← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 37

Sashe 7

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta faÉ—awa Umma da Abba cewa Gwamna da kansa ya ce ta zo gida amma ba ta gaya musu akan wani dalili ba ne. Ga sauran 'yan gidansu cewa ta yi saboda bikin Faty da za ayi ne ta zo.
Sumayya ma bata san ainihin dalilin zuwansu gida ba, amma kamar yadda Inna Yaha da Hindatu ba su yarda cewa saboda biki ta zo ba, haka itama ta yarda cewa akwai matsala ne tsakaninta da Gwamna.

***

Ranan Monday aka watsa labarai cewa kaso biyu cikin uku na majalisar jaha sun zaɓi ayi watsi da maganar tsige Gwamna, sun faɗi cewa abubuwan da ake tuhumar Gwamna da shi shati faɗi ne na 'yan adawa.

A ɓagaren Umaru Kwom kuma jaridar sa ta Climax ta cigaba da fitar da labarai marassa daɗin ji gameda Gwamna.
Alhaji Kwom ya É—aura aniyar a zama na gaba a kotu zasu kawo Mr Silas ya bada shaidah.

Ranan Laraba aka yi Primary election. Gwamna mai ci Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya zamo ɗan takarar Gwamna a jihar Congo a zaɓe mai zuwa a ƙarƙashin jam'iyyarsu.

Duk wannan bidiri da ake yi tsakanin Bilkisu da Alhaji Sani Kachallah da ma mutanen da ke goya masa baya, shi Uban gayyar hankalinsa ba a kwance yake ba, babu nitsuwa a tattare da shi. Kowacce rana yana wuni ne da abinda ya dace yai wa Asiya. Duk ta inda ya ɓullowa lamarin sai ya ga zuciyarsa ta kasa gamsuwa da shawaran daya yanke.

Ya aureta ne da niyyar rabuwa da ita amma yanzu ga dalilin rabuwan yana da shi amma zuciyarsa ta ƙi amincewa da hakan.

***

Duk wani hidiman biki da aka yi, Asiya ta yi shine cikin rashin jin daÉ—i. Ta É—auka da House suka janye maganar tsige shi Gwamna zai nemeta, amma shiru, yanzu fatanta kawai komai ya tafi dai dai ranan da za ayi zama na gaba a kotu.
Ranan ɗaurin auren Faty, Fou'ad Salisu ya kirata, ba yadda za ayi ta fita dan haka sai Queen Bee ta aika ta karɓo saƙon.

Ranan Alhamis. Alhaji Umaru Kwom yana zaune a falo ya ƙurawa TV ido jira yake a gama yanke hukunci ya ji sanarwar da za a yi. Yana da mutanensa da za su halarci zaman kotun duk da kuwa zama ne za a yi ba tareda 'yan kallo ba.

Duk da ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, yana da dama a kansa idan shari'ar ta tafi yadda ya tsara. Idan kotu bata wanke Saifuddeen Kachallah ba yana da damar da zai soke shi a lokacin yaƙin zaɓe.

Sama da awa ɗaya bai samu labari daga muƙarrabansa ba, haka duk tasoshin da yake jira su kawo labari da ɗumi-ɗuminsa, har yanzu ya ji shiru.

"Hello Halliru, mi yake faruwa ne? Alƙali bai faɗi hukunci bane har yanzu?"

Halliru yace " akwai matsala, Ranka shi daɗe komai ya lalace. Yanzu dai an tafi hutun rabin lokaci idan an dawo Alƙali zai zartar da hukunci"

"Wani matsala kuma? Mr Silas yana nan, Lami na nan, wani shaida kuma suke nema?"

"Allah ya taimaki Excellency. Ga saƙo nan ance a kawo maka"

Alhaji Umaru Kwom ya dakatar da mai maganar yana cigaba da bibiyan bayani daga bakin Halliru. Amma Halliru ya ƙi faɗa masa komai, ƙarshe ma wayar yankewa tayi.

Ya duba mai aikinsa da ya kawo saƙon yace " saƙo daga ina?"

"Ance daga wajen Matar Gwamna"

"Matar Gwamna?" Ya dai karɓi dogon envelop ɗin daga hannunsa.

Yana yaga envelop ɗin ya duba abinda ke ciki. Hoton Lami Ninja ce tana zaune akan wani mutumi, shigar da tayi a hoton ya bayyana cewa ita ɗin ba kamilalliyar mace bace. Hoto na gaba kuma ita ce riƙe da sigari a wajen party, wannan tsohon hotone ma, dan zai iya kaiwa shekaru shatakwas baya. Takardun gaba kuma photocopyn script ne na jarrabawar da Lami tayi aka bata carryover take iƙirarin Prof Kachallah bai bata dai dai bane saboda abinda ya faru tsakaninsu. Sai wata takarda kuma da itama photocopy ce wanda rubutu ne da Mr Silas yai ya bayyana duk abinda ya auku shekaru shabiyar da suka wuce, tareda faɗin cewa Lami Ninja ce ta biya shi dan ya aikata komai. Takardar ƙarshe kuma anyi rubutu ne da hannu inda aka rubuta
*idan ka ga saƙona ka kira* a ƙasa akayi signing da initial A wanda ke nuna Asiya ce.

Cikin kiÉ—ima ya kira numbar Asiya wacce dama kiransa ta ke jira.

"Ka ga saƙona?"

"Kin yi ƙoƙari kam" ya faɗa da ƙarfin hali

"Kar ka damu babu wanda zai kira sunanka cikin Mr Silas da Lami Ninja, amma ka shirya, Jaridar Climax za ta biya tara na rubutun bogi da ta buga ta ɓatawa Gwamna suna"

"Kina tunanin zan tsorata ne?"

"A'ahhh! Alhaji Umaru tsoro kuma. Ni dai ina son tabbatar maka ne kawai kujerar Gwamna ta maka nisa, ka shirya congratulatory speech wa Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah"

Kafin ya kashe wayar ta riga ta kashe. Tabbas ita ce Malam Nawaso yake nufi. Ta ya zata shammace shi haka?. She completely make a fool out of him, taya ma haka ta faru?...

5

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Alkali ya zartar da hukunci.
Lami Ninja ta rintse ido lokacin da ta ji hukuncin da Alkali ya karanto. Ita Lami Ninja wacce take cin karanta ba babbaka a chan Lagos shine yanzu ake maganar za ta yi shekaru bakwai a kurkuku, sannan za ta biya tara kuɗi miliyan goma na ɓatawa Gwamna suna da tayi. Tana da sirrikan mutane dayawa a tafin hannunta, mutanen da akwai jarinsu acikin sana'ar da take yi, idan suka juya mata baya za ta tona musu asiri...

"Mi zai faru idan mutanen Gwamna suka samu hujja a kaina?, mi zai faru idan Alkali ya turani kurkuku?"

"Wannan ba zai faru ba, idan kuma aka samu akasi hakan ya faru to za a nemi ɗaukaka ƙara. At most ki biya tara, ko da za a turaki kurkuku ba zai wuce na wata shida ba"

"Ka san akwai abinda zan faÉ—a ya zamowa wasu mutane matsala"

"Ba abinda zaki faÉ—a Lami. Rayuwarki da ta shegiyar 'yarki yana da mahimmanci a gareki"

Hirarta da Umaru Kwom kenan.

Ba dan kanta za ta yi shiru ba, sai dai ba za ta so a taɓa lafiyar 'ya ɗaya tal data mallaka ba. Ta san mutane irinsu Umaru Kwom ba wani abu bane a wajensu su sa a kashe rai.

Mr Silas zai yi shekaru uku a kurkuku amma shi ba zai biya tara ba.
A hakan kotu ta masa sassauci ne saboda halin da ya ke ciki wanda yai iƙirarin wasu 'yan kidnappers ne suka kama shi suka lakaɗa masa duka, da suka ga bashi da komai suka sake shi.

Dukkansu biyun kowa da nashi dalilin na ƙin ambaton sunan Umaru kwom.

***

"Gobe za a buɗe Kamfen ɗin Saifuddeen, muna buƙatar goyon bayan ku" Alhaji Sani ya faɗa yana kallon Yallaɓai

"Alhaji Sani, jam'iyya tana tareda Saifuddeen É—ari bisa É—ari sai dai dole ne ya É—au alkawari akan ba zai juyawa Jam'iyya baya ba idan aka rantsar da shi" Alhaji MacciÉ—o ya faÉ—a yana kallon Alhaji Sani Kachallah da ke fuskantarsa.

"Dole ne ya É—au alkawari, idan ba haka ba we'll not support his campaign" Mr Paul yai maganar yana jijjiga hannu, jijiyoyin wuyansa har sun fara tashi.

"Da mutane nake magana, ban saka dabbobi cikin maganata ba" Alhaji Sani ya faÉ—a yana yiwa Mr Paul mugun kallo

"Alhaji Sani are you calling me an animal?"

"So?"

"Enough!" Yallaɓai ya buga sandarsa da ƙarfi.

"Muna magana mai mahimmanci kuna mana zancen yara. Wata uku muke da shi wajen tabbatar da cewa Saifuddeen Kachallah ya samu matsuguni a kowanne lungu da saƙo na jihar nan"

"Sorry Yallaɓai, Ka san akwai tsohon banza a cikinmu" Mr Paul ya faɗa yana dariya

Alhaji Sani ya miƙe tsaye, cikin fushi yace "ba zan zauna yaron bayana yana gaya min magana ba. Yallaɓai za mu haɗu a zama na gaba"

"Alhaji Sani, Alhaji Sani..." Alhaji MacciÉ—o ya shiga kira amma ina, tuni Alhaji Sani ya cikawa babbar rigansa iska.

Bayan tafiyarsa Yallaɓai yaiwa Mr Paul faɗa saboda ko ba komai Alhaji Sani Kachallah ya girmeshi nesa ba kusa ba.
Damuwar Mr Paul dai shine a san yadda za a yi Saifuddeen ya saka hannu a buƙatun jami'iyya saboda kar ya zo ya hau a samu matsala.

***
Gwamna na tareda COS lokacin da aka bayyana hukuncin kotu a talabijin.

"Congratulations your Excellency"

"Thank you Mr Lamara"

"Yanzu babu wata matsala sai mu fara Kamfen kawai"

"Allah ya shige mana gaba"

Har ya bar office bai daina mamakin Asiya ba, bai san takamaimai mi tayi ba amma ya san tanada hannu wajen yadda komai ya warware. Lokacin da ya shiga gida yana isa falo Bilkisu ta miƙe da sauri ta zo ta rungumeshi tana faɗin "Congratulations Darling, we won. Yanzu bamuda wata matsala sai ta Kamfen. Ita kuma tsinanniyar nan Lami na so life imprisonment aka rubuta mata"

Chan ƙasan ransa yake tunanin babu wacce ta dace da wannan rungumar sai Asiya. Kafin ya bar office yasa an binciko masa duk abinda ya faru kuma ya samu bayanai kan cewa Asiya ce ta aiko da hotunan Lami Ninja wanda ya nuna ita ɗin tun asali 'yar bariki ce, sannan script ɗinta da aka samo an saka wani Professor ya duba marking ɗin kuma ya tabbatar abinda Saifuddeen ya bawa Lami Haladu, shi ta ci.

Ko da ita ta sa aka yiwa Mr Silas duka saboda ya faÉ—i gaskiya, to tayi ne domin shi. She went this far just for him.

"Come here Darling, na saka an girka maka favourite food É—inka"

Bilkisu ta katse shi. Da ta yi maganar girki ƙwaƙwalwarsa tuno masa tayi da kwana biyu da ya ɗanɗani girkin Asiya matarsa. Akwai professional Cook da yake musu girki a gidan, amma albarkar dake girkin mata ga mijinta yana da yawa.

Bilkisu ta kama hannunsa ta wuce da shi É—aki dan ta taya shi kimtsawa...

Har ƙarfe tara na dare Asiya na jiran kiran Gwamna. Abu biyu take juyawa a ranta. Ko dai idan Gwamna ya kira yace ta dawo gida ko kuma idan ya kira yace ya saketa. Tun tana jiransa har ta fara gyangyaɗi, ƙarshe bacci ya sace ta.
Chapter 7 · 0% Book details