Sashe 29
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama ta yi kan one seater tana kallon Wahida da take shayar da Æ´arta mama.
"Gaskiya gidanki ya yi kyau sosai! Abin da ya rage miki sai ki kama maigidan da kyau, yadda babu wata ƴar iska da za ta shigo miki gida, domin irin mijinki shi ne mace ke hauka in zai ƙara mata kishiya."
"Lallia ma Wahida, har yanzu kamar kallon ƙaramar yarinya kike mini. Kin san yadda na samu har aka yi auren nan? Sau biyu ana sanya ranarmu ana fasawa. Ai yadda na sha fama kafin na shigo cikin gidansa ku ƴan'uwansa sai na ga dama zai rinƙa kula su, ballantana wata kishiya. Ni Allah ya tsare ai gaba da baya zan tsare don no kishiya in my house."
Dariya suka kwashe da shi tare da tafawa.
"Ai ban ga laifin ki ba Wajnah, don ko ni mijina shi da wata sai dai matan aljannah da ban isa na hana shi ba, amma a duniya babu macen da ta isa na yi sharing mijina da ita, in kuwa ta kuskura ta aurar mini miji sai na nuna mata mijin wata ta aura. Don ba zan yi shukar Æ´aÆ´an itatuwa ba mu ci da wata." Mardiya ta ce.
"Yadda mijin ki yake jarumin namiji, dole sai kin zama jaruma in ba haka ba kina ji kina gani za a yi miki sakiyar da babu ruwa."
"Duk wacce ta kuskura ta shigo mini gida nice ajalinta, don sai na canza mata kammanni ta yadda ko iyayenta suka ganta ba za su gane ta ba ballantana shi."
"Ato ai gara ki kula saboda kula da kaya yafi ban cigiya."
"Shi ya sa maganin da Hajiya Zauzau ta bani ta ce na sha ƙwara ɗaya tall! Kin san Allah? Guda uku na shanye."
"Kan uban nan! Wallahi babu ruwana in kika kashe kanki, kin san ƙarfin maganin mata na bature?" Cewar Wahida tare da zare idanunta.
"Ai in za ka sha giya ka sha ta dubu." Ta furta tana dariya.
"Wallahi babu ruwana kar ki kira ni."
Dariyar ya yi ita ba ta ce komai ba.
Huwais da Najib a gaban Abu suna zaune yana mishi nasiha.
"Ƴar'uwarka ce Wajnah, kuma yau ta koma matsayin matarka. Tana da haƙƙi da dama a kanka, wanda in har ba ka sauke mata ba Ubangiji xai tambaye ka. Kana da sani kuma kai ba yaro bane, kasan haƙƙin da Allah ya rataya maka, don haka kar na ji na ga abin ƙi a rayuwar aurenku. Ka riƙeta tsakani da Allah Ubangiji zai jiɓanci lamarinka, sannan ka sani zaman aure bauta ne na Ubangiji ba zaman jin daɗi ko san rai ba. Duk abin da ka yi mata na cutarwa Allah sai ya tamabaye ka, kamar yadda in har ta saɓa maka ita ma Ubangiji zai hukunta ta. Don haka a matsayina na mahaifinka ina mai jawo hankalinka da ka riƙe amanar Allah sai Allah ya jiɓanci lamuranka."
Shiru ya yi jikinsa ya yi sanyi, har yana jin hawaye na son zubo masa, jin nasihar da Abu ya ke masa.
"Shin ko zuciyata za ta aminta na xauna da ita, bayan bana sonta kuma ban taɓa jin ta burge ni ba?" Ya yi wa kansa tambayar cikin damuwa.
"Na gama za ka iya tafiya, sai dai in mahaifiyarka na da abin cewa." Ya ƙarashe maganar yana kallonta.
"Ai ka gama cewa komai, sai dai na ƙara masa da cewar ya kula da ita, ya san cewa ita ƴar ƴaƴata ce, wacce muka fito ciki ɗaya, sam ba zan lamunci ya cutar da ita ba, kamar yadda ita ma ba zan barta ta cutar da shi ba. Ya riƙe ta tsakani da Allah don ɗorewar zumuncinmu "
"To ka ji abin da mahaifiyarka ta gaya maka. Ka tashi ka tafi gidanka Allah ya yi maka albarka." Abu ya ce yama kallonsa.
Har ya miƙe, sai kuma ya kasa tafiya ya ɗago idanu suka haɗa ido da Ummu, da tun da ya miƙe take kallonsa.
Jikinsa ya ƙara sanyi da ya tuna nasihan da suka yi masa, wanda ba ya tunanim zuciyarsa xa ta iya amincewa ya aikata hakan. Ji ya yi kamar ya xauna ya gaya musu wacce yake so, amma ya san a matsayin mahaukaci za su ɗauke shi.
"Zan wuce Abu, Ummu ku yafe mini." Ya furta yana share hawayen da ya fara zubo masa.
Ummu ce ta zura masa idanu tana ji ita ma tamkar xa ta yi kuka.
"Na san abin da ke ranka Huwais, ina matuƙar sonka da damuwa da halin da kake ciki. Sai dai abin da kake so da muradi sam ba mai yiwu ba bane!" Ta furta tana kallon sa cikin tausayawa.
"Ma za ka tafi ga iyalinka Allah ya yi maka albarka."
"Amin," Ya amsa jin abin da Abu ya faɗa da shi ma ya miƙe yana gayra zamansa.
A kasalance yake tafiya Najib na bayansa.
Yana fita Ummu ta sauke ajiyar zuciya. Tun lokacin da yaran nan suka mallaki hankalinsu na daina bacci mai daɗi. Haƙiƙa yau zan rama baccin da na daɗe tsawon shekaru ban yi ba." Ta furta tana kallonn Abu da ya ƙura mata idanu sai ta ɗora da ce wa,"
Ko da yake an sare kan maciji ne ba a yarda gangar jiki ba, domin matuƙar Hilah ba ta yi aure ba hankalina ba zai kwanta ba gabakiɗaya."
"Kar ki damu ita ma aure zan yi mata, karatun na ta saura shekara É—aya ne."
Huwais kuwa yana fita ya shiga mota sai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar. Kuka yake son ya yi kuka sai mai ƙarfi. Wataƙila ya samu sauƙin tafarfasar da zuciyarsa take yi, tamkar kwatamin da aka cika shi da ruwan zafin da ya fara tafarfasa za a kaiwa mai jego.
Idanunsa sum kaÉ—a sun yi ja kamar jan gauta. Ji yake wani irin miyau mara daÉ—i ya taru a bakinsa, wanda ya kasa haÉ—iyawa kuma ya kasa tofarwa.
Ga mamakinsa, sai ya ji hawaye masu tsananin xafi waɗanda suka fi garwashin wuta ƙuna sun wanke masa fuska.
"Be a man Huwais! Ka yi addu'a karka karaya."
"Na rasata har abada! Ashe dama ba zan aureta ba kullum zuciyata take mini ƙawazucinta!"
"Sheɗanne yake ƙawata maka don kawai ya ci galaba a kanka."
"No Najib, na yadda da kaina. Soyayar da nake mata ba ta sha'a ba ce. Jikina yana bani kamar a kwai ɓoyayyen sirri ko kuma lamarin da zai iya halasta aurenmu."
"Wane hujja kake da shi Huwais? Yarinyar da ita ce ƙanwarka ta uku. A gabanka aka yi rainon cikinta kuma aka haife ta, sannan kai ka yi rainon ta har ta girma. Wace hujja kake da shi wanda zai iya halasta mka ita a matsayin mata?"
"Ban sani ba, amma ima sonta ita ce zaɓin raina. Don Allah ka yi mini addu'a zuciyata za ta buga, sam ba zan iya adalci ga matata ba."
"Ka ƙoƙarta Allah zai shiga lamarinka."Ya ce masa cikin tausaya.
"Ina son na yi sallama da ita. Ina son na ganta kafin na yi bacci. Na san cewa Ummu ta yi mini aure ne, don ta rana ni da ita. Sai dai ta yi kuskure saboda mutuwa ce kawai za ta zamo katanga a tsakaninmu."
"Huwais, karka kunna wutar da ba za ka iya kashewa ba, kuma ba ya zama ba ka da mafita a lamarin, bayan ka ɓata sunan ahalinka."
Girgiza kansa ya yi, ya kasa ce masa komai domin duk abin da ya faÉ—a gaskiya ne.
Ƙoƙarin buɗe motar ya fara ganin Najib na ƙoƙarin tada motar.
"Ba zan iya tafiya ba tare da na ganta ba."
Hannunsa ya kama yana kallonsa."Ka kira wayarta karka sanya Ummu ta yi mata faÉ—a."
Kamar umurni ya ba shi, sai ya koma ya yi cikin motar ya zauna tare da É—aukar wayarsa don ya kiranta.
Tana zaune a ɗakinta kan gado ta haɗe kai da gwiya tana hawaye. Abin da mahaukacin masoyi ya yi mata yake ƙara ɓata ranta.
Hawaye masu zafi suke ƙara shatato mata a saman ƙuncinta.
Wayarta da ke kusa da ita ya sanya ta kai hannu xa ta kashe wayar. Ƙaramin tsaki ta yi domin a tunaninta Hamad ne, amma dai dai ganin mai kiran, ya sanya ta ɗauka tare da yin sallama cikin siririyar murya.
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 18
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
Wayarta da ke kusa da ita ya sanya ta kai hannu xa ta kashe wayar. Ƙaramin tsaki ta yi domin a tunaninta Hamad ne, amma ganin mai kiran ya sanya ta ɗauka tare da yin sallama cikin siririyar murya.
"Ki zo waje ina jiranki muyi sallama."
Karo na farko ta ji wani iri a rayuwarta.Ganin Yayanta wanda yake ji da ita da ƙaunarta yau xai bar gidan. Haƙiƙa a rana ta yau ba za ta taɓa mantawa da ita ba, domin ta rasa abubuwa da dama. Ta san cewa duk soyayyar da yake nuna mata zai rage tun da ya yi aure, musamman in ya haihu soyayyar za ta koma kan yaransa. Wataƙila ya manta da ita ba zai damu da lamarinta ba. Tunanin hakan ya ƙara sanya mata damuwa fiye da ta ɗazu, wanda sai da ta ji dama bai kirata don su yi sallama ba.