Sashe 18
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kanta bugawa ne bai yi ba saboda yawan tunani. Ƙarshe da ta ga ba sarki sai Allah ta turawa Gwamna text akan tana son magana da shi idan ya dawo.
Mi tsohon nan yai wa Sumayya har ta ke iya maida mata magana?.
Sumayyan da take tsananin tausayinta saboda ta rasa uwarta tun tana 'yar shekara shida. Lokacin tana gidan Ale ita ce gatan yarinyar nan saboda ba uwarta a gidan kuma babu wanda ya jata jiki.
Tun tana jami'a take turawa Sumayya kuɗi saboda kada ta rasa abin buƙata. Kuɗin jarrabawarta na WAEC, JAMB dama registration da tayi da ta shiga Jami'a duk cikin aljihun Asiya ne.
Yarinyar da take ganin bayan Ummanta babu wanda take kusa da ita sama da ita.
Gwamna bai dawo ba sai ƙarfe goma saura na dare. Lokacin da Asiya ta ji shigowarsa gidan da sauri ta miƙe ta wuce sashensa. Baya falonsa dan haka ta wuce ɗaki dan maganar dake cinta bazata iya jiransa ba.
Rage kayan jikinsa yake lokacin data shigo, daga shi sai singlet da kuma wandon da yake shirin zugewa lokacin da Asiya ta shigo É—akin.
"Afuwan. Barin jira a falo"
Tayi saurin komawa da baya tana rufe ido kamar ta ga abinda bai dace ba.
Minti shashida sai ga Gwamna ya fito sanye da jallabiya ruwan ƙasa.
"Barka da dare" ya faÉ—a lokacin daya zauna.
"Ina so ka jawa Alhaji Abdullahi kunne ya fita harkan Sumayya. Mutumin nan ya haura hamsin amma ƙwaƙwalwar kifi gareshi. Can you imagine yana koyawa Sumayya iskanci? Ya manta yanada nashi 'ya'yan ne? Ɗan iskan mutum kawai, Wawa, Dabba, Bunsuru, Mahaukaci. Wallahi sai na sa an ɗaure shege idan bai fita harkan ƙanwata ba, Alade kawai, mtssw" ta ƙarisa maganar tana sauke numfashi.
Gwamna ya zuba mata ido, yadda ta harzuƙa tana masa faɗa kaman shine Alhaji Abdullahin.
"Miya faru?" Ya tambaya daya ga Asiya ta É—an nitsu.
" wai soyayya su ke da Sumayya. And there exchanging nude pics"
Gwamna ya zaro ido waje. Ya san halin abokinsa da shegen neman mata wanda hakanne ma ya sa ba sa taɓa zama ba su yi faɗa ba. Sai dai bai ɗauka abin yayi ƙamari har haka ba.
"Mi Abdullahi yake nema ne?" Gwamna ya faÉ—a a ransa. Matansa uku, ta huÉ—un sun rabu shekara É—aya da rabi daya wuce. Mata shida ya aura a rayuwarsa, ya rabu da uku yana tareda uku yanzu.
"Ka san saboda na yiwa Sumayya faÉ—a yarinyar nan ta shiga gayamin maganganu marasa daÉ—in ji. Ka faÉ—a masa ya fita harkanta ko kuma na yi maganin Shege"
Bai ji haushin zagin Alhaji Abdullahi da take ba saboda shi ya jawa kansa. In fact ya ji daÉ—in yadda ta same shi da maganar kai tsaye ba tareda tayi wani abu a bayan idonsa ba.
"Ki bita a hankali Asya"
"Da É—in da zafi nake binta?" Ta faÉ—a tana kumbura baki.
"Ina nufin idan kina so ta fahimce ki sai kin bita a hankali. She's in a phase da take jin kanta dai dai da ke, idan kika bita da faɗa ba zata taɓa ganewa ba sai dai ma ta fara gaba da ke. Zan mata magana amma zai kai gobe saboda a gajiye nake yanzu"
Asiya ta sassauta murya tace " ya jiki? Kwanaki Mahirah tace baka da lafiya"
"Kin damu da ni ne?" Ya tambaya yana tsura mata idanu.
Asiya tayi narai narai da ido kaman za ta yi kuka. Ba dai shima gaya mata magana zai yi ba kamar yadda Sumayya ta chaka mata magana É—azu da rana.
"Ba ruwanki da Abdullahi, zan masa magana da kaina. Akwai wani abu ko na shiga ciki?"
"Babu komai"
Sai da ta miƙe ta fara tafiya sai kuma ta dawo tace " a kawo maka abinci ne?"
"Kin damu dani ne?" Ya maimaita tambayarsa ta É—azu.
"To... to sai da safe"
"Allah ya baki haƙuri Asya. A taimaka min da ruwan shayi Dan Allah"
Asiya ta fita da sauri ba tareda ta sake cewa komai ba.
Ita da kanta ta shiga kitchen ta haÉ—o masa shayin ta kawo.
Tana ajiye masa ta juya da sauri ta bar falon saboda yadda ƙirjinta ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi.
Gwamna yai murmushi. Yau É—aya dai sun yi magana ta nitsuwa tsakaninsu...
***
Washegari Sumayya ko leƙa Asiya ba ta yi ba ta kaɗa kai ta wuce makaranta. Cikin ranta Asiya kishi take da ita dan tana tarayya da Alhaji Abdullahi wanda shima wani hamshaƙin ne a jahar Congo kuma jinin Kachallah duk da ma ta ɓangaren mace ya zo.
Asiya ta haɗa breakfast na musamman ta kai falon Gwamna ta jera komai a ƙaramin dining area dake haɗe da falon. Bata san ina Bilkisu ta je ba, amma ta lura kaman tunda ta fita jiya da safe bata dawo gidan ba.
Lokacin da Gwamna ya fito. Asiya ta zubawa Junior abinci yana ci ita kuma tana zaune tana danna waya.
Bai yi niyyar tsayawa ya karya ba, amma ba zai bari wannan damar ta wuce shi ba. Ɗan chanjin daya gani tattare da Asiya jiya ya bashi ƙwarin gwiwa.
Yana zama Asiya ta shiga serving É—insa. Data gama ya mata godiya.
"Ina Sumayya?"
"Ban ma san lokacin da ta fita ba" Asiya ta faÉ—a cike da mamakin wannan chanji na bai É—aya da Sumayya tayi duk saboda namiji.
"Kar ki damu a hankali za ta gane gaskiya. Ki dinga mata addu'a"
Asiya ta gyaÉ—a kai sannan ta fara cin abinci duk ranta babu daÉ—i...
Ƙarfe shaɗaya na safe Asiya ta wuce chan gidan Gwamna, wasu kayanta zata ɗauko tunda dama bata zo da kaya dayawa nan gidan Gwamnati ba. Da ace ba abinda ya haɗata da Sumayya da ita zata aika ta ɗauko mata kayan idan ta taso daga school to amma...
Sun gaisa da Uwani sannan ta wuce sashenta dan ta haÉ—a kayan.
Minti arba'in da biyar ta ɗauka tana zaɓan kayan da zata ɗauka da wanda zata bari. Ƙarshe akwatuna huɗu ta cika da kaya. Ta kira Uwani tace ta kai mata su mota.
Har zata fita ta lura da Qur'aninta da ke kan dressing mirror. Tanada wani a chan gidan, amma kuma tafi jin daɗin karatu da wannan saboda da shi ta ƙarisa haddarta, ta saba da shi, dan sama da shekaru goma kenan tana amfani da shi.
Cikin handbag É—inta ta saka Qur'anin sannan ta fita.
Lokacin da Asiya ta isa gida ta samu Bilkisu ta dawo tana meeting da wasu mata. Sama sama ta amsa gaisuwan matan ta wuce É—akinta.
Wasa wasa bata ga Sumayya ba har aka yi Isha, hakan ya sa ta kira Gwamna. Lokacin data kira yana tareda Alhaji Abdullahi yana masa faÉ—a.
"Wacece kuma Attaruhu?" Alhaji Abdullahi ya tambaya da shaƙiyanci. Gwamna bai kulashi ba sai ya swiping ya amsa kiran da sallama.
"Sumayya bata dawo gida ba. Ka kira Aladen nan ka tambayeshi ina ya kai min ƙanwata"
"Ki kwantar da hankalinki, za ta dawo"
Yana kashe wayar ya dubi Alhaji Abdullahi fiska a murtuke...
Sumayya bata shigo gidan ba sai ƙarfe tara da rabi na dare, dake Asiya tace idan ta shigo a mata magana tana shigowa Safiya 'yar aiki ta zo ta sanar da ita.
"Ina kika je?"
"Lectures" Sumayya ta faÉ—a ko kallon Asiya ba ta yi ba.
"Lectures har ƙarfe goma na dare?"
"Na tsaya a hostel nayi assignment ne"
Asiya ta kai mata mari tace " kar ki raina min hankali. Yaushe kika fara assignment a hostel"
"Idan gorin gida zaki min sai na koma inda na fito"
"Kafin ki koma kuwa sai na gyara miki zama a gidan nan..."
12
"Subhanallah!" Gwamna Saifuddeen ya furta ganin Asiya na kaiwa Sumayya duka. Ya sa hannu ya jawota yana faÉ—in "haba Asya, miye hakan?"
Kirjinta na bugawa da ƙarfi ta fara magana "har zata ce min ina mata gorin gida, how dare she talk to me that way. Ka barni na cire mata duk wani matsamatsen dake kanta, saboda nawa jujun yafi nata" ta ƙarisa maganar tana shirin kaiwa Sumayya wani dukan.
Gwamna ya jawota jikinsa yana faÉ—in "ya isa haka, mu je É—aki" akwai wani sinadari na saka nitsuwa a maganarsa dan kuwa yana maganar wani sanyi ya ratsata ta kasa yi masa musu haka kuma bata janye jikinta daga nasa ba har ya mata jagora suka koma nata É—akin.
Zaunar da ita yai akan gado yace " ba kya jin magana Asya. Nace miki zan mata magana ko"
"Ban san inda taje ba. Mi na san tsinannan tsohon nan yake mata. Idan wani abu ya sameta ni za a zaga. I've being taking care of her since she was a baby. Mahaifiyarta bata da dangi saboda cirani sukazo da iyayenta Ale ya aurota. After her death babu wanda ya san danginta saboda sun bar gari. Bata da dangin Uwa sai mu, kuma gidan mu anyi yawar da sai dai ka ci kanka. I took care of her, na zama mata uwa, na jawota jikina amma yanzu har tana da bakin gaya min maganar banza saboda wani Bunsuru"
"Idan kin daketa hakan zai sa ta gane abinda kike faÉ—a mata ne?"
"I will beat the hell out of her, har sai ta fara gudun maza"
"Learn to control your anger Asya. Learn to listen and use your brain instead of your heart. Sumayya bata haɗu da Abdullahi ba yau, he was out of town, yana shigowa gari na je na sameshi a gida. Ƙila hostel ta je ko kuma ta je chan gidan ku"
" Ko hostel zata je ba zata kirani ta sanar dani yau ba zata dawo da wuri ba, ta faÉ—i dalili"
"Asya!"
Yadda ya kira sunan da kuma hannunta daya riƙe yai daidai da wani halbawa da zuciyarta yai wanda sai da cikinta ya amsa.
"Ki rage fushi Dan Allah"
Asiya tayi shiru tana jan hanci tana ƙoƙarin danne kukanta amma ina abin ya gagara. Kukan dake cikinta yana dayawa. Kukan gazawarta, kukan yawan fushinta da kowa ke mata faɗa akai, kukan maganganun Sumayya, kukan yanzu bata da mahaifiyar da zata samu ta yiwa ƙorafin matsalarta, kukan ta kasa fuskantar rayuwan aurenta ta karɓi ƙaddararta, kukan kukan...