← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 37

Sashe 2

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har yanzu da shekaru suka ja mata akwai sauran burbuÉ—in son Saifuddeen a ranta. Amma ya za tayi aikin gama ya gama...

***

Lokacin da Asiya ta shirya gidan Saifuddeen ta wuce saboda Uwani ta shaida mata Gwamna yana gidan amma yace baya son ganin kowa.

Ƙirjinta sai bubuk-bubuk yake lokacin da take haurawa matattakala. Ƙofar falonsa a kulle yake da key, ta fito da key ɗin data karɓa a wajen Uwani ta buɗe da shi.
Ta ja dogon numfashi sannan ta kutsa kai ciki ta wuce É—akinsa.
Yayi wanka ya chanja kaya zuwa T-shirt ruwan toka da wando ruwan ƙasa, yana zaune kan gado ya jingina bayansa da filo yana rubutu.

Ta ji daɗi da ta murɗa ƙofan ta ji ta buɗu. Suna haɗa ido ya sauke idonsa ya cigaba da rubutun da ya ke.
Duk wani ƙarfin gwiwar da take da shi sai da ya sace da ta ganshi, gashi nan kamar kullum fiskarsa wasai babu alamun yana cikin tashin hankali. Kamar ba shine Gwamnan da aka jefa ɗazu ba, kamar ba shine Gwamnan da ake shirin tsigewa ba.

"Kin zo ki duba ko zuciyata ta buga ko?" Yai maganar ba tareda ya É—ago ba.

Gwiwowinta biyu ta sa a ƙasa ta fara magana. " na san ba lallai ka yarda ba, amma wallahi ban san da abinda ake tuhumarka ba kenan, sai yau na gani, ba ni na rubuta ba. Ka yafe min"

ÆŠagowa yai ya dubeta yace
"A matsayina na Uba bana tunanin zan iya yafe miki nan kusa. A matsayina na Gwamna kuma zan barki ki cigaba da zama hajar Kamfen"

"Dan Allah ko zaka sake ni ka bari na wanke sunanka tukunna"

Dariya ya fara har sai da fararen haƙoransa suka bayyana.

"Waya gaya miki zan sake ki?"

"Kayi haƙuri"

"Haƙuri akan kin ci amanata?, ko haƙuri akan kina so ki tozarta 'yata a idon duniya, ko haƙuri akan da aurena kike mu'amala da Umaru Kwom ba tareda izina ba"

"Za ka iya yi min komai amma dan Allah ka bani dama na taimakeka"

Shiru yai na tsawon minti uku kafin yace " bana buƙatar taimakon ki, Allah ne shaidata kuma shi zai taimakeni"

Ta zauna kusan minti goma amma bai sake magana ba, hakan yasa ta miƙe ta fice daga ɗakin. Tana isowa falo ta haɗu da Bilkisu.

"Mi ya kawoki?"

Asiya tayi shiru, Bilkisu ta ja tsaki ta mangajeta ta wuce É—akin Saifuddeen.

***

Wasu samari guda biyu ke zaune a majalisa suna jira sauran abokansu su ƙariso.

"Wannan lamari akwai É—aure kai, gaskiya ban yarda Gwamna SSK zai iya cin zarafin mace ba" mai farin jumfa yai magana yana cigaba da latsa waya.

"Kai kabar ustazai masu gemun nan, yawancinsu ustazancinsu a baki ne"

"Kaiiii! banda Prof S Kachallah, ya koyar damu Shekaru goma da suka wuce, a lokacin mata ke binsa yake gudunsu. In fact, lokacin da muke school in za a kira malaman da basa neman mata to Prof S Kachallah za a fara kira"

"Tunda kace haka na yarda"

"Lami Ninja fa karuwace, ance a Lagos wani ƙaton gidan karuwai take da shi, shine za'a yarda da magananta"

"To Allah ya fitar da shi"...

***

Lokacin da Asiya ta koma gida numbar MD na Hill TV ta kira, fili take son siya wanda za a rinƙa ɗaura wani shirin da take son farawa gobe. Suna gama waya da shi ta kira CY. Satin CY ɗaya da shigowa ƙasar.

"CY akwai aikin da zaka min"

"An gama your Excellency"

Bayan ta gama waya da CY ta zauna ta kunna laptop ɗinta ta fara rubutu. Fou'ad Salisu ya ce mata Lami Ninja ta taɓa aure, shekara biyu ta rabu da mijin ta koma Lagos da zama sannan kuma ita ce ke da Sunlight Club a Lagos.

"Idan har alƙalamin ɗan jarida na iya kawo fitina to lallai ko zai iya kawo gyara. Lami Ninja ko Lami Spider kike, sai kin ƙwammace baki biyewa Umaru Kwom ba"

Asiya ta furta a fili...

2

*Ilimi, nitsuwa, tausayi, jajircewa, kawaici, kwarjini.KaÉ—an kenan daga halayen Prof Saifuddeen Kachallah lokacin da yake koyarwa. #SSK is innocent*

*babu salihin malami a Jami'ar Congo sama da Prof S S Kachallah. #the Gov is innocent*

*i've never seen a gentleman like him. #Our Gov is innocent*

Bilkisu Kachallah ta cigaba da karanta tweets na mutane da ke supporting Gwamna. Wasu ma sun faÉ—i yadda Gwamna ya biya musu kuÉ—in Makaranta lokacin da yake koyarwa.

"This is good ai, mutane na bayanka Saifuddeen"
Ta yi magana tana ajiye wayar a kusa da dressing mirror, ta gyara ɗaurin ɗankwalinta da kyau sannan ta ɗau gyale ta saƙala a kafaɗa, a karo na biyu ta ɗau janbaki ta sake gogawa a leɓenta. Ta saka waya a jaka ta ɗau jakar ta fice daga ɗakin.

Asiya na zaune akan kujera ta ƙurawa TVn ɗakinta ido. Lokaci zuwa lokaci tana duba agogon wayanta, jira take ƙarfe tara da rabi ya cika a sako shirin da ta ɗau nauyi. CY ya gaya mata cewa ya yi hira da mutane takwas kuma duka za a saka su a shirin. Tun jiya da dare take ganin tweets na mutane suna bayyana kyawawan halayen Gwamna lokacin yana koyarwa.

Ƙofarta da aka fara bugawa da ƙarfi ba kakkautawa yasa ta miƙewa da sauri tana faɗin lafiya? .

ÆŠaya daga cikin ma'aikatan gidan ne tana tsaye jikinta na rawa

"Madam, your brother"

"What happened?"

"He has run mad"

Har ta fito daga ɗaki sai kuma ta koma ciki da sauri ta buɗe closet tana neman hijabi. Ta jawo wani skirt tana ƙoƙarin sakawa kafin ta ankara cewa ba hijabi bane. Ta jefar da skirt ɗin ta ɗauko hijab ta saka ta fice waje. Tunanin Asiya ɗaya, Allah yasa ba wani Yaya Bello ya shaƙe ba, dan Yaya Bello idan ya sha abubuwansa baya gaya masa dai dai. Ba zata taɓa mantawa da lokacin da ya kusa sanadiyar bugawar zuciyar Ale ba.

Ma'aikata da security sun yi cirko-cirko, wasu kuma na ƙoƙarin taro Yaya Bello da ke saman mota.
Bilkisu Kachallah na wajen ta taɓe baki tana ganin drama. Babban mutum daya kusa cika shekaru arba'in shine ya ke a tuɓe daga shi sai wando three quarter yana tiƙan rawa a saman motan Bilkisu Kachallah.

"Miya faru?" Asiya ta tambaya tana kallon Hansa'u dake gefen Bilkisu Kachallah.

"kawai na fito raka Hajjajuna bakin mota sai muka ga ya zo da gudu ya hau saman motan yana tiƙan rawa wai shine wannan afton nan Krish"

Bilkisu Kachallah ta juyo ta kalli Asiya tace " ƙusumbi, kurmanta, hauka, what else kuke da shi a zuri'arku?"

Asiya ta kalleta cike da takaici tace "babu wanda yafi ƙarfin jarrabawar Ubangiji"

"Hansa'u kai min jakata É—aya motar, wannan da mahaukacin ya hau ta riga ta zama condemn"

Hansa'u ta kalli Bilkisu sannan ta kalli Yaya Bello da wani security ya damƙo ƙafarshi ya jawoshi da ƙarfi har ya faɗo ƙasa, tim. Illar irin miyagun ƙwayoyin da suke shigowa da shi kenan. Shiyasa ranan data kama Nana da Zunnairah suna shan syrup bata gayawa kowa ba, saboda ta yarda cewa abinda Bilkisu ta shuka ne take girba.
Ta wuce gefe tana faÉ—in "Allah ka bashi lafiya alfarmar Annabin tsira"

Bilkisu ta bi bayanta tana murmushi. Sai da aka samu aka ɗaure Yaya Bello, sannan Asiya ta samu bayani akan ainihin abinda ya faru. Wai basu san miyasha ba, mai gyaran flowers bai iso ba sai ya ɗau kayan aiki ya je wai zai gyara flowers, ashe zuwa yai yana ta sare flowers ɗin yana tuɓɓuke jijiyoyinsu. Da aka zo aka hanashi sai yace zai je yai wanka, basu sake ganinsa ba sai da Bilkisu Kachallah ta fito zata shiga mota suka ga ya taho da gudu da shovel a hannunsa ya hau saman motar ya fara tiƙar rawa.

Asiya ta kame kai tana salati, yanzu kowa a gidan ya san Yaya Bello na shaye-shaye. Ga damuwar abinda ya faru da Gwamna da ta sa kanta ciki tana fama da shi, ga kuma Yaya Bello anan yana so ya ƙara mata ciwon kai.

Sai da ta ga an wuce da shi Quarters na ma'aikata kafin ta juyo ta kalli wani matashi da take ganin yana da matsayi a cikin security É—in, ta masa kashedi akan idan har ta ga video na abinda ya faru a media sai ta sa an hukuntasu.

Lokacin data shiga gida saura minti biyar a kammala shirin da take biÉ—a. Mutum É—aya ta gani da yai bayani akan kirkin Gwamna lokacin da ya koyar da su.

Ana ƙare shirin ta kira CY tace ya turo mata da interview ɗin ta gani. Tana magana da CY kiran Fou'ad Salisu ya shigo.
"Hello akwai labari?"

"Na samu labarin inda tsohon mijin Lami Ninja yake"

"Ka mishi magana?"

"Yana buƙatan kuɗi"

"Kanbuuu! Gaskiyar da zai faÉ—a ma sai an biyashi"

"Mutane kenan"

"Ok nawa yake buƙata?"

"Miliyan biyar amma ya bari a miliyan biyu"

"He's crazy, manta da shi Fou'ad"...

***

"Ina so a rufe case É—in nan kafin ayi primary election. Na san kanada hanyar da zaka yiwa House magana su bi umurninka, ina so maganar Lami Ninja ya zama tarihi daga gobe Monday"

"kasancewar Lami Ninja ta shigar da ƙara kotu ne, inaga sai kotu ta wanke Gwamna kafin House suyi wani abu akai. Akwai wanda zai binciko sirrinkan Lami Ninja nanda kwana uku, za'a iya amfani da haka wajen kashe maganar"

Bayan tafiyar Kachallah. Yallaɓai ya shiga shafa gemu yana murmushi. Lallai Saifuddeen Kachallah ɗan gata ne...
Chapter 2 · 0% Book details