← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 37

Sashe 9

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan kika kashe aurenki dan ki auri Ubaydullah, ban yafe ba. Idan aurenki ya mutu saboda Allah bai yi zaku jima tare da Gwamna ba, wannan kuma Allah ne masani. Amma ki manta da Ubaydullah, ki rungumi auren ki bilhaƙƙi. Sannan ki rage dogon buri, wani kwanciyar hankalin, wani jin daɗi da soyayyar sai a Aljannah. Idan kuma Allah ya rubuta za ki samu a duniya to ki godewa Allah da ni'imar da yai miki amma ba yin ki bane. Ki dai cigaba da ƙoƙari kina addu'a idan Allah ya baki kwanciyar hankali ta jikin mijinki wannan ni'ima ne da zaki gode masa. Idan kuma ya jarrabce ki da mijinki kuma kiyi iya naki ƙoƙarin ki barwa Allah sauran, idan kuma zaman ya kai akwai cutarwa har kina ganin zai jawo ki dinga aikata zunubi to inaga rabuwa shine mafi Alkhairi. Ina miki addu'ar Allah ya baki kwanciyar hankali a gidanki. Abu na gaba shine, abinda haƙuri bai bayar ba inaga faɗa ba zai ba da shi ba, idan baki so kanki ba, idan baki samarwa kanki zaman lafiya ba komai mijinki zai miki ba zaki taɓa godewa Allah ba. Na yadda, gidan da kika taso yanada nasaba da yawan zafin ranki amma kuma ya kamata ki daure ki cire komai a ranki, ki ɗauki rayuwa da sauƙi. Allah ya miki albarka ya kuma baki 'ya'ya na gari Amin"

Zuwa lokacin Asiya kuka kawai take yi. Zuciyarta ya karaya da maganar Umma, sai yai mata kamar wasiyyar ƙarshe Umma ke yi.

Kusan ƙarfe biyu na rana wasu securities biyu suka yi sallama a ɗakin da aka kwantar da Umma. Umma tayi bacci, Asiya na danna waya, ƙaninta Gwani kuma na cin abinci.

"Hajiya, Excellency yace mu taho da ke"

"Ni kuma?"

"Yes Ma, in fact emergency ne"

"Barin kira nayi confirm" kafin ta danna wayar message ya shigo wayarta *ki biyosu Asya, Bello ba lafiya*

"Yaya Bello, mi kuma ya sameshi?"

Ta dai san lafiya lafiya ya kawota Asibiti da safe. To ko wani abin yaje ya sha ya fara haukan daya saba.

"Gwani, idan Umma ta tashi kace Gwamna ne ya kirani, ba zan jimaba zan dawo"

"To"

Lokacin da ta miƙe securities ɗin suka sara mata yayinda ɗaya ya shige gaba ɗayan kuma ya tsaya a bayanta. Haka suka ƙarisa wajen wasu motoci guda biyu. Yanayin motocin bai sawa Asiya wani shakka ba.
Aka buɗe mata ƙofa ta shiga tana addu'ar Allah yasa Yaya Bello na lafiya.

Suna fita daga Asibitin aka kunna wani turare daga ɓangaren Dreba. Asiya ta riƙe kai saboda wani ciwon kai data fara ji, ta fara ƙoƙarin toshe hancinta amma ina ta riga ta shaƙi abin, idanunta suka fara rufuwa a hankali, tana ƙoƙarin magana ta faɗa ɗaya gefen sai bacci...

6

Gwamna Saifuddeen Kachallah yana zaune a dinning room yayi tagumi Bilkisu ta shigo sanye da wata doguwar riga na material kalar abin cikin ƙwai.

"Darling ka manta wayarka a É—aki" tayi maganar tana ajiye wayar a gefensa.
Ta maida dubanta ga Junior da ke wasa da abinci, sai ya ɗebo shinkafa a cokali sai ya zuba a kan dinning table ɗin yana barbazasu ɗai ɗai "Junior eat your food, ko na saɓa maka"

"I'm not hungry"

"Mi kake son ci?"

"Ice cream"

"Ice cream fa ka sha shekaranjiya ya sa ka gudawa. Eat, gobe sai a siyo maka ice cream É—in"

Ta kalli Gwamna da har yanzu ko taɓa abincin bai yi ba, tace

"Darling Dan Allah ka ci abinci, jiya kayi Azumi, yau baka karya ba ka fita and now..."

Gwamna ya kalleta yace " Bana tunanin iyayen yaran nan suna cin abinci. Bana tunanin suna samun bacci"

"To Saifuddeen ya zamu yi musu? You are doing your best, wanÉ—annan kidnappers É—in suna yiwa 'yan adawa aiki ne, da sannu za a kama su"

"Ni ake kallo Bilkisu, nine Shugaba"

"Ka yi iya naka ai, tunda ka saka jami'an tsaro su nemo su, ko so kake ka É—au bindiga ka shiga daji farautar Kidnappers?. Please, akwai abubuwa dayawa a gabanmu, za mu fita campaign gobe ka kwantar da hankalinka, za a samesu"
Ta ƙarisa maganar tana riƙo hannunsa tareda ɗaura murmushi a fiskarta.

***
Ubayd ne ya kawo Habibu da Ali a motarsa, suna shiga É—akin Umma suka samu ta tashi tana yiwa Gwani magana.

Abu na farko da ta tambaya shine ina Asiya?
Daga gida suka taho sun san Asiya bata nan, shiyasa sukayi tunanin ko tana chan gidanta ne.

Wasa wasa ana jiran shigowar Asiya har aka yi sallar la'asar amma shiru, numbarta kuma a kashe. Lokacin da Sumayya tazo Asibitin tayi ta ƙoƙarin kiran numbar Asiya amma still a kashe, ƙarshe ta kira Yaya Bello ta tambayeshi ko Asiya tana gidan Gwamna ne ko gidan Gwamnati.

"To ai ni tuntuni nake jiran kiranta"

"Yaya Bello aka ce Gwamna ne ya aiko aka É—auketa da rana, kuma har yanzu numbarta baya shiga. Umma ce take nemanta tun É—azu"

"To ni dai ban sani ba, amma zan sa a duba mini cikin gidan"

Kusan minti goma sai ga kiran Yaya Bello inda yace Hansa'u tace Asiya bata zo gidan ba.
Sumayya ta kira Uwani ta tambaya ko Asiya ta zo gida amma zancen É—aya ne, tunda Asiya ta fita da sassafe bata dawo ba.

Jikin Sumayya yai sanyi, amma tunda akace Gwamna ne ya aiko ta je, ƙila tana Kachallah House ne ko kuma wani wajen daban.

Babu wanda ya kawo komai a ransa sai da aka ga har anyi sallar Magariba Asiya bata dawo ba sannan bata kira ta faÉ—i dalilin rashin zuwanta ba ga kuma numbarta har lokacin a kashe.

Kusan ƙarfe takwas na dare, Sumayya ta shimfiɗa sallaya ta fara sallar Isha. Mazan tun da suka fita sallar magariba babu wanda ya dawo cikinsu.

Sumayya na sallah Umma ta fara wani irin nishi, daga ƙarshe kuma sai shiru. Da Sumayya ta idar da sallah sai ta kwanta akan sallayar, ta buɗe wayarta ta cigaba da chatting, da sabon saurayinta take chatting kafin ta fara sallan kuma har yanzu yana online shiyasa ko azkar bata yiba ta ɗau wayar dan ta maida masa reply ɗin chat daya turo.

Minti shabiyar bayan haka Abba ya shigo É—akin da sallama.
"Har yanzu ba a ji daga Asiya ba?" ya tambaya bayan Sumayya ta masa sannu da zuwa.

"Har yanzu Abba, Abba nace ko zaka kira Gwamna ka tambaye shi ne?"

"Sumayya mutum ya kira matarsa sai mu fara bibiyarsa ko lafiya, ƙila wani wajen suka je kin san ana kan kamfen"

Ya É—an matsa kusa da gadon Umma dan ya tambayeta ya jiki amma yana ganinta zuciyarsa ta harba.

Sumayya tana cikin chatting ta ji Abba ya furta Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun.

"Abba miya faru ?" Ta furta a firgice.

"Kira min likita" ya furta a hankali yana faman gyara kwanciyar Umma.

Lokacin da Sumayya ta dawo da likita samun Abba tayi zaune gefe yana waya, kaman da Ubayd yake magana dan taji yace "ka kira Yahanasu ka faÉ—a mata sannan ku taho da Habibu"

Ba abinda likita ya iya yi sai dai kawai jaddada rasuwar Umma da yai.
Sumayya ta fashe da kuka mai shiga rai.

Kusan ƙarfe tara da rabi na dare aka kawo gawar Umma gida. Inda Inna Yaha da wasu mata ke zaune jugum suna jiran dawowarsu Abba. Tunda Ubayd ya sanar da Inna Yaha mutuwar Umma, ta fashe da kuka tana sunbace sunbace, kuka da kururuwarta ne ma ya ja hankalin maƙota.

Tun a Asibiti Abba ya kira Gwamna amma numbarsa a kashe. Ƙarshe dai Yaya Bello aka kira akace ya gayawa Gwamna saƙon mutuwar saboda numbarsa bata shiga.

Yayinda ake wannan, Gwamna yana meeting ne da jami'an tsaro kan ɗaliban da aka sace. Rikiɗe musu yai a wajen yana ta faɗa, yace ya basu awa arba'in da takwas su gano inda yaran suke, ko su gano su waye kidnappers ɗin, sannan mi suke so. Idan babu wani labari mai ma'ana, zai sauke dukkansu daga muƙamansu.

Commisioner of Police yana shiga mota ya kira wani number yace "Gwamna yayi fushi sosai fa, ya bamu 48hrs mu nemo yaran nan, kasan abinda zaka yi ko kuma na bawa yarana daman kama su" yai shiru yana sauraran bayani daga ɗaya ɓangaren. Ƙarshe ya amsa da "To, to na ji"...

Lokacin da Gwamna ya isa gida, ana buɗe masa ƙofa Yaya Bello ya iso ya sara masa yana yi masa sannu da zuwa.
"Ranka shi daɗe ina da saƙo daga wajen Abban Asiya"

Gwamna ya kama hannunsa suka wuce cikin gida.
Falon farko suka zauna. Gwamna yai yai Yaya Bello ya zauna akan kujera amma ya ƙi wai ba girmansa bane Gwamna ya zauna a kujera shima ya zauna.

"Lafiya dai ko?" Gwamna ya tambaya bayan sun É—an nitsu.

"Ranka shi daÉ—e. ÆŠazu Malam Nuhu ya kirani ya sanar dani an masa rasuwa"

"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun, wa ya rasu?"

"Allah yai wa Umman Asiya rasuwa"

Gwamna ya dafe kansa yana addu'ar Allah ya jiƙanta, ya gafarta mata. Lokaci guda kuma ya ɗago kansa jin abinda Yaya Bellon ya faɗa.

"Yace a faÉ—awa Asiya rasuwan, idan da hali kuma ta zo ta ga mahaifiyarta kafin a mata sutura"

As far as he know, Asiya tana Asibiti tun safe.

"Ban gane ba. Asiya bata Asibitin ne?"

Yaya Bello ya É—ago ya kalli Gwamna cikin rashin fahimta yace "ai tunda ka aiko aka É—auketa bata sake dawowa ba, kuma nambarta a kashe tun lokacin"

"Na aiko aka É—auketa? Yaushe? Wa zan sa ya É—aukota idan ba kai ba. Su waye suka zo suka É—auketa? Bata chan gidana kuma?" Yai maganar duka lokaci guda.

"Ance bata koma gida ba tun lokacin data fita da safe. Ƙaninta yace mutane biyu ne suka zo sanye da baƙaƙen kaya suka ce ka ce su ɗaukota"

Gwamna ya miƙe tsaye yana faɗin "kana so kace ba a san inda Asya ta shiga ba tun da rana?"

"Ranka shi daɗe ayi haƙuri"
Chapter 9 · 0% Book details