← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 37

Sashe 26

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da video da yake kallo ya kai ƙarshe yake maida shi farko ya sake maimaita kallon. Yana bin kowanni movement na iyayensa a cikin videon, musamman mahaifiyarsa, wacce ita ce bai san kowa nata ba, akwai iyayenta a video ɗin suna yi mata kari da kuɗi amma su kaɗai ya sani daga danginta. Ya sha jin Dadda na cewa mahaifiyarsa 'yar babban gida ce amma kuma gashi har yau babu wani nata da ya taɓa nemansa, hakanan shima ya kasa zuwa nemo su. A mafiya lokuta ya kan sa a ransa zai je Gambia ya nemo dangin mahaifiyarsa amma sai wani abu ya sha gabansa.

Asiya ta zauna gefensa ganin hankalinsa ya tafi kan screen É—in TV dake falon. Ta É—aura hannunta akan hannunsa É—aya tace "Excellency"

"They were in love. Very much in love. Ki kalli nan, baki ga irin murmushin da suke yiwa junansu ba? My father is shy, but my mother is witty. Ki ga yadda take bashi cake a baki tana dariya har da ja masa hanci" ya ƙarisa maganar yana dariya.

Sai yanzu ta fahimci mai yake faruwa. Lokacin da take tafiya gidan biki Yaya Bello ya faÉ—a mata gulmar abinda ake cewa a gari amma hankalinta baya wajen.

"Ka yi haƙuri. Jita-jitar mutane ne kawai saboda a hana jama'a zaɓenka"

"Na sani"

"Kada ka bari wannan ya taɓa ka. There are more important things..."

"Than my parents honour?"

"Kayi haƙuri, ba haka nake nufi ba?"

"Ko da sau ɗaya ne zan iya bada duk abinda na mallaka dan na gansu, na taɓa su, na ji ɗuminsu, na yi hira da su. Ko da..."
Asiya ta rufe masa baki da nata. Da farko bai responding ba, hakan yasa ta janye bakinta tana shirin miƙewa daga wajen amma ya riƙota ya jawota jikinsa da kyau ya shiga kissing ɗinta a hankali.
Chan bayan ya saketa sai yace " you are right, there are more important things to do"

Asiya ta zaro ido tace "like what?"

Kumatunta ya ja ya miƙe yace "like zamu shiga ɗaki ki sake min abinda kika min yanzu"
Asiya ta shiga wiki-wiki da ido tana faÉ—in "ni ni fa ban yi komai ba"

Yadda tayi maganar sai ya bashi dariya. Yace " kwantar da hankalinki, Sallar Isha zan yi"

Har ya shige É—aki Asiya bata bar jin fargaba ba dan tunaninta wani abin daban yake nufi.
Tunda yace bai yi sallar Isha ba ta san kenan ko abinci bai ci ba, hakan yasa ta kira a kawo musu abinci dan yadda jikinta yai lakwas ba iya shiga kitchen zata yi ba.

Har suka gama cin abinci suka kwanta bata daina jin tsoro ba sai da ta ji fitar numfashinsa ya chanja alamar bacci ya É—auke shi...

17

*MATAR GWAMNA*

Washegari Asabat aka fita zaɓen shugaban ƙasa. Gwamna da Bilkisu sun je sun jefa ƙuri'ar su amma Asiya bata bisu ba, duk da itama an chanja mata katinta zuwa polling unit ɗaya dana Gwamna, wanda ke kusa da ƙofar Kachallah House.

Tun daga zaɓen shugaban ƙasa count down ya fara, saboda zaɓe na gaba shine na Gwamnoni.

A ɓangaren Gwamna Saifuddeen ya fawwalawa Allah lamarinsa, ya sani yana da goyon baya na manyan manyan jahar amma duk da haka mulki na Allah ne.

Bilkisu Kachallah kuwa ta shirya 'yan shaye-shaye domin duk inda aka ga wani ya samu ƙuri'u fiye da Gwamna Saifuddeen to a sace akwatin zaɓen. Duk da ta sani cewa akwai ƙanshin Gwamna Saifuddeen ne zai lashe zaɓe, amma ba zata bar wata ƙofa da za a ɓata mata duk wani shiri da tayi ba.
Ta sani Umaru Kwom zai yi ƙoƙarin dagula zaɓe idan bai ci ba amma kuma duk ta inda ya ɓullo zai samu babu hanya.

Shima Umaru Kwom ya shirya nashi jama'ar da zasu sace akwatunan zaɓe, ya fitar da kuɗi na fitar hankali wanda in har bai ci zaɓe ba kafin ya farfaɗo daga ɓarnar kuɗin da yai sai an ɗau shekaru sama da biyu.

Masu faɗa aji a jahar kowa ya baza ido yana jiran sakamakon zaɓe. Daga ƙarshe dai ƙuri'ar ɗan talaka shi zai bada kujerar Gwamna.

Cikin satin biyun da ake zaman jiran ikon Rabbana, kowa ya duƙufa da abinda suka yarda da shi. Masu addu'a na yi, ma su bin duhun dare na bi, masu tura 'yan aike a musu duba duk sun bazama yi.
Bilkisu Kachallah bata da kwanciyar hankalin da Gwamna Saifuddeen ke da shi. Ita da Alhaji Sani babu wanda yake iya bacci da kyau, kowa da fargaban da yake.

A wannan lokacin ne ma Saifuddeen ya tattara nitsuwarsa kan iyalinsa musamman 'ya'yansa da suke hutu, da kansa ya je ya ɗauko Mahirah daga wajen Dadda yace sai an koma makaranta zata koma mata. Nana ma dai saboda yana son ta warke sarai ne shiyasa bai ɗaukota ba, duk da kuwa Asiya ta nuna masa ya kawota gida, zuwa a gama zaɓe sai ya mayar da ita amma ya ƙi, sai dai duk bayan kwana bibbiyu yana zuwa ya duba Nana a Rehab.

*Ranar zaɓe*

Duk son Asiya ranan zaɓe bai faɗa kwananta ba. Amma duk da haka ta yi tsayuwar dare akan Saifuddeen, inda tai masa addu'ar samun nasara idan hakan shine mafi alkhairi a gareshi. Idan kuma babu alkhairi to Allah ya bashi ikon karɓar ƙaddararsa hannu bibbiyu.
Da Asuba ta tura masa text tana masa fatan samun nasara, ko minti ɗaya bai cika ba ya turo mata da saƙon godiya.

Ta yi niyyar zuwa zaɓe wannan karan saboda kar ace bata bawa mijinta support ba. Dama ita bata taɓa yin zaɓe ba, tana dai da katin saboda mahimmancinsa.
Mahirah ta nuna mata kayan da zasu saka, wai anko Mommy ta musu har da Daddynsu. Tunda shigar fari za su yi itama zata saka fari, sai kuma ta chanja ra'ayi ta ce ba zata saka pure white ba.
Ta jima tana neman takamaimai kayan da zata saka, daga baya ta fito da wani Bangladeshi Abaya gown. Fari ne fat amma zanen flowers na jikinsa kalar royal blue ne, ta yi rolling da gyalensa kalar royal blue sannan ta saka wani high heel da ya zo da purse ɗinsa dukka kalar royal blue. Ta ɗan kalli fiskarta a madubi ta furta Masha Allah, domin ko bata saka komai ba a yadda take ta yi kyau babu ƙarya. Ta ɗan bi idanunta da kwalli saboda su sake fitowa dan kaman wanda ta sa da farko bai yi raɗau yadda take so ba.

Junior ne ya shigo É—akinta da gudu yana faÉ—in "Anty Asiya, i'm ready"

"Zo nan handsome É—ina"

Turare ta fesa masa kaÉ—an duk da akwai turaren a jikinsa. Ta karanto addu'a ta shafa masa a kai tana nema masa tsari daga duk wani sharri da kuma kanbun baka.

Ta ƙara kallon kanta a madubi sannan ta fita hannunta riƙe dana Junior.

A bakin ƙofa ta tsaya chak tana binsu da kallo zuciyarta na wani tafarfasowa.

"You look handsome my Governor"
Bilkisu ta faÉ—a bayan ta gyara masa zaman hularsa.

"Daddy, Anty Asiya is here" Junior ya faɗa da ƙarfi. Hakan ya sa dukkansu biyu suka juyo suka kalleta.
Lokacin data haÉ—a ido da Gwamna idonta ne ya ciko da hawaye, tayi saurin komawa da baya tun kafin tayi abin kunya, wato tayi kuka a gaban Bilkisu.

Miyasa ma ta damu da shi? miyasa take jin haushi idan ta ganshi da Bilkisu? Tambayar data kasa bawa kanta amsa kenan.
Hawayen dai data ke ɓoyewa sai da suka zubo.
"Asiya kina son Gwamna Saifuddeen" abinda wani ɓangare na zuciyarta ke faɗi kenan, amma ta shiga ƙaryata hakan.

Kusan minti huÉ—u sai ga Gwamna ya shigo É—akin.

"Lafiya?" Ya tambaya ganin tana faman goge fiska tareda jan hanci.

Magana take son yi amma kuka ne ya ƙwace mata.

"Asya minene? Miya faru?"

yana ƙoƙarin riƙeta ta wafce jikinta ta koma gefe tana sauke ajiyar zuciya.

"Kina kuka saboda kina ganin zan faɗi zaɓe ne?"

Wani kallo ta wurga masa. Ɗan rainin hankali kawai, saboda rashin cin zaɓe za ta yi kuka?

"Ki fito mu tafi, ke ake jira"

"Ba zan je ba"

"Miyasa?" Ya tambaya yana tsareta da idanu.

"Zaɓen shugaban ƙasa ma ban biku ba, wannan ma na fasa zuwa"

Ya É—an yi shiru kafin yace " shikenan, ayi zaman gida lafiya"

Ganin da gaske yayi hanyar ƙofa sai tayi saurin cewa "shine ko ka bani haƙuri"

Murmushine ya suɓuce masa saboda ya riga ya sani kishi takeyi.

Ya haɗa hannu yace "Ranki shi daɗe, ayi haƙuri"

Bayan minti uku ta fito idonta sanye da baƙin glass. Tana ganin Bilkisu tana yiwa Mahirah faɗa wai gyalen data saka yayi girma amma bata ce komai ba ta samu kujera ta zauna, ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya.

"Kwata-kwata baki da fashion taste Mahirah. Miye wannan dan Allah? Inaga zaki dawo zama a nan permanently, ya isa haka zama da tsohuwar nan"

Mahirah ta zumɓura baki tana magana ƙasa-ƙasa
Bilkisu ta gama mita ta haƙura dan Mahirah bata da niyyar chanja mayafin data saka wanda Asiya bata ga wani aibu a jikin gyalen ba.

Zaman minti biyar suka yi a babban falo, har Bilkisu ta miƙe zata je ta dubo Gwamna sai kuma gashi yana saukowa, fiskarsa ɗauke da murmushi amma deep down yana jin tsoro. All this while, bai saka damuwar zaɓe a ransa ba, yau da za ayi zaɓen sai ya fara jin duk wani ƙwarin gwiwarsa na ƙoƙarin sacewa.

Shine a gaba iyalinsa na baya har suka kai wajen da motoci ke jiransu.

Gidajen talabijin na jahar duk sun nuna jefa ƙuri'ar da Gwamna da iyalinsa suka yi, hakanan an nuna na babban abokin adawa ma, wato Alhaji Umaru Kwom.

Daga polling unit Gwamna da iyalinsa suka koma gida dan su saurari abinda Allah zai yi.

***

Zaɓe ya fara tafiya lafiya-lafiya sai daga baya kuma a wasu rumfunan zaɓe aka fara tada tarzoma. 'Yan bangar siyasa suka dinga sace akwatunan zaɓe. A wasu wajen kuma jayayya tsakanin mutanen da Bilkisu Kachallah ta baza ne da kuma na Umaru Kwom shi ya tada fitinar.
Chapter 26 · 0% Book details