← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 40

Sashe 17

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ummu, in har auren Wajnah, shi ne farincikin ki na aminta." Ya ce tare da miƙewa zai fice. Har cikin zuciyarsa yake jin zai haƙura ko da a ce son na ta zai zamo ajalinsa, da ace ya zama sanadiyar ɓacin ran mahaifiyarsa gara ya haƙura. In ya yi ajalinsa ya huta da baƙincikin da yake ƙurba a dalilin sonta.Ya miƙe yana layi tamkar zai faɗi.

Bin shi da kallo ta yi cikin tsananin tausayawa. Tana matuƙar son ɗan na ta, saboda yaro ne mai matuƙar biyayya.

"Huwais," Ta furta cikin sanyin murya.

"Na siyo maka kayan da za ka ci biki da su set biyar. Na bawa Telanmu gayu. Ka duba kayan na tura maka a wayarka, in ba su isa ba sai na ƙara. Sannan ya kamata ku shirya kai da ƙannenka ku je ku gaida Hajiya, domin tana mini mitar baka son zuwa gurinta."

"In sha Allah, za mu je. Bari na gaya wa Hilah su shirya bayan sallar la'asar sai mu je."

"Kar ka damu je ka zan gaya mata, kuma ga kamata ka samu lokaci ka je zance, saboda Mommyn Wajnah ta gaya mini ba ka taɓa zuwa ba, don yarinyar na son ka ne ba ta ƙorafi."

Maganar ƙarshe ya baƙanta ransa, domin ya kasa cewa komai sai kansa da ya kaɗa, tare da watsa mata kallon na rashin yadda da har yanzu ta kasa yi da shi. Wataƙila tunaninta zai iya cutar da Hilah ne, ko kuma wani abin take hasashowa a ranta. Sai dai kuma har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin matuƙar ta yi masa aure shi kuma sai ya san yadda zai yi ya ƙirƙiro abin da zai sanya Hilah ta koma rayuwa a gidansa, kafin ya samu hanyar da za ta zamo mallakinsa.

Ɗaki ya shige tare da zama bayan ya ƙara ƙarfin A.C ya zauna kan kujera. Remote ya ɗauka ya kunna labarai.

Wayarsa ya janyo ya kunna data. So yake ya yi hira da ita, tun da suke magana bai taɓa kiran ta da rana ba, amma yau a yadda ya a ganta cikin abaya baƙa sai ya ji ba zai iya haƙurin har dare su yi waya ba.

A lokacin tana kicin tana yanka salat kiran ya shigo. Ba tare da ta kalli wayar ba, sai ta ci gaba da aikinta domin ba ta ƙaunar abin da zai katse mata girkin, musamman da ta yi ranar yin girkin.

Ƙara kiran zuciyarta ta raya mata ko mahaukacin masoyi ya kirata.Da sauri ta kalli fuskar a zuciyarta tana addu'ar shi ne.

Ga mamakinta sai kawai ta ga numbarsa da sitikar soyayya da ta yi saving da su.

ÆŠauraye hannunta ta yi tare da danna amsa kira ta kanga wayar a kunnenta.

"Ina cikin damuwa masoyiyata rayuwata matuƙar babu ke! Haƙiƙa ba zam iya numfashi ba."

Wani irin tashin hankali ya ziyarce ta, domin in har ba gizo kunnenta suke yi mata ba, muryar Ya Huwais ta ji.

"Ya Huwais?" Ta kira sunan shi cikin ƙara da raji.

Saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga bai san lokacin da ya yi wurgi da wayar ba, domin ya rasa yadda aka yi ta gane muryarsa.

Jikinsa na rawa ya É—auki wayar cikin tsananin firgici da tsoro yana duba ko ya fita daga tsarin ne.

Salati kawai ya yi tare da dafe kansa yana jin shikenan ruwa ya ƙarewa ɗankada! Domin bai san wane irin kallo za ta yi masa ba, matuƙar ta gane shi yake kiranta.

Idanunsa suka firfito tashin hankali ya ƙara ninkuwa a fuskarsa. Jikinsa har wani mazari yake na tsananin tashin hankali.

Dafe kansa ya yi a lokacin da ya shiga gurin tsarin ya ga ashe saitin ya fita. Tsananin mamaki ya kamasa domin shi bai son lokacin da ya cire tsarin ba.

Dama masu iya magana sun ce kwana ɗari ba ɗaya na ɓarawo, kwana ɗaya na mai kaya. Yau asirinsa ya tonu. Wani irin kallo za ta yi masa? Yana wannan tunanin ya ƙara mai da tsarin, sannan ya danna numbarta don ya kira.

A lokacin da ya fita Ummu ta bi shi da kallo har ya ƙarasa fita. Dafe ƙuncinta ta yi cikin takaicin, ganin yadda ya takurawa rayuwarsa game da abinnda ya tabbatar wa kansa haramcin hakan. Ko wani lokacin ta ji haushinsa sai kuma tausayinsa ya dabaibayeta, wanda ba ta san dalilin yin sa ba.

ÆŠaukar wayarta ta yi tare da nufar kicin don ta ga ko Hilah ta kammala abincin.

Ƙarar da ta ji na ta tare da sakin wayarta ta faɗi ƙasa, bayan ta kira sunan sa da ƙarfi.

A razane ta faÉ—a kicin tana tana salati.

"Lafiya, kike ihu da kiran Huwais?" Tsananin razana ya bayyana a fuskarta, domin ko kasheta Ummu za ta yi, ba za ta gaya mata dalili ba, saboda gargaÉ—in da ta yi mata kan kar ta sake ta kula shi.

Hawaye sosai suka wanke mata ƙuncinta, cikin rawar murya ta kalleta, da ta yi tsaye cikin ɓacin rai tana kallonta.

"L.a.f.i.ya l.au! Ƙawata ce ƴar ajinmu aka sanar da rasuwarta, s.h.i.ne na firgita." Ta tsinci kanta da shirga mata wannan ƙaryar wanda ta faɗa cikin in'ina da rawar murya.

"Sai ki rasa wanda za ki kira sai sunan Huwais?"

"Eh, da yi ke ya santa."

"Munafuka! Kin ji na gaya miki matuƙar na ji da abin da kuke ƙullawa. Wallahi sai na zama ajalinki, domin ba zan bari ku ja mini abin kunya ba."

Maganar da ta yi, da abin da ya yi mata suka rikita kwanyarta da take aiki bisa rashin ƙa'ida.

"Ko dai Ummu na tunanin ni da Ya Huwais, muna aikata masha'a?" Ta yi kanta tambayar cikin tsananin razana jin abin da ta ce.

Ta"awizi ta fara tare da jin wasu zafafan hawaye suna sauka da ga ƙuncinta, ganin rashin yaddar da mahaifiyarta ta yi mata, amma kuma da ta duba abin da ya yi mata, sai kuma duk ta ɗora masa laifin in har abin da ta gani a idanunsa, wanda ya sa take nesanta ta da shi.

"Ummu, wallahi babu abin da ya shiga tsananina da Yaya. Shaƙuwarmu soyyaya ce ta jini." Da sauri ta danna wayarta ta kasheta gabakiɗaya ganin kiransa na shigowa. Ƙirjinta ne ya ƙara dukan tara-tara.

"Rufe mini baki." Ta ce tare da sakin tsaki ta buga ƙofar da ƙarfi ta wuce.

"Sha'anin yarannan kullum cikin damuwa suke sanya ni. Gara ayi auren su hankalina ya huta." Ta ce cikin tsananin damuwa.

Tana fita ta kashe gas ɗin tare da rugawa zuwa harabar gidan. Can cikin shuke-shuken gidan ta ɓoye sannan ta kunna wayarta.

Kafin ta yi ƙoƙarin kira kiransa ya shigo.

"Ya Huwais!" Ta kira sunan cikin tsananin tashin hankali da ɓacin rai. A ranta ji ta ke in har shi ne yake kiranta sai ta cire kunyarsa ta yi masa rashin mutunci, domin ya cuci rayuwarta. Idan ya yi da wasa ne haƙiƙa ya sanya mata tabon da ba za ta taɓa mantawa ba. Tana matuƙar son mahaukacin masoyi da take jin a yanzu son shi ya zama tamkar maganaɗisu a rayuwarta, domin in har babu shi rayuwarta kamar gangar jiki ne da babu numfashi.

"Kin san ni mutum ne mai tsananin kishi! Duk da cewar na san shi yayanki ne, kan me za ki danganta muryarta da ta sa. Shi yana da kishiyoyi, saboda kina da wasu ƴan'uwan, amma ni kuwa Allah ya halicce ki ne don ni kaɗai, ko mutuwa na yi ba za ki taɓa aure ba!"

Tsananin mamaki ya sa ta kasa cewa komai, jin muryarsa ta rikiÉ—a ta koma muryar mahaukacin masoyi. Cire wayar ta yi daga kunnenta ta duba ko Huwais ya kira ta ba ta lura ba ta É—auka shi ne, amma sai ta ga da numbarsa dai ya kira ta.

"Kenan muryar Ya Huwais ne take mini gizo ta koma kamar na mahaukacin masoyi?" Ta yi ma kanta tambayar cikin ruÉ—ani!

Ta É—an É—auki mintina tana auna hakan a mizanin hankalinta. Har zuciyarta ta amintar da ita gizo muryarsa ta yi mata.

"Wataƙila don na damu da halin da yake ciki ne." Ta furta hakan a cikin ranta a fili kuwa buɗe baki ta yi ta ce,

"Ka yi ha..."

Ƙit ya kashe wayar, yana hamdala tare da saituwar zuciyarsa da ke dukan tara-tara. Dama so yake ta yarda. Hankalinsa ya kwanta yana ajiyar zuciya ganin ruwa bai ƙarewa ɗankada ba.

"Hmmmmmh! In har da ta gane yau na shiga uku! Domin girmana da ƙimata zai zube a gurinta, wanda ba zan iya lamuntar hakan ba."

Ƙwanciya ya yi, yana mai da numfashi saɓanin da yake ta safa da marwa, yana ta share zufa duk da A.C dake cikin falon.

Bin layin ta yi, amma a kashe wanda ya ƙara tada hankalinta matuƙa, domin a yau ya yi mata alƙawarin sanar da ita sunansa.

Hawaye masu zafi suka wanke mata fuska. Hannu ta sanya ta share. Da sauri ta ruga zuwa ciki tuna rage gas É—in kawai ta yi ba ta kashe ba.

Sororo ta yi ganin Ummu a kicin ɗin dama tum kafin ta shigo ƙaurin kuskus ya cika gidan.

Wani irin kallo ta watsa mata tare da kai mata mari. Da sauri ta matsa cikin muryar kuka.

"Ummu, ki yi haƙuri ba..."

"Fita ki bani guri! Sakaryar yarinya kawai." Ta furta cikin ɓacin rai wanda ya aanya ta ruga zuwa falo tana hawaye.

Yana kwance a kan kujera yana ta tunani har yanzu zuciyarsa ba ta gama bugu ba.
Su

Tashi ya yi jikinsa babu ƙwari ya shiga bayi don ya watsa ruwa su tafi gidan Hajiya.

Bayan ya yi wankan ya shafa mai sannan ya sanya dakakkiyar shadda ruwan sky blue. Shaddar ta yi matuƙar ɗaukarsa domin ya yi kyau sosai duk da damuwar da yake ciki, bai hana fito da zallar kyawunsa ba.

Turarensa mai daɗin ƙamshi ya fesa sannan ya kulle ɗakinsa.

Ya shigo falon da sallama zuciyarda na dukan tara-tara. A ransa yana fatan Allah ya sanya ta yarda ba shi ya ke kiranta ba.

Ita kaÉ—ai ce a falo tana tsaye a gaban dining da tsumma a hannunta tana goge kan dining É—in da ta gama ba Umnah abinci.
Chapter 17 · 0% Book details