Sashe 24
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi ta yi jin abin da ya ce tana satar kallonsa da ya ƙara kici-kici da fuska.
"Ina wuni?"
Kamar ya amsa kamar kuma motsi kawai da bakinsa ya yi. Ganin haka ya sanya Najib ya miƙe,"Ni bari na baku guri da fatan za ki kula mini da shi?"
Yaƙe kawai ta yi ganin yadda yake cisgata, amma a zuciyarta ta ji daɗin fitan nasa, musamman da tun da ta shigo ta nemi natsuwarta ta rasa, yayin da kayan matan da take sha suka fara aikinsu.
Ji ta yi kamar ta rungume shi ko ta faɗa jikinsa. Tana mishi wani irin so musamman yanzu da take jin baba so akwai buƙatar ta ji ta a jikinsa.
"Ya Huwais don..."
"Please, ba na zo bane don ki ɓata mini rai. Bisa tursasawar iyayena nazo. Na sha gaya miki bana ƙyaunarki. Sam ba ki a cikin jadawalin matan da na ke so, amma kin na ce dole sai kin aure ni, don haka ki shiryar kurɓar ruwan guban da yafi na maciji dafi a cikin gidana, saboda ba za ki taɓa samun farinciki a cikin gidana ba."
"Eh na ji kuma na amince, matuƙar zan rayu a ƙarƙashin inuwar aurenka, a shirye na ke da ko wane irin zama a cikin gidanka."
"Shikenan, sai ki je gidan ga shi nan ki zauna, amma ni ba za ki taɓa mallakata ba, kuma na gaya miki ina da wacce nake so, nake burin ta zamo uwar ƴaƴana."
"Don Allah Ya Huwais, ka taimaka mini wallahi a shirye na ke na ba ka farinciki, domin ina matuƙar sonka."Ta ce bayan ta duƙa ta kama rigarsa.
Fisge rigar ya yi cikin ɓacin rai," Ba za ki taɓa mallakar zuciyata ba, domin ba ki da matsuguni a cikinta."
Kukanta ya ƙaru jin abin da ya ce. Fara tafiya ya yi. Tsaye ta yi cikin damuwa tana kallonsa. Lokaci guda ta ji ranta ya ƙara ɓaci, wanda har ta gwammace da bai zo ba.
Yana ƙoƙarin fita Najib ya murɗa ƙofar ya shigo. Kallonsa ya yi da ya fice ba tare da ya tanka masa ba, sai kuma ya kalli Wajnah da har yanzu hawaye take sharewa.
Kunya da takaici suka lulluɓe shi, ya kasa ce mata komai sai dai ya juya ya fice.
Wajnah ji ta yi kamar ta kashe kanta. Wani tangaras da aka yi kwalliyar fulawa da shi, ta ƙwada shi da ƙasa tare da fashewa da kuka ta yi sashin Mommy.
"Ya Huwais ba ya ƙaunata mommy."
"Ki daina ɓata hawayenki mai wuyar ki shiga cikin gidan, domin kina da kyau da babu namijin da zai wulaƙnata ki."
Abin da ta faɗa ya ɗan sanyaya zuciyarta, amma har yanzu tana jin tana mata ƙuna. Rintse idanunta ta yi tana kin kamar ta mare shi lokacin da yake gaya mata yana da wacce yake so, wani irin mugun tsanarta ya shiga cikin ranta har take jin za ta iya ajalinta.
"Yanzu abin da ka yi ka kyauta? Don Allah ka tausayawa yarinyar nan, masoyinka ba ya taɓa zama maƙiyinka." Najib ya furta cikin ɓacin rai ya ɓna kallonta.
"Yanzu mu da muka zo yin maganar abin da za mu ba su da biki ga shi nan ka ɓata komai, wallahi kunyar yarinyar na ji ya sanya na kasa magana."
"Duk abin da na yi mata laifinta ne ai ba a aure dole."
Tsaki kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba cikin takaici.
Haƙiƙa Ummu ta shirya wa bikin nan domin kayan lefen da aka haɗa kaya ne na gani na faɗa.
A falo aka baza kayan suna ta gani cikin sha'awa. Hilah ita kanta kayan sun yi mata ƙwarai! Don Ummu ta yi ƙoƙari sosai.
Gidan da Huwais zai zauna gida ne mai tsananin kyau da tsari. Gidan part biyu ya kuma haÉ—u sosai. Daga sashin Wajnah sai na shi mai É—auke da É—aki biyu da dining kamar dai Wajnah.
Abu ya gina masa gidan mai kyau da tsari.
Iyayen Wajnah sun yi matuƙar ƙoƙari, domin hatta sashinsa sai da suka cika da kaya, duk da cewar Abu ya hana domin Huwais zai gyara bangarensa, amma suka buƙaci su sanya masa kayan.Kaya ne na gani na alfarka aka yi.
Kasancewar mahaifin Wajnah shahararren É—an kasuwa ne, da yake da shoping mall da yawa a garin Abuja. Ya yi bajinta sosai gurin yin mata kayan, musamman da take ita ce Æ´a ta farko da zai fara aurarwa.
Mahaifiyarta ma ba a barta a baya ba, saboda ita ma tana business na atamfa less sa sauran kayan amfanin mata.
Haƙiƙa gidan ya tsaru matuƙar gaske.
Ya rage saura sati ɗaya biki hankalinsa ya tashi matuƙar gaske! Domin abu biyu suka haɗe masa tare da rikita ƙwaƙwalwarsa.
Cikin dare sam baya bacci, yana tunanin rayuwar da zai yi da Wajnah da kullum ƙara tsanarta yake a cikin zuciyarsa. Sannan ga shi Hilah ta takura masa kan yazo bikin. Abin duniya sun haɗu sun yi masa yawa. Gabakiɗaya ya rame ya fita hayyacinsa, wanda ya tsorata iyayensa, amma kuma hakan shi ne kawai zai kawo maslaha.
Wata shawara ta bijiro masa take ya amince da zai zo. In ya so ranar ɗaurin auren sai ya yi mata wani ƙaryar. Duk da ya san cewa za ta yi fushi dashi mai tsanani, amma ba za ta iya rabuwa da shi ba, saboda kamar yadda yake jin sonta a cikin zuciyarsa, ya tabbata tana jin kwatankwashinsa duba ga yadda take gaya masa yadda ta damu da shi, kuma ya san Hilah ba za ta taɓa gaya masa ƙarya ba.
Hilah tsaye a kicin tana dama kunun gyaɗa da ta ke son ta kai masa. Har cikin zuciyarta tana matuƙar tausaya masa domin rashin masoyi babu daɗi. Tana ji a ranta yadda take son mahaukacin masoyinta, matuƙar aka raba ta da shi za ta iya shiga kwatankwacin halin da yake ciki.
Bayan ta dama masa kunun ta É—auka ta nufi sashinsa. Yana kwance da waya a hannunsa. Hotonta yake kallo yayin da hawaye suka taru a gefen idanunsa.
Ƙwaƙwansa ƙofar ta yi tare da kiran sunansa wanda ya yi maza ya aje wayar.
Yana buɗewa suka zura wa junansu idanu.Tausayinsa da damuwa da halin da yake ciki suka ƙara kamata
Tsayawa ta yi cikin yanayi na jimamai, sai kuma ta ɗauke idanunta ganin ya ƙi cire nasa.
"A haka za ka yi angwancin?" Ta yi masa tambayar cikin tausayi.
Ƙaramin tsuka ya ja jin tambayar da ta yi masa.
"Ya Huwais, ka ga yadda ka koma? Dubi gashin ƙasumba da ka tara. Don Allah ka cire komai a ranka ka yi addu'a kar ka janyo wa kanka cuta mu shiga uku."
"Ina jin zuciyata tana zafi! Ummu ba za ta gane É—acin da na ke ji ba, saboda auren soyayya ta yi da Abu. Hilah, Ummu ta gama kashe mini farincikin rayuwata tun da ta hana ni da wacce zuciyata ba ta muradinta."
"Please, ka daina faɗin haka. Aurenku sai family ɗinmu sun yi alfahari da shi. Anty Wajnah na da kirki ba za ka yi dana sanin zama da ita, kuma Ya Huwais, Allah ya ba ka damar ƙarin aure, in har ka samu damar auren wacce kake so za ka iya ƙara aure."
"Ta yi mini nisa ba za ta aure ni ba, amma na san sonta shi ne ajalina."
"Ka so abin da ka san za ka samu ba wanda ba za ka samu ba. Na ce ka gaya mini inda take zan je na gaya mata yadda kake son ta na kuma roƙe ta ta aureka."
A ransa ya ce,"Ke ce Hilah! Kece wacce zuciyata take mafarkin samu a matsayin mata, amma kuma ba zan taba mallakarki ba."
A fili kuwa zura mata idanu ya yi, wanda ya sanya ta ɗauko kunun gyaɗar ta iba ta miƙa masa a baki.
Kauda kansa ya yi, yana faÉ—in,"Ba na jin É—anÉ—anon abinci na rasa É—andanon bakina."
"Ka ci kar ka yi wa kanka horar yunwa."
Babu musu ya karɓa jin abin da ta ce. Yana cikin sha su Abidin suka shigo.
"Yauwa Hilah, dama neman ki muke a cikin gida. Tun ɗazu muka kawo masa break amma ya ƙi ci. Yaya yana son ya yi mana asarar kansa, bayan ya san in har babu shi ba zamu iya rayuwa." Affan ya ce tare da zaunawa a gefensa
Tausayin ƙannin na sa ya kamashi ganin yadda suka nuna tsantsar damuwarsu.
Hankalinsu bai kwanta ba, har sai da ya shanye tas! Hilah ce ta miƙe don ta gyara ɗakinsa.
"Bari muje zamu karɓo ɗinki mu a gurin tela. Hilah ki kula da shi."
Murmushi ta yi tare da É—aga kanta ta ci gaba da gyara falon.
Tana aikin duk ta É—ago idanunta sai ta ga yana kallonta.
"Gaya mini Hilah in har mahaukacin masoyi ya bayyana yana da mata zaki aure shi?"
"Mai yasa ka tambaya Yaya?"
"Saboda ni ma na gane, in har wacce nake so ta ji ina da mata za ta iya aurena." Ya ba ta amsa jin tambayar da ta yi masa a maimakon amsar wace ya yi mata.
"Eh, zan iya aurensa saboda ina matuƙar sonsa, in har zan auresa matuƙar ya cika duk sharuɗan da ya kamata na aure shi a addini ban damu ba."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 15