Sashe 16
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da dare Bayan Isha Ubayd ya zo dubiya. Ganinsa da Asiya tayi ya tuno mata da wasiyyar Umma. Shikenan ta rasa Ubayd har abada kenan?
Shima Ubayd É—in a daddafe ya gaisheta ya fita, tsoron kasancewa da ita yake saboda abubuwan da zuciyarsa ke ayyana masa. Asiya Shahidah ce first love É—insa, kuma har yanzu daya amince zai auri Salma bai ji ko kaÉ—an wani abu ya ragu na soyayyar da yake mata ba, sai dai kawai zai cigaba da danne zuciyarsa har lokacin da Allah zai yaye masa soyayyarta gaba É—aya, duk da kuwa hakan ba lallai ya faru nan kusa ba.
CY ne ya zo na ƙarshe kafin Asiya ta yi bacci. Ya zo da yamma ya samu ƙofar ɗakin cike da mutane sai ya juya bai ƙariso ba.
Yana sane cewa zuwansa dubiyan zai iya zama wani abu amma bai damu ba saboda zuciyarsa ba za ta taɓa samun sukuni ba har sai ya ganta. Tunda aka nunota kwance akan gadon Asibiti ya ji tsananin tausayinta ya kamashi. Ita ɗin wata ɓangare na zuciyarsa ne da ba zai iya yakicewa ba.
"CY the CY, mi ka kawo min ne?"
CY ya miƙa mata ɗan ƙaramin box ɗin daya shigo da shi. Asiya ta karɓi box ɗin hannunta ya shafi hannun CY. Duk da hannun na roba ne hakan bai hana CY jin wani abu ya ratsa jikinsa ba.
Asiya ta buÉ—e box É—in cike da farinciki.
"Chocolate?. Shine ka kawo guda ɗaya, marowaci kawai" ta cire chocolate ɗin ta ɓare ta fara ci
"Allah ya shiryeka CY, harda wani yin karama ka saka a box kamar abin kirki"
CY yai murmushi itama Asiyar murmushi tayi sannan ta cigaba da cin chocolate É—in.
Sallamar Abba ya saka CY da Asiya É—agowa suka dubi Abba da yake bin Asiya da wani irin kallo.
CY ya gaishe shi sannan yai wa Asiya sallama ya tafi. Su biyu ne a ɗakin saboda shigowar CY ɗakin yayi dai-dai da ficewar Sumayya data je kiran nurse da zata zo ta cirewa Asiya ruwan da aka ɗaura mata saboda ya kusa ƙarewa.
Abba yace "Asiya!" sai yai shiru saboda Sumayya data shigo tareda wata nurse.
Bayan an cire ruwan Abba yai musu sallama ya tafi.
Asiya ta san akwai magana a bakin Abba kuma koma minene abu ne da ba zai mata daÉ—i ba saboda yanayin fiskarsa tunda ya shigo babu walwala a tattare da shi.
Ƙarfe shaɗaya da rabi na dare Sumayya na kwance a kan ƙaramin katifa a ƙasa tasa earpiece a kunne tana kallo aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. Ba ta ji da farko ba sai a na uku ta miƙe ta kunna wutan ɗakin sannan ta je ta buɗe ƙofa, ganin Gwamna tsaye a bakin ƙofa tayi saurin matsawa gefe tana faɗin "sannu da zuwa"
"Ya mai jiki?" ya tambaya lokacin daya shigo É—akin.
Ta amsa "da sauƙi ance ma gobe za a sallameta".
"Ta yi bacci ne?"
"Tun É—azu" Sumayya ta faÉ—a tana komawa gefe.
Gwamna ya matsa kusa da gadon Asiya ya zuba mata manyan idanunsa. Bacci take hankalinta kwance dan har hulan kanta ya zame gefe.
Murmushi Gwamna yai ganin wani baƙi-baƙin abu a gefen bakin Asiya. Hannu ya kai zai goge mata, Asiya ta ɗan juya gefe ta kwantar da fiskarta akan hannunta.
Maimakon ya sa hannu a wajen sai ya sa hannu a kanta ya fara shafa lallausan gashinta, ya warware bun ɗin da tayi saboda ya ga tsayin gashin. Ya kai hancinsa yana shinshinar gashin wanda ke ƙanshin coconut da jasmine oil.
Ya kai bakinsa ya sumbaci gashinta, goshinta da kuma saman hancinta. Ya kai harshensa ya lashe baƙin abinda ya gani wanda yake tunanin ragowar abinda ta ci ne. Ɗan zaƙin daya ratsa harshensa ya tabbatar masa da chocolate ne. Ya kissing lips ɗinta a hankali sannan ya miƙe sai ya ji tace "i love you Asya, mtsww... munafuki, what did he think of himself mtsww ... Sumy kina jina ko?..." ta yi maganar tana nuna yatsa, sai kuma ta juya ɗaya gefen ta cigaba da bacci.
Gwamna yai murmushi, Junior da Nana ne masu magana cikin bacci. Bai san manya ma suna iya magana cikin bacci ba sai yanzu. Ya ji daÉ—i daya fahimci abinda ke ranta shine sirrin daya bayyana mata jiya.
Yai wa Sumayya sai da safe sannan ya fita. Bayan tafiyarsa Sumayya ta fito da dariyar da take ta gimtsewa tuntuni...
Washegari da safe Sumayya ta shiga tsokanar Asiya akan jiya Gwamna yazo ta faÉ—a masa tana son shi cikin bacci.
"Sumy bana son maganar banza"
"Inada shaidah fa Anty"
"Maƙaryaciya"
Sumayya ta fito da wayarta ta nuna mata hoton da ta yi musu jiya dai dai lokacin da Gwamna ya kissing goshinta da kuma lips É—inta. Asiya ta zaro ido tana faÉ—in "na shiga uku. Sumy hoton nan gaskiya ne kuwa?"
Sumayya ta haÉ—e rai tace " ke da bakinki kika ce masa i love you, please kiss me. Shi kuwa yai kissing É—inki"
"Zan ci ƙaniyarki Sumayya"
"Ni ƙarshe dana ga kin kanainayeshi ma bar muku ɗakin na yi"
Asiya ta yi saurin É—aura yatsarta a baki tana tantamar maganar Sumayya.
Ta sani tana da magagin bacci musamman lokacin da take yarinya, dan har cewa ake tana taÉ—i har ma tayi faÉ—a cikin baccinta. Amma anya za ta iya faÉ—in abinda Sumayya tace ta faÉ—a? Wani dalilin ne zai sa ma ta faÉ—i haka? "Kai Nooo!" Ta furta a fili tana goge bakinta da bayan hannunta da babu canula. Sumayya ta fashe da dariya.
Duk yadda ta nace akan Sumayya ta faɗa mata gaskiyar abinda ta faɗa cikin bacci ƙi tayi, sai maimaita mata maganarta na farko ta ke yi. Hakan ya sa wani ɓangare na zuciyarta ya fara yarda da maganar yayinda ɗaya ɓangaren yake ƙaryata haka. Ko a mafarki Allah ya sawwaƙa ta cewa Saifuddeen I love you balle har ta roƙe shi ya kissing ɗinta.
Ƙarfe shabiyu na rana aka sallameta. Ba su san ya akayi 'yan jarida suka san da sallamar ba. Suna fitowa daga cikin Asibitin 'yan jarida suka musu chaa suna neman ƙarin bayanin sace ta da aka yi da kuma jinyarta, ko kidnappers ɗin sun mata wani abu?, sannan su wa ta ke zargi da wannan aikin?.
Idan ba ta yi magana ba matsala ne, idan tayi ma matsala ne, dan ko mi ta faÉ—a ma sai an fassara shi zuwa wani abun daban. Shirun dai shi yafi dacewa tayi.
Yaya Bello da Habibu ne suka sata a tsakiyarsu suka ratsa 'yan jarida suka wuce da ita har wajen mota...
***
Asiya ba ta samu zama da Abba ba sai dare bayan sallar Isha.
"Ya jikin naki?"
"Da sauƙi Abba"
"Alhamdulillah"
Shiru ne ya biyo bayan abinda ya faÉ—a. Sai chan kuma ya É—ago maganar rabon gadon Umma da za ayi.
Miyasa da wurwuri haka? Miyasa kayan Umma zai kasance na magada? "Mutuwa" zuciyar Asiya ya bata amsa.
"Ban ji daɗin yadda na sameki da wannan yaron ba. Asiya ki riƙe aurenki da daraja dan Allah"
"Abba gaisheni fa ya zo yi"
"Shine kike mishi tarban da ba kya yiwa mijin ki?"
Asiya ta É—ago da sauri ta kalli Abba cike da rashin fahimta.
"Ban san mi kuka tattauna ba amma na wuce naji kina É—agawa mijinki murya. Kina ganin hakan ya dace Shahidah?"
"Allah ya gafarta wa Ummanki, har na koma ga Allah addu'a zan dinga yi mata, saboda ita É—in macen da ta dace da a kira da suna mar'atul saliha ce.
Mahaifinki da ya zo ta'aziyya a nan ya zauna yana zubda hawaye yana bayyana mini kyawawan halayenta a iya zaman da suka yi. A lokacin tanada ƙarancin shekaru ma kenan.
Asiya ba ki ɗauki aurenki da mahimmanci ba, ba ki ɗauki mijinki da daraja ba. Idan har saboda mun raba ki da Ubaydullah ne kika yi watsi da aurenki to ki sani abinda kike ba abinda zai haifar miki sai baƙin ciki. Ban ji daɗi ba Asiya. Shikenan ba zaki saki ranki ki rungumi aurenki a matsayin ibada ba"
"Abba shine bai É—aukeni da daraja ba. He's using me for his campaign"
"Sai me?"
"Abba!"
"Sai me idan yayi amfani dake wajen kamfen É—insa, ba mijin ki bane?"
Asiya ta saka hannu ta fara goge hawayenta. Ita kam akan Gwamna Abba kamar baya sonta.
Sauran nasihar Abba ma dai Asiya ba ji tayi ba, dan rabi kuka rabi saƙe-saƙe ta ke yi a zuciyarta.
A rana ta uku da dawowarta sai ga Mahirah da Junior sun zo gaisheta. Lokacin da take Asibiti Hajia Umma da wasu 'yan tsiraru cikin 'yan uwan Gwamna sun zo sun gaisheta.
Sai yau ne Asiya ta zauna da Mahirah saboda duk zaman da tayi a gidan Gwamna Mahira tana Kachallah house. Yarinyar kam ba laifi akwai hankali ba kamar Nana ba. Maganarta sanyi, kominta a sanyaye.
Ta yi tunanin Bilkisu Kachallah ce ta turosu amma ga mamakinta sai Mahira tace mata Gwamna ne ya ce su zo su gaisheta.
Junior ya sake jiki da su Ali da Gwani suka tafi da shi yawo.
"Ya jikin Nana?" Asiya ta tambaya ganin shirun yayi yawa dan Mahira bata da yawar magana kamar 'yar uwarta.
"Da sauƙi"
"Har yanzu ba a dawo da ita gida ba?"
"Sun ce sai ta cika wata shida a wajen"
"Amma kuna zuwa dubata ko?"
"E muna zuwa duk weekend"
Asiya tana ƙoƙarin updating wayarta saboda lokacin da aka bata wayar kafin a sakota sun share kusan komai na kan wayar.
"Anty Shahidah dan Allah ki kula da Daddy, wallahi bashida lafiya"
Asiya ta kalleta da mamaki.
Kanta a ƙasa ta cigaba da bayani "tunda aka ɗauke ki bashida lafiya. Akwai ranan da ya zo gaishe da Dadda da zai tafi sai kawai gani muka yi ya faɗi. Ya cewa Dadda kar ta faɗawa kowa, kuma har yanzu ya ƙi yaje a duba shi. He was busy, Mommy ma kuma kamfen ne a gabanta yanzu"
"Miyasa kike gaya min wannan?"
"Because...because you are a good person"
Asiya ta kauda kanta kamar bata damu da abinda Mahira ta faÉ—a ba.