Sashe 31
Matar Gwamna Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan fitan Sumayya daga ɗaki Asiya ta maida hankalinta ga zane da take yi a jikin baƙin masking tape wanda za a ɗaurawa wata Amarya gobe. Idan har babu aikin da za ta yi a gidan gara ta koma sana'arta na da. Akwai ma wani offer da aka bata na aiki wanda article ne zata dinga rubutawa amma bata karɓa ba saboda wanda ya ajiyeta a gidan bai saurareta ba balle ta masa maganar.
Kaman daga sama ta ji muryan Junior yana ƙwala mata kira, tana miƙewa ya shigo ɗakin da gudu yana dariya.
"Juni Juni kai ne ka girma haka?"
"I miss you Anty" ya faɗa yana ƙara shigewa jikinta. Sallamar Mahira da Nana yasa ta ɗaga kai da sauri har lokacin fiskarta ɗauke da murmushi. Ba ƙaramin daɗin ganinsu ta yi ba.
Haka suka wuni tare suna hira, ƙarshe dukkansu suka shiga kitchen suka tayata girki. Ma'aikatan gidan suka ja gefe suna mamakin yadda yaran suka sake da Asiya. Lokacin da Bilkisu Kachallah ke zaune a gidan bata taɓa shigowa kitchen dan ta dafa wani abu ba balle har ta shigo da yaran su tayata aiki. Abin gwanin sha'awa dan har Junior sai da aka bashi aikin mummula meatballs kafin aka zo aka soya su.
Lokacin da aka haÉ—u ana cin abinci suka dinga dariyan shiriritan Jummai, magana É—aya tayi sai kaga sun kwashe da dariya wai hausanta abin dariya.
Zuwan yaran yasa Asiya ta samu walwala ta sake sosai kamar bata da wata damuwa a ranta. Basu bar gidan ba sai dare bayan sun yi sallar Isha. Shi Junior ya so su kwana ne ma amma sanin halin Mommynsu yasa dole suka tafi.
***
Washegari da safe misalin ƙarfe tara sai ga wasu mata biyu sun zo wajen Asiya. Bata san su ba amma yanayin shigarsu ya nuna mata cewa su ɗin manyan mata ne.
Bayan sun gaisa sai suka fara wani batu daya ɗaurewa Asiya kai. Wai su daga ƙungiyan mata suke, suna so ta shiga ƙungiyarsu saboda su bata kariya daga Bilkisu Kachallah dama duk wani wanda zai so takata.
"Ban gane zaku bani kariya ba?"
Baƙar cikinsu ta sassauta murya tace "wai baki da masaniyar cewa an ajiye ki a nan ne saboda baki da wani amfani? Ko ba kya jin abinda ake faɗa a gari?"
Ganin idon Asiya ya buÉ—e na mamaki sai ta cigaba " Bilkisu Kachallah ke juya Gwamna"
Da ta lura maganar yai wa Asiya shigar ba zata sai ta cigaba. "Mun san ba haka ta zauna ba shiyasa muke so ki shigo cikinmu mu baki kariya. Idan kina tare da mu babu abinda zai gagareki a jahar nan domin..."
"Idan har na fahimce ku so kike na shiga ƙungiyar ku ku bani kariya daga Bilkisu Kachallah ko?"
ÆŠaya matar, fara 'yar duma-duma ta ce "bayan kariya, zaki samu ki juya mijinki yadda kike so. Muna tareda matan Gwamnoni da kuma..."
"Ban katse ki ba Hajiya, amma a iya karatuna Allah kaɗai ke kare mutum. Bana tunanin akwai waninsa da zai iya kareni daga wani abu ko da kuwa tuntuɓene. Sannan ni ban san mi ake nufi da juya miji ba, shin maida shi muciyar tuwo za a yi ne ata juya shi ko ya abin yake?"
Matan suka kalli juna. Sun lura raina musu hankali Asiya ke son yi.
Sai kuma farar matar tace "ki zauna kiyi shawara da zuciyarki kafin zaman gidan nan yafi ƙarfin ki"
Sai da suka miƙe sannan suka ajiye mata card ɗinsu wai ta kira su idan tayi shawara.
Asiya ta bi bayansu da kallo, yadda suke iya juya bayansu ma sai Allah dan ba ƙaramin mazauna garesu ba, irin matannane da zaka gani a bikin yarabawa suna chanja ɗaurin zani duk bayan minti ɗaya.
"Allah ka raba ni da sharrin mutanen nan" Asiya ta faÉ—a bayan sun fice daga falon.
Ta jima tana alhinin wanɗannan baƙi wanda ko sunansu basu faɗa mata ba har suka tafi, duk dama dai wani abu da suka faɗa ya tsaya mata a rai, wato batun Bilkisu da aka ce tana juya Gwamna. Queen Bee ta mata maganar amma ta shashantar da batun saboda ba ta son zargin abinda bata da tabbas a kai. Sai dai kuma a yanzu da waɗannan mata suka yi maganar sai take ganin ƙila akwai ƙanshin gaskiya a batunsu idan ba haka ba taya Gwamna zai juya mata baya lokaci guda haka, miyasa zai guje ta?. Anya kuwa babu wani abu a ƙasa?
Tana cikin wannan saƙa da warwara Halima Kachallah ta yi sallama a falonta. Sai data ganta ma ta tuna da cewa ashe yau suka yi zata mata ƙunshi.
"Kin san Allah Anty Halima ko yanka cellotape É—in ki banyi ba"
"Ai kuwa yau za a yi ta a gidan nan. Ko sama da ƙasa zasu haɗu ba zan bar gidan nan ba sai an mini lalle, kuma irin design ɗin dana zaɓa za ayi"
"Ai kuwa sai dai ki kwana dan maigidan ya hana"
"Taɓ! Ai ko Anty Bilkisu ce ta hana sai anyi, balle kuma na san Yayana ba shi da matsala"
Asiya tayi dariya sannan kuma suka shiga gaisawa. Bayan sun gaisa ta tambayi jikin Dadda.
Minti shabiyar da zuwan Halima Asiya ta kira Jummai ta bata saƙo ta kaiwa Yaya Bello a waje zai kaiwa Queen Bee a chan shagonsu. Minti biyu da fitar ta ta dawo da gudu tana haki wai Aljanu sun taɓa Yaya Bello. Asiya na jin haka ta san ya sha wani abu kenan.
"Da gaske Anty Shahidah Aljanu sun sace masa ƙafa, ga ƙafa a jikinsa amma sai neman ƙafafunsa yake, inaga sun tafi da nashi ne sun saka masa nasu"
Takaici ya kama Asiya, yau gashi ƙanwar bayansu ce take tsokalar Yaya Bello wanda da ya yi aure da wuri kaman sauran 'yanuwansa da zai haifi 'ya kamar Jummai.
"Anty Shahidah ba za ki je ki masa addu'a ba?"
"Ki bawa Inuwa Driver saƙon zai kai min"
"Anty Asiya dama maza na samun Aljanu ne?" Halima ta faÉ—a bayan tayi dariyar abinda Jummai ta faÉ—a.
"Ba wani Aljanu fa, he's jus high ne"
"Dan Allah? Barin je na gan shi"
Halima da Jummai suka fice daga falon da sauri. Asiya kan ta san ranta ne kawai zai ɓaci idan ta fita shiyasa tayi zamanta.
Ai kuwa sun fi minti goma kafin suka dawo, Halima Kachallah har da ƙwalla a ido tsabar dariya.
"Kai Anty Asiya kin missing show Wallahi. Kinga yadda yake kuka wai an sace masa ƙafa?"
"Sai dai Allah ya shirya min shi. Yaya Bello case ne ai. Akwai wani lokaci shekarun baya tun ina gida Ale ya tara buhuhhunan wake da masara a store zuwa lokacin da zai yi tsada sai ya fitar, kawai sai Yaya Bello ya je ya buɗe store ya kira mutane yana raba musu wake da masara wai an masa wahayi ya fitar da zakkah. Ale baya nan ya tafi kasuwar ƙauye aka kira aka sanar da shi, tsabar ruɗewa gudawa ya fara har suka shigo gari, kafin ya iso an riga an gama raba kaya, store ya koma wayam babu komai. Da Ale ya fara rashin lafiya saboda asaran da yai an ɗauka ba zai yi rai ba"
Halima tsabar dariya zama ta yi daɓas a ƙasa tana riƙe ciki tana dariya, tsabar dariyan ma sai da wuyanta ya riƙe.
Halima Kachallah bata bar gidan ba sai ƙarfe tara na dare, kafin lokacin Yaya Bello ya warware sarai kaman ba shi yake ta hauka da rana ba. Tsabar rigima Halima ta ce ta gaji wai Asiya ta sa Yaya Bello ya kaita gida ba zata iya tuƙi ba.
A cikin motar kuwa ta dinga tsokalar Yaya Bello tana masa dariya tun yana sharewa har abin ya fara bashi haushi, dariya ya ƙi ci ya ƙi cinyewa akan abu ɗaya.
Lokacin daya sauketa a ƙofar sashensu ta kalleshi tace " idan gobe an sace maka ƙafa ko hannu ka kira ni zan haɗaka da cousin ɗina lawyer ne zai ƙwato maka haƙƙinka"
Ya bi wayar da ta miƙa masa da kallo. Ya sani so ta ke ya sa mata numbarsa amma abu biyu ya ɗaure masa kai. Na farko tunanin matar aure ya ke mata, na biyu kuma shi bai iya amfani da babbar waya ba.
Ganin ya ƙi amsar wayar sai ta ce " ka bani wayarka na sa maka number na"
Ganin ta dage sai ya fito da ƙaramar wayarsa daga aljihu ya miƙa mata ta amsa ta sa numbarta ta flashing numbarta.
Da ya isa gida ko fitowa daga mota bai yi ba ya ga shigowar kira. Yana ɗauka ya ji ance " ka taɓa ƙafafuwanka suna nan ko an sace?"
Ya É—an haÉ—e rai kamar tana ganinsa yace " suna nan"
Halima ta kwashe da dariya, sai da ta yi mai isarta kafin tace "Sai da safe Yayanmu"
Ƙarfe huɗun Asuba Halima Kachallah ta kira Asiya ta sanar da ita rasuwan Dadda. Duk da tsohuwar ta ja miya amma hakan bai hana Asiya jin mutuwar a jikinta ba.
Da safe ƙarfe shida da rabi a Kachallah house ya mata. Ƙarfe tara na safe za ayi jana'izarta amma tun ƙarfe bakwai gidan ya fara cika.
Mutuwar Dadda ya girgiza Gwamna Saifuddeen Kachallah. Dadda ita Kaka ce sannan Uwa a gareshi, duk wani tarbiyyan da zai yi tinƙaho da shi to kaso saba'in ciki ya samo daga Hajiya Dadda ne.
***
Ranan da Dadda ta rasu mashahurin marubucin nan KaSaSa ya rubuta waƙoƙi guda bakwai saboda tunawa da Hajiya Khadijah Kachallah. Asiya bata samu karanta waƙoƙin ba sai bayan kwanaki huɗu da rasuwan. Wani abu ne ya ɗaure mata kai bayan ta karanta waƙoƙin, kamar akwai alaƙar jini tsakanin marubucin da kuma Hajiya Dadda.
Idan har haka ne to KaSaSa zai iya zamowa É—aya daga cikin jikokin Dadda.
Ba daɗi ta kira Halima Kachallah ta shiga yi mata tambayar ƙwaƙwafi kwanaki kaɗan bayan rasuwan kakarta da take matuƙar so. Dan haka sai ta bar zancen a ranta zuwa wani lokaci...
21
Not edited.
A ofishin NDLEA na Abuja kuwa Agent Maryam Dahlia Aliyu ce ke ta tiriri saboda wani batu daya taso ake son rufewa.