← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 37

Sashe 11

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya tana ganin rahoton amma hawaye ko É—aya bai fito ba, zuciyarta ya yi mata nauyi. Tana ji kamar kumbura zuciyar take, nan da anjima kaÉ—an zata fashe, idan ta fashe kuma sai itama a kaita inda aka kai Umma.
Sai dai haka ta zauna a wajen tana jiran zuciyar ta fashe amma taƙi fashewa, bata ma da alamar zata yi komai saboda duk yadda take dokawa cikin ƙirjinta babu abinda ya faru.

Kamar wata zararriya ta tashi tsaye tana safa da marwa a ɗakin tana faɗin "sun kashe Umma, sun kashe min mahaifiya, ba abinda ta musu suka kashe min ita, bata magana ma amma basu barta ba, tana fama da cancer amma basu barta ba, ɗan albarka da take sa min kullum ma sun katse" ta dinga safa da marwa ƙarshe ta faɗi ƙasa tim saboda hajijiya...

Ba a gama juyayin rasuwar sirikar Gwamna ba, special adviser na Gwamna ya fito ya bayyana cewa an sace matar Gwamna Asiya Kachallah.

Umaru Kwom yana gidansa yana sauraren masu kawo masa gulmar yadda mutanen gari ke yabonsa aka fito da labarin da ya girgiza shi.

"An sace Asiya Kachallah?. This is a set up" ya faÉ—a cike da damuwa domin ya hango ma'anar hakan. Saifuddeen Kachallah ba zai iya amfani da iyalinsa wajen Kamfen ba amma akwai wanda zai iya...Alhaji Sani Kachallah.

Kafin dare maganar Siyasa ba gaba bace ta rikiÉ—e ta koma *#Save Asiya Kachallah?*

Ale FaruÆ™ ya zo ta'aziya dan bai samu sallar jana'iza ba. Daya zo ne kuma ya samu labarin sace Asiya da akayi. Abin ya É—aure masa kai, taya za a sace Matar Gwamna guda?.
A matsayinsa na Uba ya ji ba daɗi, ya shiga ruɗu, dan har gwada kiran numbar Asiya yai ko za a dace ta ɗauka, ƙila wani wajen ta shiga ba a sani ba.
Bai bar cikin jaha ba sai chan yammaci, ya tafi da niyyar idan anji wani labari akan Asiya zai dawo.

Ga sauran ahalin Malam Nuhu kuma, kowa ka gani ciki kasan baya cikin kwanciyar hankali. Abba dannewa kawai yake amma kusan shi yafi kowa damuwa a gidan, shi daya rasa matarsa uwar 'ya'yansa uku, biyar idan ka haÉ—a da wanda ya rasu kafin a haifi Ali da kuma wanda ta tafi da shi a cikinta.

Tun bayan rasuwan Hassana mahaifiyar Ubayd sai daya auri Zainabu Kurma ya samu nitsuwa. Kai, zai iya cewa Zainabu tafi Hassana saboda zaman da yai da Hassana shekaru biyune da burbuÉ—i, ita kuma Zainabu shekaru goma shatara ba wata biyu.

***

"Saifuddeen...Saifuddeen...Darling. idan baka ci abinci ba taya zaka samu ƙarfin yiwa Jahar nan aiki?"

Gwamna Saifuddeen ya ɗago rinannun idanunsa ya kalli Bilkisu. Abinci ne ƙarshen abinda zai sa a ransa yanzu.

"We can fix this amma sai ka kwantar da hankalinka. Without food, ƙwaƙwalwarka ba zata iya aikin komai ba"

"Azumi nake Bilkisu"

"Idan anyi Azumi ai ana shan ruwa, rabonka da abinci tun jiya fa Saifuddeen"

"Kawo min Apple"

"Apple kaÉ—ai za ka ci?"

"Ki haÉ—o da ruwa mai sanyi"...

A ɓangaren Asiya bata farfaɗo ba sai lokacin da aka kawo mata abincin dare. Suna ganinta haka hankalinsu ya tashi suka shiga yayyafa mata ruwa har sai da suka ga ta jaa dogon numfashi kafin suka daina yayyafa ruwan.
Babu yadda ba suyi ba akan ta ci abinci amma ta ƙi, dan su tunaninsu abincin da bata ci bane tunda aka kawota ya sa ka ta suma.

Sai da ta shammacesu sun sake jiki suna mata magana tayi wuf, ta nufi hanyar ƙofa da gudu amma bata kaiba aka sake mata bindiga a baya. Harsashin dake cikin bindigar wata allura ce dake saka mutum bacci dan haka allurar na cakarta ko sakan biyu bai cika ba, ta faɗi a wajen.

Bilkisu Kachallah tana zaune kusa da Gwamna tana yanka masa Apple wayarta ya shiga ƙara.

"Ki É—auka mana" Gwamna ya faÉ—a ganin ta share wayar duk da kuwa ta gama yanka Apple É—in.

"Ƙila masu neman kuɗi ne"

Gwamna bai ce komai ba ya dai cigaba da cin Apple a hankali, ba dan daÉ—i ba sai dan dole ne ya sa wani abu a ciki duk da ya É—au alkawarin yin Azumi har ranan da za'a ga Asiya...

"Nace ban yarda ta fita ba, idan taƙi cin abinci ruwanta ne. Idan kuka ga ta galabaita ku mata ɗure, ban damu da lafiyarta ba but keep her alive"

"Waye a nan?" ta faÉ—a lokacin data juyo tana sauke waya daga kunnenta.

"Lah! Hajjajuna dama ina so na nemi wani alfarma ne"

Bilkisu Kachallah ta harari Hansa'u tace "shine zaki shigomin É—aki ba sallama"

"Kwarankwatsi tun ɗazu nake ta sallama a bakin ƙofa ba ki amsa ba, shine na shigo"

"Minene?" Bilkisu ta faÉ—a da kakkausar murya.

Hansa'u ta tsugunna tace "An bugo wai Gyatumata bata da lafiya"
Ba zata taɓa manta farkon zuwanta gidan ba. Watarana Bilkisu ta kirata ɗaki, tana shigowa sai ta tsaya a tsaye. Kafin ta farga har ta kai ƙasa saboda wani maka da Bilkisun ta kai mata tana faɗin "ina tsaye kina tsaye"

Bilkisu tayi tsaki tace "Bakin kine gyatumar ai. Mi kike so?"

"Hajjaju ina so Dan Allah ki bani kwana biyu na je na gaisheta"

"Kwana biyu? Are you mad, wa zai kula da Junior?"

"Ranki shi daÉ—e akwai su Onome, su Safiya su..."

"Duk ciki waya saba da su idan ba ke ba. Ba inda zaki je, zan baki kuÉ—i ki aika mata, Allah ya bada lafiya"

Hansa'u ta langwaɓa kai. Idan kaji Bilkisu tana maganar kula da Junior, zaka ɗauka jariri ne. Yaro ɗan shekara shida amma yadda ake nuna masa gata sai ka ɗauka ɗan goye ne.

"Hajjaju a taimaka ko kwana É—aya ne naje na dawo. Ban sani ba ko jinyar mutuwa ne, ina so mu gana kafin rai yai halinsa"

"Idan mutum yai abu sai ku ce shi mugu ne. Kin san dai tunda aka fara Kamfen ba zama nake ba, sannan Junior yana buƙatar kulawa ta musamman"

"A taimaka dai, a duba Dan Allah"

"Fine. ki je ki dawo a goben"

"Nagode Hajjaju" ta faɗa tana riƙe ƙafar Bilkisu. Bilkisu ta yarfe ƙafarta tareda jan tsaki ta fice daga ɗakin. Tana fita Hansa'u tayi murmushi.

Washegari Hansa'u data fito daga gidan Gwamnati Keke ta nema ya kaita wani madaidaicin gida. Tana shiga suka gaisa da matar dake kula mata da gidan sanan ta wuce banÉ—aki tayi wanka.

Tana fitowa sanye da towel ta kalli kanta a madubi, shekaru sun ja amma har yanzu tana da kyau. Ba zata taɓa manta ranan da aka kawota gidan Alhaji Rufa'i ba, 'yar ƙauye da ita. A shekaru shashida ba abinda ta sani na uƙubar rayuwa sai data shigo gidan. Ita 'yar ƙauye ce amma a ƙauyensu ita ɗin 'yar babbar mutum ce saboda Baffanta yafi kowa Shanu a ƙauyen dan haka ba cikin wahala ta fito ba.

"Aaah, kai Masha Allah! Ashe kyakykyawar Bafulatana aka samo maka Alhaji" maganar Madam Bintu ya sake maimaituwa a ƙwaƙwalwarta.

"Wannan ai dana haihu da wuri ai sai dai nayi jika da ita, ba kishin da zan yi da ita Alhaji, ai ni 'ya ka kawo min"

Munafukin mutum akwai shi da iya daÉ—in baki. Ranan da Alhaji Rufa'i ya haÉ—asu yana musu nasiha Madam Bintu yadda ka san matar Aljannah haka ta dinga maganganu masu daÉ—i tana nunawa mijinta babu komai.

Ita ɗin kamar sadaka ce aka yiwa Alhaji Rufa'i. Tana shekara shauku aka mata baiko da ɗan uwanta Siddiƙu. Watanni uku da baikon aka fara shirye-shiryen biki. Ranan da za a ɗaura aurensu Allah ya masa rasuwa. Daga nan aka yaɓa mata baƙin jini akan tana da farar ƙafa idan ba haka ba taya za ayi mutum lafiyarsa ƙalau ace ranan aurensa ya rasu. Duk wanda aka yiwa tayi a ƙauyensu sai yace a'a yana tsoro, wasu ma har maita suka laƙa mata. A wani zuwan da Alhaji Rufa'i yai ne Baffanta ya masa maganar ko zai sama masa miji a birni dan 'yarsa tayi kwantai. Mamaki ya kama Alhaji Rufa'i lokacin da ya ji shekarun yarinyar shashida amma har ana faɗin tayi kwantai.
Duk bayanin da Baffa Kabiru ya masa gani yai kawai jahilci ne irin na 'yan ƙauye.
Daga ƙarshe dai da Baffa Kabiru ya masa tayin Rabi'atul Badawiyya sai ya amince, a tunaninsa ƙila za a dace ya samu haihuwa tunda matarsa Bintu shekaru ashirin da ɗaya da aure amma shiru babu haihuwa.
Alhaji Rufa'i yana shekara hamsin da biyar ya auri Rabi'atul Badawiyya.
Shi ba mazaunin ƙasar bane amma saboda auren sai da ya zauna a gida na watanni uku ko za a dace.
Farko farkon aurensu da Madam Bintu yayi ta yawoce yawocen Asibitoci ciki da wajen ƙasa amma duk zancen ɗaya ne, ba shi da matsala. Bai san dalilin dayasa ya kasa ƙara aure ba tun lokacin, duk da irin matsin lamba da ya ke fuskanta daga 'yanuwansa. Kafin rasuwar mahaifiyarsa sai da aka aura masa mata amma zamansu bai jima ba ta gudu, tace dole sai dai ya saketa har yau bai san dalili ba kuma bai nemi sani ba.

Ƙaddarar aure ne ya shiga tsakaninsa da Badawiyya shiyasa har ya ji sha'warta bayan Baffanta ya masa tayinta.

Watanni uku yai bai fita ko'ina ba yana addu'ar Allah yasa a dace. Shiru kuwa har ya tafi ƙasar Germany duba wani kamfaninsa dake chan.
Satinsa biyu a chan Likitansa ya kira shi yana masa barka domin Amaryarsa tana ɗauke da cikin sati biyar. Kaman Alhaji Rufa'i yai tsalle ya ganshi a Nigeria haka ya dinga ji, murna a gunsa ba a magana. Jirgin washegari ya booking zai dawo amma ɓarayi suka shiga gidansa suka harbeshi har lahira.

Tunda Madam Bintu ta ji bayanin Likita lokacin da ta kai Badawiyya Asibiti bayan ta suma, hankalinta yai mugun tashi. Ƙarshe ta tura kuɗi chan Germany wani Assassin ya je ya kashe Alhaji Rufa'i har gidansa.

Lokacin da aka zo maganar rabon gado haka Madam Bintu ta ƙeƙasa kasa akan sai dai a bari Badawiyya ta haihu tukunna wai ai ba sauri suke ba. Ita ta hana 'yanuwan Badawiyya su tafi da ita tace zata kula da ita sosai.
Chapter 11 · 0% Book details