← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 37

Sashe 27

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk abinda yai farko dai zai yi ƙarshe. Duk wani ƙoƙari na ganin an wargaza zaɓe a mafiya yawancin rumfunan zaɓe hakan ya faskara, saboda jami'an tsaro sun yi maganin abun da wuri. A chan ƙauyuka da ba a samu jami'an tsaro ba ma suma sun yi zaɓe lafiya, duk wanda yazo da niyyar tada husuma, tuni zaratan sammari ke yin waje da mutum.
Rumfunan da aka tada husuma wanda hukumar zaɓe ta tabbatar kuma, an kashe zaɓukan wajen, sannan yawansu bai kai har ace za a sake zaɓe ba.

A ɗan wannan tsurkuki da ake jiran sakamakon zaɓe 'yan siyasa da dama kan rasa imaninsu.
A ɓangaren Bilkisu Kachallah tayi imanin idan har mijinta bai lashe zaɓe ba to kuwa babu abinda zai hana a tada yaƙi a jahar.
Shima Umaru Kwom yana da shirin kota kwana.

"Mune muke gaba a ƙaramar hukumar Layyat. Darling we are winning"

Gwamna yace "Hmmm" ya cigaba da rubutun da yake saboda ya kau da hankalinsa akan sakamakon zaɓe. An riga an gama jefa ƙuri'u, babu abinda ya rage sai dai su zubawa sarautar Allah ido.

Da yaga Bilkisu ta dame shi da maganar wanda ke gaba akan irga ƙuri'u da ake, sai ya miƙe ya wuce cikin ɗaki...

Ranan Litinin da ƙarfe goma na safe Gwamna da iyalinsa suna zaune a falonsa sun ƙurawa tv ido, a yau ɗinne za a sanar da wanda ya lashe zaɓe, duk da kuwa sun san a bisa ƙuri'u da aka irga Saifuddeen Kachallah ne a gaba.

A ɓangaren Umaru Kwom shi ɗaya ya kulle kansa a ɗaki yana kallon talabijin duk da kuwa zuciyarsa ta karye saboda ƙuri'un Saifuddeen sun fi nashi yawa, amma duk da haka he's holding up to last minute miracle.

Ƙarfe goma da minti talatin da uku aka sanar da wanda ya lashe kujerar Gwamna a jahar Congo.

Shugaban zaɓe na jaha yana kiran sunan Saifuddeen Sa'ad Kachallah a matsayin wanda ya lashe zaɓe Bilkisu Kachallah ta daka tsalle tareda yin ihu ta faɗa jikin Gwamna.
Asiya kam sujudush shukri ta yi ita da Mahirah, shima Junior ganin sun yi sujjada sai ya yi.

Gwamna ya tura Bilkisu gefe dake ta ihun we won, we won, shima ya kai goshinsa ƙasa yana yiwa Allah godiya...

Umaru Kwom na jin sunan Saifuddeen sai da ya samu temporary shock na wasu sakanni. Chan ya É—au kwalbar giyarsa ya kwankwaÉ—a sai kuma ya É—au waya ya kira wata numba yace "a hargitsa gari"

Nan da nan mutanen da aka biya suka shiga ihun "bama yi- bama yi, Umaru Kwom ne ya ci zaɓe" kafin kace me aka shiga ƙone-ƙone a wasu gurare.

Gwamna yana magana da Alhaji Sani Kachallah a waya Asiya ta taɓa shi tana nuna masa wayarta. Sallama yai da Alhajin sannan ya maida hankalinsa ga Asiya.

"Wasu matasa sun fara riot. Dan Allah ka sa a É—auko Nana daga Rehab. Hankalina bai kwanta ba"

Kafin ya bata amsa COS ya kira shi. Ya É—auki wayar hannu na rawa. Asiya tace "zan É—aukota"
Ta fita ba tareda ta jira amsarsa ba.

Ikon Allah Asiya da Nana suna barin Rehabilitation centre É—in ko minti takwas bai cika ba 'yan banga suka iso wajen suna neman 'yar Gwamna amma babu ita a ciki. Hakan yasa suka cillawa wajen wuta, marasa lafiya da likitoci kowa ya fara ta kansa.

"Hello, nace a tura fire service Rehab centre dake layin Kura"

Daga ɓangaren data kira aka ce " babu fire service a ƙasa, motar ƙarshe tana Kachallah Mall da aka saka wa wuta"

"Da mall da Asibiti wanne yafi mahimmanci? Yanzu yanzu a tura mota wajen"

Asiya ta kashe wayar tana faÉ—in Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun. Hanya ta uku kenan da Yaya Bello ke chanjawa saboda samun tsira, ana ganin plate number mai É—auke da Kachallah to sai ta Allah.

Nana ta ƙanƙame Asiya tana kuka.

"Yaya Bello ka tsaida motar nan, gari ya hargitse zamu iya shiga matsala"

"Ina zamu je idan na tsaya?"

"Daga nan babu nisa zuwa gidan Abba, zamu ƙarisa gidan da ƙafa"

"Da ƙafa kuma?"

Asiya tace "Shine mafita"

Tsabar ruÉ—ewa Yaya Bellon kawai ta tiso gaba babu security É—inta.

Hijab ne a jikin Asiya dan haka ta ciro É—ankwalin atamfar data saka ta rufe baki da hancinta, yai kamar face mask ta saka.
Ta kama hannun Nana suka fita daga motar, bayan sun fita ta gyara mata ɗan ƙaramin gyalenta ya rufe mata rabin fiska.

"Yaya Bello ka cire plate number É—in nan Dan Allah"

"Kar ki damu ba abinda zai faru"

"Ban yarda ba, ka cire"

Sai data tabbatar da ya cire numbar kafin ta ja hannun Nana suka fara bin lungu lungu, tafiyar minti shabiyu ta kaisu gidan Abba.

Gwamna tun da aka kira aka ce masa an cinnawa rehabilition centre wuta ya shiga tashin hankali. Bai san halin da Nana ko Asiya ke ciki ba, gashi numbar Asiyar ta ƙi shiga.

Itama Bilkisu Kachallah jin an ƙona rehab sai hankalinta ya tashi, duk wani murnan lashe zaɓe da Saifuddeen yai sai ya ɓace, ta shiga kiraye kirayen waya dan ta tabbatar da lafiyar 'yarta.

Kusan awa uku akayi ana ƙone-ƙone kafin sojoji da aka baza suka ci ƙarfin abun, dan wannan faɗa yafi ƙarfin 'yan sanda. Tuni aka shiga yin kamen samari bayan ƙura ta lafa. Da wanda ya ji da wanda bai ji ba idan hau ta hau ka sai kawai a rafkeka a je a kulle.

Curfew aka saka na ƙarfe biyar na yamma. Zuwa ƙarfe huɗu ma gari yayi tsit, sojoji na ta shawagi a ko'ina.

Asiya tana gidansu tanata ƙoƙarin kiran numbar Gwamna dan ta sanar da shi suna lafiya amma ta ƙi shiga.

Sai ƙarfe shida da kusan rabi na yamma Gwamna ya ga saƙon Asiya wanda ta tura tun da rana.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!" Ya faÉ—i yai sujudush shukri. Ikon Allah ne ya kaishi wannan lokaci ba tareda wani abu ya same shi ba saboda rashin sanin halin da matarsa da 'yarsa su ke ciki.

ÆŠakin Bilkisu ya shiga ya sanar da ita Nana da Asiya na lafiya. Damuwarta Nana ce ba Asiya ba amma koba komai tunda ta taimakawa 'yarta she's grateful.

Ƙarfe takwas na dare Gwamna da kansa ya je gidansu Asiya dan ba zai iya samun nitsuwa ba sai yasa su a idonsa.
Yai wa Abba godiya sannan ya masa sallama ya É—au matarsa da 'yarsa suka tafi. Asiya da Nana suka shiga baya saboda mota É—aya ya zo da shi, daga shi sai Dreba.

A ɓangaren Umaru Kwom rashin sace Nana Kachallah ya fi komai dagula masa lissafi. Dan yasa a ransa zai yi amfani da ita wajen samun wani abu a wajen Saifuddeen.

Suna shigowa falo Bilkisu ta zo da gudu ta rungume 'yarta. She might be a bad mother amma kamar kowacce uwa, tana son 'ya'yanta.
Sauran yaran ma suka zo suka rungumi yayarsu suna kuka...

"An ce mutane shatakwas suka mutu, anyi asaran dukiyoyi dayawa. Excellency shin wannan ne siyasar?"

Asiya tayi tambayar idonta cike da hawaye.

"Asya" Gwamna ya kira a hankali

"Mun tsira, amma sauran al'umma fa?. Duk wani É—an siyasa akan talakawa zai sauke takaicinsa, Miyasa? Miyasa?"
Wannan karan sai ta fashe da kuka.

Ya jawota jikinsa ya shiga bubbuga bayanta a hankali. Chan sai yace " Insha Allahu zan yi ƙoƙari naga irin haka bata sake faruwa ba. I'll try my best Insha Allah"
Ya kwantar da kansa a kafaÉ—arta...

Cikin sati guda komai ya lafa. Dama abinda ya faru ɓata gari ne 'yan shaye-shaye da aka biya suka tada husuma.
Umaru Kwom ya fito ƙarara ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon wannan zaɓe tareda iƙirarin cewa zai shigar da ƙara kotu, wai dole wajajen da aka soke zaɓensu a sake yi musu sabon zaɓe. Ya manta cewa ratan da Gwamna Saifuddeen ya bashi ko da ya samu ƙuri'un duka wajajen da aka soke to ƙuri'unsa ba za su zo kusa da na SSK ba balle har ya wuce shi.

***

"We need to celebrate this victory Yallaɓai"

"Kachallah" Yallaɓai ya faɗa yana murmushin nasara.

Kaman yau ne Chief of Staff ya kawo Kachallah wajen Yallaɓai.

*"Ina so a kashe Gwamna Saminu Bacchi, ina so mijina ya hau kujerar Gwamna"* kalaman Kachallah kenan a wannan lokacin.

Bayan fitan Kachallah daga falon Yallaɓai. Ta kalli zoben dake hannunta wanda dutsen dake saman zoben daga fari ya koma ja. Ta yi murmushi saboda maganar Shri Hari Bansari ta tabbata, idan zoben ya koma ja to ya fara aiki kenan.

"The whole state is now mine. Saifuddeen, Yallaɓai, Baba" ta yi murmushi sannan ta dunƙule hannunta gam alamar ta musu kamun talala.

A cikin mota ta fara tuno yadda komai ya samo asali.

Watanni kusan bakwai da suka wuce matar Gwamna Saminu Bacchi ta ci mata mutunci, ta mata walaƙancin da tunda aka haifeta ba a taɓa yi mata ba.

Ta sake tuno hirarta da Babanta lokacin da ta kai masa ƙorafi

"Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?"

Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata.

"Wace tambaya ce kuma wannan?"

"Baba dan Allah ka amsa min tambayata"

Alhaji Sani Kachallah ya kalli idon 'yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce " idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba"

"A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?"

Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe, ya É—aura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido.

"Babu yadda za'ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka É—aura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar masu zuwa sun yi nisa sosai"

"Bilkisu!"

"Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and own the state"
Chapter 27 · 0% Book details