← Book details Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 37

Sashe 35

Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"No no no no nooooo" CY ya fasa ihu a ƙaramin office ɗinsa bayan ya karanta hot news daya gani a waya.
Bai yi tsammanin haka ba, bai hasaso haka ba. This is bad, it's going to be very bad.

A ɓangaren Alhaji Sani ma hankalinsa ba ƙaramin tashi yai ba da wannan batu. Ya shiga kiraye-kirayen mutane. Babu abinda zai shigo jahar ba tareda izininsu ba, taya za a bawa jami'an NDLEA damar bincikan gidan Gwamna? balle har a arressting Matar Gwamna.

Yallaɓai na gama waya da Alhaji Sani Kachallah ya baro ɗakinsa a fusace dan tabbas abinda Bilkisu Kachallah ta ɓaro abu ne mai girma, it can backfired.
Matattakala uku ya taka ya dafe ƙirjinsa yana ƙoƙarin shaƙar numfashi da ƙyar, yana ƙara taku ɗaya ya suɓuto daga benin ya faɗo ƙasa tim, sandar hannunsa tayi tsalle ta faɗo gefensa.
Yallaɓai shi kaɗai ke zama a gida sai masu aiki, dan iyalensa kaf a ƙasar waje suke rayuwarsu, sai ƙarshen shekara suke kawo masa ziyara. Sai da yai kusan minti ishirin a wajen kafin wani mai aikinsa ya shigo ya ganshi kwance a wajen...

23

Kwalaben giya da ke gaban Clement Yohanna sun yi biyar kuma duka sai da ya shanye giyan dake cikinsu tas. Shi ba ma'abocin shan giya bane, ko a baya yakan sha ne a lokutan da ake hidima balle yanzu ya kai kusan shekara ɗaya da rabi bai sa giya a baki ba tunda suka yi wani jayayya da Asiya akan shan giya illarsa da kuma rashin dacewarsa ga shi ma dake bin addinin kristanci. A yau kam dole ne ya sha giya saboda ya samu ya kauda damuwarsa koda na lokaci kaɗan ne. Sai dai, the more yake sha the more yake sake jin zafin kama Asiya da aka yi. Idan da zai iya bada rayuwarsa domin a saketa to zai bayar. Idan da zai iya zama a kurkuku a madadinta to da zai iya ƙarisa rayuwarsa a kurkuku just so that she could be free.

Yau kwana na uku kenan da aka garƙame Asiya Kachallah a kurkuku. Ranan litinin za'a fara sauraran ƙara amma har zuwa lokacin Asiya Kachallah remains in prison. Abinda ake tuhumarta da shi ya fi ƙarfin a bada bail ɗinta, infact a yadda ake ganin abinma koda an je gaban Alkali ba lalle ne ya granting bail ba har sai an gama binciken da ake yi.

CY ya mirgina gefe yana so ya jawo kwalbar giya ta huɗu wanda yake tunanin akwai saura aciki, sai dai yana taɓata da hannunsa na roba kwalbar ta gangara chan nesa da shi alamun kwankwataran babu komai acikinta.

Ya rufe idanunsa sannan ya buɗesu yana tunanin mace ɗaya ce ya sani da zata iya taimakon Asiya. Ya riga ya yanke alaƙa da ita kuma baya fatan neman taimako a wajenta har abada amma Asiya means everything to him ba zai bari damar da yake da shi na taimakonta ya kuɓuce masa ba. Tunda mijinta Gwamna ya cire hannunsa akan lamarin, yayi iƙirarin ba zai sa hannu a binciken da ake ba to shi zai yi koma minene dan ganin Asiya ta samu nasara.

CY ya tashi da ƙyar yana tangal-tangal har ya kai tsakiyar falonsa ya shiga neman wayarsa, ya shafe minti ishirin yana laluben wayar da ke maƙale a Aljihun wandonsa kafin ringing ɗin wayar ya ankarar da shi inda wayar take.
GrandMa ne a screen É—in amma saboda ba a hayyacinsa yake ba sai idanunsa suka nuna masa sunan Aseey kamar yadda ya saving lambar Asiya.

"Aseey are you ok?"

"Clement" Kakarsa ta kira sunansa da ɗan ƙarfi.

Maimakon ya amsa sai ya fashe mata da kuka. Kakarsa ta san yana son Asiya shiyasa ma yake ƙin maganar aure, shiyasa duk yarinyar da yai tarayya da ita basa jimawa saboda zuciyarsa tana ga Asiya.
Abinda ya faru ya sa ta kirashi, da ke ta je ƙauye bata ji labarin da wuri ba sai yau.

Sai da ta tabbatar ya dena kuka kafin ta kashe wayar tareda alƙawarin gobe zata dawo. Tsoronta ma kar wani abu ya sameshi kafin goben dan a maganar da suka yi ta fahimci cewa ba a hayyacinsa yake ba.

Bayan ya gama waya da Kakarsa sai ya danna wasu lambobi, bai saving lambar a wayarsa ba amma ya haddacesu ta yadda ko a mafarki aka tashe shi zai karanto su tsaf.

Dr Kimberly Yohannah Anderson ya kira, matar Secretary General na United Nations (UN) mahaifiya a gareshi, duk dama alaƙarsu ta ƙare tun ranan data haifeshi ta ajiyeshi ga iyayenta sannan ta gudu.
Mahaifiyar CY mai suna Godiya Kimberly Yohanna tanada shekara shabakwai ta yi cikin shege, lokacin tana aji shida a sakandare. Saurayin daya mata ciki ɗan ajinsu ne wanda ko a haife ta bashi watanni bakwai. Abin kunya ne gareta da kuma iyayenta, musamman da Daniel ya ƙaryata cikin lokacin da mahaifin Godiya Kimberly ya je gidansu da maganar.
Cikin na wata uku Godiya tayi ƙoƙarin zubar da shi amma hakan bai yiwu ba. Iyayenta musamman mahaifiyarta wacce take strong catholic ta nuna tsananin ɓacin ranta akan haka. Dan a wajenta da a kashe rai gara an haifi cikin, tunda dai ba laifin yaron bane, laifin iyayensa ne.

A haka Kimberly ta raini cikin har ta zana jarrabawarta na WAEC. Watanni biyu bayan ta zana jarrabawar ta haifi É—anta namiji wanda ya É—auko kamanninta. Ashe tun kafin ta haihu ta riga ta yankewa kanta abinda za ta yi. Dan haka kwana goma shauku da haihuwar ta gudu daga gida, ta bar yaron a wajen iyayenta.
Ba a san inda ta shiga ba, haka kuma iyayenta basu nemeta ba tunda sun fahimci guduwa tayi.

Godiya Kimberly ƙasar Ghana ta je wajen wata distant cousin na mahaifinta da ke zama a chan. A nan ta samu scholarship na karatu a ƙasar America. Ta yi karatu tun daga digiri na farko har na uku. Sai data zauna da ƙafafuwanta kafin ta waiwayi iyayenta da ɗanta, lokacin shekarunta biyar da auren wani baAmurke amma ba su taɓa haihuwa ba, kuma likitoci sun tabbatar mata da cewa da wuya idan ta sake haihuwa.
Ga mijinta Mark Anderson, rashin haihuwa ba matsala bace a wajensa dan bai damuba, ya taɓa haihuwa da matarsa ta farko amma yarinyar ta mutu tun bata fi shekara shida ba. A yanzu karensa Jerry yafi masa mahimmanci sama da samun ɗa ko 'ya na cikinsa. A wajen Kimberly wacce ta kasance 'yar Nigeria, 'yar Africa. Rashin haihuwa matsala ce a gareta musamman idan ta tuno ɗan data haifa a lokacin ƙuruciyarta tayi watsi da lamarinsa ko ya rayu ko bai rayu ba batada masaniya saboda shekaru ishirin cur bata waiwayi gida Nigeria ba, bata waiwayi iyaye ko 'yanuwanta ba.

Lokacin da ta zo Nigeria ta samu mahaifinta ya mutu, ƙaninta yayi aure da yaransa biyu sannan Clement ya zama saurayi, yana aji uku a Jami'a. Ɗan da ta yi yunƙurin kashe shi lokacin yana cikinta, ɗan da tunda ta tafi bata damu ta san wani hali yake ciki ba balle ta waiwayeshi...
Shekaru goma da suka biyo bayan zuwanta Nigeria ko kaɗan babu wani jituwa tsakaninta da Clement. Mahaifiyarta da ƙaninta sun yafe mata kuma sukan gaisa a waya lokaci zuwa lokaci amma banda Clement. Zuciyarsa, zurfin cikinsa da riƙo sun hanashi yafe mata balle har ya kirata da kalmar Uwa. Har yau babu wannan mu'amala ta uwa da ɗa tsakaninsu. Kimberly ta yi kukan ta yi magiyar amma Clement ya tsaya kan bakarsa cewa uwarsa ta mutu tun yana jinjiri bai da alaƙa da ita ko kaɗan. A koyaushe tana saka tsammanin Clement zai yafe mata har kuma ya dawo gareta sai dai kuma yana ƙara girma yana ƙara tsanarta ne, but she's ever hopeful zuwa lokacin da zuciyar ɗanta zai karkato gareta.

A yanzu data ɗauki kiran Clement kuma ta ji muryansa farin ciki ne ya mamayeta, in dai har saboda matar nan Asiya Clement zai kirata ya roƙeta alfarma to ba ƙaramin mahimmanci take da shi a rayuwarsa ba dan haka zata gayawa mijinta ayi duk abinda za ayi akan wannan maganar.

***

A Babban ofishin NDLEA na Abuja kuma cecekuce ne ya kaure tsakanin Agent Vic da kuma Agent Dahlia. Kowannensu gani yake abinda yake akan gaskiyarsa ce shiyasa babu wanda yaiwa waninsa uzuri.

"It could be a set-up, she's innocent"

"Oh please Vic! Kar ka kawo min maganar banza. Ba a rubuta criminal a goshin mutane balle ka ganesu. I will lead this investigation to the end and i will make sure she rots in jail"

Daga haka Agent Dahlia ta juya ta bar ofishin Vic a fusace.
Agent Vic ya sauke ajiyar zuciya, tabbas babu mai iya dakatar da Dahlia saboda ta kowanni fanni tana da kariya. Mahaifinta babban mutum ne a ƙasar sannan ita ɗin American citizen ce kuma babbar jami'a a hukumar DEA. Bai san dalilinta ba amma tunda ta zo she's being obsessed with tracking drug traffickers. Amma a wannan case ɗin gaskiya yana ganin akwai lauje cikin naɗi saboda a iya tunaninsa Asiya seems innocent.

***

Gwamna Saifuddeen Kachallah ya ƙurawa agogon da ke manne a bangon ɗakinsa ido yana bin kowanni tik tik tik da agogon ke yi.
Cikin kwanakin nan yadda yake ganin rana haka yake ganin dare. Maganin baccin daya ke sha ma duk a banza ne, dan sai dai jikinsa ya mutu amma baya iya yin barci.

Bai san dalilin daya sa yai wannan ɓaran-ɓaramar ba ranan da ya fito yai jawabi wa duniya gameda case ɗin Asiya ba.

*"Banida hannu cikin binciken NDLEA. Hukumar NDLEA tanada damar kama duk wanda ta samu da laifi, ko wanni irin matsayi gareshi. Ina tabbarwa jama'a cewa Gwamnatinmu ba zata yiwa kotu katsalandan ba, zamu bata goyon baya tayi duk wani bincike daya dace"*

Ba abinda yake son faɗa ba kenan, it was what Bilkisu wanted. Saboda haka ne ma tace lawyansa ba zai wakilci Asiya ba. Wani ɓangare na zuciyarsa na gaya masa cewa cire hannunsa a case ɗin Asiya was a betrayal amma kuma ya rasa ƙarfin aiwatar da wanni abu a kai.

***

Barrister Zaytoonah Tijjani Abubakar ta ja dogon numfashi sannan ta sake gwada sa'arta a wajen maigidanta wanda ya kasa-ya-tsare tun É—azu.
Chapter 35 · 0% Book details