← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 37

Sashe 6

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki na rawa Mr Silas yace " suna so na faÉ—a musu gaskiyar abinda ya faru ne 15 years back"

"Ka faÉ—a musu?"

"Ranka shi dade ba dan duka na faÉ—a ba, sun ce za su kashe family É—ina."

"Yanzu dai ka faÉ—a musu komai?"

Mr Silas ya karya wuya yace " i'm sorry"

Wani da ke gefen Umaru Kwom yace "Ranka shi daÉ—e ai magana ta tashi kenan, tunda na san zasu naÉ—i abinda ya faÉ—a"

Umaru Kwom yai murmushi yace " gaba ta kaimu ai, we can still use it against them. Idan suka kawo confession É—insa mu kuma sai mu bayyana cewa sace shi aka yi aka gana masa azaba, shiyasa ya faÉ—a musu abinda suke son ji"

Mutumin yai murmushi. Bayan an fita da Mr Silas. Umaru Kwom ya faɗawa muƙarrabinsa cewa aje a ƙara dukan Mr Silas a ɓata masa fuska sannan a kaishi Asibiti sai a ɗauki hotonsa a gadon Asibiti, ya ƙara da cewa "Ku faɗawa Gideon ya rubuta headline mai kyau a jaridar gobe"

Lokacin da wani ƙaton bodyguard mai zubin Samudawa ya mari fiskar Mr Silas da kacha, sai da haɗoransa biyu suka zube ya faɗi ƙasa a sume. Da ya farfaɗo a gadon Asibiti ya tsinci kansa an ɗaure masa fiska hannu da ƙafa. Abinda Yaya Bello ya masa ashe ba komai ba ne akan bugun daya sha a gidan Alhaji Umaru Kwom.

***

"CY ba ni da bakin yi maka godiya"

"Anything for you Aseey. Oops! Excellency"

"Kai bana son Excellency É—in nan. Har yanzu Aseey É—in da ka sani ce"

"A'a rufa min asiri. Ke yanzu tsauni ce ni kuma ɗan ƙaramin dutse"

"Thank you my brother from another mother"

"Kai! you should thank your brother ooo. Ba dan shi ba inaga Mr Silas ba zai faÉ—i komai ba"

"Ai Yaya Bello. Allah dai ya shirya mana shi"...

Bayan sun rabu da CY Asiya ta godewa Allah da bata yi gaggawar tafiya Lagos ba. Shiyasa aka ce gaggawa aikin ShaiÉ—an, gashi da ta sallamawa Allah komai sai gashi ta hango nasara.

Abinda ya faru shine washegari da safe bayan ta bi dare tana addu'ar Allah ya taimaketa ta warware wannan matsalar kafin Gwamna ya saketa sai ga kiran CY yana faɗin ya kamata su haɗu akwai abunda zai nuna mata. Ba shiri ta shirya ta wuce shagonsu tace Yaya Bello ya koma gida zata kira shi idan ta gama. A office ɗin Queen Bee ta saka dogon hijab da niƙaf, ita da Queen Bee suka wuce wajen da CY yace su sameshi. Ganin CY tareda Yaya Bello sai abin ya ɗaure mata kai.

"CY mi yake faruwa?"

"We've got the script" ya faÉ—a yana murmushi.

"Dan Allah?"

"Ashe akan wasu tsohin litattafai har ake ɓatawa Gwamna suna" Yaya Bello ya sa baki.

"Yaya Bello ba zaka gane ba"

Bayan ta zauna ne suka mata bayanin Mr Silas da kuma sato shi da suka yi har suka samu wasu bayanin ma da basu tsammanta ba.
"Mun yi recording confession nasa, za a iya presenting a kotu ai"

Asiya tayi shiru.

"Ya ba kya murna?"

"Umaru Kwom ba wawa bane. Ɗan siyasa ne, he will manipulate the evidence, hakan zai ƙara dagula lamari"

"To kawai mu presenting script É—in ba tareda an bayyana abinda Mr Silas ya faÉ—a ba"

Asiya ta yi shiru na kusan minti huÉ—u tana nazari, chan kuma tace " i have a plan"...

***

Washegari jaridar Climax ta fitar da hoton Mr Silas kwance akan gadon Asibiti cikin mawuyacin hali. Aka rubuta cewa Gwamna ne ya sa aka sace shi saboda kar ya faÉ—i gaskiya a kotu, domin shekaru kusan goma shabiyar da suka wuce shine ya kama Gwamna yana cin zarafin Lami Ninja.

"Your Excellency jaridar Climax tayi sabon rubutu"

Gwamna ya kalli COS yace " bayan sun ce na auri Asiya da ciki, me kuma ya rage, sun gano ina da 'ya'yan shegu a waje ne?" Ya ƙarisa maganar yai dariyar takaici.

"Ka karanta Sir"

Gwamna ya jawo jaridar ya fara karantawa.
Cikin É—ayan biyu ne, ko Alhaji Sani ne da wannan aiki ko kuma Asiya.
Ya naÉ—e jaridar ya jefata cikin kwandon shara.

"Akwai matsala Excellency, an fara kirana daga Gwamnatin tarayya ana son sanin gaskiyar wannan magana"

Gwamna ya ajiye biro ya É—ago ya kalleshi yace "akwai hukumar bincike ai, wannan ba aikin ka bane"

COS ya hangame baki yana kallon ikon Allah. Bai san wani irin zuciya ce da Gwamna ba. Ta ya zai iya kwantar da hankalinsa a yanayin da ake ciki. Yana zaune akan kujerar da take gargada tana shirin kifar da shi amma ko ajikinsa...

Kiran da Alhaji Sani ya masa yana tambayar ko ya ga abinda aka rubuta ya tabbatar masa babu hannunsa a ciki.
Can she be this cruel?
Shin a dalilinta na son ganin ta goge laifinta a wajensa, za ta iya yin wannan abu?

Da fargabar sanin zai iya yiwuwa ita ta aikata hakan ya je gida.

Asiya na waya Hansa'u ta shigo É—akinta da sallama.
Ganin ta shigo ya sa Asiya ta juya harshenta zuwa turanci dan kar Hansa'u ta ji abinda ta ke faÉ—a.
Hansa'u ta yi murmushin gefen baki, Yare biyar ta ke ji: Hausa, Fillanci,. Turanci, Larabci da Faransanci.

Da Asiya ta gama wayar ta kalli Hansa'u tace "lafiya?"

"Mai Girma yace wai ki sameshi a falonsa"

"Gwamna ya dawo?" Ta tambaya dan ba ta taɓa gani ya dawo da wuri haka ba, ƙarfe shabiyu ta ɗan wuce ne yanzu, ko zai dawo da wuri to irin ƙarfe huɗun nan ne.

"Na ji".

Riga da wandon jeans ne a jikinta sai ta É—auko Abaya ta saka akai.
Ba ta sameshi a falonsa ba, dan haka ta wuce É—akinsa kai tsaye.

A tsaye ta sameshi yana kallon bango, ya goya hannunsa baya.

"Assalamu Alaikum, Barka da dawowa"

Ta yi minti biyu tsaye kafin ya juyo ya kalleta, tayi saurin sauke idanunta ƙasa saboda yadda ta ga fararen idanuwansa sun rine sun koma ja.

"Ki gaya min gaskiya. Kinada hannu a abinda ya faru da Mr Silas Isege?"

"Ehm...Ehm..."

"Answer me!"
Ta yi saurin matsawa baya saboda firgita da tayi.

"Na ce ki cire hannunki, na ce bana buƙatar taimakon ki, miyasa kike da taurin kai ne?"

"Ba gaskiya jaridar Climax ta faÉ—a ba, ba a ji masa rauni har haka ba..."

"Ki je gida"

"Hahn!"

"Ki je gidanku zan nemeki"

'Ka yi haƙuri Dan Allah, zan maka bayanin komai idan aka warware wannan case ɗin' abinda ta ke son faɗa kenan amma kalmomin sun tsaya a maƙoshinta sai ma hawaye da ta ji ya ciko mata yana barazanar saukowa. Tayi saurin ficewa daga ɗakin ba tareda ta furta komai ba.

Bayan ta fita Gwamna ya sauke ajiyar zuciya yana tunanin wannene cikin shawaran da zuciyarsa ke bashi zai yi.
Ya datse igiyar da ke tsakaninsu ne ko kuma ya cigaba da haƙuri da ita zuwa lokacin da Allah zai gyara tsakaninsu?...

Ta san zai iya fushi da ita amma ba ta san irin wannan matakin zai ɗauka ba. Ta san ko ba daɗe ko ba jima zai saketa saboda abinda tayi masa ya kai ya rabu da ita na har abada. Sai dai atleast ta ɗauka zai haƙura zuwa a warware matsalar da ke ƙasa tukunna.
Ta haÉ—a kayanta dana Sumayya ta kira Hansa'u tace ta fita mata da su waje.

"Hajiya ina za ki je?" Hansa'u ta tambaya data ga akwatunan.

"Zan koma É—aya gidan ne"

"Ai nan ma gida ne"

"Nan gidan Gwamnati ne Hansa'u, ba a zama a cikinsa na din din din"

Hansa'u na fita ta kira Sumayya tace idan ta bar makaranta ta wuce gidan Abba.

Da ta cewa Yaya Bello ya kaita gidan Abba, tambaya yai ko lafiya? tace masa lafiya.
"Ka san saura sati É—aya bikin Faty, zan je mu fara shirye shirye ne. Nima ta tsaya min lokacin bikina"

Da suka isa gida kuwa, aka shigo mata da akwatuna Inna Yaha ce a tsakar gida ta shiga tafa hannu tana salati wai auren da bai kai wata uku ba har an yi saki. Asiya bata kulata ba, ta shige É—akin mahaifiyarta da ke kwance saboda bata jin daÉ—i.

***

"Na ji ance jikar maiƙusumbi ta tafi. Ka saketa ne?"

Gwamna ya juyo ya kalleta sai kuma ya juyar da kai ya cigaba da duba ipad É—insa.

"Ba wai ina son zamanta bane amma ko zaka saketa, ka bari a gama rikicin zaɓe tukunna. Na gaji da jin ana ɓata maka suna a kanta"

Sai a lokacin ya buÉ—e baki yace " ki dinga sawa ranki ba a tabbata akan mulki. I might not win the election ko da babu maganar Lami"

"TabÉ—i!" ta saka dariya. "Wallahi shekara takwas É—in nan sai munyi ko za a mutu. Ai mutanen Congo ba su da wani Gwamna sai kai. Ko suna so ko ba sa so"

"Allah ke bada Mulki Bilkisu"

"Allah ma ya baka Saifuddeen, rantsarwa ya rage"

Gwamna ya miƙe saboda idan ya cigaba da wannan magana ransa zai ɓaci fiye da yadda yake ji yanzu...

Da dare Asiya sai juyi take ta kasa bacci. Ba wai tana son zama da Gwamna bane, ba wai ta fara sonsa bane. Amma tana ganin ba zata samu nitsuwa ba sai an kashe zancen nan gaba ɗaya. Maganganun da suka yi da Ubayd ya sa ta gane cewa akwai 90% cewa abinda ta ji ranan a office ɗin COS rabin hira ne. Ƙila Alhaji Sani Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna dan ɗansa ya hau. After all, idan Saifuddeen ya hau kamar shine akan mulkin.
Wani ɓangare na zuciyarta na tunanin ƙila Saifuddeen ya san da maganar za a kashe tsohon Gwamna amma bai iya yin komai ba, saboda ba shi da zaɓi.

Koma minene gaskiya, yanzu ta gane cewa al'amarin 'yan siyasa sai su. Idan ta samu ta wanke kanta a wajen Gwamna zata rabu da shi hankalinta kwance.

Sai dai kuma akwai wani ƙaramin gurbi a cikin zuciyarta da ya fara kwaɗaito mata rayuwa tareda Saifuddeen Kachallah. Ƙila tunanin da wannan gurbin yake ne ya hanata bacci, amma Asiya ba za ta taɓa yarda da hakan ba...
Chapter 6 · 0% Book details