Sashe 18
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar da ya yi ta ji zuciyarta ta buga wanda ba ta san a tare suka buga da na sa ba.
Kallonsa ta yi cikin ido tana son ta ga rashin gaskiya a tare da dashi, domin har yanzu zuciyarta na ƙara tanbatar mata da muryarsa ne.
"Ya Huwais!" Ta kira sunan daidai lokacin da ya ƙaraso gurin dining ɗin cikin daurewa.
Basar da kallon da yake mata take yi."Ina su Umnah? Ummu, ya gaya muku zamu fita."
"Eh, amma ta ce ban da ni."
Kallonta ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sai kuma ya zauna yana kallonta.
"Je ki gaya musu su fito kuma ke ma ki shirya."
Jim ta yi kamar za ta yi masa magana sai kuma ta jiya ta sanar musu tare da dawowa da sauri.
Ganin da magana a bakinta ya sanya shi miƙewa da sauri tare da ije remote ɗin da ke hannunsa.
"Ki É—auko mayafinki bari na É—auko abu na yi mantuwa."Tsaya ya yi ganin Ummu ta fito da carbi a hannunta.
"Ka shirya ne Huwais?
"Eh, Ummu. Su yi sauri domin ina son na je gidansu Najib."
"Amma daga nan za ku je gidan su Wajnah ko?"
"No Ummu, ba yau ba." Ya furta cikin É—aure fuska.
"Ma za ki kira su Amnah." Ta ce.
"Na sanar musu Yaya ya fito." Kafin ta gama maganar suka fito dukannninsu a shirye.
"Bro you look gorgeous!"Naufal ya ce cikin murmushi yana kallonsa.
Ba tare da ya amsa ba, ya fara ƙoƙarin tafiya ganin sun kama hanyar fita, sai kuma ya juyo ya ce,"Ummu, Hilah ba za ta je ba ne? Ko ranar da muka je Hajiya ta yi maganar tana son ganinta." Ya yi maganar cikin basarwa.
"Eh, ku barta kawai jibi in zani sai mu tafi tare." Ta ce wanda ya sa ya ƙara ɗaure fuska ba tare da ya kalle ta ba.
"Ok,." Ya ce amma a ransa a jagule ji yake kaman shi ma ya fasa zuwa.
"Please Ummu, don Allah mu je da Anty Hilah." Umnah ta ce wanda jin haka ya sanya Amnah ta ce,
"Please Ummu,"
"Hilah, ki É—auko mayafinki ku je." Ta ce tare da juyawa cikin É—akinta wanda ya sa yaran suka saka ihun murna.
ÆŠaki ta koma cikin tsallen murna ta sanya abaya ja tare da rolling É—in É—ankwalinta. Ta yi kyau sosai kamar ka sace ta gudu.
Wayarta ta ɗauka sai ƙaramar pos ɗinta ta fito.
Bayan sun shiga cikin motar har ya tada mai-gadi ya buÉ—e Umnah ta ce,
"Ya Huwais, Ummu ta bar Anty Hilah ta bi mu. Shiryawa ta ke yi."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 11
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

Ransa ne ya yi fari kamar farar takadda, ba tare da ya ce musu komai ba. Ya kashe motar yana shafa sajensa.
Ba ta ɓata musu lokaci ba ta fito tana tafiyarta cikin sanyi.
Ta madubin motar ya hangota yayin da ya ƙura mata idanu ganin yadda ta yi kyau kamar ka sace ka gudu.
"Ya Allah!" Ya furta da ƙarfi tare da dafe zuciyarsa daidai inda ta buga.
A hankali ta ƙaraso, ta shiga bayan motar wanda sai da ya ɗan ɗauke numfashinsa, jin yadda ƙamshin turarenta ya cika masa hanci yake rikitar da kwanyarsa.
Ba tare da ya kalleta ba ya ja motar yana sauke gwauron numfashi.
A hanya tafe suke shi da ita babu wanda ya yi wa juna magana. Kowa da abin da yake tsaƙawa a ransa musamman ita. Da take son sanar masa da incident ɗin da ya faru da ɗazu.
Shi kuwa hankalinsa na kan hanya, amma tunaninta yake yi, satan kallonta yake yi wanda ba ya son su haÉ—a idanu, domin za ta iya fahimtar wani abu, musamman yadda idanunsa suka canza.
Su Naufal ne kawai suke ta hirar su, wanda yawanci suna sako su a ciki. Hilah ce kawai take sanya musu baki, amma shi da ga um sai a'a.
Kafin su isa ya tsaya ya siyawa Hajiya Fruits sannnan suka wuce.
A ƙofar gidan ya tsaya tare da yin hon, wanda Ilu maigadi ya taso da sauri ya buɗe masa, ya shiga da motar cikin ƙaton harabar gidan.
Bayan ya yi parkinng sun fito ban da Hilah da ta tsaya nawa tana ƙoƙarin sanya takalminta.
Saboda murna suka ruga cikin gidan ba tare da sun jira ta ba.
Ta ɗauki takalmin tare da buɗe murfin ƙofar za ta fita, ba tare da ta ce masa komai ba, da hannunsa dafe da sitiyarin mota yana kallon gefe.
Ganin za ta fita ya sanya shi juyowa da dara-daran idanunsa ya watsa mata.
Wani irin faɗuwar gaba ta tsinci kanta da shi. Sai kuma ta rikice domin ba taɓa ganin ya yi mata kallon ba.
"Yaya," Ta ce sai hawaye suka wanke mata fuska.
Ƙaramin tsuka yaja don jin haushinta, domin shi ya kamata ya yi kuka ba ita ba.
"Ba na hana ki sanya turare ba?" Ya yi mata tambayar cikin ɓacin rai.
Ganin ba ta ce masa komai ba, domin ita ba wannan maganar take son su yi ba ya ɗora da cewa," Ke malama ce kina da sanin ki, kuma kin san hukuncin sanya turare wani namijin da ba muharraminki ya shaƙa ba."
Ya Huwais, mahaukacin masoyi ya kita ni da rana." Ta yi masa maganar tana kallonsa ko zai ce wani abu, amma sai ta ga ya tsuke fuska hankalinsa na kan wayarsa da yake shafa bayanta.
Gyaran murya ta yi, wanda ya É—an juyo da idanunsa ya yi mata wani jirgitaccen kallo.
"Damuwarki mahaukacin masoyinki, sam ba ki damu da rayuwar É—an'uwanki da ake shirin yi masa auren dole ba."
Yadda ya yi maganar da abin da ya faÉ—a suka sanya ta sakin dariya babu shiri.
A hargitse ya juyo yana kallonta ganin dariya take. Ransa ne ya ƙara ɓaci ya buɗe furfin motar zai fita.
Ganin haka ya sanya ta gimtse dariyar tare da kama hannunsa ta riƙe.
"Please, Ya Huwais, don get me wrong." Ta fura tare da riƙe hannunsa duka biyu.
"Ina cikin damuwa, amma ba kya tausayina. Tun da kika samu mahaukacin masoyinki kin daina kula da ni."
Rau ta yi da idanunta."Kai ma ka san babu wanda na damu da rayuwarsa kamar kai. Bayan ƴan'uwanta ka ta jini har da shaƙuwa da soyayyar jini, wanda ta kai da har muryar mahaukacin masoyi tana rikiɗa tana zama irin taka."
Gwauron ajiyar zuciya ya saki jin abin fa ta ce. Zuciyarsa ta yi fari ƙal tare da hamdala ganin ba ta gane ba.
Da mamaki ya kalle ta ya ce,"So kike ki yi mini wayo na É—auka kin damu da ni, amma na tabbata da ace babu son mahaukacin masoyi a rayuwarki, sai ki tausaya mini halin da na ke ciki."
"I do care you! Wallahi kana raina ko da yaushe, amma ka sani Ummu, gata take yi maka, domin duk wanda ya auri mace kamar Anty Wajnah ya yi dace."
Ƙara ɓata rai ya yi tare da buɗe murfin motar ya fito."Please, akwai buƙatar mu tautauna sis, ina tsananin buƙatar shawarki."
"HaÉ—uwarmu xai yi wuya Yaya, Ummu sam ba ta son ganinmu a tare."
"In mun gaishe da Hajiya ki same ni
a waje ki raka ni gidan Najib."
Kallon sa ta yi da nufin ta musa, amma kallon da ya yi mata ya sanya ta kasa tare da sauke kanta ƙasa.
Ganin ya fita ya sanya ita ma ta fito tare da rufe ƙofar suka jera suna hira.
Hajiya na zaune a falon, su Umnah sun sanyata a tsakiya sai hira suke mata. Sallamar su ya katse dariyar da suke yi mata.
Ganin su ya sanya ta washe bakinta da ke cike da goro tana tafa hannunta.
"Lale marhaba da zuwan jikokina!" Ta furta cikin tsananin farinciki domin tana matuƙar son jikokinnata.
Huwais da fara'a ya isa gareta, tare da zaunawa a gefenta ya ciro wayarsa da ke gana aljihun rigarsa zai É—auke su hoto.
"Bari na yi hoto da gimbiya autar mata." Ya ce cikin tsigar tsokana.
Hannnunta ta sanya ta ka masa duka da carbin da take ja, ta ture shi tare da kai hannu kamar za ta buge shi, wanda hakan ya sanya ya miƙe yana dariya.
"Bari na gudu domin hannunki kamar icce yake."
"Eh, ai gara ka gudu in ba haka ba, sai na karyaka saboda kishi. Don za ka yi aure sam ka daina zuwa inda na ke. To daÉ—in abin ba a canzawa tuwo suna, kuma tsohuwar zuma da ita ake magani"
Fara'arsa ta ragu jin abin da ta ce, amma sai ya share ba tare da ya ce komai ba.
Hilah kuwa rungume ta yi cikin tsananin ƙauna ta ce,"I miss you ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe."
Murmushi ta ƙara saki tana cewa,"Sannu malama tun da kika ci gaza kika yi kuɗi kin guje mu."
"Kai tsohuwar nan kin iya rigima. Kana jin abin da take cewa Ya Huwais, bayan ko da na dawo sai da na kawo mata nata kason."
Murmushi kawai ya yi,ba tare da ya ce komai ba, ya zauna gefen da Hilah ta zauna hankalinsa na wayarsa da Najib ya turo masa da tsaƙo.