Sashe 32
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban gane za a dakatar da binciken nan ba. DEA suna da interest akan wannan case, miyasa za a ce a rufe shi. Ina buƙatar mutumin da BBC eye ta yiwa interview"
Kallonta kawai suke yi saboda abu ne da ba zai yiwu ba domin kuwa daga sama aka aiko akan a rufe file É—in.
"Ba kallona zaku yi ba, i need answers"
Wani dogo a cikinsu ya sassauta murya yace "Gwamnati ba zata saka hannu a binciki Matar Gwamnan jahar Congo ba"
Agent Dahlia ta ƙura masa jajayen idonta tana mamakin kalamansa, chan kuma ta furzar da iska sannan tace "inaga ka manta cewa ni ɗin Gwamnatin America nake yiwa aiki ba taku Gwamnatin ba. My country does not take shit"
Ta kalli sauran jami'an dake wajen É—aya bayan É—aya sannan tace " mark my words, sai na kai matar Gwamnan jahar Congo kurkuku"
Daga fitar ta daga ɗakin taron aka shiga tattauna yadda wannan iƙirari nata ba zai zamo gaskiya ba, a wani ɓangare kuma suna tsoron fushin Gwamnatin America idan wani abu ya samu jami'arsu.
***
Bilkisu Kachallah ta sake kallon documentary na BBC eye a karo na uku, chan cikin zuciyarta tana ayyana wani abu mai girma wanda zai iya girgiza jahar Congo sannan ya ƙarawa Gwamna Saifuddeen Kachallah farin jini.
"What if she goes to jail?. Wannan zai zama sakamakon amsa sunan matar Gwamna da tayi iya tsawon waÉ—annan watanni"
Da tayi maganar kuma sai ta fashe da dariya musamman da idonta ya hasko mata Asiya cikin kayan firsina.
"And the uniform will suit her, hahahaha" ta cigaba da dariya har sai da Junior ya farka daga bacci a firgice.
Ganin mahaifiyarsa na irin wannan dariyan sai abin ya bashi tsoro, dama tunda tace idan ya sake zuwa wajen Asiya zata bari macijinta ya sare shi yake matuƙar tsoronta.
***
Wannan ne karo na farko da zata je gidan Ubayd tunda yai aure. Ba zai kyautu taji Salma tayi ɓari har an mata wankin ciki sannan ta ƙi zuwa dubiya ba.
Tareda 'yanmatanta ta tafi wanda har a cikin mota sai da suka yi faɗa saboda kowa na son zaman window ƙarshe dai Jummai ce ta zauna a tsakiya bayan Asiya ta daka musu tsawa.
Sun samu Inna Yaha a wajen dan dama ita da Umma Hussaina suke karɓa karɓa wajen kwana da Salma a Asibiti kafin a sallamota.
Sun samu Salmar na barci dan haka basu jima ba suka fito. A dai-dai bakin ƙofa suka haɗu da Ubayd yana ɗauke da wasu manyan ledoji. Da ganinsa kaga magidanci dake cikin kwanciyar hankali, ta jima bata ga Ubayd ba amma duk da haka zata iya rantsewa cewa ya chanja sosai a yadda ta san shi da, yayi naman wuya, ga kumatunsa da suka cicciko suka yi ɓulɓul da su.
"Asiya"
"Ina wuni Ya Ubayd" Asiya ta faɗa tana ƙoƙarin tare wani abu daya taso mata daga ƙasan zuciyarta wanda ta san Shaiɗan ne ke ƙoƙarin kitsa mata wani abun daban a ranta.
Gashi dai tana auren Gwamna amma bata da ko kwatan kwanciyar hankalin da Salma ta samu a tattare da Ubayd.
"This was suppose to be my house" ta faÉ—a a zuciyarta dai dai ta matsa masa dan ya shigo falon. Ta bi bayansa da kallo lokacin da yake amsa gaisuwan Sumayya da Jummai.
Kafin yanzu, ta taɓa shigowa cikin gidansa lokacin ana kan aikin gini. Tsarin gidan gaba ɗaya ya tafi ne da ra'ayinta. Saboda tun daga planning Ubayd yake tambayarta wani irin gini za a yi? Mi za a sa mi za a cire? Daga ƙarshe gida ya zama na Salma.
"Har za ku tafi Asiya?"
"Mun daÉ—e da zuwa ai, akwai inda zamuje daga nan"
"Shikenan, mun gode. A gaishe min da Excellency Dan Allah"
Wani kallo Asiya ta masa wanda yasa shi fahimtar maganar da yai bai mata daÉ—i ba. Kafin yai wata maganar ta fice daga falon.
Gidansu Queen Bee da take son zuwa ma fasawa tayi saboda ranta babu daÉ—i.
Da suka je gida ɗaki ta shiga ta kulle ƙofa ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta.
Ita ne ya kamata tayi irin wannan chanjawar da Ya Ubayd yai, ita ne ya kamata tace "Excellency yace na isar masa da gaisuwa. Allah ya kawo wani rabo mai albarka"
Ta kalli fiskarta da kyau ta ga yadda idanuwanta suka yi wuri-wuri da su kaman an kama yaro a kitchen hannu nasha-nasha da miya da kuma naman daya ɗauka a tukunya da dare bayan koya yayi bacci. Fiskarta ya koɗe, hatta foundation data shafa bai iya ɓoye koɗewar da fiskarta yai ba. Rashin bacci ya haifar da ƙaton jaka mai tudu a ƙasan idanunta. Asiya ta cire mayafin dake kanta gashinta ya bayyana. Gashin yai buzu-buzu da shi irin yadda masu kinky hair ke tashi daga bacci idan sun kwana da tsefaffen kai babu hula ko ɗankwali.
Kenan wannan Ya Ubayd ya gani? Ta faÉ—a bayan ta gama nazartar fiskarta.
Dole ne ma yace ta gaida masa Excellency ai. Asiya-Shahidar da ya sani watanni takwas da suka wuce ba itace wannan ta jikin madubin ba. 'Yar gata 'yar ƙwalisa mai faran-faran da jama'a, wannan kuma fayau kamar fatalwan cikin film.
Minene aure idan babu kwanciyar hankali?
Minene aure idan za ayi dare har gari ya waye ba ka ji É—umin mijinka ba?
Minene aure idan mijinka ya zamo tamkar wata a sararin samaniya, sai dai ka kalleshi daga nesa amma ba zaka iya isa gareshi ba?.
Minene aure idan ba zaka iya kiran mijinka ka ji muryansa ba balle kuyi taÉ—i ko ku tsokani juna ayi wasa a dara?
"Anty Asiya. Anty Asiya"
Muryan Halima Kachallah ya dawo da Asiya daga tunanin da take.
"Anty Halima ke ce agidan namu?"
Asiya ta faɗa tana murmushi bayan ta buɗe mata ƙofa.
"Ba dole ba, yaushe rabonki da hawa online? Na tura miki saƙo sun fi arba'in amma ba ki duba ba"
"Yi haƙuri Antyna ni ɗin ce yanzu sai a hankali"
Bayan sun zauna Halima ta kalli Asiya tace "ni kam lafiyar ki kuwa? Ko dai za a yiwa Junior ƙani ne?"
Asiya Shahidah tayi murmushin yaƙe wanda sai da ƙwalla ya zubo mata a ido ɗaya.
Ina dai sai an taɓaka za ka samu ciki?
Tayi saurin shafe fiskarta da hannu biyu kafin Halima ta lura da hawayen daya zubo mata.
"Wani zance ne latest?" Asiya ta faÉ—a tana buga kafaÉ—ar Halima.
"Ina addu'ar da kika bani lokacin da zan tafi seminar É—in nan?"
"Uhm?"
"Akwai wani mentor É—inmu daya min magana"
"Alhamdulillah! Kice Anty Halima mun kusa cin shinkafa"
"Idan Hajiya ta bari ba"
"Miya faru?"
Halima ta sauke ajiyar zuciya sannan tace " Albino ne, na yiwa Hajiya maganar tace sam bata yarda ba. Inaga Anty Bilkisu ce ta zugata dan da farko ta min fatan alkhairi daga baya kuma tace wai ba ta yarda da haÉ—a zuri'a da Albino ba. Tell me Asiya su É—in ba mutane bane?"
"Sosai Halima. Suma mutane ne"
Sun jima suna taÉ—i kafin Halima ta tafi bayan Asiya tace ta cigaba da addu'a.
Tun lokacin kamfen suka ɗinke da Halima Kachallah, ƙaunar da babu tsakaninta da 'yar uwarta Bilkisu shine ya shiga tsakaninta da Asiya. A ɓangaren Asiya tausayin Halima take saboda a rayuwarmu ta yau ba abu ne mai sauƙi ba ga mace ta kai shekara talatin da biyar a gidansu babu aure. Dole ne ta fuskanci tsangwama da zunɗe a wajen mutane.
***
"Sadaka maganin musiba da bala'i, Sadaka yana kauda fitina, Sadaka yana kawo alkhairi" Jummai ta maimaita kalaman da taji a cikin mafarkinta. Bata fiye mafarki ba amma idan tayin kaso saba'in cikin ɗari yana zama gaskiya. Sati uku kafin rasuwar mahaifiyarta Delu sai da ta jera kwanaki uku tana mafarkin rasuwan. Da farko bata gayawa Delun ba sai da ta yi na biyu sannan ta sanar da ita. Dariya Delu tayi ta banzatar da zancen da cewa Aljanunta ke son ɗaga mata hankali, ita kam tana nan da ƙarfinta sai ta tsufa kamar Ayya ta ƙauyen mahaifinta wanda ake cewa sai da ta shekara ɗari da talatin kafin ta rasu.
A madaidaicin dinning set na falon Asiya Sumayya ce da Jummai ke faman karyawa. Masu aiki ne suka yi girkin hakan yasa aka jera abinci har kala uku a gabansu duk da kuwa Asiya ta hana almabazzaranci. Shayi da biredi, dankali da soyayyan ƙwai sai kuma pepper soup noodles wanda Sumayya ce ta shiga kitchen ta bada umurnin a dafa mata shi.
Ko ta ina toothpaste ya zo dinning É—in?.
Sumayya ta É—ago kai sai ta ga Jummai na matsa MaClean akan biredi, ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah. Jummai ta haÉ—e biredi ta fara turawa baki tana ci tana korawa da shayin dake gabanta.
Allah kaÉ—ai ya san inda Ale ya samo tsatson su Delu. Sumayya ta faÉ—a a ranta ganin 'yar uwartata har yanzu da ta shafe sati biyu a gidan bata fara nuna alamun zata waye ba.
"Dama da Maclean kike cin bread?"
Ta tambaya dai dai lokacin da Jummai ta sake matsawa akan sabon slize na bread data É—auka tana baza maclean É—in akan bread É—in da yatsarta manuniya.
"Yo kince na goge baki da shi. Alƙur'an zaƙi gareshi har da ƙanshin citta da yaji-yaji a ciki, shine nake cin biredi da shi, ai kema kina saka wani jan abu akan naki biredin wani lokaci"
" 'yar ƙauye, jam nake sawa ba toothpaste ba, jam Jummai." Tayi maganar da ƙarfi kaman zata bugeta.
"Ki mata a hankali mana 'yar Birni. Daɗin abinma dai dukkanmu daga ƙauyen muka fito"
Asiya ta faÉ—a tana zama a kujerar dake fuskantar Sumayya.
Ganin bowl ɗin dake gaban Sumayya da kuma sauran abincin dake kan table ɗin sai ta ƙwalawa Uwani kira, duk da chan ƙasan ranta bata son yi mata irin wannan kira saboda Uwani ta girmeta.
"Ranki shi daÉ—e an fito"
"Uwani ba nace kada a dinga girki ya wuce biyu a gidan nan ba sai dai idan da baƙi? "
"Na riga nayi wannan É—in kafin Sumayya tace zata ci indomie peppersoup shine na É—ibi peppersoup É—in da kika yi jiya na mata da shi"