Sashe 15
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asiya tace "Sumy zan sha ruwa"
Sumy ta miƙe ta wuce wajen ƙaramin fridge dake ɗakin.
Sai da Bilkisu Kachallah ta gama waya kafin tace "sannu fa, ya jikin?"
Asiya ta kauda kai gefe.
"ÆŠarling ya zo kina bacci, yace a isar masa da gaisuwa"
Asiya ta miƙe zaune tace "tunda ke da mijinki kun samu abunda kuke so, sai ku barni ai, ku bar ni na ji da damuwata"
Bilkisu tayi murmushi tace " mijinmu dai ko ? Don't pretend cewa ba kya jin daÉ—in kasancewarki matar Gwamna."
"Allah ya sawwaƙa"
Bilkisu ta miƙe tace " zan wuce, Allah ya kawo sauƙi"
Daga Asibiti, Bilkisu gidansu ta wuce saboda Hajiyarsu data kira meeting. Sai da ta isa gidan ta samu meeting É—in su uku aka kira. Ita, Saudah da kuma autarsu Halima.
Hajiya tayi musu bayani akan bata ji daÉ—in yadda aka watse family meeting da suka yi kwanan baya ba, an rabu ranan ba da daÉ—i ba. Dama tsakanin Bilkisu da Halima babu jituwa to amma bata san miya haÉ—a Bilkisun da Saudah ba, kasancewa a baya sun fi kusa da junansu.
"Hajiya yanzu har na gayyaci Halima da Saudah wajen Kamfen ɗina su ƙi zuwa"
Bilkisu ta faÉ—a tana kallon Hajiyar.
"Ni na je Kamfen É—inki Bilkisu. Allah ya tsare" Saudah ta faÉ—a tana tafa hannu
Hajiyarsu tace " Saudah wani irin magana ne wannan?"
"Hajiya taya zan amsa gayyatarta bayan abinda ta yiwa 'yata"
"Oh! Saboda shegiyar 'yarki kike fushi. Chan ta matse miki dan ko yau na ganta a gidana sai na cire mata ƙafa"
"Hajiya kinji mi take kiran Zunnairah ko?"
"To ba 'yar shegiyar bace. You are 6 weeks pregnant lokacin da aka É—aura miki aure kuma..."
"Bilkisu! " Hajiya ta daka mata tsawa.
"Oh Lalala! Aikin ya fara warwarewa kenan" Halima ta faɗa tana miƙe ƙafa akan kujera tareda fashewa da dariya.
Saudah ta miƙe a fusace tana faɗin "Bilkisu kar ki manta akwai sirrinki a tafin hannuna. Zan ga da wani ido zaki kalli Yaya Saifuddeen idan ya san kin je an cire miki mahaifa"
"Subhanallahi!. Wai lafiyarku kuwa?. Ke Bilkisu da gaske ne abinda Saudah ta faÉ—a?"
Bilkisu ta miƙe tsaye ta ɗau jakarta tace " cire mahaifa ba abin kunya bane Hajiya, saboda lafiyata na cire. Amma ki jawa Saudah kunne idan bata kama kanta ba, ni da kaina zan faɗawa duniya cewa Zunnairah 'yar wani Bamaguje ne a jahar Benue"
"Yau ana drama a gidan nan" Halima ta faÉ—a tana kwashewa da dariya.
"Halima!" Bilkisu ta faɗa da ƙarfi
"Allah ya huci ranki excellency" Halima ta faɗa tana haɗa hannu biyu. Bilkisu ta fice daga falon ranta a ɓace.
Bayan fitan Bilkisu Hajiya ta kalli Saudah tana neman ƙarin bayani gameda abinda Bilkisun ta faɗa, amma Saudah tayi shiru itama nadama ya damaimayeta.
Hajiya ta san da batun cikin shegen da Saudah tayi, kuma ƙaryar da tayi cewa cikin na Usman ne shiyasa ta bari aka yi auren cikin gaggawa.
Ƙuruciya a lokacin da kake ji da kuɗi, jin daɗi da kuma 'yanci irin na turawa yana iya sakawa ka shagala da biyewa son zuciya. A wajen party ta haɗu da mutumin da har yau ba za ta iya tuna sunanshi ba. Sau ɗaya da suka kasance tare a yanayi na maye ta samu ciki. An riga an saka bikinta da Usman kuma shima sun taɓa sanin juna shiyasa ta jona masa cikin.
Yanzu shekaru sun ja, amma har yau bata dena nadamar ƙuruciyar da ta yi ba.
***
Da safe bayan fitar Bilkisu Kachallah, Hansa'u ta shiga ɗakinta ta ɗauko akwatin sirrin Bilkisu, ta saka password da aka aiko mata da shi nan da nan akwatin ya buɗe. Zaro ido tayi ganin dami damin kuɗi na dollars. Sai data ɗebe kuɗin ta zuba a kan gado sannan ta ci karo da wasu takardu, takardun duk wani business da take ne. Takardan ƙarshe wanda yake cikin wata jar file shine wanda take nema.
Kwanan wata da saka hannu da duk wani bayanai gameda harkan safarar ƙwayoyi da suke yi tsakanin ƙasar Mexico, America da kuma Columbia yana ciki.
Ta zaro wayarta ta fara É—aukan takardun a hoto, da ta gama ta maida takardun cikin akwatin tareda jera kuÉ—i a samansu kamar yadda ta samesu. Ta maida akwatin inda ta É—auko shi, kafin ta fice daga É—akin.
Ta riga ta samu abinda take so dan haka a yau zata bar gidan. Kayan aikinta kawai ta ɗauka ta saka a jaka ta rufe da wasu tsummokara ta fito, ta yiwa masu aiki sallama akan za ta je ta dubo mahaifiyarta a ƙauye. Ita ɗin ta hannun damar Bilkisu ce dan haka ba su zargi komai ba.
Tana fita daga gidan Gwamnati kai tsaye gidanta ta wuce. Tayi wanka ta chanja kaya sannan ta fito, har zata fita sai kuma ta tuna cewa ya kamata ta gayawa Asiya wacece Bilkisu Kachallah. Ta ga rahoton da aka yi da safe, inda aka nuna Bilkisu Kachallah tana matse ƙwalla a gefen gadon da aka kwantar da Asiya, tana faɗin ba za su yafewa wanda yai wa Asiya wannan ba.
Idan ka san waye maƙiyin ka zaka iya yaƙarsa, amma maƙiyin ɓoye da wuya ake cin galaba a kansa. Saboda ba a san fiskarsa ba, ba a san ya yake ba sannan ba a san ta ina zai ɓullo ba.
Ta nemi takarda ta yi gajeren rubutu sannan ta naÉ—e ta saka a envelop.
Dogon hijabi ta saka a kan kayanta ta fice daga gidan, ta nemi Keke ya kaita gidan Gwamna.
Tana shiga gidan ta tambayi masu gadi ina Yaya Bello aka ce mata ya tafi Asibiti. Ba lallai ta sake dawowa gidan ba sannan kuma tana tsoron bawa wani takardar. Sai kawai ta shige cikin gidan. Suka gaisa da Uwani tace mata an aikota ne ta É—auki abu a sashen Asiya.
Tana shiga ɗakin Asiya ta fara neman inda zata ajiye mata wasiƙar da wani ba zai gani ba, sannan Asiya zata gani da wuri. Ƙarshe ta saka wasiƙar a tsakiyar ƙur'ani data gani a kan wardrobe na gefen gado tana addu'ar Allah ya sa Asiyar da ta ajiyewa ce kawai za ta gani.
Daga gidan Gwamna kai tsaye office ɗinsu ta wuce. Ofishin Oga ta shiga fiskarta ɗauke da murmushi, ko da hukumomin Nigeria ba su kama Bilkisu Kachallah ba akwai hukumomi na ƙasar waje da za su shigo cikin lamarin, kuma za su iya sawa a hukunta Bilkisu Kachallah da Madam Bintu Chadi.
Oga na ganinta hankalinsa ya tashi suna gaisawa zata fara magana yace "Badawiyya ba ki duba wayarki bane?"
Wayarta yana silent a koda yaushe saboda aikinta shiyasa ba ta ji ƙaran shigowar saƙonsa ba.
Ta ɗauko wayar a jaka ta karanta saƙon da ya turo mata kusan minti goma da suka wuce.
*Badawiy ki bar gidan Gwamna, an aika wasu suje su kama ki. Ki ɓuya a inda kika san ba za a sameki ba*
Badawiyya ta ɗago kai cikin rashin fahimta. Oga ya miƙa mata wayarsa yana ɗaura yatsa ɗaya akan bakinsa alamar tayi shiru. Ta karɓi wayar ta karanta abinda ya rubuta.
* ki bar nan, ance a arresting É—inki. Idan kika yi gardama an bada umurnin a halbe ki*
Badawiyya ta É—ago ido da sauri cikin kaÉ—uwa. Mi tayi? Tana yiwa Gwamnatin Nigeria aiki sama da shekaru takwas kenan.
Oga ya mata nuni data ƙarisa karantawa.
*ance ke É—in 'yar ta'adda ce da kika shiga aikin nan dan ki samu bayanan sirri. Ance kina shirin tada Bomb a gidan Gwamna. Na gaya miki dama Bilkisu Kachallah tanada protection daga sama*
Badawiyya ta shiga maimaita Innalillahi... a ranta. Ta miƙe da sauri ta fice daga office ɗin Oga.
Tana kaiwa bakin ƙofar da zai fitar da ita daga building ɗin aka ɗaura bindiga a ƙeyarta aka ce " Agent Rabi'atul Badawiyya Kabir, you are under arrest"...
10
Bilkisu Kachallah na isa gida kai tsaye ɗakinta ta nufa ta je ta ɗauko akwatin sirrinta. An gaya mata duk abinda ya faru kuma da izininta aka rufe Agent Badawiyya a kurkuku. Bilkisu ta fito da damin kuɗaɗenta ta gansu yadda ta barsu sai kuma ta duba takardunta duka sun cika. An riga an karɓe wayar Agent Badawiyya dan haka bata da wata matsala.
Tabbas ta ji zafin yadda aka yi tayi sake irin haka, bata jan mutane jikinta amma kuma Hansa'u ta daban ce. She carried her disguise so perfectly, ta yadda tsawon wannan lokaci bata taɓa zarginta ba. Ta jinjinawa Agent Badawiyya saboda a rayuwarta tana son mata masu jajircewa akan aikin da suka sa a gaba. A tsarinta, mace is very powerful...
***
Bayan Azahar ɗakin Asiya ya cika da 'yan dubiya. Motoci uku suka biyo bayan ta Ale Faruƙ cike da 'yan gidansu. Fulani da Tabawa ne suka zo a manyan mata, a maza kuma Ale da Baffa Malam. Sauran kuma yayyu da ƙannenta ne da kuma jikokin gidansu.
Ran Asiya a ɓace yake tun tafiyar Bilkisu Kachallah saboda Sumayya ta faɗa mata cewa wasu 'yan jarida sun zo sun yi hira da Bilkisu lokacin da take bacci.
Bata da lafiya ma ba za a ƙyaleta ba. Ta sake tabbatarwa kanta cewa ita ɗin bata da wani matsayi a rayuwar Gwamna da Bilkisu Kachallah.
Sai dai zuwan 'yan gidansu ya washe duk wani baƙin ciki da kaɗaici da take ciki. Ta yi kewansu sosai.
Kaka Tabawa da ta fara ɓaran-ɓarama a ɗakin haka Asiya ta ɓigire da dariya har da ƙwallah. Yau ne rana na farko da tayi dariya tun rasuwan Umma.
Tabawa ta dage wai sai ta ga Gwamna kafin ta tafi hakan ya sa Asiya ta tsuke fiska.
Tabawa ta shiga tsokalarta wai kota ɓata rai ba za ta janye batunta ba, ai Gwamna mijinsu ne duka.
Ba su bar Asibitin ba sai yamma liƙis, sun so kwana amma Baffa Malam ya hana.