← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 37

Sashe 33

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya ta kalli Sumayya sannan ta kalli Uwani ta ce "banda Man shanu babu abinda Sumayya bata ci, daga yau idan kin yi girki kada ki sake karɓan order daga wajen ta. Idan tana son cin wani abu ta gaya miki kafin ki fara girki, idan ba zata iya cin abin da aka girka ba ta haƙura da cin abincin"

Sumayya ta tura bowl ɗin gabanta gefe tana tura baki ta miƙe zata bar wajen Asiya ta daka mata tsawa "zauna!"

Bayan Uwani ta bar wajen Asiya ta kalli Sumayya rai a ɓace tace "dan kina zaune a gidan nan ba zaki dinga min iskancin da kika ga dama kuma na zuba miki ido ba. Ko ni da nake matar gidan kin ga ina wannan almabazzaranccin? Bana son rashin godiyar Allah Sumayya"

"Ni dai kawai kice kin gaji dani a gidan nan. Dan nace kawai a dafa min indomie shine sai kin min gori"

"Ungo naki dake da indomie. Uwani sa'ar ki ce da zaki shiga kitchen kina bata umurni? Ko kuma munyi da ke zata dinga yi miki bauta?"

Ta kalli Jummai dake zazzare ido tace "idan na sake gani kin sha Maclean sai na sa Yaya Bello ya zubar miki da haƙora. Tukunna ma kin aske hammatarki?"

Jummai ta maƙe kafaɗa tana wiki-wiki da ido. Tun kwananta uku a gidan da Asiya ta lura da hammatarta ta bata shaving stick ta mata bayanin yadda zata yi amfani da shi.

"Kin aske?"

"Kwaranƙwasi tsoron askar nake, ji nake zata kwashe min fatar hammata"

Takaici yasa Asiya ta hangame baki, chan ta girgiza kai tace " idan kin gama cin abinci ki sameni a É—aki"

"Now, ku saurareni da kyau domin sau ɗaya zan faɗa ba zan maimaita ba. Daga yau babu mai aiki da zata sake gyara muku ɗaki, ku dinga karɓa-karɓa kuna gyarawa tsakaninku, sannan na yiwa Queen Bee magana zaku fara aiki a salon ɗinmu. Ke Jummai tunda kin iya kitso zaki dinga yi a chan, idan kin fita da safe sai ƙarfe uku ki dawo ki wuce Islamiyya. Idan za a shiga sabon term sai na saki a makaranta"
Ta maida dubanta ga Sumayya tace "inada timetable na classes naki dan haka bana son ƙarya. Duk lokacin da baki da lectures ki wuce Halal Salon kije su koya miki aiki idan anyi hutu kuma ɗinki zaki fara koya"

"Anty Asiya É—inki kuma?"

"Yes É—inki"

Har aka ƙare cin abinci babu wanda ya sake magana. Sumayya ce ta fara miƙewa ta bar wajen dan dama abincin ya riga ya fita a kanta tunda Asiya ta dizgata a gaban Uwani, ta ƙarisa ci ne kawai saboda Asiya tana wajen.

Sumayya na kwance kan gado Asiya ta shigo É—akin hannunta É—auke da sabon shaving stick.

"Ina Jummai?"

Sumayya tayi banza da ita kaman bata jita ba

"Ba tambaya nake miki ba?"

"Bata shigo ba"

Asiya ta ja tsaki ta fice daga É—akin.
A falo ta samu Jummai ta zauna gaban TV tana kallo. Zuwa tayi ta kashe TVn sannan tace "muje" babu musu Jummai ta bita jiki a sanyaye dan har ga Allah tsoron shaving stick É—in take.
Lokacin da suka shiga banɗaki kallo ɗaya Asiya ta yiwa gashin daya cika hammatar Jummai tana mamakin yawansa, kaman cikin sati biyu data yi dasu ya ƙara cika, gashin kaman an cukwuikwuye baƙar leda an manna a wajen, idan ta sauke hammatar kana iya ganin gashin ya firfito har ta gefe gefe.
Allah ne masani, amma tana tunanin a tarihin rayuwar Jummai bata taɓa cire gashin hammatarta ba. Ba tareda ƙyanƙyami ba ta aske mata gashin tas sannan ta ce ɗauko shaving cream a banɗakin ta matsa tace ta ɗaga mata rigarta. Bata amfani da shaving stick a ƙasanta saboda yana sa mata ƙuraje.

"Wayyo na shiga uku! Adda Shahida mi zaki sa min a..."

"Ungo naki" Asiya ta mata daƙuwa.

Bayan ta gama gyara mata wajen ta barta a banɗakin akan tayi wanka. Still sai da Jumman tayi ƙunƙuni wai ai tayi wanka da sassafe. Lokacin da Asiya ta fito waya Sumayya take, yadda take murya ƙasa-ƙasa babu tantama da namiji take magana. Asiya ta girgiza kai ta fice daga ɗakin, ita yanzu fargabanta ma Jummai ce kar zamanta da Sumayya ya sa ta kwaikwayi halinta, ga ita nan ko shekara shabiyar bata kai ba. Allah dai ya bata ikon kula da amanar su Amin, da wannan ta shige ɗakinta.

Da yamma lis Asiya ta kira Jummai akan ta mata kitso. Yadda gashin baya samun gyara gara kawai ta kitsa shi ta huta.
Da aka fara kitson ne kuma Jummai ta faÉ—a mata mafarkin da ta yi jiya da dare tareda cewa shi mahaukacin data gani yace Asiya tayi sadakan kaji.

"Ba sadakan kaji ba sadakan giwaye zan yi"

"Allah mahaukacin cewa yai kiyi sadaka har waƙa ya dinga yi yana cewa..." ta karkata baki zata rera waƙa Asiya ta katseta

"Kar ki yadda ki kawo min zancen Aljanunki na ƙarya dan duka zaki sha a wajena"

Duk da Jummai ta sa wasa a abinda ta faɗa amma tabbas mahaukacin data gani yace tayi sadaka amma bai faɗi da minene ba ita ce ta ƙara nata gishirin.

"Adda Shahidah Wallahi yace ayi sadaka amma nina ce ayi da kaji tunda kullum sai an yanka a gidan nan"

"Jummai ƙarisa min kitson nan inada abin yi"

Jummai tayi shiru da maganar amma gaskiya mafarkin ya tsaya mata a rai.
Da farko ma bata yi niyyar faÉ—awa Asiya ba amma baccin da ta yi da rana sai ta sake wannan mafarki sai dai wannan karan ba a ce ayi sadaka ba sai dai yadda aka sakawa Asiya ankwa aka shigar da ita gidan yari a mafarkinta na jiya haka ta sake gani a mafarkin da ta yi da rana. Koma minene gaskiya tana fata babu wanda zai zo ya kai Adda Shahidarta gidan yari...

22

Matar dake gaban wani ƙaramin maciji mesa ta ajiye wata ƙaramar ƙwarya a gabansa, mesar wanda yake baƙi ƙirin da shi ya kafa kai ya shanye ruwan nonon da ke cikin ƙwaryan tas. Ance sai ta yi kwana ashirin da ɗaya tana bashi ruwan nono kafin ta fara bashi irin abincin daya dace da halittar shi. Ta shafa kan mesar a hankali tace "well done baby"

***

Plan na yadda komai zai kasance ranan inauguration tun daga safe har dare Bilkisu Kachallah ta nunawa mahaifinta. Sai dai ransa ya matuƙar sosu da abinda ya gani. Na farko ba a jima da yi musu rasuwa ba, sannan idan har aka yi yadda Bilkisu ta tsara to duniya zata zage su da yin almabazzaranci ba zai so Saifuddeen ya buɗe tenure ɗinsa da irin wannan ɓarnar kuɗin ba.

"Bilkisu ya kamata ki adjusting event É—in nan, mutane za su yi magana"

"I don't care, abinda na ke so kenan kuma shi za a yi"

Kamar wanda aka ɗaure harshensa haka ya haɗiye duk wani ƙorafin daya taso daga cikinsa bai iya furta mata komai ba sai gyaɗa kai kawai da yai.

Daga wajen mahaifinta gidan Yallaɓai ta wuce domin ya aiko mata da saƙo akan yana son ganinta.

"Ban gane na dakatar da abinda nayi niyya ba. This is what i want and nobody can change that"
Bilkisu ta faɗa a fusace, cikin 'yan kwanakin nan Yallaɓai yana mata taurin kai kafin ya amince da buƙatarta sai ya kawo ƙorafi wanda Saifuddeen da mahaifinta basa iya yi. Anya kuwa Yallaɓai ya zauna haka?

"Tura matar Gwamna kurkuku ba abunda zai kawo sai rikici da tashin hankali. Nothing good will come out of this"

"Babu rikici a cikin wannan lamari sai É—aukaka. Idan Gwamna ya tura matarsa kurkuku zai amsa sunan adali, duk wani abu da zai yi musu na zalunci the fools will still praise him"

"Ba zan bari ki aikata wannan ba, ba zan bari ba. You will ruin him"

Ƙirjin Bilkisu ya buga da ƙarfi saboda jin kalaman Yallaɓai, anya kuwa zoben hannunta na tasiri a kansa?

Ta dai san babu wani doka data taka cikin dokokin da aka bata to mi yasa haka?
Ta dai ƙara gwada sa'arta dan ta tabbatar Yallaɓai bai kufce daga ɗairinta ba, idan ya kufce ta nemi abin yi kafin ya ɓata mata shiri.

"Yallaɓai ina so ka sanar da su su zo su binciki matar Gwamnan Congo Asiya Kachallah sati ɗaya bayan inauguration. She will go to jail Yallaɓai"

Yallaɓai yai shiru yana ƙoƙarin yaƙar zuciyarsa daga faɗawa tarkon Bilkisu amma ya kasa. Tun da ya ankara da cewa ya fara bin umurnin Bilkisu Kachallah ya shiga neman mafita sai dai babban malaminsa baya ƙasar kuma shi ɗin ne ya tabbatar masa da zarginsa cewa Bilkisu ce ta ɗaure shi sai dai wanda yai wannan aiki ba ƙaramin babban malamin tsubbu bane dan a tunaninsa idan ba a je an ciro abinda aka jefa cikin teku ba da wuya ya samu mafita.

Bai iya sarrafa kansa ba dan ji yake idan bai aikata abinda Bilkisu ta ce ba mutuwa zai yi.
Daga ƙarshe dai wayar tasa ya ɗauko ya danna wasu lambobi ya ƙara a kunnensa.

***

Tun saura kwana biyu ayi bikin rantsarwa, manya manyan hotels da gidajen sauƙe baƙi suka fara cika. Baƙi ne ke ta shigowa cikin jahar Congo daga kowanni lungu da saƙo na ƙasar dama ƙasashen ketare. Duk wani artist da ke ji da kansa ya samu halartar wannan biki domin Bilkisu Kachallah ta shirya girgiza kowa da shirin da ta yi.
Chapter 33 · 0% Book details