Sashe 21
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallonta ya yi ganin yadda ta É—auki maganar serious, dama yadda ta ke musu kallo ya san sai ta tambaya.
"Mu shiga ciki mai kika gani?"
"Abin ne da mamaki suna rayuwarsu, kamar masoya ko dai akwai aure a tsakaninsu ne."
"Ƙanwarsa ce uwa ɗaya uba ɗaya. Karki manta na gaya miki bikin shi ya rage kwanaki, ita kuma da zarar ta kammala karatunta akwai wanda za ta aura a family ɗinsu yake."
"Ikon Allah! Gaskiya wannan soyayyar tasu akwai lauje cikin naÉ—i!"
"Please, kar ki sanya kokwato a zuciyarki shaƙuwar jini ce."
"Hmmmmmmh!" Kawai ta ce tare da fara tafiya sai kuma ta tsaya ta kalle shi ta ce,"Karka manta psychology na karanta so zan iya fahimtar komi. Kamata ya zo mana da wacce zai aura ba ƙanwarsa ba, amma har ya tashi ban ji ya ambaci sunanta ba."
Shiru kawai ya yi, don ba shi da amsar da zai ba ta don haka shirun yafi, domin masana iya magana sun ce shiru ma magana ce.
A mota ya miƙa mata wayarta da Ummu ta ƙara kira."Ummu ce take ta kirana shi ya sa na taho, amma bacin haka sai na tabbata wancan mai kama da mayen ya tafi."
"Zai iya kwana tun da É—an gida ne." Ta furta masa hakan.
Harara ya wurga mata ba tare da ya ce komai ba ya ci gaba da tuƙi.
"Innalillhi! Ka ce Ummu ta kira?"
"Eh, sai ki san yadda za ki kare kanki, ai duk ke kika ja, wa sani ko ke kika sanar masa da zuwanki ya wani kwaso jiki ya taho?"
"Wallahi bani ba ce Ya Huwais." Banza ya yi da ita ya ci gaba da tuƙunsa, wanda ganin hakan ya sanya ta kama bakinta, tana tunanin darun da Ummu za ta yi.
Ba su ƙara magana ba har suka isa gidan. Hajiya da ta yi kici-kicin da ranta yana ƙarasowa ta buga masa dundu a baya.
Dariya ya kwashe da shi,"Wayyo yar tsohuwar nan ashe akwai sauranki! Kin ji hannu kaman guduma."
"Amma sam ba ka da kirki Huwaisu, sai ka É—auke ta ku tafi, bayan ka san yana jiranta?"
Satan kallonsa ya yi da ya ɓata fuska zuciyarsa a tuƙe, domin da ace bai yi wa mahaifiyarsa alƙawarin ba zai ƙara kula shi ba, babu abin da zai hana bai kai masa mari ba.
Miƙewa ya yi ya kalleta da ta yi tsuru-tsuru tausayinsa ya kamata, domin abin da suka yi ta san cewa ba ta kyauta ba, amma ya za ta yi? Ɗan'uwa ta yana gaba da komai kuma takan hana kanta farincikinta ta ba shi na sa.
"Gimbiya, muje waje ina son magana da ke!" Ya furta da murya mai sanyi da kuma ɓacin rai.
"Babu inda za ta je domin gida zamu je, Ummu na ta kiranmu." Ya ba shi amsa yana kallon agogo fuskarsa a haÉ—e.
"In ina magana ka daina sa mini baki da iyalina, domin ba zan duba tazarar da ka bani ba, wallahi yanzu za a yi ɓatacciya." Ya furta cikin zafin rai.
"Mara kunya dukana za ka yi? Karka manta Æ´ar'uwata ce na jini, na fi ka iko da ita, domin ina da isan da zan hana aurenku."
"Inda kuma ka yi kaÉ—an kenan, domin Hilah tawa ce, duk son da kake mata da nuna kishinka sai dai ka yi a banza, saboda kana ji jana gani zan É—auketa a matsayin iyalina ta haifa..."
Marin da ya kai masa ya hana shi ƙarashe maganar, amma sai bai same shi ba saboda ya kauce.
Huwais jin ya kirata da matarsa ya sanya shi yin marin babu shiri.
"Au, tarihi ne zai maimaita kansa? Har yanzu ba za ku daina wannan haukan ba? Duk fa ƙaunar da kake mata gidan wani za ta Huwaisu. Anya kana da hankali kuwa?"
Ransa ne ya ɓace jin shika kaɗai ta bawa laifin.
"Please, Ya Huwais ku daina. Don Allah Ya Hamad, ka je za mu yi waya." Ta furta cikin muryar kuka bayan ta shiga tsakaninsu.
"Ki barshi rashin kunya zai yi mini." Ya furta yana huci.
"In ba za su daina ba kai Affan, kira mini Babansu Hamisu ya zo ya yi wa abin tufka."
Wani wulaƙantaccen kallo ya watsa masa har zai yi magana sai ya fasa, domin ya san abin da ya shirya yi masa sai ya ƙuntata masa fiye da maganar da zai yi masa.
"Zan wuce Hilah. Ki kular mini da kanki ina sonki, na tura miki kuÉ—i a account É—inki sai mun yi waya. I love you." Ya furta mata a kusa da kunninta ya watsa masa harara da zuciya ta kai masa wuya ya wuce.
Ilai kuwa, kamar yadda ya yi tunanin sai ya fi baƙanta masa haka ya faru. Har ya fara taku zai bishi ta kama hannunsa tana kuka.
Fita ya yi daga falon zuwa motarshi ba tare da ya yi ma Hajiya sallama.
"Umma ta gaida ashsha! Ja'irin yaro kawai. Wannan kishin da kake nunawa da a kan matar da za ka aura kake yi sai armashi zafi fiye da ƙanwarka."
Hon ɗin da yake yi musu babu ƙauƙautawa, ya sanya suka kwashi kayan su suka fito da sauri.
Figar motar ya yi a guje suka bar harabar gidan.
A gida kuwa Ummu ta kasa zaune ta kasa tsaye. Ta kira wayarsa ya fi a ƙirga, amma ya ƙi ɗagawa, wanda hakan ya ƙara baƙanta ra ta ainun.
Numbar Abu ta kira ta fara yi masa ƙorafi.
"Ina kan hanya na kusa gida ki jira ni." Ya kashe wayar bayan ya ce mata haka.
Yana mamakin yadda take zafafa lamarin. Shi a tunaninsa duk abin da take hange bai kai nan ba, domin yana da hankali da addini ba zai aikata wa ƙanwarsa mummunan abu ba, amma sai ta ɗaga hankalinta ta gadda za ta kasa sukuni.
Yana shigowa ta fara hawaye tare da buÉ—e baki za ta ce.
Dakatar da ita ya yi ta hanyar É—aga mata hannu.
"Duk ke kike rikita lamarin nan Lailah har yaran nan suka fara zargin wani abu, tun da an kusa bikinsa don Allah ki ƙyale shi har ayi bikin nan ya koma gidansa mu huta."
"Laifi ne don na sanya idanu a kan tarbiyar Ƴaƴana? Karka manta yarannan amana ce Allah ya bamu domin ya ce dukkannnin mu masu kiwo ne, kuma rabar gobe kiyana sai a an tambaye mu. Kuma kula da kaya, ai yafi ban cigiya. Musamman yadda shi yake nuna soyayyanta ɓalo-ɓalo."
"Duk ban ga laifin ki ba, amma kina zafafa lamarin ne, kuma hakan zai iya haifar da wata matsalar. Don Allah na roƙe ki in suka zo dawo kar ki hausu da faɗa ki yi musu kyakyawar fahimta."
"Hmmmh!" Kawai ta ce tare da komawa ta zauna, tana jin haushinsa na ƙin ganin abi da da take hangowa, wanda tun a wancan lokacin take nuna masa, amma ya kasa hangowa ga shi hakan ya haifar da ɗa mara ido, kuma har yanzu bai fahimta ba.
"To ai shike nan, tun da laifina kake gani, sai na daina sanya idanuna a ka su, kuma duk abin da ya faru kar ka yi kuka da ni."
"Babu abin da zai faru sai alkhairi.Na yarda da tarbiyar da na bawa yarana, ba za su aikata abin da duniya za ta la'ance su ba, duk da shaƙuwar dake tsakaninsu."
Suna isa ƙofar gidan gabansu ya buga a tare, domin sun san ba za su ji da daɗi a gurin Ummu ba.
Ajiyar zuciya ta saki da sauri, ta buÉ—e motar ta bi bayan su Umnaah, da suka ruga da gudu suna murnar tsarabar da suka dawo da ita.
Yana zaune a cikin motar yana hangen ta har ta shige cikin gidan. Kamar ba zai fito ba sai kuma ya buÉ—e motar ya bita ciki.
A falo suka samu Ummu, da ke riƙe da waya a hannunta tana magana da Hajiya.
"Yanzu dama abin da yaronnan ya aikata kenan? Shi ya sanya ya na ce sai sun tafi tare? Ki bar ni zai dawo ni da shi ne."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 13
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Yanzu dama abin da yarannan ya aikata kenan? Shi ya sanya ya na ce sai sun tafi tare? Ki bar ni zai dawo ni da shi ne, domin ina ji ina gani ba zai ɓata mana zumunci ba."
Hilah ta tsaya cikin tsoro tana zare idanu jin abin da take faÉ—a.
Ta yi sallama a cikin falon, daidai lokacin ta gama wayar, tare da kashewa ta ije a kan kujerar da take kai.
"Sannu da hutawa Ummu." Wani mugun kallo ta watsa mata daidai lokacin da Abu yake saukowa daga saman bene.
"Ina kuka je?"
"Ta raka ni gidan Najib." Ta ji muryar Huwais ya amsa, a maimakon ita da aka yi wa tambayar.
Idanunta ta mayar kansa, da yake shigowa hannunsa riƙe da ledar costimetics da matar Najib ta ba ta.
"Sai yaushe za ka daina sa ni damuwa Huwais? Yanzu abin da ka aikata ka kyauta kenan? A tunanin shekarun da ka ɗauka a waje zai sanya ka daina sanya ni cikin damuwa." Ta furta cikin ɓacin rai tana kallonsa.