Sashe 25
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin ta dage da danne masa baki dan kada yai magana hakan yasa ya fara mata cakulkuli, nan da nan ta sake mai baki tana ƙoƙarin riƙe hannunsa tareda faɗin ya dena, bai denan ba kuwa har sai da ta birkice tana dariya sosai tama manta cewa dare suke. Tuni ya samu daman haɗe bakinsu ya shiga kissing ɗinta passionately. Jikinta ya riga yayi laƙwas dan haka ta kwanta shiru tana karɓan zazzafan saƙo daga Gwamna. A hankali kuma ba tareda ta shirya ba ta shiga maida masa da martani tana kwaikwayon yadda yake mata. Sun jima suna kissing junansu, sun manta da duniyar da suke ciki dama wani damuwar dake cikinta, sun manta ƙiyayya ko soyayya domin all that matters a lokacin shine wannan kiss ɗin, wanda shaƙar numfashine kaɗai ke raba bakunan su. Kusan minti takwas suka ɗauka a haka kafin Asiya ta yi saurin juyar da kai gefe tana fitar da numfashi da sauri sauri saboda hankalinta ya fara dawowa jikinta.
Ganin haka yasa Gwamna ya janye jikinsa yana faÉ—in "sai da safe"
Dukkansu sun tsinci kansu cikin wani sabon yanayi. Gwamna ya shiga jin wani matsananciyar buƙatarta, ya dinga sauke ajiyar zuciya yana ƙoƙarin saito nitsuwarsa, ƙarshe ya miƙe ya shige banɗaki ya sakewa kansa ruwan sanyi.
Sai da ya shige banɗaki Asiya ta samu damar motsawa, ta mirgina gefenta ta lulluɓe duk jikinta da duvet sannan ta sa yatsu uku ta danne lips ɗinta tana ajiyar zuciya akai akai. Ba zata iya fassara yanayin da ta shiga ba, duk da tana jin kunyarsa amma yadda jikinta da ruhinta ya amsa wannan saƙo, ji take kamar ta miƙe ta bishi banɗaki ta haɗe bakinsu su dawwama a wannan yanayi har abada. Haushin kanta ma ta fara ji data katse wannan daɗin, at least da ta bari sun ƙara koda minti ɗaya ne, kai koda sakan talatin ne. Zuciyarta ya shiga ƙiyasta mata abubuwa dayawa har Gwamna ya dawo ya kwanta. Deep down tana fata ya sake yi mata chakulkuli, ya sake kissing ɗinta ya sake faɗin "i didn't know you are a good kisser" wanda sai yanzu ta tuno in between kissing ɗinne ya faɗi hakan. Ko mi itama ta faɗa masa cikin yanayin nan oho. Haka ta dinga tariyo komai a zuciyarta, tun daga cin abinsu tare zuwa kwanciyar da ta yi, zuwa shima shigowar sa ɗaki, wanka da yai da kuma kwanciya da yai yana mata addu'ar Allah ya tashe su lafiya bayan tace masa sai da safe, zuwa tusar da ta yi, chakulkuli and then...kiss.
Washegari ita ta fara tashi ta bar É—akin da wurwuri tun kafin ma alarm É—inta ya buga dan ba wani baccin kirki ta yi ba.
***
Ƙarfe biyu da rabi ta isa gidansu. Gidan ya cika da 'yan biki, ana ganinta aka shiga ihu ana mata kirari. Inna Yaha ta shiga nan nan da ita, yadda Asiya take bata girma bayan ta san irin zaman da suka yi da Ummanta, hakan yasa ta ke jin kunyan abubuwan da ta aikata a baya. Yarinyar da ta ke wa gori da Agola itace ta ke da matsayin da ya ɗaukaka darajan gidansu a anguwa. Gidansu ya koma abun kwatance. Sai dai ka ji ana cewa Muna layin gidan su matar Gwamna. Gidanmu na daura da gidansu matar Gwamna. Gidan da zanje da ka wuce layinsu matar Gwamna kaɗan sai ga layinmu. Wasu masu abin hawar ma kana cewa gidansu Asiya Kachallah to a ƙofar gidan Abba za a saukeka.
Asiya ta halarci walimar Amarya amma bata jima a wajen ba. Haka kawai kuma data ga Amarya sai ta ji zuciyarta yayi sanyi. Ta sani Salma na son Ubayd kuma zata kula da shi. Nan da lokaci kaɗan tsakaninsu zai daidaita, Ubayd zai manta da cewa sun taɓa soyayya.
Asiya bata koma gida ba sai ƙarfe tara na dare. Ba ita ke da kwana ba shiyasa kawai ta wuce ɗakinta ta murɗa key ta kwanta bayan tayi wanka.
Sumayya bata nan anyi hutun zaɓe ta koma gida. Koda tana nan ma tsakaninsu har yanzu basu daidaita ba. Suna dai magana kam, amma babu wannan walwala kamar da, ko ɗakin Sumayya bata shiga sai da dalili itama kuma Sumayyar hakane.
Yanzu a gidan Junior ne ya maye mata gurbin Sumayya domin indai yana gidan to yana maƙale da ita, wannan nema yasa ta jajirce wajen koya masa karatu na addini saboda ta nan ne yake da naƙasu. Malamin dake zuwa koyar da shi ba kullum yake zuwa ba, kuma kaman yana koyarwar ne da tsoro tunda baya iya tsawatar masa saboda Bilkisu Kachallah ta gindaya masa sharuɗɗa lokacin da aka kawo shi.
Dalilinta ne yaron ya fara sake jiki da yaran ma'aikatan dake gidan duk da yasan idan Mommynsa ta sani ya kaɗe dan faɗa zata masa sannan tasa a zane yaran(Allah Sarki basu da gata)a ganinta sune zasu ɓata mata yaro, sannan a dalilin yaran ne ma har Junior ya fara magana da Hausa sosai.
Bilkisu ta yiwa Asiya magana akan ta dena shiga harkan 'ya'yanta tun ranan da ta gansu a wajen kamfen É—inta. Asiya ta yi banza da maganar. Bilkisun bata zama a gidan balle ta sanya musu ido, shima yaron da ya gane mahaifiyarsa bata so ya dinga zuwa jikin Asiya sai ya dena faÉ—a mata abinda suka yi da Asiya, ko wani abu ta siya masa baya faÉ—a mata sai dai ya faÉ—awa Daddynsa...
A ɗan tsurkukin kwanakin daya rage ayi zaɓe aka fara yaɗa jita-jita wai Gwamna Saifuddeen bare ne ba ɗan asalin jahar Congo ba. Iyayensa 'yan ƙasar Gambia ne, Alhaji Sani Kachallah ne ya adopting ɗinsa saboda ba shi da ɗa namiji. Yayinda wasu ma suka sheganta Gwamna Saifuddeen, suka ce Dr Sa'ad Kachallah bai haihu ba har ya rasu. Alhaji Sani kwarton Aicha Jallow ne wanda baƙin cikin hakan ne ya kashe Sa'ad Kachallah. Maganganu dai marassa kan gado da ake yi duk dan a ruɗar da mutane a karkatar da hankalinsu daga zaɓan Gwamna Saifuddeen...
"This is rubbish. Dole ne mu maka jaridar Climax a kotu. Sai sun nemo mana hujjojin da suke iƙirarin suna da shi" Bilkisu ta faɗa a fusace
Ta É—ago ido ta kalli Saifuddeen ta ga idanunsa sun kaÉ—a sun yi ja, har lokacin kuma idonsa na kan jaridar hannunsa.
Ta dafa hannunsa tace "kar ka bari wannan ya girgiza ka. Duk sharrin Umaru Kwom ne, we will win this election ko sun ƙi ko sun so"
Ta karɓe jaridar hannunsa ta zauna a cinyarsa ta tallafo fiskarsa tana masa magana.
Asiya ta shigo falon saboda ta tambayi Gwamna ko zai dawo da Nana gida saboda zaɓe na matsowa, amma ta tsaya chak saboda ganin su tare cikin wani yanayi da ya motsa mata kishin da bata san tana da shi ba.
Ya za tayi tunda ita ta kawo kanta wajen, dama saboda zata je gida ne take son yi masa maganar yanzu, jiya data dawo basu haÉ—u ba balle ta masa maganar.
Har ta shiga mota hoton Bilkisu zaune akan cinyar Gwamna take gani. Yadda take taɓa masa fiska ma waya sani ko sun... tayi saurin shafa laɓɓanta tana tuno zazzaƙar kiss ɗin Gwamna.
A wajen biki ma kasa walwala tayi, Inna Yaha harda mata guntun nasiha wai Allah bai haɗata da Ubaydullah bane saboda Gwamna Saifuddeen yafi dacewa da ita. Ta dinga nuna mata karamcin Gwamna gareta. A tunaninta saboda yau aka ɗaura auren Ubayd da Salma shi ya dameta har ta kasa sakewa, bata san cewa Gwamna shine silar ɓacin ran Asiya ba.
A ɓangaren Gwamna kuwa duk yadda yai ƙoƙarin danne zuciyarsa daga ƙarairayin daya karanta a jaridar Climax ya kasa, mutuncin iyayensa aka taɓo, iyayensa da suka jima a cikin ƙasa. Da farko ya ji a ransa zai bi shawarar Bilkisu, amma daga baya ya gane ɓata lokacine saboda biyewa wannan jita jitar ma kaman buɗe ƙofa ne na sawa mutane su yarda da maganganun, gara kawai ya share. Duk abinda zai faru gameda makomar kujerar Gwamna a jahar Congo, Allah ne masani.
Bai samu halartar ɗaurin auren Ubayd ba duk da Abba har office ya kawo masa katin gayyata. Ya dai kira Abban ya bashi haƙuri tareda yiwa Amarya da Ango addu'a.
Asiya da wuri ta dawo gida amma bata bi ta kan Gwamna ba duk da kuwa kwananta ya fara yau ne. A ɗaki wani zazzaɓi ne ya rufeta har lokacin zuciyarta ya kasa samun sauƙi. Miyasa Bilkisu zata zauna a cinyarsa bayan ya san daga karyawar safiya lokacinta ya shiga. Idan ma karyawar suke miyasa zata zauna a cinyarsa?, shin shi yace ta zauna ko kuma ita ta ga dama ta zauna saboda duk abinda suka yi daren jiya bai isheta ba.
"Bilkisu zauna a cinyata na ji É—uminki" ta yi maganar tana kwaikwayon muryarsa.
"Mtswww" ta yi tsaki a karo na ba adadi tun safiyar yau. Yunwa take ji dan ko a gidan biki bata sa abu a bakinta ba, kamar mai azumi haka ta wuni da yunwa. Yanzun ma yunwar ne ya fara murɗa mata ciki amma taƙi tashi ta nemi abinci ko ta kira a kawo mata ɗaki. Ƙarshe ta gama juye-juye ta tashi ta sa ƙaramin hijab akan riga da wando na bacci ta wuce sashen Gwamna. Idan ta tarar da Bilkisu a wajen sai dai ayita da wajewa tunda dai lokacin ta ne. "Lokacina" ta faɗa a hankali tana tabbatarwa kanta cewa ba zaƙewa take son yi ba, hakkinta zata bibiya.
Bawan Allah na zaune akan kujera a falo yana kallon tsohon ajiya. Saboda abinda ya karanta gaba É—aya wunin ranan yayi shi ne babu walwala da kuma tsananin ciwon kai.
Saboda ta nuna masa ranta a ɓace yake, sai ta wuce cikin ɗaki ba tareda tayi masa magana ba. Kusan minti ashirin tana ɗaki amma bai yi niyyar shigowa ba balle har ta ganshi a ɗakin.