← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 40

Sashe 3

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh, yana da gaskiya domin a gaskiya abin da Ummu take yi sam ba ta kyautawa. Anty Hilah 'yar'uwammu ce biogically, amma sam ba ta barin ta huta kullum cikin aiki, kuma ta hana mu taimakon ta. Ta manta karatunta yana buƙatar lokaci."

"You are right sis Umnaah, kuma ba ta duba ɗaukakarta da nasararta. Abin na ci mini tuwo a ƙwarya, ya kamata muje har ofis ɗin Abu mu yi mishi complaining, saboda a gida muna fara magana za ta hana mu." Naufal ya faɗa yana gyara zamansa.

"Eh, mu je gaskiya don abin na ci mini tuwo a ƙwarya." Cewar Abidin da yake danne-danne a wayarsa.

Wani irin tsananin ƙaunar 'yan'uwansa ya ƙara kama shi, ganin ba sa son abin da take mata ya kalle su zai ce daidai lokacin da Fu'ad. ya tari numfashinsa.

"Mu ma yana ci mana tuwo a ƙwarya kuma na sha ganin su Umnaah sun je za su taimake ta, amma sai ta hana su. Ni kaina mun taɓa zuwa a tare taki. Kuma ban san dalilin da kullum take maganar ya kamata ayi mata aure da wuri ba, domin ta so ace kafin ka dawo an yi aurenta da Hammad."

Idanunsa ne suka kaÉ—a bayan shi sheda ne kan Hilah 'yar'uwarsa ce na jini, domin a gabansa aka samu cikinta aka kuma haifeta ta girma sai ya ce a kwai lauje cikin naÉ—i, amma shi sheda kan hakan."

"Bari gobe zamu same shi a ofis mu yi mishi magana karku damu kun ji 'yan ƙannina."

"To." Suka haɗa baki gurin faɗi tare da bin sa da kallo lokacin da ya miƙe ya nufi hanyar kicin.

A hankali ya tura ƙofar kicin ɗin tana tsaye a gaban gas tana juya damen tuwon semonvita da ta yi.

Ba tare da ta san ya shigo ba tana aikinta tana rero karatun qur'ani suratul Maryam kasancewar tana matuƙar son surar.

Bagan ta juya sai kuma ta koma ta zauna ta leƙa duniyar tunani wanda kusan 'yan mintina ta yi nisar kiwo.

Kamar wacce aka tsikara ta miƙe da sauri ta ƙarasa gurin talgen da har ya fara zuba.

Buɗewa ta yi tana juyawa sai kuma ta mayar da murfin ta ije muciya ta ɗauki garin za ta tuƙa.

Tana tuƙin yana kallonta, kamar wanda ya kunna fim har ta kusa gamawa, sai cikin rashin sa'a tuwon ya fallatsar mata a hannu, wanda ta yi ɗan ƙara ta yarda muciyar tana tsallen azabar zafi.

Da sauri ya ƙarasa gurinta tare da kama hannu ta yana hura mata wanda ta kalle shi idanunta tab da hawaye.

"Ya Huwais, ashe ka shigo."

"Ki rinƙa aiki a hankali kar kije ki rinka cutar da kanki. Kinga ga shi nan har kina ƙona kanki." Ya faɗi cikin ɗan ɗaga murya ganin yadda gurin ya yi ja.

"It pains me." Ta ce tare da saka kuka wanda hakan ya ƙara tana da hankalinsa.

Janta ya yi zuwa tap, ya buɗe tare da tara kyawawan hannuta da suka sha jan lalli, waɗanda suke fisgar zuciyarsa zuwa ƙara ninka sonta.

"Am sorry sis. Bari na ci gaba da tuƙa tuwon." Ya ce tare da ƙarasawa gurin gas ɗin ya ɗauki muciyar bayan ya wanke ya sanya a cikin tuwon.

"No ka barshi zan iya Ummu za ta yi faɗa in ta gani." Ta ce yayin da hawayen da suke maƙale a fuskarta suka gangaro mata.

Mayar da muciyar ya yi, tare da kamata ya zaunar ya kai bakinsa yana hura gurin, kamar sakwan talatin sai ya koma gurin tuƙin yana faɗin,

"Let her do, ciwo kika ji saina kasa taimakon ki."

Kallon da ya yi mata sai ta ji a karon farko ta ji wani abu game da kallon wanda ta kasa tantance ko mene ne shi.

Idanunta ta sunkuyar ƙasa ba tare da ta ce komai ba, sai dai ƙarƙashin zuciyarta tana addu'ar Allah ya sa kar Ummu ta shigo, wanda ta san faruwar hakan ba ƙaramin faɗa za ta sha ba.

"Zan yi wa Ummu magana, ba zai yiwu ace duk kuɗin mahaifinmu ba kina girki ba dare ba rana, kina buƙatar time Hilah, kar ta manta watanni ya rage ku yi musabaƙa, duk da na san you gonna rock it, amma kina buƙatar hutu sosai don kina da 'yancin hakan. I don ma don kar kije gidan aure ba ki kowa ba, zuwa yanzu sai dai ki kowa ya wasu"

"Ummu, uwa ce a gareni wanda ko wane ɗa zai yi alfaharin samunta, domin ta gina rayuwata da gishirin duniya wato ilmi. Ba zan yi baƙinciki don ta sani aiki ba Ya Huwais, don Allah karka ka yi mata magana ko Abu. Ina son mahaifiyata ba na son na ɓata mata rai. Bayan haka ma gani za ta yi kamar ƙararta na kai maka."

Sosai ta ba shi tausayi musamman da mood ɗin da ta yi maganar. Bai amsa mata da zai yi mata magana ba ko a'a ba, ya fara zuba garin tuwon a cikin tuƙunya yana tuƙawa, wanda ganin hakan ya sa ta saki dariya.

"Kai ya Huwais! Dama ka iya girki ne?"

Dariya ya yi jin yadda ta yi masa tambayar cikin zallar mamaki ganin yana tuƙin da ƙwarewa.

Rufe tuwon ta yi bayan ya gama ya rage gas É—in wanda take kallon shi har yanzu mamaki É—auke a fuskarta.

Sai ya matsa gab da ita zai ɗauko kular da zai kwashe tuwon wanda ta riƙe hannunsa tana faɗin,

"A ka barshi zan iya kwashe na gode."

Matsowa ya yi kusa da ita har tana jin kusancin ya yi yawa domin a tare suke saukar da numfashi kuma suna jin hushin juna.

Dubara ta yi ta matsa ƙarshen sink ɗin tana mamakin hakan da ya yi mata.

"Mamaki kike yi ko? Ai da na je London na kasa cin abinci na kowa sai tunanin na ki, shine na gwammace gara na yi girki da kaina ya É—an fi kama da naki, tun da ina lura da yadda kike yin na ki."

"Ikon Allah!." Ta ce da ƙarin mamakin a fuskarta.

"Abincin kowa baya mini daÉ—i sai nawa. What if ka yi aure ya za ka yi da na matarka?"

Tambayar ta ƙona masa rai domin ya so ya ji tace in suka yi aure ya huta da cin abincin kowa sai na ta, amma to in ta faɗi haka ta ya ya kenan?

"Sai na É—auke ki na kaiki gidan har sai ta koyi girkinnki."

Jinjina kanta tayi tana mamakin menene a abincin ta da har ya bambanta daÉ—insa da sauran na mutane.

"Ai da yake da sauƙi tun da Anty Wajnaah ce duk da cewar tana da girman kai ba lallai bane ta koya, amma ina da yaƙinin ba za ta iya rasa ƙwarewa kan dafa abinci ...."

"Sai kuma aka ce miki ita zan aura?" Ya jeho mata tambayar cikin ɓacin rai, yana miƙa mata tuwon da ya saka a leda tana nannaɗawa tana sakawa a kula.

"Eh, na ga tun kafin ka tafi aka yi emgagement É—inku, dalilin tafiyarka ya sa aka É—aga auren sai ka dawo. Ga shi yanzu har ta gama servise kamar ta samu aiki na ji Ummi na faÉ—i." Ta yi maganar cikin É—an shakku da rashin gasganta maganar sai kuma ta É—ora da cewa,

"Eh haka ne, Uncle Nauhis na ji yana mata murna a lokacin da muka je bikin 'yar gidan Mummy Binta."

"To ba ita zan aura ba domin bana sonta."

"Haba Yaya! This isn't right. A kan me za ka sa ta ɓata lokacinta for almost two years, kuma yanzu ka ce ba ka sonta? Gaskiya in ka yi mata haka sam ba ka yi mata adalci ba."

Tabbas ya san gaskiya ta faɗa, to amma kuma da ya aureta ya kasa bata haƙƙinta ya cutar da ita, wanda in ba mai iya riƙe kanta bane sai ta faɗa harkar banza ai gara ya ƙi aurenta, domin duk matar da zai aura ba ƙanwarsa ba matar shige take a gurinsa.

"Kin san mene ne soyayya?" Ya tambayeta cikin sanyi tare da barin kwashe tuwon.

"Ban sani ba Ya Huwais saboda har yau ban wani ji ina son Hamad ba, sai don mahaifiyata ta yaba da shi, kuma besides ya cancanci ko wace 'ya mace ta so shi."

"Wannan dalilin ya sa kike ganin baike na, kuma duk abin da zan gaya miki ba za ki fahimata."

"To Yaya, wata ka kamu da sonta?" Ta yi masa tambayar cikin mamaki har zuwa lokacin tana jin bai kamata ya yi mata haka ba.

"Eh, ita ce zuciyata kuma rayuwata. Ita ce nake jin zan iya rayuwar aure da ita, ma kuma zauna da ita ko da ta kasance musaka. Ita ce mace ta farko da zuciyata ta kasa bacci take tunaninta babu dare babu rana har ya taɓa sashi na rayuwata."

Mamakin abin da yake cewa ya kamata duk da cewa ba sa ɓoyewa junansu komai, amma sai take ganin bai kamata ya gaya mata waɗananan kalaman ba. Ita mamakinsa ma take yi da yake bai cika shiga rayuwar mutane ba har ya iya soyayya haka. A she ɗan soyayya ne.

"Hilah ina jin in ban aureta mutuwa zan yi domin ta zamo rai da numfashi a gareni. Kin ga kuwa babu rayuwa in har babu ita, domin rasa yarinyar daidai yake da rasa rain.."

"Wace ce ita, wace ce wacce take son ta yi mana sanadin ɗan'uwanmu? A ina kuka haɗu? In har kuɗi na iya komai ba su Abu ba ni kaina da kuɗin da na mallaka zan nemar maka aurenta ko 'yar shugaban ƙasa ne." Ta ƙarasa maganar cikin hawaye ganin yadda idaunsa suka cika da ƙwalla domin ɓata taɓa ganin abin da ya sa shi cikin wannan yanayin ba.

"Wanne kike so na amsa miki Hilah? Tarin tambayoyin sun yi mini yawa?

"Duka Ya Huwais. Duka nake so domin kawo ƙarshen matsalarka, saboda ba zan iya ganinka cikin wannan hali ba."

'Ba 'yar kowa bace kuma ba ta wuce matsayinmu ba, amma ta yi mini nisa da tazara;tazaran da yake kamar kwatankwacin sama da ƙasa. Ba zan same ta ba har abada.
Chapter 3 · 0% Book details