Sashe 33
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Babu wata aljana tsabar ƙiyayya ce da taurin kai. Ba ki ji yadda ya rinƙa kushe ni yana yabon wacce yake so ba. Ni da ya kamata jiya ya zamar mini rama memorable sai ga shi na yi kwanar wahala." Ta ƙarashe maganar tana cije baki.
"Ikon Allah, ni kam ban san wane irin miji kika aura ba, amma duk ƙawayenmu da suka yi amfani da shi sun ce ya yi musu."
"Wash! Ki taimaka ki gaya mini abin da zan sha na samu na rintse. Jiya sam ban rintsa ba."
"Kai amma wannan gayen ya ɓata mana show. Ni da na kasa bacci sai zumuɗi na ke yi Allah ya kaimu gobe musha labari. Kuma wallahi ya ja miki abin kunya, saboda duk ƙawayenmu kowa sai ya ba da labarin first night ɗinsa a group sai ke? Kin san yau daren farkon ki shine topic of discussion ɗinmu."
Tsuka taja tare da jin wasu zafafen hawaye sun wanke mata fuska, saboda yau ta yi ninyar babu abin da za ta rage wanda ya faru a tsakaninsu."
Wa'iyazubillahi
"Ya zan yi? Haka nan zan shirga musu ƙaryar period ɗina ya zo kafin na gama na san yadda zan yi seducing ɗinsa."
"Gaskiya ya kamata domin hakan kamar wani abin kunya yake son ya ja miki."
"Ya ma isa ina babban yarinya kamata ya ce zai toxarta ni gurin ƙawayena."
"Allah ya kyau abu dai yi daÉ—i ba." Cewar Wahida cikin takaici.
"Ko gaya mini abin da zan sha."
"Ki sha kanwa za ki samu sauƙi." Ta ce tare da yi mata sallama ta kashe wayar.
Sororo ta yi cikin takaici da damuwa. Sai yanzu ta fara dana-sanin gaya mata da ta yi. Ta so ace ƙarya ta shirga musu sai dai kuma hakan ba zai yiwu ba, kasancewarsu ta san su da shegen bin ƙididdifi har sai sun gano gaskiya.
Miƙewa ta yi tana tunanin inda za ta samu kanwa amma ba ta gani a kicin ɗinta ba.
Wayarta ta ciro tare da sanar mata ta aiko direba da kanwar.
Huwais kiran sallar farko ya tashi farka daga baccin da ya ɗauke shi. Miƙewa ya yi bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga bacci, sai kuma ya yi salati yana miƙa.
Bayi ya shige ya yi wanka sannan ya fito masallacin gidansa. Shi ya ja musu sallah suka yi sannan ya É—an zauna a masallacin har gari ya yi sha.
A lokacin da gari ya waye ya fito daga masallacin ya shiga gida, daidai lokacin da Wajnah ta fito direba ya kawo mata kanwar.
Cikin rashin sa'a ya kalle ta wanda ya sanya shi ɗauke kansa da sauri. Dariya ƙeta yake mata a zuciya ganin yadda ta yi wujuju da ita, alamun sam ba ta rintsa ba.
Wucewa ɗakinsa ya yi, yayin da ta bishi da kallo tana ji kamar ta jawo shi ta rufe shi da duka. Da idanu ta raka shi har ya shige ɗaki ya rufe ƙofar. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta wuce kicin ta kaɗa kanwar a kofi tasha.
Sai a wannan lokacin ta É—an fara sanun natsuwa ta shiga bayi ta yi wanka da alwala ta fito.
Bayan ta yi sallar tana idarwa ta É—auki waya ta kira Mommy. Tana É—auka ta fashe da kuka.
"Mommy, ban san cewar ƙiyayyar da Ya Huwais, ya ke mini ba ta kai haka! In kika ga yadda ya wulaƙanta ni sai kin tausaya mini. Momy kulle ɗakinsa ya ya bar ni a falo."
Tausayin ƴar tata ya kamata da ma ta san xa a rina, wai an saci xanin mahaukaciya. Sam ba ya ƙaunarta su ne suka nace auren.
"Kina jina ko Wajnah? Dole sai kin yi haƙuri kin zama jaruma, domin kin san babu so a tsakaninku. A hankali cikin kissa da kisisina irin ta ƴa mace za ki karkato da hankalinsa."
"Hmmmm! Ba ki san shi bane, jiya na tsorata da lamarinsa."
"Sam karki tsorota ki ci gaba da yi masa duk abin da kika san zai faranta ransa, kuma karki nuna masa kin ji haushi. In muka ga yaƙi canxawa sai mu sanar da mahaifiyarsa ayi wa abin tufka hanci, amma bai kamata daga aurenku afara kai mata ƙorafi ba."
"To Mommy, yaushe za ki zo? Har na fara kewarki."
Dariya ta yi jin abin da ta ce. "Ina nan zuwa ni da Anty ki Hibba, za ta kawo sauran kayan turaren wutan da ba gaba ma."
"Sai kun zo na gode Mommy." Tana gama wayar bacci mai ƙarfi ya kwasheta.
Huwais kuwa alla-alla yake gari ya waye ya bar gidan. Tun da ya farka idanunsa suke masa gizagonta, musamman da ya kwana mafarkinta.
Yana dawowa daga masallaci, ya shirya cikin shiga mai kyau ya shiga motarsa ya fice daga gidan.
Ƙarar buɗe get ɗin, ya tashe ta wanda ya sa ta miƙe a zabure tare da jaye labulen ɗakin tana hangen harabar wajen
"Kan uba! Ina wannan É—an rainin wayon xai je da safiyar nan?" Ta yi wa kanta tambayar cikin mamaki a zuciyarta tana ji kamar ta danna masa ashar.
Sakin labulen ta yi, daidai lokacin da ya fice maigadi ya rufe get É—in yana É—aga masa hannu.
Zama ta yi tana huci kamar mesa, sai kuma ta shige É—aki fuuu! Ta jawo waya. Har ta fara neman numbar Wahida za ta gaya mata, sai ta fasa tuna yadda take ta cika musu baki, wanda sanin zaman doya da manjar da suke yi, zai iya sanya wa su yi mata dariya, da gulmanta ko da a bayan idanunta ne. Fasa kiran ta yi ta fara neman numbar Ummu sai kuma ita ma wata zuciya ta hana ta musamman da ta tuna maganar da Mommy ta gaya mata.
Wayarta ta yi jifa da ita, tare da kwanciya a kan gadon tana birgima!
Huwais kuwa, a hanya yana tafe yana tunanin yadda za su kwashe da Ummu, in ta ga ya yi sammakon zuwa gidan, amma duk abin da xai faru sai dai ya faru, domin idanuwansa babu wanda suke son gani sai ita. Saboda tsoron kar ya tashi mutanen gidan a waje ya yi parking ɗin motarsa ya shiga ciki. Kai tsaye falo ya shiga, amma babu wanda ya gani sai ɓuruntu da ya ji a kicin. Ba tare da ɓata lokaci ba, ya nufi kicin ɗin domin ya san ita ce a ciki.
Hilah bayan ta tashi ta shiga bayi sai ta ga ta fara fashin sallah. Gyara kanta ta yi, ta fito daga bayin ta shiga É—akin su Umnah ta tashe su, sannan ta wuce kicin don shirya abin karyawa.
Ita da autar su Ummu, Sauwama suka fara haÉ—a abincin karyawar suna yi suna hira.
Bayan sun gama kammala abincin, suka sanya a cikin fulas sannan suka sanya wanda za su kai gidan Huwais a basket.
Hilah na gyara zaman abincin yayin da bakinta É—auke da tasbihi tana faÉ—in Subuhanallahi wa bihamdihi wa subuhanallahil azeem. Hadisi ne inagacce wanda ya yi maganar cewa,
Kalomi masu sauƙin faɗi a harshe, kuma mafi soyuwa a gurin Allah masu kuma nauyaya mixani.
Da wannan hadisi take amfani yawanci bakinta É—auke da shi.
Tana ƙoƙarin ɗaukar basket ɗin ta kai mota ta ɗago idanunta.
Turus! Ta tsaya cikin tsananin mamaki tana kallon agogon da ke manne a saman bangon kicin É—in. Mamaki ya sanya ta kasa magana sai kallonsa take yi.
"Yauwa ma za ki je ki kai mota. Ni ma bari na gama dama wa Fitha custard sai na É—auko mayafina muje, saboda yau nake son na koma Gobbe.
Jin ta yi shiru ba ta amsa mata ba, ya sanya ta É—ago idanunta, tana kallon inda take kallo.
"A'a ango da sassafe haka, lafiya ko dai Wajnah ce babu lafiya?"
Shafa kansa ya yi cikin jin kunya yana kallonta da har yanzu ta kasa magana.
"Lafiyarta lau, kewar gida ne kawai ya dame ni.
Dariya ta kubce mata jin abinnda ya ce." DaÉ—i ne ya yi maka yawa kawai Huwais. Kuma in ban da abin ka namiji ne da kewar gida? Ai kamata ya yi a ce Wajnah ta faÉ—i haka."
"Please Anty Sauwama yunwa na ke ji, ni fa tun jiya rabona da abinci." Ya faÉ—a yana shafa cikinsa.
Daga ita har Hilah suka zaro idanu."Ace jiya bikinka amma ka zaina da yunwa? Ita Wajnah aikin mai take yi da ba ta tabbatar ka ci abinci ba kafin ka kwanta?"
Taɓe bakinsa ya yi yana ƙoƙarin ɗaukar filet.
Hilah kuwa karɓar filet ɗin ta yi cikin damuwa tana faɗin,"Yayana, don Allah karka ƙara horar da kanka da yunwa."
Watsa mata kallo ya yi bai ce komai ba.
"Kamata ya yi ya tafi da abincin sai su je can su ci, wataƙila Wajnah ba lafiya ba za ta iya musu abin kari ba"
"No bari na ci nawa anan."Ya ce yana kallon Hilah wacce ta daina ƙoƙarin zuba masa, jin abin da ya ce ta fara zuba masa.
Miƙa masa ta yi sai kuma ta fasa ba shi."Bari na kai maka dinning."
Ba tare da ya ce komai ba ya bi bayanta.
"Thanks," Ya furta yana kallonta da ta miƙa masa ta tsaya a gabansa tana kallonsa.
Bayan Sauwama fa gama haÉ—a wa Æ´arta custard É—in, sai ta É—auki kofin ta yi cikin É—akin Ummu wanda anan suka kwana.
Ummu na zaune da carbi a hannunta, tana wa Allah godiya da ya nuna mata auren ta samu guri ta zauna.
Lamarin Huwais sai a hankali." Ta ce tana dariya wanda ya sanya ta juyo da sauri yayin da gabanta ya faÉ—i.
"Wai shi da yake da amarya, amma har ya baro ta yazo gidan nan yana ihun yunwa."
Gabanta ne ya ƙara faɗi, wanda ya sa ta miƙe cikin ɓacin rai, tana jin kamar ta kifa masa mari.
"Huwais É—in ya baro gidan matarsa yana nan?"
"Ki je yana falo yana cin abinci kika sheda, don har mun haÉ—a abin lari za mu je a kai mas..."
Ba tare da ta ƙarasa jin abin da take faɗi ba ta wuce falo da sauri.
Turus ta tsaya cikin tsananin ɓacin rai, tana kallonsa da ya kashe Hilah da ke xaune gabansa tana murmushi.
Tsananin ɓacin rai ya ƙara kamata. Ji ta yi kamar ta rufe su da duka.
"Huwais," Ta kira sunasa da ƙarfi tana huci.