← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 37

Sashe 3

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwamna na zaune a office ya kalli program ɗin da Hill TV suka watsa. Duk cikin mutanen da suka yi magana, mutum ɗaya kawai ya iya tunawa, wani mutumi wanda yanzu ya zama babban magidanci. Loƙacin da ya koyar da shi kusan shekaru goma ko shabiyu baya, sai daya maimaita course ɗinsa sau biyu a na ukun Prof Saifuddeen ya sa shi a gaba kaman ƙaramin yaro yana biya masa karatun da Hausa, a hankali yana masa haka har ya zo ya zamana duk wani darasi da baya ganewa sai ya kawowa Prof SSK ya biya masa koda ba shi ke ɗaukan darasin ba.
Abubakar Talle sai daya maimaita shekaru biyu amma ranan da yai presenting project nashi yai bayani da Hausa da kuma Turanci kowa tafa masa yake saboda ya burge kowa, dalilin wannan project ɗin ya samu scholarship a ƙasar waje. Duk da ya jima basu haɗu ba amma ba a wata ɗaya ko biyu Abubakar Talle bai kira sun gaisa ba.

Ya sani aikin Asiya ne, amma hakan bai burgeshi ba ko kaɗan. Zai fi so ma ace ta cire kanta daga wannan matsalar. Yana da yaƙinin cewa Allah daya kuɓutar dashi daga sharrin Lami Ninja shekaru shabiyar baya shi zai fitar da shi daga wannan ma. Shi yanzu ko da za'a tsigeshi ba zai damu ba, After all mulkin da komai ya fita a ransa.

Sakatare daya shigo ne ya sa shi yin firgigit, ya ajiye jaridar Congo Daily a gabansa

"Your Excellency ka duba shafi na uku"

"Idan akan maganar nan ne ka É—auke jaridan"

"Sir?"

"Ka É—auke please"

Sakatare ya É—auka ya fita da shi.
ÆŠazu da Bilkisu ta kira shi ta masa maganar abinda aka rubuta a jaridar. Yana jin brief na abinda aka rubuta ya san Asiya ce. Ta rubuta cewa Lami Ninja karuwa ce Uwar Karuwai da take da gidan karuwai A Lagos.

***

Madam Bintu ta shigo ofishin Bilkisu Kachallah jiki na rawa.

"Mi yake faruwa? Ya haka?"

"Na ji labarin za ki tona asirin Lami Ninja"

"Ofcourse, inada shaidah akan cewar tana fitar da 'yanmata yin karuwanci a ƙasashen waje"

"Hmmm! Bilkisu ki haƙura da batun nan"

"Mi ya sa?"

Madam Bintu ta sassauta murya tace "idan kika tona mata asiri, Umaru Kwom zai tona naki"

"Ban gane ba?"

"Yadda kike da hanyar nemo ɓoyayyun bayanai haka shima Umaru Kwom keda hanyar nemowa. Infact shiya kirani ɗazu yace idan maganar sex trafficking da Lami Ninja takeyi ya fito, zai fitar da namu sirrin"

Bilkisu ta buga teburin gabanta tana faÉ—in "DAMN"

Da bata shiga harkan ƙwaya ba shekaru biyar da suka wuce da babu yadda za ai Umaru Kwom yai mata barazana. Yanzu kenan ga samu ga rashi.

"Ba zan bari a tsige Saifuddeen ba Bintu"

"Bilkisu sai dai ta wani hanyar amma ba wannan ba"...

Washegari ma an watsa shirin Asiya inda wasu É—alibai daban suka sake bayyana kyawawan halayen Gwamna lokacin yana Malami. A kafar sadarwa ta twitter ma sai campaign ake yiwa Gwamna ana faÉ—in Gwamna bai da laifi.

A washegarin ne kuma gidan rediyon 'Yanƙasa ta sako shiri inda mutanen da Umaru Kwom ya biya suka dinga muzanta Gwamna suna ɓata masa suna, akwai wanda yace ma lokacin yana ɗalibi Prof Kachallah ya ƙwace masa budurwa.

"Damn it, CY, Umaru Kwom yayi amfani da rediyo saboda ya san zai fi shiga lungu da saƙo"

A ɗaya ɓangaren CY yace " munada supporters a twitter"

"Ba ka gane ba CY, wannan abin Kamfen ne. Koda ba a tsige Gwamna ba, Umaru Kwom ya riga ya ɓata mishi suna zai affecting zaɓe. Kasan mutane sunfi ɗaukan maganar ƙarya akan na gaskiya"

"Zamu iya sa shirin a gidan rediyo muma"

"Sai dai haka. Ina fata Fou'ad zai nemo wani abu akan Lami Ninja before it is too late. Sati É—aya Gwamna keda shi, idan house suka voting ayi trial ka san idan Gwamna bai iya wanke kansa ba cikin watanni uku, automatically ya tafi kenan"

"Mi zai hana ki je department ɗin daya koyar kiga ko zaki samu wani abu. Ai tace ya bata carryover ne saboda ya nemeta ta ƙi, if you can prove her wrong then inaga za a zargi maganarta"

"CY ashe dai jinya da kayi bai taɓa maka ƙwaƙwalwa ba"

CY yai dariya.

Ƙarfe biyu na rana ta shirya ta fito. Tsayawa tayi chak lokacin data ganshi yana takowa. Tun ranan da sukayi magana bata sake ganinsa ba sai yanzu. Half jamfa ya saka na baƙin Geztner da baƙar hular Zannah, komai na jikinsa baƙi ne, takalmi, agogo da ma gilashin daya ɓoye idanunsa da shi. Yayi kyau sosai.

Sai da ya zo daf da ita ta saka masa murmushi tace "sannu da zuwa Your Excellency"
Hannu ya ɗaga mata ya wuce ba tare da ya amsa ba, ta shaƙi ƙanshin turarensa, ƙanshin ya shige har chan ciki ya fara kaɗa mata hanji.

Ta rasa kunyarsa da take ji yanzu ne ya kawo wannan baƙon yanayin, ko kuma tun dama tanajin nannaɗewar hanji idan suka haɗu?. Taku biyu ta yi ta juya ta ƙara kallonsa, mutum biyu ne a bayansa wanda zasu rakashi zuwa ƙofa, kanshi zuwa ƙeyarsa kawai ta gani saboda ya kere securities ɗin tsayi.

Tana shiga mota ta tambayi Yaya Bello ko ya sha wani abu kafin ya fito.

"Yasin ba abinda na sha sai ruwa"

"Ni dai kayi tafiya da hankali Yaya, idan kuma so kake a kaiwa Ale gawata ne, to"

Yaya Bello yasa dariya yace " yanzu kam ai kin zama ta Gwamna, ko mutuwa kikayi shi ke da iko da gangar jikinki"

A take maganar Gwamna ya faÉ—o mata *"Ki faÉ—i koma minene, hakan ba zai chanja cewa daga yau gangar jikin, zuciyar da ruhin duka Allah ya mallaka min ba"*

Da wani ido zata kalli Ubangiji idan ta mutu Gwamna bai yafe mata ba?

A dai dai department na Political science Yaya Bello ya ajiyeta. Makarantan ya ƙara yiwa Asiya cika, rabonta da cikin makarantar tun watarana da tazo yin rahoto lokacin da ɗalibai sukayi riot saboda 'yan cult sun kashe wani ɗalibi.

Sau ɗaya ta taɓa zuwa department ɗin saboda akwai wani course da sukayi da 'yan Pol Science lokacin tana aji huɗu. Ba ta san Prof SS Kachallah ba a lokacin saboda a shekarar ya ajiye aiki.

Ita É—aya ta fito daga motar ta nufi cikin department É—in. Ba kamar Bilkisu Kachallah ba, tunda ta zama Matar Gwamna duk fitar da za ta yi ita É—aya ko kuma ita da Sumayya suke fita. Bilkisu idan zata fita to da motoci biyu ko uku ne, tareda securities da mai É—auka mata jaka.

Wasu É—alibai da suka fito daga cikin department É—in suna ganinta suka fara ihu "Wow! First lady ce, Asiya Kachallah"

Saboda ma kar a ganeta da wuri yasa ta saka ƙaton glass ta toshe fiskanta, amma duk da haka sai da aka ganeta.
Ta tambayi É—aliban suka nuna mata ofishin HOD.

Sakatariyar HOD na ganinta ta miƙe jiki na rawa ta mata iso zuwa ofishin HOD. Matsayi kenan, da ace bata auren Gwamna bata tunanin wannan tsohuwar matar za ta yi rawar jiki dan tana neman ganin HOD.

"Sunana Asiya Shahidah FaruÆ™ Baba, MATAR GWAMNA" Asiya ta faÉ—a lokacin data zauna.

HOD ya gyara zaman gilashinsa daga kan hanci zuwa ido yace " sannu da zuwa Excellency"

3

Kafin Asiya ta fara magana wayarta ya shiga ƙara.
Ganin Sumayya ne ke kira ya sa ta katse kiran ta saka wayar a silent.

"Dr Nuru ina neman haÉ—in kanka ne bisa wani bincike da nake yi"

"Bismillah Hajiya" HOD ya faÉ—a yana rarraba idanu.

"Ina son ganin file ɗin wata ɗaliba mai suna Lami Haladu, ba sai nayi dogon bayani ba kasan wa nake nufi. Sannan ina son ganin exam scripts ɗinta na shekarar 2000, abu na ƙarshe kuma ina son sanin wanene Dean na faculty da kuma HOD na department a shekarar"

"To Ranki shi daɗe naji daɗi ƙwarai da zuwanki, abinda zan iya faɗa shine scripts na jarrabawa basa wajenmu a yanzu haka, ana kaiwa exam and record ne, dan haka ba zan iya cewa ga inda za a samu script na Lami Haladu ba amma zan iya sawa aje a duba miki ko akwai ko babu. Abu na gaba kuma ki bani minti ɗaya na duba wani file"

Dr Nuru ya miƙe ya je wajen shelf ɗin dake office ɗin ya fara dube-dube. Kusan minti uku bai samu ba, ƙarshe sai ƙwalawa Sakatariyarsa kira yai. Miss Ifunanya na zuwa ko minti ɗaya bata kai ba ta fito masa da file ɗin da yake nema.

Dr ÆŠanladi shine HOD a lokacin kuma ya riga yayi retire sannan shekaru biyu kenan da rasuwarsa. Shima Dean É—in lokacin ya jima da rasuwa.

Asiya ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin abinda za tayi. Mutumin da aka aika ya je exam and record ya dubo script shine yanzu kawai zaɓinta.

Kusan minti goma shabiyar sai ga shi ya dawo. Ƙasa-ƙasa yaiwa HOD bayani, bayan ya gama HOD ya gaya mata cewa babu scripts na shekarar 2000 duk an riga an ƙona su wanda suke ƙasa daga shekarar 2007 ne.

Gwiwa a sace Asiya ta fito daga department É—in ta nufi wajen motarta.
Bayan ta shiga motar ne ta kira C Y ta faÉ—a masa cewa bata samu abinda ta je nema ba.

***

"Anty lissafin mi kike ne?" Sumayya ta tambaya tana riƙe ƙugu

Asiya bata kulata ba, ta cigaba da rubuta ranaku tana lissafin yaushe ne ranakun girkinta. Gwamna bai fito ya raba musu kwana ba amma lokacin tana chan gidansa satinta É—aya ya koma yana zuwa yai mata kwana biyu duk da ma ba wai ta sa masa ido bane amma lokaci zuwa lokaci Sumayya na faÉ—a mata cewa Gwamna ya kwana a gida yau.
Bayan kusan minti shabiyar sannan ta samu bakin zaren, idan lissafinta ya tafi dai dai to gobe zata karɓi girki. Abu ɗaya take so a wajenta shine ya yafe mata abinda ta aikata.

Babu sallama babu komai Bilkisu Kachallah ta shigo É—auke da jarida a hannunta, tana zuwa ta jefa gaban Asiya da ta bararraje a kan kafet.

"Fix this, matsalar Lami Ninja ya ishemu ba sai an haÉ—a da taki ba"
Chapter 3 · 0% Book details