Sashe 11
Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
â˜€ï¸ *First Class Writers Asso* ☀ï¸
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAÆŠI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a É—ora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyayeâš ï¸
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 7
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Wai ke baki da hanyar da za ki sanar ma mutum kina cikin damuwa sai kuka?" Ya yi mata tambayar cikin takaici ganin hawayen sun ci gabaa da zuba.
Ƙoƙarin sharewa ta yi tare da kallonsa da yake tsaye shi ma ita yake kallo.
"Kin san fa ba kya ƙarya wannan dalilin ya sa da kin yi nake gano ki, ko a yarinyatarki." Ya ce mata wanda ya sa buɗe baki za ta gaya masa haskiyar damuwarta.
"Mahaukacin masoyi ya daina kir..." Maganar ta maƙale mata sakamakon wani birkitaccen kallo da ya yi mata.
"To kuma kan me za ki damu kanki don ya daina saboda dama neman hanyar rabuwa muke yi da shi, cikin sauƙi kuma ya kori kansa? Ni banga dalilin damuwar hakan ba." Ya faɗa ransa a ɓace.
"Ni ma haka nake gani, amma ban san dalilin da ya sa zuciyata ta damu da hakan ba, domin sati biyun sa bamu waya sai na ke jin na kasa sukuni. Duniyar ta yi mini zafi." Ta ba shi amsa cikin wauta wanda hakan ya sa ya yi sororo yana kallonta.
"To kan me za ki yi tunaninsa na ga kina da wanda kike so? Ke da bakinki kin gaya mini ba ki da ra'ayi akansa?"
"Eh, haka nace. Ni ma haushin zuciyata na ke ji a bisa abin da ta bijiro mini da shi."
"To wannan ba damuwa bane, kuma da yau kar na ƙara ganin kin saka kanki damuwa, domin kamar kin tsose ƙwallon mangwaro ne kin huta da ƙuda."
"Har yanzu ka kasa fahimta ta Yaya, na gaya maka zuciyata ta aminta da shi."
Kallonta ya yi kamar na baki da hankali tare da zare idonsa.
"What! Mai kika ce? Kin ko san girman abin da kika saka kanki a ciki? Ni fa cewa na yi ki nuna masa soyayyar ƙarya, don mu gane wanda yake wasa da hankalinki amma ban ce ki aminta da shi ba, domin in har bai bayyana kansa ba bani da hanyar nemo miki shi." Ya faɗa yana kallonta da mamaki tare da kishi sosai a ransa ganin haka take da sauƙi da yawa, don ya ɗauka zai sha wuya sosai. To in da kuma ba shi bane shi ke nan ya rasa ta kenan.
"Ba laifina bane laifin zuciyata ce. Kuma in har za ka iya ganin laifina tabbas za ka iya ganin laifin jaririn da ya faÉ—o duniya a mace."
"Humh." Ya ce don ya rasa bakin magana sai kallonta yake yi.
"Yanzu to mene ne abin yi?" Ya tambayeta cikin rashin dubura.
"Ni ma ban sani ba kuma na ga kai ka ga kawo sharawar." Ta ce tana watsa hannunta.
"Mu bar maganar yanzu ma za ta shi ki haÉ—a mini abincina ki bawa wannan munafukar ta kai mini É—aki."
Duk halin da take ciki sai da ta murmusa."Ba ita ta kashe zomonn ba, rataya aka ba ta. Tun tana yarinya Ummu ta É—auko ta. Cinta da shanta duka kanta yake, idan ba ta yi mata biyayya ba ta butulce."
"Duk da haka zan yi maganinta."Ya ce yana danna wayarsa.
Da ta fita sai ya bita da kallon mamaki yana jin sam bai kyauta mata ba.
Ko da ta dawo zama ya yi, ya rinƙa kwantar mata da hankali da ƙarfafa mata gwuiwar mahaukacin masoyi zai dawo.
"Damuwata ya hana ni numbar da xan kira na ji ko da wani abu ne ke damunsa, sannan na yi masa magana ba zai kula ni ba kuma alamun ya gani."
Da ƙyar ya samu ya rararsheta har ta daina kukan.
Da fari ta jure amma daga baya sai ta ji ta kasa ta koma ruwa. Abin duniya ya haÉ—u ya yi mata yawa. Ga exam da zata fara saura kwana biyu.
Lokaci guda ta rame ta fice hayyacinta ko abincin kirki ba ta ci. Ta zama tamkar amarya, don ko fitowar da take yi su yi hira da daddare ta daina.
Ganin halin da ta tsira sai suka fara ƙorafi musamman Umnaah wanda hakan ba ƙaramin takurara ya yi ba, domon suna matuƙar son junansu. Amnaah ƙaracin shekaru bai saka ta gane ba, sai dai ƙorafi da take mata ta daina mata wasa. Dama ita Azerh cele ce ba ta damu da rayuwar kowa ba daga kallo dai chatting.
Ganin hakan su Abidin suka tuntuɓi Yayan na su tare da tsare shi da tambayoyi.
Take ya ji babu daɗi ganin a dalilin biyewa muradin zuciyarsa ya ɓata farincikin kowa.
"Ni fa ina zargin patiality da Ummu ke nuna wane ya fara damunta. Which isn't good at all, domin ina agains ita dukanninmu ita ta haife mu." Cewar Naufal.
"Don Allah Ya Huwais, ka yi mata magana domin duk mun yi mata, amma fa ce babu komai. Muna damuwa da yanayinta ko abinci kirki ba ta ci, domin breakfast sai ta kai har 11 ba ta yi ba."
Sosai ya ji babu daÉ—i yayin da zuciyarsa take gasgata masa ya tabbata azzalumi mai son zuciyarsa.
"Ku yi haƙuri in sha Allahu, za ta daina I will talk to her. I think distressed na karatun exam ne."
"You have to, kuma bana tunanin haka domin exam baya bata tsoro saboda kafin lokacin ma ta gama karatun shi, ina ga dai kamar yadda Ya Naufal ya faÉ—a haka ne." Cewar Abidin
Binsu da kallo ya yi har suka fice daga É—akin.
Daga ɗakin na sa kai tsaye gurinta suka nufa, tana kwace da waya a hannuta tana kallon tsaƙon da ya yi mata kafin ya daina mata magana.
Kuka take sosai tana jin matuƙar kewarsa da ƙaunarsa na mamaye zuciyarta.
"Anty Hilah kuka? Ummu ne ta dake ki?" Amnaah ta furta wanda ya sa suka yi saurin hawa gadon suna tallafo ta.
Share hawayenta ta yi tana girgiza musu kai sai kuma ta tsinci kanta da ƙara sakin kukan wanda dukansu suka rungumeta suna taya ta.
Bayan fitarsu ya miƙe tsawonsa a kan gadon yana dana-sanin biyewa zuciyarsa, na ba shi shawarar ya fara mata magana, domin ga shi yanzu ya afka kogin nadama.
Miƙewa ya yi ya ɗauko wayar duk da gargaɗin da zuciyarsa take masa amma ba shi da zaɓin da ya wuce ya yi mata maganar.
Tun da suka shigo suka gama kukan, sai ba su fita ba suna ta hira da ƙoƙarin ɗauke mata damuwa.
Kiran sallar magariba ce ta fitar da su wanda Huwais ya ja su a Masallacin gidan su.
Ko da suka dawo É—akinta suka koma, ba su bar ta ba har sai da Ummu ta kora kowa ya je ya kwanta.
Bayan sun fita ta yi shirin kwanciya, ta janyo wayarta tare da jero addu'in da ta saba zubawa kan ya kirata.
Buɗe datar da fara shigowar tsaƙon sai na sa ya shi go kamar haka:
"Barka da Juma'a kyakyawa mai farar aniya. Ina mai baki haƙuri bisa ƙin kiran da na yi, wanda na yi ne don ki fahimci soyayyar gaskiya kike mini ko ta ƙarya."
Babu jan aji kamar ba ita mai daraja da kima ba. Ta tura masa stiskers na kuka sau ba adadi. Sai kuma ta ƙara da rubuta
"Eh na faɗa soyayarka saboda iya kalamanka da adinin ka , don Allah kar ka ƙara guje mini."
Tun daga wannan lokacin suka manne da juna a waya. Hilah da ba ma'abociyar waya ba, amma a yanzu datarta a kunne take barin shi, saboda dakon jiran tsaƙon mahaukacin masoyi.
Wani lokacin sai dai ta danna waya tana murmushi. GabakiÉ—aya ya sanya ta canza É—abi'unta. Don Allah ya yi ta da kwanya da ta samu matsala a karatunta da haddarta.
Tsananin mamaki wani lokacin take yi, tare da ganin wautarta na faɗawa son mutumin da ba ta taɓa ko jin muryarsa ba. Ballantana haɗuwa na zahiri, amma tana jin a ranta ta kamu da ƙaunarsa damu-dumu.
A da duk maganar da suka yi sai ta gaya wa masa, amma da ta ga yana mata faɗa ta daina biye masa haka, sai ta daina sanar masa da komi, wanda hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai.
Ganin ƙaramar magana na nema zama babba sai ya yi tunanin dainawa, saboda ranar yasha mamakin kukan da ta sanya masa, tare da yi masa magiyar ya tura mata hotonsa ko ya kirata ta ji muryarsa.
Da sauri ya kashe gabakiÉ—aya tare da jifa da wayar yana gumi.
Safa da marwa ya shiga yi a cikin É—akinsa. Lokaci guda ya birkice saboda ya yarda cewar ta kamu da sonshi.
"In har ta buƙaci mu haɗu ya zan yi?" Ya yi ma kansa tambayar cikin tsananin tashin hankali tare da kaiwa bango naushi har sai da ya ji zafi a hannunsa.
Saboda tsananin zafin da yake ji rage kayan jikinshi ya yi. Ya rage da ga shi sai singileti da gajeren wando.
A ransa ya yi ninyar daina kiranta gabakiÉ—aya a yau, amma kuma ya san da kamar wuya,gurguwa da auren nesa. Don yadda soyayyarta ta yi masa kamun kazar kuku, ba ya tunanin akwai a bin da zai iya dakatar da shi soyayyarta.
"Ta ya ya zan bayyana kaina a gareta, shin in har ta san nine mai zai faru? Na san babu aure a tsakaninmu, amma to ya zan yi da soyayyarta da yake ƙara ninkuwa a cikin zuciyata? Kuma wane mataki iyayena za su ɗauka?"