← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 40

Sashe 34

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabansa ne ya faÉ—i, amma sai bai ce komai ba ya amsa yana kallonta.

"Mai ya kawo ka cikin gidan nan da sassafe bayan matarka na gida?"

"Ummu, kewarku na yi kuma yunwa na ke ji."

"Huwais, zan yi maka rashin mutunci matuƙar ka ce za ka wulaƙanta ƴar yayata." Ta furta cikin tsananin ɓacin rai wanda ya sanya Hilah ta yi maza ta shige kicin.

"Ummu, laifi ne don na zo gidan nan?"

"Lai fi ne babba, domin yanzu kai magidancinne kuma matarka na buƙatar lokacinka."

Shiru kawai ya yi, cikin takaici domin ya san dalilin da ya sa take faÉ—a.

Ummu ta buÉ—e baki za ta yi magana, sai kuma ta fasa ta koma ta É—auki wayarta da take kan gado.

Numbar Wajnah ta fara kira. Ringing É—aya biyu ta É—auka dama tana kwance a saman gado tana hawaye.

"Sakacin na ki har ya kai, ki bari mijinki ya yi sammakon barin gida a washegarin aurenku? Ka da wayewa ta sanya ki kasa kula da mijinki, saboda ga shi ya zo gida yana cin abinci wai yunwa yake ji."

Takaici ya sanya ta rushe da kuka."Ummu, Ya Huwais ya toxarta ni jiya, saboda in kika ga yadda na ke buga ƙofarsa ina kuka ya buɗe mini, amma ya ƙi bayan ya yi mini zagin ƙare dangi ya sanar mini da wacce yake so a zuciyarsa."

Maganarta suka ƙara ninka tashin hankalinta har ta fara ganin jiri-jiri. "Anya yaron nan na da hankali?" Ta yi wa kanta tambayar sai kuma ta kashe wayar fuuu!Ta yi sama tana huci.

"Abu, yaron nan na lura ba zai taɓa nari na na samu sukuni a zuciyata ba. Ina murna na auren da shi hankalina xai kwanta, amma ga shi can a falo yana karyawa Hilah na gefensa."

Wani gumi ya tsatso masa kallonta ya yi da sauri tamkar yana son sanin ko ƙarya ta yi masa.

Gabansa ne ya faɗi da ƙarfi, saɓanin da tun da Ummu take zafafa lamarin sai yake ganin duk da sauƙi matuƙar aka yi masa aure, don shi a ganinsa sha'awace kawai take damunsa ya ɗora kan ƙanwarsa, amma yanzu da yake da matar da zai sauke buƙatunsa sai hankalinsa ya tashi kwatankwacin kayan masarufi.

"Nufinki yanxu yana gidan nan?"

"Ka je ka ganin ma idannunka, wallahi in har ba mu yi wa Hilah aure ba, sai ya janyo mana abin da xai wargaza farincikinmu."

Miƙewa ya yi, ba tare da ya ce mata komai ba, ya zura jallabiyarsa fara ƙal, ya fita wanda ganin haka ta bishi.

Huwais ganin ta yi hanyar ɗakinta gabansa ya faɗi. Shi kansa mamakin ƙarfin halinsa yake yi, domin duk abin da yake aikawatawa yana jin tsoron iyayen na sa.

Gyaran muryar da Abu ya yi, ya sanya shi tashi da sauri gabansa na faÉ—i ya ce,"Ina kwana Abu?"

"Kana da hankali Huwais? Kan me za ka baro Æ´ar mutane da sassafen nan ka zo gida?"

"Umm..."

"Bana son sakarci." Ya katse shi yana faÉ—in haka sannan ya É—ora da ce wa,"Ma za ka tashi ka tafi gida."

Miƙewa ya yi ba don ransa ya so ba zai fice.

"Da kun barshi ya karya, sai in ya so idan ya gama ya kaimu ni da Hilah da ma za ku kai abinci."

"Sai dai ke da su Umnah, amma Hilah za ta yi mini aiki."

"Ai ba daÉ—ewa za mu yi ba ki barta ta je, saboda tun da muka tashi take murna za ta je ganin gidan Yayanta."

Ummu ta buÉ—e baki xa ta yi magana Abu ya ce,"Ki barta ta je amma kar ku daÉ—e."

"Ba zan daÉ—e ba saboda yau na ke son na koma Gobbe."

"Ok, Allah ya kaiki lafiya." Abu ya furta wanda ta amsa da amin sannan ya juya zuwa ciki.

Harararsa Ummu ta yi sai ta juya ta bi Abu.

Sauwama Hilah ta ƙwala wa kira, tare da sanar da ita ta ɗauko mayafinta. Cikin murna ta juya ta shige ciki.

Yana jin da Hilah za su je abincin ya fita a ransa. Ture abincin ya yi tare da faÉ—in,"Anty Sauwama mu je."

"A,a ka gama cin abincin mana."

"Karki damu na ƙoshi."

Bin sa da kallon mamaki ta yi ganin bai ci abincin da yawa ba.

Azerh da ta ke saukowa daga sama, tana hamnar sauran baccin da bai saketa ba, ta ƙara so da sauri.

"Ni ma Anty Sauwama zan biku, amma sai yamma zan dawo." Ta furta daidai lokacin da ta ƙara so.

"Ok, yi sauri ki É—auko mayafinki sai ki same mu a mota."

"To," Ta amsa tare da komawa sama da sauri.

Hannu ya sanya ya karbi yarta, sai da suka je gurin mota ya miƙa mata bayan ta buɗe motar ta shiga.

Lakuce mata hanci ya yi, yana dariya ganin yadda take wangale masa bakin da babu haƙora.

Kafin ya tada motar, Hilah ta karɓe ta tana ta yi mata wasa tana dariya.

A mota Anty Sauwama ce a gaba, sai ita da su Umnah suna baya. Tana riƙe da ƴar Sauwama tana mata wasa. Sai satan kallonta yake yi ganin yadda take ɗaga yarinyar sama tana dariya. Zuciyarsa ta raya masa ina ma ace ƴarsa ce.

Yana ta satan kallonta ta madubi, in aka yi rashin sa'a suka haÉ—a idanu sai ta sakin masa murmushi, shi kuma ya É—aure fuska yana harararta cikin wasa.

Suna isa cikin gidan, ya yi parking tare da buÉ—e wa Sauwama murfin mota.

"Yauwa É—ana ashe kana son albarka." Ta faÉ—a tana fariya.

Harararta ya yi domin kusan sa'oin juna ne, kuma a hannun Ummu ta tashi.

"Kuma fa haka ne bai kamata na rinƙa girmama ki ba, saboda na san lokacin da kike yawo ba wando."

Wani irin dundu ta sakin masa a baya har sai da ya duƙa.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 21

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM

"Kuma fa haka ne, bai kamata na rinƙa girmama ki, ba saboda na san lokacin da kike yawo ba wando."

Wani irin dundu ta sakin masa a baya, har sai da ya duƙa.

"Kai Anty Sauwama, wallahi tsaf zan iya rama dundun nan, saboda ba ki ji yadda na ji zafi ba."

"Ashe kuwa zan ƙara maka wani, ka san dai ko lokacin da muke yara kuka nake saka ka."

"Ni kuma na saki birgima ba." Dariya suka kwashe dashi suna tuna yarintarsu.

Wajnah da take laɓe a windo tana kallonsa, suna wasa sai matuƙar baƙinciki ya kamata. A ranta take mamakin dariyar da yake yi.

Ganin Hilah ranta ya ɓace sosai, domin har ga Allah ta tsane ta, musamman jiya da ya sanya ta ba da tarihin rayuwarsa.

Sakin labulen ta yi, ta xauna a kan kujera tana gyara xaman guntun hijabinta.

Da sallama suka tura ƙofar suka shigo. Turus Sauwama ta yi tana ƙare mata kallo.

"Lafiya kike Wajnah? Kin ga yadda kika dawo kamar wacce ta yi ciwon shekara?"

Kuka ta fashe da shi, tare da faÉ—awa kan jikinta.

Shi kuwa tsaki ya yi, zai wuce ciki sai ya fasa yana kallon Hilah da take kallon Wajnah.

"Anty Ya Huwais ba ya ƙaunata! Duk yadda na so na faranta masa, amma kulle ɗakinsa ya yi ya bar ni na kwana a falo."

"Falo?" Ta faɗa da ƙarfi tana kallonsa da ya yi halin ko in kula da su yana kunna tibi.

"Kai Huwais, kana da sukuni kuwa? Amarya sukutun da guda xa ka bari ta kwana a falo?"

Ɗago idanunsa ya yi, ya kalle su sai kuma ya mayar gurin Hilah, da ta yi jugum tana kallon ƙasa.

"Fitina ta sanya wa ranta ai na gaya mata bana son..."

"Kul kar na ƙara ji ka faɗi haka musamman a gaban ƙanninka. Ke Wajnah mu shiga bangarensa."

Ta ce wanda babu musu ta riga su murɗa ƙofar.

Harara ya bita da shi sannan ya miƙe.

Zama ya yi a kusa da Sauwama, yana sauraren Wajnah da take gaya mata ƙarya da gaskiya.

"Ya gaya mini ya tsane ni ba ya ƙaunata, yana da wacce yake so. Jiya Anty na yi burin da ma mutuwa na yi, kan baƙar rana da na gani."

"Kar ki ƙara faɗin haka, kuma ki kasance mai biyayya da haƙuri za ki ci ribar hakan. Kai kuma Huwais abin da ka yi sam ba ka kyauta ba.."

"Laifin me na yi? Gaya mata na yi bana buƙatarta a rayuwata, kamar yadda tuntini na sanar mata, amma ta yi kunnen uwar shegum Ta shafa ma idanunta toka a dole sai ta aure ni."

"Mene ne laifina don na ce ina sonka? Ko ba ka soni don soyayya ba, ai ka soni saboda dangantakar da ke tsakaninmu. Ni na sam wannan tsinannanniyar da kake so ne take sanyawa kana mini wulaƙanci, kuma wallahi idona idanunta sai na yi ajalinta in ya so ka kashe ni nima, don matuƙar ina raye babu kai ba wata ƴa mace..."

"Anty kina jin abin da take cewa ko? In har za ta rinƙa zagin xaɓin raina, wallahi watarana sai dai ku zo ku ɗauki gawarta."

"Eh ka kashe ni zan fi buƙatar hakan da na yadda wata ta ƙwace mini kai. Na san wacce kake so ba wata bace face kilayar karuwa, saboda in ta gari ce ai ya kamata ka nuna ta."
Chapter 34 · 0% Book details