← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 37

Sashe 4

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Asiya ta É—auki jaridar ta kalli hoton da ke shafin farko na jaridar. Hotonta ne ita da Gwamna ranar dinner aurensu daidai wajen da take shirin faÉ—uwa Gwamna ya tarota.
Tana ganin headline É—in ta É—ago ido ta kalli Bilkisu wacce itama ido ta zuba mata.
Asiya ta sake maida dubanta ga jaridar ta buÉ—o shafin da akayi rubutu ta fara karantawa. Bata san tana hawaye ba sai da Sumayya tace "Anty mi aka rubuta? Anty lafiya?"

Asiya ta yi saurin miƙewa ta je ta ɗau wayarta da ke kan gado. Numbar dai da suke communicating da Umaru Kwom ta buga.

Ana ɗauka kafin ta yi magana yace " kinga saƙona?"

"Ka san zan iya yin ƙarar jaridar Climax. Ka san zan iya ƙaran ƙazafi da kuka mana"

"Ahaf na É—auka ai so kike ki rabu da mijinki"

"Babu ruwanka da rayuwata, sannan ka sani Insha Allahu babu wanda zai tsige Mijina"

"Bana tunanin kinada ikon yin komai. Fou'ad Salisu kike taƙama da shi kuma na dakatar da shi daga yi miki aiki"

"Da Allah na dogara ba da Fou'ad ba kuma Allah yana tareda masu gaskiya"

"Idan na hau kujera zan iya shigo dake a ta huÉ—u"

"La'ananne" ta faÉ—a tana kashe wayar.

Sai kuma ta fashe da kuka. Dama wutar fitina kunnata kawai zakayi amma baka isa ka ce ga inda zata je ko kuma ga inda zata tsaya ba. Ga shi dai Jaridar Climax da ta rinƙa yi musu rubutu a ɓoye tana zagin Gwamna tana aibata shi da iyalinsa sai gashi yau itama Jaridar ta kirata Karuwa sannan ta auri Gwamna da ciki.

"Anty" Sumayya ta dafa kafaÉ—anta.

"Sumy ya zanyi?, komai ya lalace mini, idan aka tsige Gwamna ban san da wani ido zan kalleshi ba. I'm confused"

"Addu'a za ki mishi, In Allah ya yarda gaskiya zata fito"

Asiya ta cigaba da sheshsheƙar kuka sai ga wayarta ya sake ƙara. Baƙuwar number ne kamar ba zata ɗauka ba sai kuma ta ɗauka.

"Hello Fou'ad ne"

"Fou'ad na ji ka shiru, mi yake faruwa?"

"Umaru Kwom yana bibiyata. Numbar ƙanwata ce wannan idan na samu evidence zan kiraki da numbar, but kafin nan kar ki kirani"

"Amma...". Kiit aka kace wayar.

***

A chan gidansu Asiya. Hankalin Umma ne ya tashi saboda Hindatu ta nuna mata abinda aka rubuta a jaridar Climax. Tunda aka fara maganar Asiya da Gwamna bata iya baccin kirki sai da akayi bikinta, É—an kwana biyu da ta fara sakewa kuma gashi an sake kawo wani zancen.
Ta dai karɓi ƙaddara ne amma zuciyarta bai so auren Asiya da Gwamna ba. Ƙarshe da ta ga damuwa zai jawo mata illa sai ta ɗau ƙur'ani ta fara biyawa...

A chan Jami'ar Congo kuwa CY ne da Yaya Bello suke tsaye da wani guntun mutum wanda ke rarraba ido alamar marar gaskiya.

"Mr Silas yanzu dai kana nufin akwai script ɗin Lami Ninja a ƙasa"

"Na rantse da jinin Yesu yana nan. Lokacin da aka ce mu je mu tattare scripts na shekarar 2000 mu ƙona na san saboda case ɗin Gwamna ne shiyasa na cire nata na ɓoye"

"Kenan akwai script na course É—in da ake magana akai?"

"Duka scripts na first and second semester nata na sace"

"Ina suke?"

"Oga Clement you know nah. 5M to my account zakuga script"

Yaya Bello da ba wai ya gama gane maganarsa bane yace " amma kasha giyar wake, akan takarda za a baka miliyan biyar"

"Oga Clement, idan ba za ku iya bayarwa ba zan kai wa waÉ—anda zasu biya"

"Za mu tura maka daga nan zuwa dare"

"Haba baƙin Inyamuri..."

CY ya sa hannunsa na ƙarfe ya dafa kafaɗar Yaya Bello yace " takardun sun fi kuɗin mahimmanci, ka barshi"

Bayan Mr Silas ya bada account numbarsa sannan ya bar wajen, yana tafiya yana waige-waige.

"Dan kawai dukkanku ba kwa Sallah shine zaku cuci ƙanwata. Kwaranƙwasi babu wanda zai bashi miliyan biyar koda Gwamna ne da kansa kuwa. A barni na buge shege wallahi sai ya fitar da takardun nan"

C Y yai dariya duk da maganar Yaya Bello ya ɓata masa rai. Da ya san matsayin Asiya a zuciyarsa da babu abinda zai sa ya ce wai zai cuceta kuɗi. Duk da ya rasata har Abada, duk da ta kasance Mallakin wani hakan ba zai hanashi taimaka mata ba, koda kuwa zai rasa rayuwarsa ne.

Lokacin da Asiya ta gayawa CY cewa ta zo makaranta ance an riga an ƙona scripts ɗin shekarar, shine ya jarraba tasa basirar. Maimakon ita da taje wajen manyan department shi ya bi ta wajen wanda suke ƙasa ne, mutanen da sune ke sanin duk wani shige da fice na department ɗin.
Bai sha wahalar gano cewa Mr Silas shine ya fito ya dinga ihu ya tara mutane lokacin da ya shiga office ɗin Prof SS Kachallah ya ganshi suna kokawa da Lami Ninja ba. Yanzu da suka yi magana da shi ya sake tabbatar da cewa akwai hannun Mr Silas a abinda ya faru tun shekaru shabiyar da suka wuce, idan ba haka ba taya zai san mahimmancin scripts ɗin Lami Ninja har ya ɓoye su kafin a ƙona.

Sai da suka shiga mota CY yace da Yaya Bello idan yana son dukan Mr Silas to ya shirya zuwa dare, Yaya Bello yace yanzu na ji magana.
CY ya ɓoyewa Asiya komai ne saboda baya son sa mata rai a zo ba a samu komai ba, gara kawai sai komai ya tabbata kafin ya sanar da ita.

***

Yau lauyoyin Gwamna dana Lami Ninja zasu gana. Close case za'ayi, dan haka daga Lauyoyi, Alƙali sai shaidun mai ƙara da wanda ake ƙara.

Tunda Asiya ta tashi da Asuba bata koma bacci ba, tana gama Azkar ta wuce main kitchen inda ake dafa abincin iyalen gidan, ta taɓa duba wajen sau ɗaya amma wannan karan ba wai ta je dan ta leƙa bane, ta je dan tayi girki ne. Chief cook ɗin namiji ne dan haka ta sallameshi akan ita za tayi abun kari. Daga ita sai Hansa'u da Sumayya da ta biyota suka fara shirya komai. A wajen Hansa'u ta samu bayanin yadda ake tafiyar da girki a gidan. Ba koyaushe Gwamna ke karyawa ba kafin ya fita, musamman ma ranakun Litinin da Alhamis da yake yin Azumi. Sunada menu da suke bi sai dai idan Bilkisu ta bada specific na abinda za a mata.

Bayan sun gama komai aka jera abincin a dining room inda suke haÉ—uwa su ci abinci.

Ƙarfe bakwai da rabi ta buga ƙofar ɗakin Gwamna jin ba a amsa ba yasa ta kutsa kai cikin ɗakin. Yana tsaye gaban madubi yana taje gemunsa. Ta madubi suka haɗa ido amma yai kaman bai ganta ba ya cigaba da abinda yake.

"Ina kwana" ta yi maganar tana kallon ƙasa dan tun da ta ga idonsa ta madubi zuciyarta ya shiga taka rawa a cikin ƙirjinta.

"An shirya maka abin kari, Junior yana jiranka"

"Ba aikin ki ba kenan"

"Na sani amma ina so na yi"

"Bana buƙata"

"Dan Allah ka yi haƙuri, na san abinda aka rubuta a jaridar Climax zai dameka amma..."

"Ba yau jaridar Climax ta fara rubutu akan abinda zai dameni ba"

Ta yi shiru ganin ya juyo yana fiskantarta.

"Matsa min"

"Na'am" ta faÉ—a cikin rashin fahimta.

Ta gefenta ya bi zai wuce ta riƙo hannunsa. "Allah ya bada nasara"

Cikin zuciyarsa ya furta Amin ya cire hannunsa cikin nata ya fita.

"Anya damuwa bai fara taɓa min kwanya ba kuwa?" Asiya ta tambaya bayan fitan Gwamna. Ba ta san dalilin riƙe hannunsa da tayi ba, bata ma san dalilin da ya sa take son faranta masa ba yanzu.

Ta ɗauka ba zai tsaya karyawa ba amma sai ta ga ya zauna Hansa'u tana shirin serving ɗinsa. Asiya ta yi saurin ƙarisawa wajen ta ce "Hansa'u jeki kawai"

Hansa'u ta ajiye serving spoon ɗin ta bar wajen. Gwamna yana riƙe da jarida yana dubawa amma hankalinsa na kansu.

Bayan ta gama zuba mishi soyayyen dankali da miyar hanta sannan ta ajiye masa toasted bread da shayi a gefe. Zama ta yi gefen Junior da yake cin noodles da ƙwai ta shafa kansa sannan ta ɗau plate ta fara serving kanta.

Krit krit krit krit ƙaran takalmin Bilkisu ya sanar da shigowanta dinning ɗin. Ta kalli Asiya sannan ta zauna gefen Gwamna tana faɗin "ina kuma Hansa'un ta shiga yau"

"Hansa'u, Hansa'u"
"Hancha'u where are you?" Junior ya taya Bilkisu kira

Hansa'u ta fito da gudu kamar dama a ankare take. Asiya ta tsaya kallon mamaki wai ga abinci a gaban Bilkisu amma sai mai aiki ta fito daga wata duniya ta zo ta zuba mata a plate.

"Miyasa aka yanka dankalin manya?"

Hansa'u ta fara sosa kai tana inda inda.
"Wuce ki bani waje"

Bayan tafiyar Hansa'u ta kai lomar abinci sai ta tsaya, kaman za ta ce wani abu akan abincin sai kuma ta fasa.

"Barrister Waziri is the best, Darling kar ka ji komai, we'll win this case" ta riƙo hannunsa tana murzawa.

"Daddy yaushe Nana da Mayrah za su dawo" Junior ya katse kallon-kallon da ake tsakanin Bilkisu da ke riƙe da hannun Gwamna da kuma Asiya da ta kasa sauke idonta daga kallon Bilkisu zuwa hannunta da ke kan na Gwamna.

"Daddy zan je wajen Dadda nima"

"Ba inda zaka je, suma su Nanan sun kusa dawowa gida"

Gwamna bai ƙare cin abincin ba ya miƙe ya ce ya tafi. Bayan tafiyarsa Bilkisu tace "gurin shiga kike nema a wajen Darling" ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta cigaba "idan aikin girki kika zo yi, zaki iya komawa Quaters ɗin mai'aikata saboda nan yafi dacewa da ke, "

"Indai kullum zai dinga cin girkina zan so komawa Quarters É—in"

Bilkisu ta sake bushewa da dariya wannan karan har sai da ta ƙware...

***

Zaman da akayi bai haifar da ɗa mai ido ba saboda Lauyoyin Gwamna ba su iya bada ƙwararren shaida da zai ƙaryata iƙirarin Lami Ninja ba, haka aka sake ɗaga zaman zuwa wata sati.
Chapter 4 · 0% Book details