← Book details Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 40

Sashe 13

Ranar Wanka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naunauyar ajiyar zuciya ya saki tare da shafa sumar kansa yana murmushi ya juyo yana kallonsa.

Hira suka fara yi har ta É—auko kofin ta É—aurayo ta ije masa.

"Ni bari na tafi, Yayana, sai kun dawo Allah ya tsare hanya ya dawo da kai cikin aminci." Da larabci ta furta tare da tsayawa tana kallonsa.

"Yauwa, ƴar ƙanwata. Allah ya yi miki albarka." Ya furta cikin jin daɗin addu'ar da ta yi masa.

"Amin." Ta amsa tare da É—aukar jakarta tana yi wa Najib sallama.

A hanya Najib yake driving babu wanda ya fara magana sai ya waiwayo ya kalle shi ya maida hankalinsa kan hanya.

"Ina mamakin shaƙuwarku da ƙudirinka kan ƙanwarka, wanda na tabbatar da tsoron Allah da kake da shi ne yake rinjayar zuciyarka, amma da tuni ka yi abin da ba'a so."

"Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba."

TUNATARWA
Shin kina daga cikin matan da karatun Novels yake É—auke musu hankali suke barin sallah ta wuce su? Ko kina daga cikin masu daina karanta Kur'ani ko azkar duk saboda karatun Novels? Don Allah yar'uwata musulma ki daina barin sallolinki na wuce ki saboda karatun litattafai Hausa, saboda ko mu MARUBUTA da muke yin typing da zarar lokacin sallah ya yi muke tashi mu yi sallah. A kiyaye da ibadu musamman sallah saboda ita ce farko da za a fara dubawa a cikin ayyukan mu. Da fatan za ki ji kuma ki hankalta. Fatanmu mu gudu kuma mu tsira tare. Allah ya bamu ikon aikatawa Amin. Taku Jamila lawal Zango.

Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423

*RANAR WANKA...*

NA

JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"

☀️ *First Class Writers Asso* ☀️

Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation

*GARGAGAÆŠI*

Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️

JAN HANKALI

Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.

SADAUKARWA

Kwacakwan labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.

PAGE 8

BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Ubangiji ga tsare ni Najib! Ka san ni ko wane ne? Soyayyar da na ke mata ko da zamu rage daga ni sai ita a duniya, matuƙar Ubangiji bai bani damar mallakarta a matsayin matata ba, ba zan taɓa aikata alfasha da ita ba."

"To ta ya ya, za ka mallake ta? Kar ka manta ciki É—aya kuka fito. Na sha gaya maka sheÉ—an ne kawai ke son wasa da zuciyarka, da yi mata ingixa mai kantun da xai sanya ka aikata abin da duniya za ta la'ance ka."

"Shiru ya ƙara yi kawai ba tare da ya ce komai ba, domin tuntuni shi ma yana tunanin haka.

"Gujewa haka don Allah ka tausaya Wajnah, ka aureta ka daina jiran gawon shanu, domin ko jiya sai da ta kira ni tana kuka, sam bai kamata ka yi mata haka ba."

Shiru ya yi bai furta kalami ba wanda ganin hakan ya sanya ya kunna ƙira'ar Sulaiman Ahmad Suratul Isra'i.

Bayan ya dawo ya yi wanka yana cin abinci ta shigo domin so take ta nemi shawarar shi.

"Am sorry, na dame ka ko Yaya? Kan dai maganar mahaukacin masoyi ne."

"Wannan dalilin ya sanya na ke kishi da shi, domin tun daga lokacin da ya ɓullo cikin rayuwarki, kika daina mini wata hira da magana sai na shi." Ya yi maganar yana tauna abincin a kasale.

"Ka yi haƙuri bani da zaɓi ne." Ta ba shi amsa tare da zama a gefensa.

"Ina son ya bayyana mini kansa kuma na buƙaci haka ya ƙi." Ta ce tare da ƙura masa ido tana kallon shi.

"To ni mai zai ce miki Hilah?."

"Saboda me? Karka manta kai ka bani shawarar na yi soyayya da shi."

"Soyayyar wasa ko?"

"Ya zuciya ba ta da zaɓi, ka san soyayya gaskiya ne. Kamar yadda ka kamu da son wannan budurwar kake ganin za ka iya mutuwa, matuƙar ba ka same ta ba, haka ni ma zan iya rasa raina in har ban auri mahaukacin masoyi ba..."

A zabure ya miƙe daga ƙwanciyar da ya yi cikin tsananin mamaki.

"Kin san me kike cewa? Anya ƙanwata ce? Wacce na santa da tausasa lafazinta a gare ni?"

"Ka yi haƙuri bani da zaɓi ne, domin kan son shi na kurumce kuma na makance zuciyata ba ta ji, ba ta gani. Burina na rayu da shi, saboda yana da addini da iya kalamai."

"Wane tabbaci kike da shi? Bayan baku taɓa haɗuwa na zahiri ba, kuma ba ki san ko musaki bane, wanda ƙila hakan ya sanya ya kasa bayyana miki kansa?"

"Ni fa ko ya yake zan rayu da shi." Ta ba shi amsa kai tsaye wanda hajan ya sanya ya cika da mamaki da tashin hankali.

"Ki dai sake tunani domin ko bayan wannan Ummu ba za ta taɓa yarda ki yaudari Hamad ba?"

"Kai da kullum kake kushe sa, shi ne yau za ka faɗi haka. Na yarda da kaina Yaya. Yadda na ke tsananin roƙon Allah da ya ba ni miji na gari, ba zai haɗa ni da mutumin banza ba, domin Allah ma ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki.

Shiru ya yi ya kasa cewa komai domin ko zai yi maganar bai san me zai furta ba.

Ganin yadda ta tsare shi da idanu sai tsoro ya kama shi, tunaninsa ko ta gane shi ne. Ya tattaro hankalinsa da natsuwarsa ne, sakamakon tuna in har da ta gane shi ne, sam ba za ta yi masa magana cikin natsuwa ba, kasancewar yadda za ta É—auki abin daban.

Tsoro ne da damuwa suka bayyana a fuskarsa har ya firgita sosai. Gudun kar ta gane shi ya É—aga mata hannu yana ce wa,"Please, ki je zan yi tunani na ba ki shawarar da ya makata, amma don Allah kar ki tambaye ni abin da na yanke har sai na neme ki." Ya furta cikin gundurar magana da ita.

"Ok, ba zan tambaye ka ba, sai dai ina roƙonka da ka yi mini adalci, gurin yanke shawarar, domin matuƙar ka ce za ka bani shawarar na rabu da shi, zan fallasawa su Ummu ina son shi, tare da sanar musu da kai ka bani shawarar na fara ƙaunarsa."

Mamaki ya sanya shi zaro idanunsa musamman yadda take maganar babu tsoro ko firgici.

"Hilah!" Ya furta cikin razana ganin za ta fice, amma bai gama shanye ruwan mamakin da ta ba shi daga farko ba, ya ga ta rufe ƙofar ta fice ba tare da ta juyo ba.

Dafe kansa ya yi tare da dunƙule hannunsa ya kai wa bango nushi. Naushin da yake jin dama ita ya kaiwa, saboda tsabar rainin da ya hango a idanunta.

Fara tafiya ya yi zai bita sai ya ga kuma babu amfanin hakan ya dawo ya zauna.

"Lallai na ibo ruwan dafa kaina!" Ya ce tare da sakon ajiyar zuciya mai ƙarfi. Da sauri ya miƙe ya ɗauki gorar ruwa ya buɗe murfin tare da saka murfin a dusbing ya fara sha. Sai da ya shanye tas ya saka robar a cikin mazubin sharar ya shige ɗakinsa cikin tunani.

Hilah kuwa tana fita ɗakin ta saki dariya sosai, ganin yadda ya ruɗe sosai. Godiya ta yi wa zuciyarta na ba ta shawarar ta yi masa wannan barazanar, wanda gashi tana son ta yi tasiri ganin yadda ya ruɗe, saboda ya san ba ƙaramin hauka Ummu za ta yi masa ba.

Saboda abin da ta gaya masa da daddare kasa hawa online ya yi, har sai lokacin da ta tura masa da tsaƙon karta kwana na cewar tana jirar sa.

Ƙarar shigowar saƙon suƙa ƙara rikita duk wani tunaninsa kuma ya gaza sukuni.

Ya kasa komai har sai da ya kunna data suka fara hira. Ba su daina hirar ba sai ƙarfe ɗaya, wanda shi ya umurce ta da ta kashe datar ta yi hadda.

Ganin ba ta sanar da kowa ba ya sanya hankalinsa ya kwanta. Tamkar ya yi baƙo ya mutu. Don haka ya shareta suka ci gaba da soyayya.

A cikin kwanakin ya ji yana buƙatar ya rinƙa jin muryarta, wanda ya san faruwar hakan kamar da wuya.

Dubara ta faɗo masa wanda take ya ɗauki wayarsa ya shiga cikin Ai. Ba tare da ɓata lokaci ba ta canza masa muryarsa kamar yadda ya buƙata. Bayan ya gwada kiran Najib ya tabbatar masa da babu wanda zai gane muryarsa sannan ya bari zuwa dare ya yi surprizing ɗinta.

Da daddaren misalin ƙarfe sha ɗaya saura tana tsaye a gaban madubi ta fito daga wanka tana ɗaure da tawul.

Kiran wayar da Hamad ya yi ya sanya ta fasa sanya kayan baccin da ta fito da su ta É—ora kan gado.

Amsa wayar ta yi kamar yada ta saba. Ba su wani jima ba ya kashe, don babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Shi kansa ya san ba ta son shi, amma sam bai damu ba, domin irin su mutum zai yi burin aurensu ya xauna da su, ko da ba sa ƙaunarka. Ballantana ya san yana cikin jadawalin mazajen da Allah ya yi musu tagomashi da kyawu da iya sace zuciyar mace da kalamai. Wannan ba matsala bane a gurinsa, domin yana sanya rai watarana za ta so shi ta shayar da yaransa.

Bayan ta gama wayar ta ije tana tausayin halin da zai shiga.

Kayan baccin ta sanya tare da É—aukar wayarta ta kunna data.

Mamakin ganinsa da ta yi yana online domin wani lokaci sai ta jira shi ya hau.
Chapter 13 · 0% Book details