Sashe 37
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
COS ya cigaba da shirye-shiryen naÉ—a sabon shugaba duk da ya san an shirya yin bore ranan naÉ—in, amma ya sani duk wanda ya ga Boss Lady to ba zai iya jayayya ba koda kuwa Alhaji Sani Kachallah ne da suke ta kumfar baki a kansa.
Saɓanin da da ake yin zama a gidan Yallaɓai wannan karan taron da za ayi an saka cewa za ayi shine a gidan Boss Lady. Ba su san gidan ba amma address da aka turo musu ya basu mamaki, domin gida ne da ya ja hankalin jama'ar gari lokacin da ake ginashi, babu wanda ya san takamaimai mai gidan amma girman gidan da kuma tsarin ginin ya nuna cewa mai gidan wani ƙutsar Gwamnati ne. Abin mamakin ma cikin wata uku da sati biyu aka kammala ginin da ka iya zama gida mafi kyau a duk faɗin cikin jahar.
Ƙarfe goma shaɗaya na safe aka shirya taro, kafin goma da rabi mutane suka fara isowa, ba don sun bawa lokaci mahimmanci ba sai dan curiosity da ke cinsu na son sanin wacece Boss Lady sannan koma wacece ba zasu karɓeta ba, Alhaji Sani Kachallah shi zai jagorance su dan yanzu Yallaɓai kam da shi da samun lafiya sun yi hannun riga domin duk wanda ya je ya kalleshi a asibiti kafin 'ya'yansa su ɗauke shi daga ƙasar sun san Yallaɓai yana daf da gangara, mutumin da dukkan jikinsa ya shanye ina yaga tashi balle yai mulki, ko magana baya iya yi sai idanunsa kaɗai yake iya juyawa.
Su takwas suka hallara a ƙaton falo mai kama da fada wanda Mr Lamara ne ya musu iso zuwa wajen. Wani abu mai ɗaukan hankali a falon shine wata kujerar zinari da aka ajiye a wajen wacce ke nuni da koma wacece shugabarsu a nan tayi niyyar zama. Zinari ba baƙonsu bane kuma idon su ya shaida cewa zinarin da aka ƙera kujerar da shi ainihin zinari ne mai kyau. Wace mace ce take da wannan ɓatan basirar zata sa a mata kujerar zinari? Koda yake dama mata da ƙyale-ƙyale sai a hankali. To amma wannan hauka ne ai...
Lokacin da agogon falon ya buga ƙarfe shaɗaya dai dai aka buɗe ƙofar shiga falon. Dukkanninsu suka ƙurawa ƙofar ido musamman Alhaji Sani Kachallah da yake cike fam da wannan mata da yake tunanin karuwar Yallaɓai ce da ke son karɓe matsayin da kowa ya sani nashi ne.
Daga zare ido sai suka koma buɗe baki ganin matar da ke nufo su. Babu wani a wajen da bai san wannan mata ba abinda ya ƙara ɗaure musu kai kenan.
Bilkisu Kachallah ta cigaba da shafa kan macijin da ke nannaɗe a hannunta na hagu, fiskarta ɗauke da murmushi har ta iso tsakiyar falon ta je ta zauna a kujerar da dama saboda wannan zama tasa aka ƙera mata shi.
Bayan ta zauna sai ta ɗaura ƙafarta ɗaya akan ƙaramin stool na zinari dake gabanta yayinda hannunta na dama ke kan hannun kujera tana ɗan bubbuga yatsunta kaɗan-kaɗan, ta ɗan karkatar da kanta gefe tace "akwai mai jayayya?"
Kallon kallo suka fara yi, kowa na tsoron magana.
Mr Paul da yafi kowa tsorata a cikinsu musamman ganin macijin da ke hannun Bilkisu da yai yace "babu mai jayayya"
Bilkisu tayi murmushin gefen baki sannan tace "A fara Agendar yau"
"Yes Boss Lady" Mr Paul ya faÉ—a yana duba takardar dake gabansa, lokacin da ya É—au takardar hannunsa rawa ya fara har sai daya sa É—aya hannun ya supporting takardar dan kar ta faÉ—o.
Duk wani shiri da suka zo da shi na yiwa Boss Lady tawaye ya bi ruwa, domin kowa yayi gum da bakinsa an rasa mai cewa alif a wajen.
*"Sai na fi Gwamna ƙarfi Baba, sai na fi kowa iko a jahar nan. Sai na juya jahar nan a tafin hannuna, sai na nuna maka cewa mace tana da daraja, namiji bai fi mace ba, sannan Ubangiji daya sakawa mace mahaifa dan ta ɗau ɗa namiji a cikinta ba ƙaramin baiwa da ƙarfi ya bata ba. Ka zuba ido kawai Baba, that teenage girl daka faɗawa cewa ba zata iya siyasa ba saboda ita macece ta zama matar dake juya 'yan siyasa yanzu"*
Abinda Bilkisu ke faÉ—i a zuciyarta kenan.
Alhaji Sani ya ɗaga ido ya kalli 'yarsa Bilkisu, idonsa ya ciko da ƙwalla. Mi Bilkisu tayi?, ina ta shiga?, taya ta iya juya dukkan mutanen nan? Anya Bilkisun daya sani ce kuwa? Tunanin da ya ke yi kenan lokacin da Bilkisu ta kira sunansa "Alhaji Sani Kachallah"
*"Yes Boss Lady"* ko ya akayi ya faÉ—i hakan Allahu a'alam, sai bayan ya faÉ—a ya ankara da abinda ya fito daga bakinsa. 'Yarsa ya kira Boss Lady, 'yar da shekaru arba'in da É—aya da suka wuce tana cikin mahaifa yana ta addu'ar Allah yasa a haifa masa É—a namiji. Har wajen malamai ya shiga yana fata wannan karan ya samu É—a namiji.
'Yar da a lokacin da aka haifeta nurse ta fito ta gaya masa cewa mace aka haifa masa yaji kamar yaje ya shaƙeta kawai ta koma inda ta fito. 'Yar da ko suna ba shi ya zaɓa mata ba saboda yadda zuciyarsa ta cunkushe da kasancewarta mace. Mahaifiyarta ce ta zaɓa mata suna Bilkisu ana saura kwana ɗaya ayi suna, saboda har lokacin bai zaɓa mata suna ba, kuma bashida niyyar zaɓa.
Gashi dai yanzu 'yar da ya raina a lokacin ta haye kujerar da yake nema shekara da shekaru, ta samu matsayin da yake nema shekara da shekaru, wato Mulkin jahar Congo. Ba komai bane idan ka mulki talakawa saboda shi talaka ko Akuya aka ɗaura akan ƙaragar mulki zai masa biyayya. Mulkin daya ke nema shine mulkin dake juya Gwamna ya tanƙwasa attajirai, ya juya Sarakuna sannan mulkin dake haɗa ko ya wargaza komai a faɗin jahar, mulkin da kowanni ƙorafi za a kawo idan bai amince da shi ba to banza ne.
Yau dai ga 'yarsa da wannan Mulkin...
Bilkisu Kachallah ta yi murmushin nasara ganin tsantsan ruÉ—ani dake shimfiÉ—e a fiskar mahaifinta. She has long for a day like this, a day da zata nunawa mahaifinta cewa is not all about haihuwar É—a namiji. Itama mace abun alfahari ne. Ta sani, she went extra length to get this, amma its all worth it ai. Zama a kujeran nan, jin dattawan nan suna kiranta Boss Lady, its worth all the sacrifices da ta yi.
Daga yanzu da bazar Bilkisu Kachallah zasu taka a jahar nan.
Abu ɗaya ta sani duk wanda ya goya mata baya ya tsira wanda yai jayayya da ita zai bi sahun su Yallaɓai...
***
*Ga dai Bilkisu Kachallah a kan kujerar zinari, ga Kuma Asiya Kachallah chan garƙame a gidan yari. Ko ya abin zai kasance a wannan tafiyar?*
*shin tukunna idan MACE ta juya NAMIJI ita macen wa zai juyata?.... i guess MACE 'yar uwarta ko?*
Mu haɗu a kashi na uku wanda shine kashi na ƙarshe Insha Allah.
*Taku Azizat Hamza*
*Ma'assalam*