← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 40

Sashe 7

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gurin ya yi sit! Ba ka jin komai sai ƙarar A.C da numfashin mutane. Har ta ƙare karatun cikin murya mai tsananin daɗi.

Huwais da ya koma ya zauna, hankalinsa ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana jin yadda take zubo karatun cikin murya mai daɗi, da fitar da tajweed tsantsa. Duk inda aka yanko mata sai ta ɗauka tana karantawa cikin gwanancewa. Ya tabbatar wa kansa a karo na biyu in har ya bari ta kubce masa a matsayin matarsa ya yi asarar da bai zai taɓa mayar da ita ba. To amma ta yaya? Don shi dai ko a garin gaɓa-gaɓa bai taɓa ganin Ya ya auri ƙanwa ba. To amma ya akai zuciyarsa da tunaninsa suke ƙarfafa masa watarana za ta zamo matarsa kuma uwar 'yayansa domin perspective ɗinsa kullum kuma mafarkinsa.

Kabbarar mutanen gurin ya dawo da shi daga tunanin da yake yi wanda shi ma ya É—auki nasa kabbarar.

Kuka sosai take yi tana ganin yadda mutane suka ƙoƙarin ɗaukar ta hoto.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 5

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

Kabbarar mutanen gurin ya dawo da shi daga tunanin da yake yi wanda shi ma ya É—auki nasa kabbarar.

Kuka sosai take yi tana ganin yadda mutane suka dabaibayeta suna son É—aukar hoto da ita. Tun daga kan larabawa da jajayen fata.

Da ƙyar iyayenta suka samu damar ɗaukar hoto da ita, wanda ana gamawa ta ja Huwais gefe.

"Ya ya sanar da ni yana nan tabbas kuma naji a jikina yana nan, wasa da hankalina yake yi! Anya masoyi ne ko maƙiyi? Domin ba zai tura mini tsaƙon da ya rikita ni a daidai lokacin da zan fara musabaƙar ba." Ta ce tare da kama hannunshi tana kuka.

Jikinsa ya yi sanyi sosai duk da ya san cewa bai kyauta ba, amma sai ya ji kalamanta tamkar dafi na maciji, musamman da kunnuwansa suka ƙara ji masa lokacin da take cewa.

"Na tsane shi bana sonsa! Idan ya yi hakan ne don ya samu soyayyata, haƙiƙa ya yaudari kansa, domin a halin yanzu ba ni da maƙiyi sama da shi, kuma wallahi da ya sanya na faɗi a gasar nan, burina ya tashi a tutan ma'aho da bazan taɓa yafe masa ba, kamar yadda ba zan yafe ma kaina ba, domin lokacin da na fara shiga gasa na sawa burin karɓo wa Ƙasata kabbu!"

"Bai kyauta ba shima ya yi kuskure! Tabbas ya zama cikkaken mahaukacin da baya iya gane komai sai cimma soyayarsa." Ya ce mata domin shi ma ya ga wautarsa.

"Yana nan gurin ta ya ya zan iya gane sa na kikkifa masa mari ko zuciyata za ta yi sanyi." Ta ce tana kallon sa sai kuma ta fara dube-dube.

"Ba za ki iya ganinsa ba duba ga dubban mutanen da suke gurin nan."

"Zan iya Yaya, na yarda mahaukaci ne don haka dole ya fita daga siffar masu hankali." Ta ce cikin É—an É—aga murya.

"Anya hanyar da na ɗauko mai ɓullewa ne, domin na gane a maimakon ta soni sai dai na ta tsane ni, tunkafin ta san ko ni wane ne." Ya ce tare da rintse idanunsa.

Ba tare da ya hana ta ba ya koma kujerarsa ya zauna, yana ganinta tana dube-dube, amma bai ce mata komai ba, domin haushin maganarta sun sanya shi jin haushinta.

Ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana dube-dube ya sanya shi miƙewa. Cikin rashin ƙarfin jiki ya isa gareta, tare da kama hannunta zuwa mota.

Faɗawa ƙirshijin shi ta yi tare da sakin kuka mai ƙargi ta ce,"I hate him."

Ji ya yi tamkar ta coka masa mashi a zuciyarsa har sai da ya rintse idanunsa, jin abin da ta furta.

Bayanta ya shiga shafawa domin ya kasa janyeta daga jikinsa har tsawon lokaci. Suna a haka ya ga Ummu ta nufo motar da sauri wa da ya sanya shi zare ta daga jikinsa ya nuna mata Ummu.

Da sauri ta fita daga motar tana zare idanunta. Ummu na isowa ta aika mata da mugun kallo cikin ɓacin rai ta juya ba tare da ta ce mata komai ba.

Ganin ta yi tsaye ta kasa bin bayanta ya sanya shi fitowa daga cikin motar. Hannunta ya kama suka fara tafiya zuwa gurin mutane.

Cikin nasara ta samu nasarar lashe gasar domin ta zamo zakaran gwajin dafi a tsakanin rawuna. Ta samu kyautittika da dama ita kanta ba za ta manta da wannan ranar ba, domin rana ce na musamman gareta. A ranar da ta kasance zinariya ga mutane ta amso wa ƙasarta kimarta da darajarta. Iyaye da dama sun mafarkin ace ita 'yarsu ce, wanda har da waɗanda suka tako suka nuna hakan.

Bayan sun dawo sun yi hutun gajiya. Suna zaune a falo suna cin abincin da aka shirya mata.
GabakiÉ—aya abincin oder É—in shi aka yi.

Hira suke cikin nishaɗi da fara'a wanda rabin hirar duk kan gasar da ta ciyo ne. Ummu ne kawai ba ta cika soma baki ba sai dai ta yi murmushi, amma fuskarta cike take da farinciki matuƙa.

Hamsiya mai aiki ce ta yi sallama ta shigo tare da duƙawa cikin girmamawa ta ce,

"Inusa, direba ya ce na kawo wannnan wani ne ya turo tsaƙon a bawa Hilah har da mota a waje."

GabkiÉ—aya suka kalleta cikin tsananin mamaki.

Hilah kuwa Huwais ta kalla, yayin da idanunta suka firfito saboda ta zargi tsaƙon daga mahaukacin masoyi ne.

Amma sai ta ga ko a jikin shi domin ba ita yake kallo ba, wayarsa ya maida hankali kanta yana dandannawa.

A daidai lokacin tsaƙo ya shigo cikin wayarta, wanda har sai da ta miƙe a zabure ta kasa kallon wayar, ballanatana ta ga wanda ya turo mata.

Sai da ta ɗan ɗauki sakanni sannan ta duba. Hasashenta ya zama gaskiya domin shi ne. Mahaukacin masoyi ne ya ƙara turo mata tsaƙo kamar haka:

"Amincin Allah ya tabbata ga wannan abociyar haske! Na san na yi miki laifi, don Allah ki yafe mini ga tsaƙo nan. Ina miki murnan lashe gasar da kika yi." Tsanananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta.

"Waye shi wanda ya kawo tsaƙon irin wanna tsadaddiyar wayar da mota ya siya mata haka? Kai Huwais, ma za ka je ka gani." Ummu ta furta fuskarta bayyane da mamaki.

"No, bari na je tun da ina nan." Abu ya ce tare da dakatar da shi da ya miƙe fuskarsa babu yabo ba fallasa sai ya koma ya zauna yayin da Ummu ta bi shi da kallo.

"Inusa, ina wanda ya kawo tsaƙon?" Abu ya ce masa yana waige-waige tare da kallon tsadadiyar motar cikin tsananin mamaki.

"Ranka ya daÉ—e, bayan ya gaya mini sai na je na gaya wa Hamsiya, kafin na dawo na neme shi na rasa kamar aljani."

Mamaki ya ƙara kamasa sosai yana mamakin ace wanda ya kawo irin wannan tsaƙon ya ƙi bayyana kansa.

"Ikon Allah!" Ya ce cikin mamaki tare da juyawa ya koma ciki wanda ya same su cirko-cirko ban da shi da yake ta cin abinsa hankalinsa kwance.

Zama ya yi kan kujera domin ya ji abincin ya gimshe shi.

"Ɗan tsaƙon ya tafi." Ajiyar zuciya ya saki domin ya ɗan ji fargabar kar su kama wanda ya turo, amma jin hakan sai hankalin shi ya kwanta tamkar ya yi baƙo ya mutu.

"Waye wannan ya yi mata wannan kyautar! Ke Hilah kin san shi ne?" Ummu ta jeho mata tambayar da ya sanya ta É—ago a razane tana girgiza kanta.

"Magana za ki yi mini ba girgiza kai ba, ko kin zama kurma ne? Ai na lura tun da aka gaya tsaƙon kika ruɗe. Uban me kike ɓoyewa."

"Um ni wallahi babu! Dama an um!" Ta shiga faɗin haka sai kuma ta fara in-ina sai ta saka kuka, wanda hakan ya sa ta zargeta ranta ya ɓace.

"Za ki rufe mini baki daga magana sai kuka ke ga ki mai fuskar kuka ko!" Ta daka mata tsawa tana faÉ—in hakan, wanda ya sanya ta haÉ—iyar kukanta cikin tsoro, don tsawar harta sauran 'yan'uwanta sai da suka razana.

"Haba Laila, ki yi mata a hankali."Abu ya ce tare da kamo hannunta ya zaunar da ita kusa da shi.

"Kin san shi ne?" Ya tambayeta cikin tautausar murya.

"Eh! A'a." Ta ba shi duka amsar cikin rawar murya sai kuma ta É—ora da cewa,

"Da ma ya turo mini da tsaƙo kwanakin baya da kyautar miliyan ɗaya sai kuma ranar da musabaƙa ya tura mini tsako, amma wallahi ban taɓa ganin shi ba." Ta ce cikin kuka.

Mamaki ya kamasu ƙwarai Ummu har da salati tana tafa hannu.

Ganin yadda suka ruÉ—e sai ta ci gaba da gaba da magana cikin inda-inda,"Na gaya wa Huwais, shi ne ya ce kar na sanar muku." Ta ce tana kallonsa cikin jin haushin komin kula da ya nuna kan lamarin ga shi an tsareta an tambayarta ko a jikin shi.

"Innalillahi! Yaushe kuka girma har kuke yanke shawara iya kanku? Huwais, shi ya haife ki, na ga dukkaninku ikonmu ne, amma ba ku sanar mana ba?" Ta ce cikin zafi zata mare ta wanda ta ɓoye cikin sauri bayan Abu tare da dafe ƙuncinta tana kuka.

"Karki taɓata ga babban kwabo nan, duk da cewar shin a yaro bane, wataƙila yana da dalillinsa."
Chapter 7 · 0% Book details