← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 40

Sashe 22

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya amsa ta É—ora da cewa,"Kam me za ka tafi da ita, ba tare da ka sanar mini ba?"

"Huwais, zauna magana za mu yi." Abu ya furta bayan ya samu guri ya zauna kan kujera.

Yadda ya yi maganar, ya baƙanta mata duk da cewar ta san ba zai ɗauki lamarin da girma ba, amma ya kamata ya tsawata masa.

"Ya kamata ka yi masa faÉ—a, saboda wallahi kan wani banzar tunaninsa ba zan lamunta ya raba mana zumunci ba." Ummu ta faÉ—a tana kallon Abu da Huwais yake kallo, sai kuma ya juya yana kallon Hilah wacce take tsaye tana mazurai.

"Kai ba yaro bane. Sam bai kamata ace mun tsaya, muna gaya maka abin da ya kamata ba. Da ga yau kar na ƙara jin ka yi faɗa da Hamad. Karka manta ɗan'uwanka ne na jini. Ku wuce ciki ku bani guri." Ya ƙarashe maganar cikin ɓacin rai.

Jin abin da ya ce masa ya ƙular da Ummu cikin fushi ta miƙe fuuu! Ta yi cikin ɗakinta.

"Ka tabbatar da ka je gurin amaryarka tsakanin yau da gobe, kuma ka bata duk abin da take buƙata." Abu ya ce masa daidai lokacin da ya miƙe zai fice.

Kaɗa masa kansa kawai ya yi cikin takaici ya fice yana jin zuciyarsa na yi masa tuƙuƙi.

Bayan sun tafi dariya ya yi ya girgiza kansa ya bita zuaa É—akin.

Hilah ta ji daɗi da Abu yake gida, domin ta san cewa wataƙila da sai ta sha mari. Tana shiga cikin ɗakin ta rage kayanta, daga ita sai silet da vest. Kan doguwar kujera ta kwanta tare da ɗaukar wayarta ta kunna data.

Da ga kunna datar tsaƙon mahaukacin masoyi suka rinƙa shigowa. Da sauri ta mayar masa da tsaƙon, wanda duk yawanci kalaman soyayya ne.

Yayana, wanda na ke masifar so fiye da komai a rayuwata zai yi aure, kuma ina gayyatarka bikin, domin saboda mahimmancin wannan ranar nake son ka bayyana mini kanka a ranar. Matuƙar ka ƙi bayyana mini kanka ba zan ƙara kula ba, kuma zan yi ƙoƙari na haƙura da kai ko da ace soyayyarka ita ce ajalina.

Huwais da ke riƙe da wayarsa, yana ta dariyar a bin da ta tura masa, sai kuma zuciyarsa ta buga da tsoron da gaske za ta iya rabuwa da shi.

Rubuta masa ta yi ta tura, sai kuma ta kasa jurewa har ya turo mata da amsa, ganin ya kara ta bai turo amsar ba.

Kiran layinsa ta Whatsapp ta yi har ta katse bai É—auka ba.

Tana ƙoƙarin ƙara kira sai ga kira sa ya shigo. Da sauri ta ɗauka tare da doka masa sallama cikin sanyin murya.

"Ina fatan ka ga tsaƙona?"

"Eh, na gani amma kuma kalamanki na ƙarshe da hukuncin da kika yanke sun yi tsauri a gareni."

"Kuma na riga na ya ke shawara. In har kan sona da aure ka bayyana kanka a ranar bikin Yayana, in kuma ka ƙi bayyana kanka na haƙura da kai, domin babu inda na taɓa jin anyi aure ba tare da anga juna ba."

Ajiyar zuciya ya saki, wanda bugun da ya sanya zuciyarta har sai da ta kauda wayar a kunninta ta rintse ido.

"Kin shirya ganina?"

"Eh, kuma na yi maka alƙawarin aurenka ko da ace kai musaƙi ne."

"Shikenan, zan yi tunani in har ya kamata na bayyana miki kaina zan bayyana."

Yana faɗin hakan ya kashe wayarsa cikin tsananin tashin hankali. Safa da marwa ya fara yi a ɗakin, saboda yana jin ko aure ya yi ba zai iya daina jin muryarta da take kwantar masa da hankali ba. To amma kuma ta ya ya zai bayyana kansa kamar yadda ta buƙata? Shin inta gan shi wane hali za ta shiga, wanda ya san lamarin da ƙarshe ba xai yi daɗi ba, saboda yadda ta riga ta mutu a kansa.

"Zuciyarsa ta ba shi shawarar ya tura wani da bata taɓa sani ba, amma sai dai kuma ta gargaɗe sa da aikata hakan, saboda in har ta ɗauka shi ne mahaukacin masoyi ta kamu da son wancan, sai ya ce an yi ba ayi ba.

A ransa ya ji ba zai iya bayyana kansa ba, domin a wannan lokacin yake son ya É—auko rigimar da zata wargaza farincikin zuriyarsu ba, don haka a kwai sauran lokaci.

Wayarsa ce ta yi ƙara alamun an turo masa da tsaƙo. Da sauri ya ƙarasa gurin wayar don ya duba tsaƙon

"Yayana, na gaya masa cewar ya bayyana kansa gareni ranar bikinka, kuma na yi masa barazanar rabuwa da shi matuƙar ya kasa yin hakan, amma bai ce mini komai ba, sai ma ya kashe waya. Na san zai kira ni kuma ya amince, saboda na san yana sona.

Wayarsa ya ije cikin damuwa ganin abin da ta rubuta.

"Anya Hilah za ta yafe mini matuƙar ta san ni nake wasa da hankalinta?" Ya yi ma kansa tambayar cikin damuwa. Ga mamakinsa sai ya ji hawaye na bin ƙuncinsa. Kansa ya dafe da ke matuƙar yi masa barazana.

Ta bangaren amarya gyara kawai ake yi babu kama hannun yaro. Tun a ranar da aka sanya bikin ta kama shan kayan mata ba tare da ta bi ƙa'idansu ba, saboda so take bayan biki, ya raina kansa. Wannan ji da kai da sham ƙanshi da yake mata ya gane kuransa.

Wajnah na cikin jadawalin mata da ba su tausayawa namiji a bangaren soyayya da aure, domin a tsarin rayuwarta. Ta auri namiji da zai zamo bawanta wanda za ta rinƙa juyashi yadda take so. Wato ta samu miji janitalau, wanda ta ci alƙawarin ko da ba ta samu ba, sai ta maida shi hakan ta hanyar shaye-shayen maganin mata.

A burinta ta so auren namiji wanda yake masifar sonta, don ta yi amfani da soyayyarsa ta juya shi yadda take so, amma cikin rashin sa'a sai Allah ya jarrabce ta da son Huwais, wanda shi ko a cikin family ta san basa shiri, saboda yadda take nuna wayewa da yawa.

A rayuwarsa ya tsani mace wacce feminism ɗinta ya yi yawa. Tun kafin ta fara nuna tana son shi, ya gane ita mace ce wacce take ganin mata sun samu daraja ne ta hanyar buƙatar da namiji yake da shi a garesu, wanda hakan ya sa take ganin kamar namiji bawa yake a garesu, kuma suna da damar da za su juya su yadda suke so.

Tun lokacin ya ɗaura mata karan tsana sam baya shiga sabgarta. Yana ganin ta a mara hankali da ƙarancin ilmin addini, domin duk wani gata da daraja mace Allah ya bawa mace, saboda ita ma halitta ce wcce ya halitta don su bauta masa.

Zaune take a cikin falon ƙawarta mai suna Fahima, da waya a hannunta tana zaɓan kayan mata da Hajiya zamzam; wacce take saida kayan mata a online ta tura mata.

Bayan ta zaɓi kayan da yawa wanda zaɓen yawanci Fahima ce ta taya ta, kasancewar ita matar aure ce har da yarinya ɗaya.

"Kin ga wannan sha ka ga aikin wallahi ki ɗauka yana da kyau, domin Hajiya Zamzam in har kika ga ta kawo kayan mata na gargajiya yana da kyau, saboda kayanta kin san duk na bature take siyarwa. Kuma da bikina na sha irinsa, shi ne na gaya miki Baban Amrah ya bani kyautar hajji, saboda duk lokacin da na sha ni kaina da ƙyar nake iya riƙe kaina."

Dariya ta kwashe da shi suka tafa. Aikuwa ya zama dalo na siye shi. Don so na ke Ya Huwais ya raina kansa. Ni fa so na ke ko kara na ije ya kasa tsallakawa, domin ya san in bai yi mini abin da na ke so ba, ba zan faranta masa rai ba."

"Eh, gaskiya. Ke ai magani sosai ya kamata ki siya saboda wannan miskilin da za ki aura. Kin ga in ba tsaye kika yi masa ba, wallahi wulaƙanci za ki sha sosai. Musamman da ba ya sonki."

Ƙuta ta yi cikin ɓacin rai." Ki barshi zai raina kansa sosai. Ba ni yake cika yake sharewa ba, saboda kawai na ce ina son shi. Wallahi sai na maida shi namijin ta ce babu boka babu malam. Don kawai Ummu ƴar'uwar mom ce, amma da ko ita sai na shiga tsakaninsu babu boka babu malam."

Dariya ta saki." Ai gara ki je da shirin ki maza yanzu babu tausayi a tsakaninmu da su, saboda kina musu sakwa-sakwa sai wulaƙanci da rashin mutunci. Sam bana son na kasance daga cikin irin matan da suke hide my identity a sirrin ƴa mace groups, kin ga kuwa dole na dage na kashe kuɗina na gyara jikina, don na siyawa kaina daraja da mutunci."

Dariya suka kwashe dashi suka tafa, ban da Habiba ta take kallonsu cikin mamaki tana murmushi.

"Ke dai sha'anin rijalu sai su. Ƙiri-ƙiri sun mayar da mata mahaukata sun sanya musu depression."

"Ai wallahi su suka so. Ke ni fa duk macen da ta zauna namiji na wulaƙanta ta ta ji za ta iya ne, don haka in har kuɗi na aiki zan siya maganin mata na gyara jikina, wanda kafin na ba shi haɗin kai sai ya yi kuka."

"Lallai ba ki da imani wallahi."

Habiba ta kalle su da suke ta magana ba ta sanya baki sai a lokaci ta yi murmushi ta ce," A tunaninku shan kayan matan shi zai gyara rayuwar auren ku? Ba zan fasa gaya muku ba a matsayina na ƙawarku aminiya. Wallahi ku guji shaye-shayen kayan nan da kuke yi, saboda ba ku san da me aka haɗa su ba musamman da bature, domin zai iya kai ku tashar dana sani. Kuna cusawa kanku abin da ba ku da tabbaci a kansa, don kawai ku juya mazajenku. To daga ranar da kuka daina shan kayan matan, ko kuma ya daina muku aiki shi kenan kun rasa damarku? Ni a ganina wannan kuskure ne, domin in har za ku riƙe biyayya da haƙuri za ku juya mazajenku yadda kuke so."

"Hmmm!Ta fara ni wallahi ban san dalilin da ya sanya kika na ce za ki zo yau ba." Wajnah ta ce tana aika wa Habiba da mugun kallo.
Chapter 22 · 0% Book details