← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 40

Sashe 8

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dalilin me Abu? Wanda zai kasa sanar mana ai duk ƙarƙashinmu suke hakan da suka yi koyi suke yi wa na bayansu." Ta ce tana harararsa cikin zargi.

Shiru ya yi kamar babu ruwan shi, ko bai san da zancen ba." Ya ce yana hararsa wanda sai a lokacin ya ije.

"Ni fa ba da wani nufi na yi ba kawai na gaya mata ne, saboda ganin yadda ta tada hankalinta, kuma a lokacin gab da musabaƙarsu ne. Ba na son ta tada hankalinta ya sa na gaya mata hakan, dama na san in har da gaske ya ke yi zai ƙara tura tsaƙon."

"Wannan ba hujja bace Huwais, ya kamata komai na ku mu sani, domin mun cancanci mu sani."

"Ku yi haƙuri mun yi kuskure." Ya ce yana kallon Ummu da take masa wani kallo don gabakiɗaya ba ta yadda da shi ba.

"To yanzu mene ne abin yi?"Abu ya tambaye sa cikin rashin dubara.

"Ban sani ba mu jira lokaci, in dai ba aljani bane, dole ya bayyana kansa tun da babu wani identity na sa, da zamu mayar masa da kuÉ—in." Ya ce musu yana kallonsu.

"Ai ya makaro ko ma waye, domin Hilah na da masoyi kuma na yi na'am da shi, sam ba ta da wani miji sai shi." Ummu ta ce cikin ɓacin rai!

"Hilah tawa ce don in ina raye babu wanda ya isa ya mallaketa sai ni, domin kanta zan iya zama makashi ko ɗan dan daba Ummu. Ki jira lokacin da zan bayyana kaina na yi yaƙi da duk wanda zai hana ni mallakarta." Ya ce a ransa amma a fili bai ce komai ba sai ya fice daga falon wanda Ummu ta raka shi da idanu hankalinta a tashe.

Ganin ya fita sai haushinsa ya kamata domin bai taɓa ɓata mata rai ba irin yau. Ɗakinta ta shige ta kulle ƙofa tare da faɗawa kan gado ta sakin kuka.

"Wane ne wannan mahaukacin masoyin da yake so ya kawo mini rashin zaman lafiya da iyayena? Domin irin kallon da Ummu take mini ya girgiza ni." Ta ce cikin damuwa.

"Anya mutumin nan ya san ciwon kuÉ—i ji motar da ya kawo mini da waya? Zuciyata ta fara zargin É—an shan jini ne ko mai safarar mutane." Ta ce cikin ruÉ—ani.

Tana kwance kiran Hammad ya shigo wanda har sai da ya yi ringing uku sannan ta fahimci ana kiranta ta É—aga. Jin yadda take amsa masa ya fahimci ba ta cikin hankalinta ya yi mata sallama ya kashe wayar, wanda ita ma jifa ta yi da wayar ta kifa kanta kan filo tana mai da numfashi.

A haka ta wuni sukuku lokaci guda ta ji ta ƙara zaƙuwa da ta ga wannan mahaukacin da ya kamata a kaisa Dawanau.

Ko da ta zo bacci duk iya satar bacci a wannan lokacin sai dai ya ganta ya haƙura, domin idanunta sun soye tamkar an soya gyaɗa mai gishiri

Ta yi juyin har kan kujera ta dawo ta kwanta amma gwanin satar ya kasa sace ta.

Duk da cewarta ba mai son rayuwar social media ba ce, don sai ta haɗa sati ba ta hau whatsapp ko facebook ba in dai ba relevant abu za ta duba ba. Don ita ba ta ɗauki wannan platform amatsayin wanda zai ɗauke mata kewa ba, sai dai amfani da shi da wasu gwara gurbin mutane suke yi suna watsa alfasha da ƙarerayi. Duk da cewar ko wane abu akwai merits ɗin sa da demerits ɗinsa.

A wannan lokacin ta tsinci kanta da son hawa whatsapp musamman da ta tuna Muktar classrep É—insu ya gaya mata ya tura houndout that is meaningfull.

Sai ta tsinci kanta da kunna datar wanda a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi daidai. Tana buɗewa ta fara duba tsaƙon

Huwais dake zaune idanunsa babu bacci ko kaÉ—an. Bayan ya kammala ayyukansa ya tura musu sannan ya kashe lap É—in ya koma kan gado ya kwanta tare da jan bargo.

Tunanin halin da ta shiga lokacin da scene É—in ya faru yake yi. Mamakin iya basarwa na sa ya nuna tamkar bai damu da lamarin ba ya kama shi, wanda a wannan lokacin Allah kaÉ—ai ya san halin da yake ciki, domin da ace Abu ya É—an matso kusa da shi sai ya fahimci halin da yake ciki. Sai dai Allah ya taimake shi Ummu ne kawai ya É—an zargi wani abu domin ta san shi fiye da kowa.

Sai ya ƙara tasbihi ga Allah, da ya rufa masa asirin domin da sun gane wata maganara ake ba wannan ba. Ya san an riga an yi disowning ɗinsa agidan duba ga wutar da yake so ya kunna a gidan.

ÆŠaukar wayarsa ya yi ya kunna data wanda yake son ko bacci ya kama shi.

Da yake gb whatsapp yake amfani fa shi. Yana hawa ya ga an rubuta; little sis online. Wanda matuƙar mamaki ya kama shi domin a iya tarihin rayuwarsa sam ba ta hawa online da daddare ko assignment za ta yi tana ɗauko wa ne tun kafin dare, ballanatana wannan lokacin da yake ƙarfe biyu vai wuce awa ɗaya ta tashi ta fara haddarta ba.

Ɗayan wayar da yake tura mata tsaƙo ya ɗauko can ƙarƙashin gadonsa tare da kunnawa ya kunna data.

Sallama ya yi mata wanda ya matuƙar razanata, a lokacin da ta ga tsaƙon ganin an ɓoye lambar ya sa ta gane ko wane.

"Matar mahaukacin masoyi! Ba ki yi bacci ba, mai kike yi a wannan lokacin? Wataƙila kuma soyayyata ce ta fara kama ki, kamar yadda ta hana ni bacci sai tunaninki nake yi." Ya turo dogon tsaƙo kamar haka.

Tsoro ne ya fara kamata domin tana tunanin anya ba aljani bane? Dama ance suna soyyaya da mutane ko ita ma hakan zai faru da ita? Saurin kawar da tunanin nan ta yi, domin a yadda take addu'a ta san in sha Allahu babu Aljanin da zai iya wasa da rayuwarta.

"Waye kai kuma mai ya sa kake ɓata lokacina?" Ta yi masa tambayar cikin haushi.

"Da sannu za ki sanni ki kwantar da hankalinki. Domin watarana zamu yi aure na kwantar dake a ƙirjina ina miki fifita. Wannan pinky libs ɗin ki zai zama sweet ɗina."

Kunyar abin da ya faÉ—a ya sa ta rintse idanunta tare da kawar da wayar tana mamakin lailai bayan zama mahaukaci tantiri ne shi.

"Aiko ka yi kuskure domin zuciyarka yaudarar ka take. Ina da wanda zan aura don haka maza ka zo ka karɓi tsiyarka don ka san ko ni ina da kuɗin da zan siya duk abin da kake tunanin za ka iya siyata da shi."

"Ina! Ke É—in tawa ce ni kaÉ—ai duk wanda ya yi gigin shiga gonata. Ina miki albishirin zan kashe shi na kuma kashe kaina."

Miƙewa ta yi da sauri sai ta kashe datar ta tura wayar can tsaƙon filo domin wani irin tsoro ne ya kamata.

Ta fara karanta addu'a tana son ta yi bacci don ta fara jin tsoron shi, amma idanunta sun bushe tamkar tekun da ya ƙafe da bazara.

Huwais kuwa ganin ta sauka sai ya tabbatar da maganar da ya gaya mata ne ya ruÉ—ata wanda ya san yanzu tana nan cikin tashin hanakali saninta muguwar matsoraciya ce.

Dariya ya yi sosai har yana buga filo, ya sannan ya rungume wayar yana kallon hotonta yana murmushi.

Mamakin jawo wayarta da ta yi ta kuma kunna datar ta yi.

Ganin bai yi mata magana ba sai ta tsinci kanta da tura masa stiker na gargaÉ—i.

Yana ganin lokacin da ta hau online ɗin shareta ya yi, ya ƙyaleta domin ta sauka ta yi karatu ganin uku daidai, amma da ta tura masa da hakan sai ya turo mata da ma soyayya.

"Ki kular mini da kanki kuma ki tashi kiyi sallah ki yi istikhara kan lamarin." Ya kashe wayar.

Ba tare da tunanin dare bane ta lalubi numbar Huwais ta kira domin ta tabbata zuwa wannan lokacin ya tashi yin sallah.

Yana ganin kiran ya saki dariya tare da É—aukar wayar ya yi shiru na É—an lokaci. Jin shirun ya sa ta fara magana.

"Ya Huwais ya yi mini magana ta whatsapp, amma ya ɓoye numbarsa still. Mutumin nan ya raina mini wayo sosai. Ya yi magana da ni sanda ya ga dama ya turo mini da presents ɗinsa alokacin da yake so.

"To shine za ki tashe mi ina tsaka da baccina kan wani mahaukaci can masoyinki! Kar fa ki manta mahaukaci ne shi." Ya ce mata cikin fusji da kuma muryar da ya yi kamar daga baccin yake.

Jin abin da yace ya É—an sa ta tsorota domin bai cika bayyana fushinsa ba, musamman a kanta.

"Am sorry. Na kasa haƙuri safiya ta yi." Ta ce kamar yana ganinta sai kuma ta tsinci kanta da jin haushin cewa mahaukacin da ya yi, wato itama mahaukaciya ce tun da ta biye masa.

Tsaki ya ce, "Me kike yi a wannan lokacin ma za ki tashi kiyi sallah ki yi hadda, kina jina da safe za mu yi maganar, kuma ina son ki cire wannan maganar a ranki."

"Ai ban sa a zuciyata ba. Hammad nake so kuma shi zan aura mai zan yi da mahaukaci." Ta ba shi amsa domin tunaninta kar ya É—auka ko ta fara sonsa.

Ya ji babu daɗi tun da shi ya jawa kansa sai ya ɓoye kishinsa ta hanyar cewa,"Ok, shikenan. Wataƙila a gida ba zamu samu damar yin magana sosa ba, ki shirya in sai na kaiki school."

"Ummi ba za ta barni na hau motar haya ba, ko na ce mata motata ta lalace za ta ce na É—auki nata ko na Ya Naufal. The worse part É—in ma za ta iya saka direba ya kai ni. Zan fita da motata sai na jira ka gaba da gidanmu."

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Chapter 8 · 0% Book details