← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 37

Sashe 21

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"My boy ya kake?"

"I'm fine Daddy"

Asiya bata É—aga ido ta kalleshi ba saboda tsoron haÉ—a ido take da shi.
Dai dai kunnenta ta ji yace " ki faɗawa Junior gaskiya, ba CY kaɗai aka zane ba, mai bada labarin ma an taɓa lafiyarta"

A fusace ta juyo tace "waya gaya ma..." bakinta ya kafe lokacin da ya kissing goshinta.

"Anty Asiya da gaske kema Monkey ya dake ki?" Junior ya faÉ—a dan ya ji abinda Gwamna ya faÉ—a.

Da ƙyar Asiya ta iya haɗa kalmomin bakinta tace " a'a Junior, CY kaɗai aka zane"

Miƙewa ta yi ta yiwa Junior good night sannan tayi hanyar ƙofa da sauri, bata kai ƙofar ba aka riƙo hannunta.
Zuciyarta yai wani tsalle lokacin da Gwamna Saifuddeen ya mannata da ƙirjinsa ya rungumeta da kyau yana faɗin "Asya ko sannu da zuwa ba zan samu ba"

Duk ƙoƙarinta na son yin magana ta kasa saboda duk abinda ya taho a maƙoƙoro yake tsayawa.

"Fatan na same ku lafiya?" ya faÉ—a bayan ya rabata da jikinsa amma bai sake mata hannu ba.

"Wanda kake son samun su lafiya suna nan lafiya, sun ma shirya maka liyafar dawowa"
Tayi ƙoƙarin raba hannunsu amma ta kasa.

"Nan da kwana biyu zaki iya shirya mini taki liyafar saboda kema na same ki lafiya" ya ƙarisa maganar yana murmushi.
Ganin ya sake mata hannu yasa ta turo baki ta fice daga ɗakin tareda banko musu ƙofa.
Har ga Allah ta É—auka zai biyota É—aki amma har bacci ya É—auketa bata ji É—uriyarsa ba.

Bayan Gwamna ya bar É—akin Junior kuma, sashensa ya wuce inda Bilkisu ke jiransa.

"Darling akwai improvement sosai a Kamfen namu. Duk anguwar daka shiga posters É—inmu suka fi yawa and..."

"Tun ban zauna ba Bilkisu"

"Sorry Darling, kayi wanka ka fito, na shirya maka special dishes"

"Cook ya shirya special dishes"

"Da izini na ba, kaga kaman ni na yi kenan"

Ya girgiza kai ya wuce É—aki bayan ya manna mata kiss a kumatu. A gajiye yake dan haka baya son dogon musu...

14

Washegari ya kama Asabat dan haka Gwamna ba zai fita da wuri ba saboda yana son hutawa.

Ƙarfe tara na safe ya kira numbar Sumayya yace ta same shi a falonsa, tun ranan ya sa Asiya ta mayar mata da wayarta.

A ƙasa ta zauna tana duƙunƙune kai dan tun ranan da ya ƙwaceta a hannun Asiya take fargaban haɗuwarsu, saboda bata san mi zai ce mata ba.

"Ya karatu" ya tambaya saboda ta sake jiki da shi.

"Alhamdulillah" ta amsa murya ƙasa-ƙasa.

Tambayoyi ya fara mata gameda karatunta da kuma burinta idan ta ƙare karatun. Wannan yasa ta ɗan saki jiki da shi.
Chan sai ya sako mata tambayar da take tsoro "Alhaji Abdullahi ya tura wajen Baba ne?"
Ta yi shiru tana rarraba idanu.

"Sumayyah?"

"Na'am" ta faÉ—a ciki ciki.

"Alhaji Abdullahi ya nemi izini a wajen Baban ki ne? Ko dai a Bello yai wa magana?"

Ta girgiza kai tana ji kaman ta nitse cikin rug saboda kunya.

"A bisa yadda na sani dai da ke da 'yaruwarki amana kuke a hannuna, kuma ni Abdullahi bai sameni akan maganar ki ba, shiyasa na tambaya ko ya wuce wajen Baba ne kai tsaye"

Ya É—an yi shiru yana nazarinta saboda ya lura maganganunsa ya fara tasiri ajikinta.

"Idan Alhaji Abdullahi yana sonki Sumayya, wajena zai zo ya nemi izinin magana da ke, wannan shi zai tabbatar da cewa da gaske ne yana son ki, ba wai ya dinga bin ki a waya yana cewa ki turo masa hotunan ki ba"

Maganarsa ta karshe tai wa Sumayya ba zata, har take ganin inama tana da layar ɓata ta ɓace ɓat a wajen.
Ya shiga mata nasiha kan rashin dacewar abinda ta aikata, daga ƙarshe yace
"Daga yanzu duk lokacin daya kira ki. Kice masa ya nemi izinin magana da iyayenki kin ji"
Sumayya ta gyaɗa kai idanunta cike da ƙwalla.

***

Asiya tana zaune gaban mirror tana shafa powder Gwamna ya shigo É—akin da sallama.

Ba tareda ta san dalili ba sai kawai ta haɗe rai. Ta yi kaman bata ganshi ba, nan kuwa har zuciyarta ya fara bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

" Madam barka da safiya" ta haɗe rai ta cize leɓe tana jin haushin kiranta Madam da yai. Madam kuma? Wa yaga irin tsohuwar nan.

Ya É—an rankwafo daidai kunnenta yace "Jiya kika gudu ba tareda mun yi sallama ba"

Dama a cike take da shi, sai ta juyo a fusace tace " ina ruw..." komai ya tsaya chak saboda haɗe bakinsu da yai, koma minene take son faɗa ya ƙare, dan har lokacin da ya raba bakinsu bata dawo dai-dai ba. Idonta a rufe, hannunta na rawa, hanjin cikinta sun cunkushe, ƙirjinta na bugawa kaman tayi gasan tsere, sannan ba zata iya cewa ga inda kanta yake ba dan kamar a kan iska ma take yawo.
Gwamna ya shafa kumatunta yace "zan fita. Na yiwa Sumayyah magana kuma nace ta baki haƙuri. Dan Allah banda duka banda tsawa, ki mata nasiha a hankali, hakan zai sa ta gane da wuri"

Ya sa hannu ya riƙo hannunta biyu da suke kan cinyarta, ya lura da yadda hannunta ke rawa, hakan yasa shi kissing kowanni hannu yace "lallen hannunki yayi kyau"

Asiya ta haɗiyi yawu maƙwot, tana jin wani abu na yawo a duk ilahirin jikinta.
"Zan je Kachallah House. Dadda tace kin kai mata ziyara, nagode da kulawa"

Ya sake kissing hannun yace "gobe ina jiran taki liyafar"

Ya hura mata iska akunne saura kaÉ—an Asiya ta shiÉ—e dan abin ya zo mata bazata.
"Na tafi"

Sai da ta ji ƙaran rufe ƙofa kafin ta sauke nannauyan ajiyar zuciya ta dafe ƙirjinta dan ta tabbatar zuciyarta bai bulloƙo waje ba.

"Na shiga uku ni Asiya" ta yi maganar tana hura iska waje saboda ta samu sauƙin cunkushewar da ƙirjinta yai.

Ba ta gane wannan sabon salo na Gwamna ba. Bata ma gane ya aka yi duk wani abu da ya mata yake tasiri akanta ba. Da ta ɗan samu nitsuwa sai ta kalli kanta a madubi. Ta yi saurin sa hannu ta taɓa laɓɓanta saboda ta tabbatar suna nan lafiya lau.
"Na shiga uku, ko dai wani abu ya saka min ne?" Ji tayi lips É—in na mata daÉ—i domin har lokacin akwai sanyin lips É—insa akan nata. It was a brief kiss amma har yanzu effect É—in na jikinta...

Bayan awa ɗaya da tafiyar Gwamna Sumayya ta shigo ɗakin Asiya. Ƙasan idanunta sun kumbura, farin idon kuma yayi ja.

Asiya na aiki da laptop É—inta amma gaba É—aya hankalinta ya kasu kashi biyu. ÆŠaya yana ga aikin da take tsarawa, É—ayan kuma yana ga abinda ya faru awa É—aya daya wuce.

"Anty Asiya kiyi haƙuri Dan Allah"

Ta sake maimaita maganar ganin Asiya bata juyo ba, balle ta amsa mata.

"Allah ba zan sake ba, kiyi haƙuri. Allah ban san ya akayi na tura masa hoton ba"

Sai a lokacin Asiya ta juyo tace " ni nasan ya akayi ai. Ya ce miki yana son nono irin naki 'yan ƙanana masu daɗin taɓawa, ki tura masa ya gani ya rage zafi tunda kince ba za ki bar shi ya taɓa ba"

Ta sani Asiya akwai saurin riƙe abu, amma bata yi tunanin har ta haddace chats ɗinsu data karanta ba.

"Da kika ce ba za ki barshi ya taɓa ba, mi ya hana kice masa ba zaki tura ba saboda da taɓawan da turawan duk sammakal. Miyasa kika ji tausayinsa da ya ce miki 'plz my Sumy, ki taimakawa Bawan Allah' ke daƙiƙiyace za ki tausaya masa bayan yana da mata uku a gida kuma kowacce tana da nonon daya halatta masa ya gani ya taɓa?. I'm dissappointed in you Sumayya, har anyi namijin da zai haɗani da ke."

Jin ta fara É—aga muryarta yasa ta tuna maganar Gwamna sai ta sassauta murya tace " to yanzu dai É—aya daga cikin matansa ta ga hoton a wayarsa kuma tace za ta wallafa hoton da chats É—inku a duniya kowa ya gani"

"Na shiga uku Dan Allah Anty ki bata haƙuri. Wallahi ba zan sake ba"

"Ina ruwana, yanzu ma data min maganar cewa nayi ta yi duk abinda ta ga ya dace ƙanwata tace babban mutum take so"

Da gaske Sumayya ta tsorata ta riƙe ƙafar Asiya tana kuka tana bata haƙuri. Asiya ta haɗe rai kamar abinda ta faɗa gaskiya ne.

"Ki shirya auren Alhaji Abdullahi dan na yiwa Ale magana, kin san dama Ale da ya ga mai kuÉ—i jikinsa ke rawa. Idan kin je kuma ku fafata da matan gidansa"

Da ta ga kukan nata yayi yawa sai ta yi gyaran murya tace " Zan ce kada ta yaÉ—a hoton. Idan kika cigaba da mu'amala da mijinsu kuma ruwanki. Tashi ki bani waje"

Sumayya ta miƙe sumi sumi ta bar ɗakin.

Asiya ta jinjina kai, rayuwa kenan. Ko a mafarki bata taɓa tunanin akwai ranan da zasu zauna suyi irin wannan magana ba. Lokacin da ta ke kamarta ina ma take da lokacin tunanin irin waɗannan abubuwa. She's so occupied da karatu da kuma sana'a, bata da lokacin mummunan tunani irin wannan, sannan soyayyarsu da Ubayd tsabtacacciya ce. They were so sure za su yi aure shiyasa suka nisanci duk wani abinda zai jawo su aikata wani abu da bai dace ba.

Ta sake taɓa leɓenta tana tuna lokacin da take gayawa Gwamna cewa gangan jikinta da ruhinta duk na Ubayd ne. Lokaci guda kuma ta tuno amsar daya bata.
*"Ki faÉ—i koma minene, hakan ba zai chanja cewa daga yau gangar jikin, zuciyar da ruhin duka Allah ya mallaka min ba"*

***

Bayan Gwamna ya bar wajen Alhaji Sani Office ya wuce saboda suna da wani meeting ƙarfe huɗu na yamma da za ayi da wasu Dakacin wasu ƙauyuka biyu da suke rikicin fili tsakaninsu. Da ke yana cikin farin ciki, kafin ya shiga meeting ɗin ya rubuta ƙaramar poem ya tura a blog na shi. Ya san zata gani, dan ranan da tayi comment akan waƙarsa ta Attaruhu , ranan ne ya gane wacece fan ɗinsa mai amfani da suna *SeeyaShahidah* ta sha tura masa message ta email tana son haɗuwa da shi, dan a tunaninta kamar kowa macece marubuciyar.
Chapter 21 · 0% Book details