ko kina da aiki in har mazan zamanin nan ne."

"A'a Habiba, kar ki yi mata baki. Ko ni da Ya Huwais baya sona ba zan taɓa bari ya yi mini kishiya ba, saboda ko ƙanwarsa da yake ji da ita wallahi ina shiga sai na raba shi da ita. Ballantana wata kishiya can."

"To Allah ya ba ku sa'a. Ni tafiya zan yi kar habibi ya dawo don zan yi masa tuwon shinkafa."

"Hmmmh! Kina wahalar da kanki ga masu aiki, amma ki je aiki ki dawo ki yi girki." Cewar Fahima.

"Ai ni kuma in dai abinci ne bani da matsala, saboda ni a shegen kishina ko abincin Ummu ya ci ba nawa ba, za a samu matsala."

"Ni dai ba zan iya girki ba, haka kawai da girkin zanji ko da rainon yarsa da É—aukar É—awainiyarsa?"

"Duka ai bautar Allah kike yi." Habiba ta ba su amsa tana riƙe da ɗan makullinta.

"Bar ni na ji da ɗaya haka kawai na ɗaura wa kaina wahala. Yawancin full house wife duk a ƙanjame suke, saboda ba sa samun lokacin da za su huta ga ɗawainiyar gida ga miji da yara."

"Allah dai ya bamu lada kawai." Cewar Habiba don ta guddura da maganar.

Wayarta ta yi ƙara, wanda ta kalla ganin numbar mijinta ne, ya sa ta ruga da gudu zuwa gurin motarta tana ɗaga musu hannu.

Bayan fitarta suka dawo cikin falon suka zauna.

"Ni fa Habiba mamaki take ba ni, yadda ta yi sakaci mijinta na ba ta lokaci in xa ta fita, domin duk yadda nake son Ya Huwais ba zan aminta da wannan dokar ba."

"Ita ta ga za ta iya, ai sai ta yi." Fahima ta ce tare da zaunawa a gefenta suka ci gaba da zaɓen kayan matan.

Huwais ransa a ɓace yake, tun lokacin da Abu ya tursasa shi zance zuwa gurinta. A ransa yana jin bai san abin da zai ce mata ba, domin shi ko kallon kirki baya tunanin zai iya mata.

Tsaki ya ja tare da ɗauko wayarsa da ke maƙale a soket yana caji. Numbar Najib ya kira wanda ringing ɗaya ya ɗauka da sallama.

"Abu ya tursasa ni zuwa gurin Wajnah, please gobe da yamma zaka raka ni." Ya na faÉ—in haka, ya kashe wayar don baya son ya ce masa komai.

Da ƙyar Abu ya shawo hankalin Ummu, har ta bar maganar don ta yi ninyar hukunta Hilah, amma maganganun da ya gaya mata, ya sanya ko a fuska ba ta canza mata ba.

A mota suna tafiya shi da Najib babu wanda ke magana. Najib ne yake tuƙi da motarsa, shi kuma hankalinsa na kan wayarsa da yake chatting da Hilah.

Duk da cewar da ɓacin rai a fuskarsa, amma duk tsaƙon da ya tura mata ta turo mishi da reply sai ya murmusa.

"Ya kamata ka sanar mata da zuwan mu fa." Najib da ya waiwayo ya kallesa yana faÉ—in haka.

Ganin bai tanka masa ba, wanda hakan ya tabbatar masa sai bai ji shi ba.

Hannunsa ya kai ya fisge wayarsa tare da duba abin da yake yi.

"Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya."

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 14

"Iska na wahalar da mai kayan kara. Wallahi Huwais, ya kamata ka farka daga mummunar mafarkin da ka yi na mallakar ƙanwarka, da ka san ba za ku taɓa zama a inuwan ma'aurata ba. Ka rungumi ƴar kyakyawar matarka ku zauna lafiya."

"Please, bana son wulaƙanci ka bani wayata. Tun da ka ga Allah ya jarabce ni da sonta babu makawa sai na auret.."

"Ta ya ya Huwais? Tun da kake ka taɓa ganin an yi irin wannan auren? Sheɗan ne kawai ke ruɗarka kaɗa maka gangar sheɗan."

"Mu bar maganar kana ɓata mini raina." Ya furta cikin ɗaga murya.

"Zan yi shiru ne don kar ka É—ora laifin a kan Wajnah, da ba ta ji bata gani ba, amma ba zan fasa gaya maka gaskiya ba, a matsayina na amininka, amma ka sani auren ka da Hilah sai dai in ana mutuwa a dawo, sai ku dawo ba a matsayin Æ´an'uwa ba."

"In kuma Allah ya ƙaddara sai ka mutu."

"Ta ya ya?"

"Ni ma ban sani ba amma jikina yana ba ni matata ce!"

"Hammh!" Kawai ya ce cikin takaici ya ci gaba da tuƙi ba tare da ya ce masa komai ba.

Da suka isa ƙofar gidan maigadi ya buɗe musu sula shiga.

Wajnah na zaune a cikin ɗakinta mai dillah na dirzanta. Ƙanwarta Batula ta ƙwanƙwasa ƙofar.

"Waye?" Ta yi tambayar cikin É—aga murya.

"Anty Wajnah, Batula ce. Mommy ta ce in gaya maka Ya Huwais na falon Daddy." Da sauri ta ture hannunta jin abin da ta faÉ—a.

"Ok, ki ce gani nan zuwa." Ta bata amsa yayin da fuskarta ya cika da farinciki.

"Ana dilkan za ki fita? Ki gaya mishi ya jira ki."

"Mijin nawa zan shanya ya jira ni? Kin san da yadda na samu ya zo?"

"To asarar dilkan za ki yi?" Ta yi mata tambayar a maimakon ta ba ta masa.

"Eh, wankewa zan yi in ya tafi na dawo." Ta ba ta amsa tare da shigewa bayi.

Saboda tsabar murna É—auraye jikinta kawai ta yi. Cikin Æ´an mintina da bai fi goma ba, ta shirya kanta cikin riga da siket masu kyau ta sanya mayafi ta fice zuwa falon.

Da sallama ta shiga, idanunta na kan Huwais, da yake riƙe da waya har yanzu chatting yake yi yana murmushi.

Murmushin da yake yi ya sa ta yi tunanin ko ita yake yi wa.

"My baby, na yi tunanin ba za ka zo ba, sai an kawo maka ni a matsayin mallakinka." Ta furta cikin kissa tare da samun gefensa ta zauna har suna gogan juna.

Ba tare da ya jinkirta ba, ya matsa can ƙarshen kujera bayan ya haɗe rai, ya ɗan tsaki ƙaramin tsuka, wanda ya sanya jikinta ya yi sanyi.

Wataƙila da ta shigo ba ta yi tunanin da wani yake ba, domin ba ta lura da Najib da yake kujera one seater, sai da ya yi gyaran murya.

Kasancewarta wayayyar mace sai ta basar da abin da ya yi mata.

"Laah, ka ce da abokinmu kake tafe?" Ta yi masa tambayar tana kallonsa, sai kuma ta mai da hankalinta kan wayarsa da yake kallo.

Datar ya kashe ba tare da ya tanka mata ba yana kallon gefe.

Najib ne ya ce,"Amarya bakya laifi ko da kin kashe É—an masu gida." Dariya ta yi tare da jin farinciki na kirarin da ya yi mata, wannan kirarin ya sanya kika shanya mu ko? Ko da yake laifinmu ne da bamu sanar miki ba."

"Ku yi haƙuri ana mini dilka ne sai dai na wanke."

"Mun haƙura dama ba mu yi fushi ba."
Chapter 23 · 0% Book details